← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 162

Sashe 144

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida ta ida shiryawa tsaf kafin ta fito tana k’arema sashen kallo, wani k’ofar glass ta gani daga can center yana bud’e gaba d’aya, lokaci guda taji tabi wanann k’ofar taga sararin waje... Cikin taku mai cikeda natsuwa ta nufi wannan k’ofar... Tai tsaye tana kallon frames d’in dake aje wajen jeri jeri wanda Mahmood ya zana... Dangin zanen k’oramu bishiyoyi da dai abubuwa masu ban sha’awa had’ida jefa natsuwa cikin zuciya idan kana dubansu...

Taci gaba da takowa a hankali tana mai kallon zanen, babu wanda yafi tafiya da tinaninta kaman wani zane da yakeda yanayi da gidan sarauta.. Ta isa jikin zanen tana tuna Taswiran da ya zamto mabud’in sirrin su Giwa a garesu... Ta jima sosai tana duban zanen kafin Ta sinkayo muryar Zahra ta shigo a guje Ta rungumeta tana fad’in “Tia, good morning, I’m glad I found you here..! I told Aunty Umaima you and Paa loves each other so much..!”Tai maganar suna rungume da juna

Muhibbah ta murmusa kad’an kana ta janyo hannun Zahra suka zauna saman wasu k’anan kujeru da aka k’awata wajen dasu..
Zahra bata daina murmushi ba take duban Muhibbar lokaci guda take ci gaba da furta “Zanfi kowa jin dad’I idan kika zama matar Paa d’ina.. Coz I know he loves you.. So much..!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta...

Ita kuwa Muhibbar har lokacin bata iya tanka Zahra ba saima k’urama beautiful art works d’in Mahmood idanu da tai...

Zahra ta dubeta taga abinda idanunta Ke duba.. A hankali ta murmusa kana taci gaba da furta “You know, Paa loves to paint.. Especially when he’s in a good mood.. Ta haka nida Maama muke gane idan wani abu na damunsa back then in Spain.. And ever since Maama passed away ya daina painting.. Har sanda muka dawo k’asar nan... Sai bayan kin shigo rayuwarmu Paa yaci gaba da painting.. Tia inada tabbacin kece sanadi, you’re the one who inspired him again... Please don’t leave my Paa shid’in masoyinki ne da gaske..!” Ta k’arashe idanunta na rau rau...

Cikin sanyin jiki Muhibbah ta kamo hannunta guda tace “Zahra don’t you think this is something your Paa and I should decide..”

Cikin rawar murya Zahra ta katseta da fad’in “I know I shouldn’t interfere, but my Paa has been through a lot... Baki tunanin ya cancanci Farin ciki... Please don’t break his heart..!”

Muhibbah ta kuma kamo hannayenta tace “Zahra kalleni..!”

Zahra ta d’ago idanunta masu d’igan hawaye tana duban Muhibbah wacce itama tuni k’walla sun ciko idanunta, lokaci guda taci gaba da furta “ Your Paa doesn’t love me, bai tab’a fad’in haka ba.. Aurenmu K’addara ne..!”

Cikin sanyin jiki Zahra tace “But I know he does, ta yuwu bai furta ba.. But as they say actions speak louder than words...”

Murmusawa kad’an Muhibbah tai tana mai duban yarinyar kana ta rik’e hannunta cikin nata, saida ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali taci gaba da fad’in “There are some points in life da zaka zamto baka da zab’i... Sadaukarwa shine zai zamto zab’inka... You might be too young to understand all that I’m telling you now, but banida zab’in da ya wuce na fad’a miki.. Inada tabbacin akwai lokacinda zaki fahimci abinda nake nufi...!”

Zahra na hawaye take girgiza kai alamun k’in amincewa lokaci guda take furta “No Tia... Maybe har yanzu bansan mecece soyayya da kamanninta ba.. but We both know that you and Paa loves each other.. You can’t deny you love him... Maiyasa zakiyi sadaukarwar da zai cutar dake...?”

