← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 162

Sashe 107

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai ya fad’a duniyar tunani, kenan Ta kuma tabbata Muhibbah tanada agenda d’inta cikin Masarautar nan... Why’s she connected to almost everything that’s been happening...? Farko rayuwarsa da Zahra, Raheema da Yazeed.. Taswiran da Baba Wambai ya basa wanda ya tsinci makamancinsa hannunta...Yanzu kuma harda Jakadiya da Jamal..? And if Jakadiya is somehow involved Toh Giwa ma might also be involved tinda yasan matsayin Jakadiya wajen Giwa... Kuma idan hakan Ta kasance zai iya yuwa tasan wani abu gameda ciwon Fu’ad tinda zuwansu asibiti shida Turaki nurse guda ya tabbatar masu cewa matar data shigo da Zahra Ta jima sosai cikin d’akin Fu’ad tana dubasa...Who are you Muhibbah...?! Mai kika shigo yi cikin Masarautar nan..?! Maiyasa kike neman ki tarwatsa ahalinmu..Duk abubuwan da suka faru, everything is pointing directly to you ne... What exactly do want from our family..?!

Har Zahra Ta fice bai fahimci Ta fice ba, sosai yai nisa a duniyar tunani... Idan Muhibbah tanada alak’a da duk abubuwan dake faruwa cikin Masarautar Toh ya zama dole yayi taka tsan tsan dan da alama bata shigo Masarautar ba saida Ta shirya... Babu wanda zai iya tunk’aran masarauta mai girma irin nasu yanda tayi ba tareda shiri ba... Shi mamaki ma abin ya soma basa... Sauri sauri ya haura sama ya kunna na’uran computer d’in yana duban abinda take a daidai lokacin...

Kuangin ne suka shigo nata da abin kari... Ta d’auki fork bayan sun fice tana k’ok’arin bud’e lock d’in k’ofa dashi...
Yayi K’uri yana dubanta yanda take dage k’arfinta gaba d’aya wajen ganin Ta bud’e k’ofar...

Cikin zuciyarta take furta “I really need to escape kafin Giwa ko d’aya daga cikin azzaluman yaranta su cimmani... Nasan mutanen da Abbah yace na taimaka masu suna b’oye cikin Masarautar nan... I need to escape kafin su cimmani..!” Ta k’arashe tana mai kuma dage k’arfinta, saidai abinka da k’ofa mai aminci ko gizau bai ba... Saima karyewa da cokalin yayi... Cikeda takaici tayi jifa da cokalin ta koma cikin d’akin ta zauna dirshan tana kuka mai tsuma zuciya...

**

Huci kurum Jamal yake fitarwa yana mai furta “I knew it.. Since from the beginning ban yarda da yarinyar nan ba Maami... But tinda ita d’in k’awar Umama ce komai yazo cikin sauk’i... Kamota bazai mana wahala ba... Umaima zata sanar damu yanda take rayuwa and believe Maami zan kawo miki ita har nan kiyi yanda kike so da ita... Kiyi gunduwa gunduwa da ita idan kina so... I promise I’d bring her here..!” Ya k’arashe yana mai kuma fitar da huci...

Giwa Ta jinjina kai tace “Na tabbata yarinyar nan koma su waye suka turota ta riga ta gama mana b’arna cikin Masarautar nan... Kuma da alama bata Zo ba saida Ta shirya... Amma zatayi nadama da danasanin sanin wannan masarauta da tayi balle har tayi gangancin shigowa cikinta... Mun gama da wanda suka fita balle ita k’aramar alhaki...

SameenaAleeyou 📚
*MUHIBBAH*

*66*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Zuwa safiya an samu Ansar ya d’an zama stable saidai har lokacin hawaye basu daina zubowa daga k’uncinsa ba... Cikin zuban hawaye ya kuma duban Mommy yace “Alfarma d’aya zaki min Mommy....! Ki sanar dani su waye suka nemi auren Muhibbah..? Ma waye aka aurar da ita..?!”

