← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 162

Sashe 140

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Guard d’in yace “We’re sorry miss.. He’s not allowed in... Kawai ku koma..”

Yazeed dake tsananin tururi matsowa sosai yayi yana furta “Cut the crap you imbecile..! How dare you..!”

Guard d’in ya kuma furta “We’re just following orders here... Bazaka shiga ba and that’s final..!”

Hawaye sukaci gaba da gangarowa Yazeed, ya dubi Raheemah dake tsaye tamkar ruwa ya shanyeta, lokaci guda Ta dubi Guard d’in tace “How much did pay you..? I’ll double the amount... Just let him in...!”

“Ma’am.. I think it will be better idan kuka tafi..”

Yazeed har wani irin rawa jikinsa yake, yau shine ake wulak’antawa irin haka, baisan ya akai ya isa jikin motar ba, kawai gani yayi Raheemah na bud’e masa marfin Mota... Bai shige ba sai wani irin kuka da ya fashe dashi yana jin zuciyarsa na masa d’aci yana tuna abubuwan sharholiya da sukayi cikin wajen shida abokansa da yanda yayita d’aukan nauyinsu suna abinda sukaso a doron k’asa yau gashi sun juya masa baya sabida halinda ya tsinci kansa ciki... Yana kuka yake furta ya zama k’ask’antacce...

Raheemah ta fuzar da huci kad’an tace “Waye yace kai k’ask’antacce ne... Kaifa mijin Gimbiya ce har yanzu, ko ka mance ba Zuhra bace kawai Gimbiya.. I’m also a Princess.. Har yanzu kai d’in mai sarauta ne... I can give you back your title..” Ta k’arashe cikeda kulawa...

Cikin huci yake furta “If you can give me back my title, can you bring me back my reputation..? Can you bring me back Zuhra..?! Can you bring me back my two children wanda na kashesu Da hannayena guda biyu...?! Tell me Raheemah can you bring back all that I mentioned..!” Kuka yaci k’arfinsa sanda yaci gaba da fad’in “Of course you can’t Raheemah.. Bazaki iya ba.. look at me now.. D’ago ki kalleni na koma babu hannaye babu mulki babu sarauta babu family babu asali da nasaba..! Toh mai ya min saura a wannan rayuwar Raheemah.. Tell me mai ya min saura..?!”

Kaman daga sama suka sinkayo muryan abokansa su Zayyad suna furta “Tabbas babu saura Yazeed... It’s all over, there’s no more Yazeed AbdulJabbar.. You’re completely ruined.. Shara ya fika daraja Yazeed dan na tabbata akwai masu bibiyan bola suna tsintar bola.. But you Babu wanda zai rab’eka sai wannan kwandon sharar ‘yaruwarka..!” Ya k’arashe yana nunida Raheemah a wulak’ance...

Wani kukan k’ura Yazeed yai yayo kan Zayyad yana kai masa bugu da gundulumin hannayensa Ta ko ina yana wane irin cazgan kuka... Da k’yar Raheemah ta iya janyesa jini duk ya b’ata Farin bandage d’in da aka rufe hannun ciki.. Lokaci guda Yazeed Ke sakin k’ara yana fad’in hannunsa zafi.. Hankali tashe Raheemah ta nufi mota dashi tai rushing d’insa zuwa asibiti...

**

A b’angaren Muhibbah kuwa tinanin abubuwan da Raheemah Ta sanar da ita su suka taru suka tsaya mata a zuciya, Ta k’ule a d’aki tana sak’awa tana warwarewa... Bazata bari Rankaidad’e yai mata wannan Mulkin malllakan ba, kafin ai masa nad’i kafin Ta tare dashi kaman yanda Raheemah tace ya kamata ta amshi takardanta daga gareshi.. Tinda idan Ta bari aka nad’asa sarauta shikenan babu hali Ta koma ga Ansar wanda sam bai cancanci hakan ba.. Life is all about sacrifice, she needs to do this for Ansar...! Ta k’arashe tinanin nata tana mai zama saman gado, toh amma idan tana so ya sawwak’a mata cikin sauk’i dole sai ta sauk’ar da kanta gabansa ta nemi abin cikin lallama babu tashin hankali... Tai shiru tana tunanin toh kodai ta kirawo Zahra ne..? Sai kuma ta girgiza kai. A hankali ta furta “No I don’t want to involve his daughter..” Ta fad’i tana mai kuma mik’ewa tsaye, lokaci guda ta kuma furta “Toh kodai Ummi zan samu da batun.?”