Muhibbah na hawaye take furta “Bazaki tab’a fahimta ba Zahra duk yanda zan so na fahimtar dake...!”

Zahra ta girgiza kai tace “But you’re married to my Paa now... You’re his wife, you’re not going anywhere right..?!” Cikin tsananin sanyin jiki tai maganar

Muhibbah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tace “Only for three days Zahra.. After three days shikenan your Paa and I will be separated... Nasan bai kamata na sanar dake wanann ba, but banida zab’i, bazaki k’yaleni da tambayoyi ba... Zahra nida mahaifinki munyi yarjejeniya.. Our marriage will only last for three days...!” Ta k’arashe cikin rawar murya..

Da tsananin mamaki Zahra ke dubanta.. Lokaci guda take girgiza kai cikin rashin yarda da abinda takeji... Muhibbah ta jinjina kai a hankali alamun tabbatarwa tace “Promise me bazaki sanar da kowa abinda na sanar dake ba.. Especially Ummi..!”

Dubanta tayi da idanunta masu zuban ruwa ba tareda ta iya furta koda kalma ba.. Muhibbah Ta kuma kamo hannunta with a straight face tace “Promise me Zahra..!” Ta kuma fad’i tana d’an jijjiga Zahran

A hankali Zahra ta shiga jinjina kai idanunta na kuma zuban ruwa take furta “As you wish your Highness..!”

Muhibbah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana mai k’ok’arin share hawayen da suka wanke fuskar Zahran... Saidai ga tsananin mamakinta ji tayi Zahra ta saka hannu ta janye hannun Muhibbar daga fuskarta.. Lokaci guda take furta “If you may excuse me Rankidad’e..!” Ta k’arashe da alamun risnawa, lokaci guda ta mik’e ta fice cikin sauri kaman zata kifa k’asa

Muhibbah tabi bayanta da kallo har ta b’ace mata hawaye naci gaba da gangaro mata, kifa kanta tayi tana kuka da gaske lokaci guda tana tambayar kanta Maiyasa rayuwa yake zuwa haka, daga wannan k’alubalen sai wancan.. Shin ta yaya zata fahimtar da Zhara cewa dole ce ta sakata rabuwa da mahaifinta.. Ta yaya zata fahimtar da ita sadaukarwa take wa mutanen da suka sadaukar da abubuwa da dama sabida ita.. Shin meye laifinta a nan..? Ta kuma fashewa da sabon kuka...

Haka yinin ranan tayisa jikinta babu K’warai, sannan bata sami kiran Rankaidad’e daga wajen Jakadiya ba dan da alama yau d’in shima ya zama busy ne da maganan nad’in sarautar sa.. Yini zubur yayi a cikin Fadarsa suna tattauna al’amaran da ya shafi cikin gidan da manyan masu sarauta na gargajiya.. Sallah ce kawai yake fitar dasu sai ko lokacin cin abinci... Tin Ja’afar yana ganin abin bak’on Al’amari a garesa har dai ya saki jiki... Neman duniya anyi ba’a san yanda Waziri yake ba, Ja’afar ya hani Ubandoma da fad’in yanda suka b’oye Waziri a cewar J’afar d’in Waziri bazaici banza ba... Ko kullesa a bak’in fursuna da sukayi suka tsoratar dashi duk dare ya ishesa horo.. Ta tabbata dai ba’a ga Waziri ba an nemesa sama da k’asa an rasa, can iyalansa ma nemansa suke.. Daga wanda suka damu da b’acewar nasa sai wanda damuwarsu kawai ya bayyana ya amsa masu laifukan da ake tuhumarsa da bakinsa ne musamman matansa da yaci amanarsu da Giwa harda d’ah tsakaninsu...
A b’angaren Fu’ad ma duk wanann kwamacala da abubuwan ban mamaki da na al’ajabi harma da tausayi da suka faru cikin Masarauta baida labari da shike yana killace ne can a asibitin masu tab’in hankali...

