Sashe 141
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan ma a hankali ta jinjina masa kai alamun amincewa...
Shiru ya d’an ratsa tsakani yana mai ci gaba da karantar ta... Lokaci guda yake furta “Ki sami Jakadiya zata sanar dake tsarin jarabawar..!” Daga haka bai kuma bi takanta ba ya nufi wata k’ofar ya barta nan tsaye tana mai bin bayansa da kallo zuciyarta naci gaba da tsinkewa da fargaban amsar sharud’an Rankaidad’e da tayi... Cikin tsananin sanyin jiki Ta nufo downstairs yanda Jakadiya Ke jiran fitowarta...
Jakadiya tana ganin isowarta ta k’araso murmushi saman fuskarta take furta “Rankidad’e an fito..?!”
Muhibbah ta jinjina mata kai a hankali tace “Eh Jakadiya.. Yace min na sameki zaki min bayanin komai..”
Murmusawa Jakadiya ta kumayi kana Ta nuna mata wata hanya tace “Rankidad’e mubi wannan hanyar..” Babu musu Muhibbah tasa kai Jakadiya na biye da ita... Wata k’ofa ce hanyar ta fitar dasu, can Ta hangi kuyangi ‘yanmata da manyan mata sai aiki suke da alama kitchen ne na musamman, wasu na yankan ganye wasu na girka abinci wasu na aikace aikace irin na kitchen... Muhibbah tabisu da kallo d’aya bayan d’aya sai aikace aikacensu suke...
Jakadiya ta tafe hannayenta biyu alamun kira a garesu, nan da nan kowa ta bar abinda take ta nufo yanda suke tsaye, gaba d’aya suka risina suka kwasa gaisuwa...
Jakadiya ta d’anyi gyaran murya tace “Kowa ta bar aikin da take ta fice..!”
Idanu waje Muhibbah Ta kaikaito tana duban Jakadiya shaye da tsananin mamaki jin tace subar tulin aikin da suke su fice...
SameenaAleeyou 📚[10/2, 12:37 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*81*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Mamaki bai saketa ba take duban manya manyan tukwanen dake bisa madafi, uwa uba tulun tsabar shinkafar data gani an ida wankewa za’a zuba... Bata ida mamaki tana ci gaba da waige waige ba Ta sinkayo muryar Jakadiya tana fad’in “Allah shi taimakeki ni zan koma zuwa lokacin da Mai Martaba ya d’ibar miki sai in dawo...” Tasa kai zata juya cikin risinawa...
Baki sake Muhibbah Ke dubanta sam bata fahimci mai take nufi ba... Kafin takai k’ofa tai saurin kamo hannun Jakadiya tana fad’in “Dan Allah karki tafi ki barni a nan ni kad’ai... Bansan mai zanyi ba..”
Jakadiya ta d’an dubeta sai kuma tace “Rankidad’e a al’ada irinta gidan nan ranan da Matar Sarki zata soma ziyartan Turakan Mai Martaba akan sakar mata ragamar girkin Fadah gaba d’aya na wannan ranan wanda harta Sarki wannan abincin zaici.. Domin a gwada jarumtar Giwar Amale a fagen Girki.... Za’a zuba saman farantai a shigar ko wani k’ofa kowa yaci ya fad’i ra’ayinsa akan girkin... Idan wanda suka yabi girkin sunfi Rinjayi Masarauta tayi dace, idan kuma wanda basu yaba ba sunfi rinjayi Masarauta Ta samu nak’asu a wannan fannin.... Tsarin kenan Allah shi taimakeki..” Ta k’arashe tana mai kuma risinawa...
Zuciyar Muhibbah yaci gaba da tsinkewa, babu abinda zuciyarta Ke nanatawa kaman cewa da Jakadiya tai randa Matar Sarki zata fara ziyartan turakansa ranan ake wannan al’ada ta girkin.. Ta lumshe idanunta a hankali zuciyarta naci gaba da tsinkewa, b’angare na zuciyarta na bata k’arfin gwiwa da fad’in zaki iya Muhibbah.. Zaki iya.. In exchange of your freedom zaki iya.. Ta k’arashe tunanin nata tana mai sauk’e huci a hankali.. Bud’e idanun da zatai taga babu Jakadiya.. Shafe fuskrta tai tana mai kuma k’are ma tampatstetsen madafin kallo... Take taji wani irin k’warin gwiwa na zuwa mata, Ta zame alkyabbarta ta aje a gefe kana ta nufi manya manyan tukwanen tana ganin abinda masu abincin Ke dafawa ciki...