“But she’s his mother, koda zatabi bayana cikin zuciyarta zataji zafin abun... I need to this alone by myself..” Ta k’arashe tana mai murza hannayenta had’ida tinanin Ta k’anda zata tunk’ari Rankaidad’e...

Daga yanda yake dubanta ya kuma karkata k’afa d’aya bisa d’aya fuskar nan nasa a tamke kaman tana ganinshi, sai faman murza hannunsa guda yake... Cikin ransa yake furta “We shall see..” Lokaci guda ya d’auki wayarsa dake saman table ya shiga dialing layin Hadiminsa Barde

Muhibbah na nan tana tunanin yanda zata tunk’ari Rankaidad’e taji ana k’wank’wasa k’ofarta, Hadimarta ce ta shigo ta risina tace “Allah shi taimakeki sabuwar Jakadiya ce take sallama..”

Muhibbah ta jinjina mata kai tace “Bismillah shigo da ita..”

Hadimar ta kuma risinawa had’ida amsawa, Jim kad’an suka shigo tareda wata Dattijuwar mace mai kamala, Ta risina tana gaida Muhibbah...

“Kece sabuwar Jakadiya..?”

Jakadiya Ta risina tace “K’warai nice Rankidad’e... Kuma sak’o ne tafe dani daga Mai Martaba, yace Lallai a sanar dake yanada buk’atar ganinki.. Allah shi taimakeki..” Ta k’arashe tana mai kuma risinawa gaban Muhibbar...

Ta mik’e zumbur cikeda mamaki saikace yasan neman hanyar tunk’ararsa take, jinjina mata kai tai tace ”Shikenan Jakadiya Ki jirani a parlor ina nan fitowa..!”
Jakadiya Ta risina tana mai amsawa kana Ta nemi izinin fita parlor..

Doguwar riga ce ta atampa jikinta anyi mata d’inkin fitted gown, sosai ya amshi suffar jikinta, Ta d’auko alkyyabrta ruwan madara ta zira alla alla take ta isa suyita da wajewa itada Rankaidad’e...

A haka ta fito suka nufi sashen nasa itada Jakadiya... Tana tafe zuciyarta na tsananta bugawa domin kaw duk sanda zasu keb’e hakan takeji... Babu kowa a parlorn nasa hakan yasa suka nufi upstairs Jakadiya na gaba tana biyeda ita, A wani madaidaicin parlor ta hangesa yana zaune bisa kujera tv gaba gareshi ya baima kallan nasa mahimmanci sosai.. Ta d’an tab’e baki a ranta tace wayaga Sarki da kallon tv... Jakadiya ce ta soma neman izinin shiga, ta shiga ta zube tana kwasan gaisuwa kana Ta sanar dashi tafe suke da Gimbiya Muhibbah...

Mahmood ya jinjina kai a hankali yace a shigo da ita.. Jakadiya ta amsa had’ida godiya da jinjina a garesa.. Nan ta k’araso ta sanar da Muhibbah sak’on Rankaidad’e..

Zuciyarta bata daina bugawa ba sanda ta kutso kai cikin d’an madaidaicin parlorn wanda yasha kwalliya da kayan sarauta irin na gargajiya da akai modernizing d’insu, gwanin ban sha’awa ko ina...

Kasa d’ago kanta tai ta dubesa dukda tasan cewa nasa idanun akanta suke, tai tsaye sororo a wajen tamkar wata dogariya...

“Meke tafe dake..?” Kalaman da taji sun fito daga bakinsa kenan saikace bashi ne ya aika a kirawota ba... Ta d’an d’ago idanu ta dubesa yayi zama irinta masu mulki k’warjininsa ya cika wajen gaba d’aya... A hankali Ta samu kanta da silalewa saman k’afarta, ta zauna nan gaba gareshi irin zaman rak’umi...
Murya can k’asa take furta kalaman gaisuwa, ya amsa a tak’aice ba tareda ya kuma cewa komai ba...

Kusan dak’ik’a biyar babu wanda ya kuma magana, da dai taga da gaske bazai kuma magana ba sai ta d’an gyara zamanta tace “Jakadiya tace kana kirana..”