**

BAUCHI

Tinda Ansar ya dawo gida baya kula kowa bai shiga hark’ar kowa, babu yanda Mommy batayi ba yayi hak’uri da al’amarin Ubangiji suci gaba da addu’a Allah ya bayyana masu Muhibbah shi kuma ya d’auki matarsa su tare can gidansu amma Ansar yak’i aiwatar da hakan... Sosai Mommy ta damu da yanayin da tilon d’an nata ke ciki, uwa Uba ga tausayin Hamida da takeji wacce sunan aure kawai tayi amma tinda tayi auren babu komai cikinsa sai tashin hankali.. Tabbas auren dole bashida wani alfanu, gashi ta gani akan d’anta... Kyakkyawar magana bai tab’a shiga tsakaninsa da Hamidar ba tinda ya dawo Sannan ko Asibiti ya daina zuwa saima tsananin fad’a fafa da ya soma, d’abi’arda sam ba nasa bane a baya yanzu kuwa ya ara ya yafa.. Daidai da iya Larai bai ragar mata ba, ‘yar wasan da suke a baya yanzu bai d’auka.. Gaba d’aya ya koma very violent kaman ba shi ba... Iya Larai kaw saidai taceda Mommy aita had’a masa da addu’a har Allah ya sassauta masa...

Yana zaune cikin d’aki ya bada hankali ma wayarsa lokaci zuwa lokaci yana sakin tsuka yana fuzar da fuci.. Hamida dake mak’ale jikin k’ofa rik’eda jug da cup tana San shigowa amma batasan ya zasu kwashe da mijin nata ba.. Tai k’arfin halin yin sallama ta shigo..

Dukda sanin darajar sallama bai iya amsa mata ba sabida tsananin tururi da zuciyarsa keyi... Tasan bazai mata magana ba koda zata kwana tana tsaye wajen.. Ta duk’a a hankali ta shiga tsiyaya masa juice d’in dake cikin jug d’in a cup d’in a hankali..

Jiki a matuk’ar sanyaye ta mik’a masa tana fad’in “Yaya kasha wannan, na kula yinin yau d’in bakaci komai ba..!”

Wani duban da ya watsa mata ya sanyata had’iye sauran kalaman nata..
Ta sadda kanta a k’asa zuciyarta na kuma harbawa..

“Ke ni sa’anki ne..? idan baki fice min a d’aki ba kinji na rantse saina b’abb’allaki Kinga sai akai ma Baffah k’asusuwanki ya had’a ya sayar ya k’ara jari kan wanda ya amsa da sunan kud’in auren Muhibbah.. Munafukar banza tashi ki fita min a nan.!”

Hameedah ta tintsire da wane irin kuka mai k’arfi ta mik’e zata fice a guje.. Ya katseta da fad’in “Dawo Ki tattari tsiyarki dan ban San mai aka baki akace ki zuba min ba.. Tattara and get the hell outta my room..!” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye had’ida nuna mata k’ofa...

Cikin kuka Hameedah ta tattari jug da cup d’inta Ta fice... Tana ficewa yaja dogon tsaki had’ida furta “Munafuka kawai..!” ya mai maida hankalinsa kacaukam kan wayarsa... Tin safe dialing wayar Raheemah yake bata d’agawa.. Cikin sa’a yaji ta d’aga... Da masifa ta taresa da fad’in “Wai kai bakasan uzuri bane a rayuwarka.. Sau nawa zan ce maka mijina baida lafiya ina asibti taredashi kan mai zaka bi duk ka d’aga min hankali..?!”

Ansar ya katseta da fad’in “And do you think I give a damn about that Bastard..?! Toh ya mutu ma mana for all I care..”

Raheemah ta katsesa da fad’in “Bana son tashanci ka gane.. Na fad’a maka matarka will soon come back to you.. I’ve already poisoned her mind... Na tabbata bayan abubuwan dana sanar da ita bazata bari ayi nad’in sarautar Mahmood da aurensa akanta ba.. So just chill lover boy..!”
Chapter 144 · 0% Book details