Saida ta kuma sauk’e wani ajiyan zuciyar tana mai ambaton Allah ya taimaka mata... Da alama tuwon farar shinkafa ne miyar taushe suke girkawa... Sa’arta guda shine sun rage k’arfin aikin k’arashi ne saiko abinda take fargaban bazata iya ba bazai wuce juya muciya cikin tuwon ba... Ta saka bayan hannunta ta share gumin da tuni Sun karyo mata... Tanayi tana fuzar da fuci.. Ga kayan k’amshi da na d’and’ano ko wanne jere saman faranti... Cikin k’warin gwiwa Ta soma k’ok’arin gudanar da aikin nata mai matuk’ar yawan gaske dukda cewa batada tabbacin idan zata iya wannan aiki wanda sam hankalinta bai kama ba..
**
A daidai k’ofar shiga sashen Gimbiya Turai suka kusan cin karo, zuciyarsa cunkushe take da b’acin rai sakamakon taurin kan da Jamal yai masa yau a asibiti.. Sam baiga zuwanta ba itama bataga nasa ba sai karo da juna da sukai.. Tai saurin komawa da baya tana rik’e goshinta had’ida ‘yar k’ara lokaci guda take Masifan “Wai ku Kuyangin gidan nan yaushe ne zaku koyi tafiya kuna kallan gabanku..!” Birki taima kamalan nata ganin namiji ne tsaye gabanta kuma cikin shiga irinta masu mulki... Ta d’ago tana dubansa har lokacin hannunta dafe da goshinta...
“Tuba nake Your Highness..!” Ya fad’i yana mai d’an sadda kai k’asa...
Murmushin da yafi kama da yak’e tai tace “Your Highness..!”
Ja’afar ya katseta da fad’in “Nafi gane Ki kirani da Ja’afar d’ina Rankidad’e..”
Nanma murmushin tai kad’an tana mai daidaita tsayuwarta take fad’in “Dole na kiraka your Highness, domin kuwa Kaid’in Mai Martaba ne a halin yanzu..! Idan Rankaidad’e ya min izini zan shige..!” Ta k’arashe kanta a k’asa..
A hankali ya d’an ja jikinsa gefe ya bata hanya, kaman wacce take bisa k’aya yana matsawa tasa kai zata shige...
Saida tai taku kad’an Ja’afar ya ambato sunanta.. Bata juyo ba saidai cak Ta tsaya zuciyarta naci gaba da bugawa...
Ya d’an tako kad’an ya tsaya daga gefenta, shiru kaman bazaice komai ba sai kuma yace “Maiyasa tinda na dawo kike guduna...?”
Shiru itama kaman bazata amsa ba sai zuciyarta dake ci gaba da tsinkewa.. Siririyar hawaye ya gangaro mata, cikin rawar murya take furta “Sabida haka ne ya kamata gudun kada mu fad’a ga fushin Ubangiji... Ja’afar nasan kanada masaniyar cewa akwai auren wani akaina..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka...
Jiki a matuk’ar sanyaye yake dubanta kana ya jinjina kai a hankali yace “Haka ne..! You’re right.. I’m sorry, you can go ahead..!” Ya k’arashe yana mai sadda idanunsa k’asa..
Umaima dake k’ok’arin matse kukan da yazo mata gadan gadan, cikin sauri tasa kai ta shige tana mai toshe bakinta... K’ok’arin saita kansa Ja’afar yai yana mai furtawa a hankali bayan Ta shige... “Everything will soon be over... Soon enough.. I promise you..!” Ya k’arshe yana mai kutsa kai sashen mahaifiyarsa...