Shiru ya d’an gifta kaman bazai amsata ba “Baki amsa min tambayata ba.. Meke tafe dake..?”

A ranta tace yau naga ikon Allah ni Muhibbah wannan wace irin tambaya ce, wata zuciya tace watak’ila damarki kenan na rabuwa da aurensa... Ta d’an kuma yin gyaran murya kad’an tace “Nima ban sani ba..!”

“Baki sani ba..?”

Ta jinjina masa kai a hankali dan bata San ta yanda zata fara ba da gaske...

Mik’ewa tsaye yayi ba tareda ya kuma ceda ita komai ba ya nufi wata k’ofar tabi bayansa da kallo tana tab’e baki kad’an... Jim kad’an Ta gansa ya fito da shiga irinta Buzaye... Tabisa da kallon mamaki har ya dawo mazauninsa ya zauna...

Saida ya daidaita zamansa saman kujerar kana yace “Kinga haka..! Toh a haka na auroki.. Kuma kaman yanda kika fad’i na auroki ne da dalili.. Toh hakan ne yake, dalili kuwa shine ki zamto min bakin zaren warware matsalolin da suka shige min duhu a cikin gidan nan.. Gaskiya ne..! ked’in kece Bakin zaren kuma kin warware... Akwai k’arin bayanin da kike nema..?!” Ya k’arashe yana mai warware nad’in fuskarsa...

Zuciyarta bata daina bugawa ba Ta had’iyi abinda ya tsaya mata a mak’oshi da k’yar.. Lokaci guda ta furta “Tinda na warware maka k’ullin dake cikin Masarautar inaga lokaci yayi da zaka sawwak’e min Rankaidad’e... Tinda wannan shine dalili na auren..!”

K’uri yai mata yana murza zobbansa a hankali kana yace “Baki da hurumin da zaki buk’aci wannan daga wajena, har sai lokacin da ni nayi ra’ayin kaina..!”

Ta d’ago a razane tana dubansa... Lokaci guda ta mik’e zumbur tana girgiza kai take furta “Kar kayi min haka Rankaidad’e.. I’ve been through a lot.. Dan Allah kar ka zamto sanadiyan da k’addarar rayuwata zata kuma sauyawa..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya hawaye na gangaro mata..

Mahmood yaci gaba da takowa gaba gareta tana k’ok’arin matsawa baya, har saida taji alamun Ta isa jikin gini kana ta tsaya ta daina motsa k’afafunta... Fuskarsu dab kusan na juna yake furta “Kinaso na sawwak’e miki..?”

Ta jinina kanta a hankali hawaye na kuma gangaro mata, lokaci guda ya saka hannunsa ya dafe ginin yai mata rumfa gaba d’aya, zuciyarta sai tsinkewa take ko k’wakk’warar motsi ta kasa... Mahmood yaci gaba da furtawa a hankali “Zan sawwak’a miki amma nima inada sharad’una..!”

Ta d’an d’ago fuskarta ta dubesa sai kuma ta maida k’Asa a hankali tana mai furta “Menene sharud’an naka...?”

Stepping back yai kad’an had’ida juawaya ya bata baya hannayensa rik’e ya bayan, saida wasu dak’ik’a suka kuma shud’awa kana Ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Kinada jarabawa na tsawon kwanaki uku, idan kinci zan sawwak’a miki kafin ayi mun nad’in sarauta...! Idan kuma kika fad’i shima zan sawwak’a miki amma sai bayan an nad’ani sarauta yanda ko na sawwak’a miki bazaki tab’a ficewa Ki auri wanda kike so ba.. Zaki k’arasa rayuwarki ne a gidan tsaffin matayen sarakuna da k’uruciyarki.. Kin amince da sharad’ina..?!” Ya k’arashe yana mai juyowa ga dubanta...

Zuciyarta taci gaba da tsinkewa da jin wanann batu nasa,tasan jarabawar zai zamto mai matuk’ar wahala amma batada wani zab’i... A hankali ta shiga jinjina kai tace cikin rawar murya “Na amince...!”

Mahmood ya murmusa kad’an for the first time tun bayan shigowarta kana yace “Buena..!” (Da kyau)

Ya d’an kumayin gyaran murya kad’an yace “Sharad’i na biyu Ummi must not know about this.. Kin amince..?!”
Chapter 140 · 0% Book details