Cikin kwantar da kai hawaye na gangaro mata tace “Ansar I’ve no idea they are..! Kuma bana tsammanin shi kansa Yawale yasan daga wata duniya suke...!”

Ansar ya kuma dubanta da tsananin mamaki yana girgiza kansa, ya kasa yarda k’iyayyan da Yawale yakewa Muhibbah har yakai wannan matakin, abinda ko wa mak’iyinka bazakayi ba..! Kan mai zai aurartaga mutanen da babu wanda yasan daga inda suke...

Ya sauk’e wane irin nannauyan ajiyan zuciya yace “Mommy this cant be possible... Dole a nemo Muhibbah kuma dole a warware wannan auren muguntar da akai mata... Yau d’in nan basai gobe ba zan shigar da Yawale k’ara... Wllhi sai na d’auresa kodai ya fito min da Muhibbah..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci...

Mommy kanta dubansa kurum take dan bata tab’a ganin d’an nata cikin yanayi makamancin wannan ba..!

Muryar Hameedah dake gefe tana hawaye suka sinkayo tana fad’in “Baffah ya aurar da Muhibbah ne ga wasu Buzaye... Wanda shi kansa baisan daga Duniyar da suke ba..! Nasan Baffah bai kyauta ba amma dan Allah kayi hak’uri Yaya Ansar kar ka shigar dashi k’ara zai zame min abin gori ne daga cikin gidanmu har izuwa mutanen unguwa... Hamma Ansar nasan baka sona ka aureni... Dole akayi maka, dan Allah naci darajan ‘yan uwantaka... Kada ka tozartani a idon duniya....!!” Ta k’arashe hawaye na kuma gangaro mata....

Tausayin yarinyar dasu kansu gaba d’aya duk sai ya kuma rufe Mommy, tasan yarinyar batada laifi mahaifinta ya jawo mata halinda Ta tsinci kanta ciki... Mommy batakaiga magana ba suka sinkayo muryar Ansar yana furta “Bak’in Buzaye..!” Sai yayi Burki ya kuma furta BAK’ON BUZU..!!” Idan bai mance ba Muhibbah ta basa labarin yanda akaita binciken wanene Bak’on Buzu a masarauta...! Duk yanda akayi Wani ne daga Masarautar yazo ya aureta cikin yanayin shiga na b’adda kamanni...! Zasu halak’ata a wannan Masarautar muddin suka fahimci wacece ita... No no bazai bari hakan Ta kasance ba...! He needs to save her..!

Su Mommy gani kawai sukai ya hau fincike igiyar drip yana shirin dirowa daga saman gado...

Mommy ta isa ta rik’esa gam tana fad’in “Ansar lafiya kake...! Ina zaka a haka..?!”

Bai daina fincika ba yake fad’in “Mommy I need to go..! Muhibbah needs me Mommy... Mommy I need to save her... Her life is in great danger...! Mommy rayuwar Muhibbah na cikin had’ari mai munin gaske..!” Ya k’arashe yana mai zira takalmansa...

Mommy da Hameedar duk sun rikice, a rikice Mommy dake rik’eda Ansar ta dubi Hameedah tace maza ta fice ta kirawo likita...
Taci gaba da fad’in “No Ansar bazan Barka ka fice a haka ba...! Ka natsu ayi komai a sannu, bakada lafiya, Maiyasa zaka fincike drip...!”

B’anb’anre hannunsa daga rik’onda Mommy tai masa yana mai furta “Mommy Wai kin mance ne.. This is my profession..! I’m also a medical Dr... Mommy I know what I’m doing... Please let me go...!”

Mommy na hawaye take girgiza masa kai tana furta “No Ansar I can’t let you go... I just can’t...!” Kuka ya hanata ci gaba da magana...