**
Iyaka jigata ta gama jigata, aiki ne na tarumi aikin gayya aikin da mutane da yawa keyi sai gashi cikin ikon Allah taci k’arfin aikin, tunaninta d’aya yanda zata tuk’a wannan Uban tuwo wanda ko gardawan maza iyaka... Ta fuzar da fuci a hankali tana mai furta “You need to do this Muhibbah..! For Ansar and Mommy, you need to be very strong..!” Ta k’arashe tana mai sauk’e huci had’ida gyara tsayuwarta gaban tukunyar, sosai ta bada wani irin balance kaikace wacce take shirin wasan dambe ce... Ta kamo muciyar wanda tuni ya d’auki zafi k’au Ta shiga juyasa da k’yar tana tamke idanu tana ciza labb’a... Ga wani uban gumin dake tsartsafowa daga ko wane mahudan gashi na cikin jikinta... Sai tayi kaman zata saki muciyar sai ta tuno sharud’an Rankaidad’e... A haka tanayi tana hutu hardai Ta samu tayi abinda zata iya dan ba’a ce tayi komai daidai ba aiki ne na gayya mutum guda Ke jagoranta..
Gefe ta koma tayi lak’was tana sauk’e huci tana duban yanda ta kammala aikin cikin ikon Allah, abinda ya rage kawai shine ta jira dahuwar abincin sai a zuzzuba kaman yanda Jakadiya tace... Ta shiga juya tafin hannunta tana ganin yanda cikin hannun yayi jajazir har kaman yanaso ya d’ura ruwa... Ta rintse idanunta a hankali domin kuwa gaba d’aya gab’ob’inta Ji take tamkar ana sassara mata su... Tana a haka Jakadiya ta k’araso tanai mata sannu... Muhibbah ta d’ago a galabaice tana duban Jakadiya... Saida Jakadiya ta isa jikin tukwanen ta lek’a ko wanne ta tabbata Muhibbah ta aikatu kana ta dawo gareta ta kuma risinawa tace “Sannu da k’ok’ari Rankidad’e.. Jibi yanda kika gudanar da komai cikin k’ank’anin lokacin nan kaman wacce aka saka miki hannu..?”
Murmusawa Muhibbah ta kumayi kad’an tana mai yarfe gumin dake kuma gangarowa daga cikin kanta zuwa goshinta..
Daga can gefe Jakadiya taja ta tsaya suna jiran dahuwar abincin.. Bayan shud’ewan wani lokaci Jakadiya ta dubi Muhibbah dake kishingid’e gefe tana maida hucin gajiya, ta d’anyi gyaran murya tace “Ki gafarceni Rankidad’e ko zaki duba girkin naki..?”
Muhibbah ta mik’e zumbur da k’yar ta isa jikin tukwanen tana k’ok’arin bud’esu, wanda girman murafen ma kawai abin kallo ne... Duk ta soye hannayenta jikin murafen tukunyar... Ta d’auko k’atoton ludayin tana juya miyar ta tabbata yayi... D’an duban Jakadiya tai tace “Jakadiya inaga abincin ya kamalla.. Ya kamata a zuzzuba na samu naje nayi wanka na gaji sosai..”
Jakadiya ta jinjina kai tace “An gama Rankidad’e... Tafe hannayenta Jakadiya ta kumayi take Kuyangin suka soma shigowa sahu sahu suna mamakin abinci ya kammala... Suka risina suna gaida Muhibbah, Allah ya gani ko iya jinjina masu kanma batayi sabida tsaban gajiya...
Wani hamshak’in paranti na alfarma mai ruwan zinari Jakadiya ta mik’o gaba gareta ta risina tace “Rankidad’e wannan parantin a ciki zaki zuba kason Mai Martaba, Kason Sarki ake soma zubawa kafin kason sauran ahalin Fadah ya biyo baya..”
Muhibbah ta amsa tana mamakin fidda ficce da al’adu irinta gidajen Sarauta... Ta isa ta malmala tuwon ta d’ora kan parantin, Jakadiya ta kuma mik’o mata wani d’an madaidaicin bowl wanda da gani basai ance maka mahad’in parantin bane tace ta zuba miyan ciki.. Tayi gaba d’aya yanda Jakadiya ta umarceta kana ta kawo wani marfi wanda da gani kasan shima marfin wannan farantin ne... Aka rufa aka d’aura saman babban tray kana aka kawo wani k’yalle mai ruwan zinari shima aka rufa parantin dashi..
Bayan an gama duka wad’annan ta dubi Muhibbah tace “Toh Rankidad’e kin gama naki, saura ya rage kije kiyi wanka Ki kimtsa Ki tafi B’angaren Mai Martaba, za’a shigo da abincin da zaran kin isa sashen nasa..”
Cikeda k’osawa Muhibbah tace “Yanzu Jakadiya abincin ma baza’a kai masa ba sai ina wajen..?”