Girgiza kai shima yake yana hawaye yake furta “Mommy I’m sorry... But I’m going... Ki min fatan nasara kawai... Na tafi ko na mutu ko nayi rai... But I must go..!” Yana ida fad’in haka yasa kai cikin sauri... Mommy na kuka sosai tana k’walla masa kira... Cak ya tsaya ya juyo yana duban mahaifiyarsa... Lokaci guda ya dawo da baya ya rungumeta sosai yace “I love you Mommy.. Please forgive me...!” Daga haka Ansar bai kuma tsayawa wata wata ba yasa kai ya fice cikin sauri...

Mommy na kuka tana kiran sunansa inaa ko juyowa baiba ya fice a d’ari...!

**
MASARAUTA

Koda Zuhra ta fito zata tafi sai taji ta lek’a Raheema taga ya ta kwana dan bataji alamun d’uriyarta ba, wata zuciya tace ina ruwanki sabuwar amaryace k’ila baccin huce gajiyan biki take... Hakan yasa bata kuma bi takan Raheemah ba ta janyo ‘ya’yanta suka nufo downstairs... Saidai tana k’ok’arin sauk’a taji kaman k’aran fashewan abu daga d’akin Yazeed... Ta d’aga idanu tana duban d’akin... Sai kuma ta dubi Hadimarta tace “Hindu fita da yaran ina nan tafe..!”

Babu musu Hadimar tayi yanda tace...
Sauri sauri Zuhra ta koma upstairs ta d’an ja ta tsaya jikin k’ofan d’akin Yazeed zuciyarta na bugawa... Wata zuciya tace idan kikaga abinda zai dameki fah..? Take b’angare na zuciyarta Ta bata amsa da fad’in “Mijin K’warai akema kishi... Toh idan kikaga abinda bai dace ba fah..?! Tai shiru tana tinanin abinyi... Tasan halin Yazeed tsaf zai iya kulle Raheema yayi tafiyarsa ba tareda taci koda abinci bane... Maiyuwa ya kulleta ne ma yayi tafiyarsa tinda ba da jimawa ba taji ficewar motarsa...
Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali zuciyarta na kuka nanata mata “Ina ruwanki, Ke naki a wanne idanma wani abin yayi mata... Ai sunfi kusa a halin yanzu...!” Dikda irin wannan batu da zuciyarta Ke mata hakan bai hanata d’an bubbuga k’ofan ba.. Kaman sautin mutum takeji amma muryar bai fita... Hakan yasata saurin murd’a handle amma da alama an kulle k’ofar... Sauri sauri ta isa ma’ajiyan spare keys na gidan Ta d’auko key d’in d’akin ta bud’e... Can jikin gado ta hango Raheema d’aure ta gama jigata ta galabaita.... Raheema na hango Zuhra ta kuma fashewa da kuka hawaye na ci gaba da gangaro mata...

Shaye da tsananin mamaki Zuhra Ke dubanta irin d’aurinda yayiwa Raheema wanda ko ita bai mata irin wannan... Ta isa da sauri ta b’alle sellotape d’in da ya manne bakin Raheemah dashi... Tai wani irin jan numfashi had’ida shak’an iska... Sauri sauri Zuhra ke kwance hawaye basu daina zubowa daga idanun Raheema ba...

Bayan ta gama kwanceta ne ta mik’e da zummar tafiya dan da alama ko idanu Raheemar ta kasa d’agowa su had’a...

Ji tayi Raheema ta rik’o hannunta guda tana kuka sosai, cikin muryar kuka take furta “Zuhra na gode... Na gode..! Dukda ban cancanci taimako a gareki ba amma kika zab’i ki taimakeni... Hak’ik’a ke d’in kinada zuciya mai kyau... Nasan nan cancanci yafiya daga gareki ba kuma banaso nati taking advantage d’in kyakkyawan zuciyarki na nemi tafiyarki dan nasan babu wacce zan mata abinda na miki ta yafe min... Amma hakan bazai hana na rok’i gafararki ba k’awata... Zuhra dan Allah Ki yafe min..! Kiji taisayina karki tafi ki barni da hakkinki... Ki yafe min dan Allah..!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya ga rawan d’ari na zazzab’i da jikinta keyi...
Chapter 107 · 0% Book details