← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 162

Sashe 4

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafe yake bisa k’osasshen dokinsa da shi kansa dokin tafiyar k’asaita da mulki yake, ko ba’ace ba zaka fahimci kilisa ya fito, bayan tattaunawa da su Galadima su Hakimi su Waziri da sauransu suka gudanar a yammacin jiya kan batun bada sarautar Masarautar dole ne ma ya fita kilisa ko zai rage wasu damuwar da sukai masa karan tsaye a k’ahon zuciyarsa...Dogarai guda biyu Ke take gabansa biyu Ke take bayansa, suna tafe suna kod’a Yazeed abinda yafi so a rayuwarsa... Kaman daga sama ya hangota tafe sun nufi sashen Mai Martaba itada Jakadiya, ‘yan mata bayi guda biyu suna take masu baya d’aukeda parantai na alfarma.....
Shu’umin Murmushi Yazeed yai kana yai gyaran murya daga nan yanda yake saman dokin, cikeda ladabi dogaran suka tsaida dokin dan sunsan mai gyaran muryar Uban gidan nasu Ke nufi....
Lokaci guda bawa guda ya k’araso had’ida duk’awa Yazeed ya taka bayansa ya sauk’o daga saman dokin, kan kace mai guda d’aya ya bud’e lema ya rufawa Yazeed wanda tuni ya doshi su Rahima da Jakadiya cikin tafiyarsa irinta masu ji da mulki da kuma isa....

Suna k’arasowa gaban Rahima ya yanke ya fad’i dan k’amshin turarensa kurum taji Ta fahimci shine ya k’araso wajen, janye hular alkyabban dake d’an rufeda fuskarta tai tana mai kuma tabbatarwa idanunta....
Tuni Jakadiya da bayin nan sun soma zubewa suna gaida Yazeed....
Duban Jakadiya yai had’ida yin gyaran murya kana ya furta “Jakadiya ina san yin magana da Rahima...!”

Jakadiya ta d’an d’ago a hankali kana tace “Allah ya taimaki Yarima Yazeed, Gimbiya Rahima tana kan hanyarta ne na ganawa da Yarima mai jiran gad.....”
Bai bari takai aya ba ya dakatar da fad’in “Jakadiya kin kaw San da wa kike jayayya...!!!!” Cikin tsananin fushi yai maganar, yayinda dogaransa Ke ci gaba da fad’in “Hattara Jakadiya, Hattara dai Jakadiya.. Allah huci ran Wakilin Sarki Marigayi....!!”

Cikeda tashin hankali Jakadiya Ta zube gwiwoyinta a k’asa tana mai furta “Tuba nake Yarima... Tuba nake Wakilin Mai Martaba...! Allah ya huci zuciyar Yarima..Tuba nake..!!!”

Baice komai ba sai gyaran murya da yai dan tuni Jakadiya ta umarci bayin nan su baiwa Yarima Yazeed da Rahima fili suyi magana...
Shima Yazeed d’in alama yayi da hannu wa dogaran nasa cewa su basu waje harda shi mai rik’e masa lemar....
Cikeda ladabi suka basu waje ya rage daga Rahima saiko Yazeed....

Shu’umin murmushin nan nasa saman fuskarsa yake dubanta, banda lugude babu abinda k’irjin Rahima keyi.... Ta soma ‘yan waige waige tana mai furta “Yazeed not here please.... Mai kake tunanin kanayi ne... What if your brother sees us here, mai kake tunanin zai zaton muna tattaunawa... Na fad’a maka daga yanzu babu komai tsakaninmu ya riga da ya k’are tin lokacin da Mahmood ya amince zai dawo Masarautar nan... So please stay away from me, as far far away as you can....” Ta k’arashe cikin huci...

Murmushin bai bar saman fuskarsa ba idanunsa a kannare yake dubanta, lokaci guda ya tsime had’ida furta “You Shut up..!! Babu wanda yake d’aga min murya bari kiji na fad’a miki...!!” Ya kuma kannare idanu yana k’are mata kallo daga sama har k’asa wannan shu’umin murmushin nasa saman fuskarsa yake furta “Does my brother knows... Yaya na yasan saurana zai kwasa....?” Ya k’arashe yana mai shafa hab’arsa...
Waige waige Rahima taci gaba da yi kana ta rage murya sosai tace “Yazeed na rok’i arzikinka karka rusa min Farin cikin da na jima ina mafarkin samu tareda Mahmood, dan Allah ka barni na cika wannan buri nawa na mallakarsa.....”

Murmushi mai d’an sauti wannan karon yayi kana yace “Bazan hanaki auren Mahmood ba, amma da sharad’i guda...”

D’agowa tai tana dubansa cikeda k’osawa kana tace “Mecece sharad’in...?”

Hannayensa ya hard’e ya maidasu baya kana yayi gyaran murya kad’an “Sharad’in shine ko bayan kin auri Yayana zamu ci gaba da mu’amala da juna... Idan yayi miki banida matsala idan kuma bai maki ba, ina mai tabbatar maki ni da kaina zan tunk’ari Mahmood na sanar dashi komai sannan zan sanar da matata Zuhra kalan cin amanar da kike mata claiming to be her best friend.... Kinsan ni Yazeed zan iya dik abinda na jero...!” Ya k’arashe shu’umin murmushin saman fuskarsa...
Lokaci guda ya kuma gyara tsayuwarsa bai daina murmushin ba yake ci gaba da fad’in “Kije ku ganada Yariman naki, idan kun gama nima akwai ganarwamu da dare a yanda muka saba had’uwa...” Ya k’arashe yana mai fad’ad’a murmushinsa...
Lokaci guda yayi alamawa dogaransa suka k’araso kana ya dubi Jakadiya da itama k’arasowarsu kenan yai gyaran murya yace “Jakadiya na bar Gimbiya Rahima lafiya a hannunki, da fatan Gimbiya zata kular min da Yayana fiyeda yanda Marigayiya Ta kula dashi...!” Ya k’arashe murmushin nan nasa mai tsorata wanda ake jifansa dashi saman fuskarsa, anayin murmushi ne aji sanyi amma na Yarima Yazeed sam ba haka bane, tsoratarwa yake, yanda ya bambambanta da sauran mutane kenan....

Zahra daketa lek’ensu Ta window haka kurum taji tattaunawar da Uncle Yazeed suka gamayi da Aunty Rahima sam bai kwanta mata ba, ita dai Allah ya gani bata k’aunar matar nan sam, bata sonta da Paa d’inta, sam tarayyarsu bai kwanta mata ba... A hankali ta sauk’e ajiyan zuciya had’ida komawa cikin parlorn ta zauna saman kujera tana jiran k’arasowarsu....

Shigowarsu yayi daidai da sauk’owar Yarima Mahmood cikin shiga ta mulki da kamala ....Yayi kyau har ya gaji... Ba Rahima data daskare tana dubansa yanda yake sauk’owa daga bene tamkar wani d’awisu harta Zahra saida ta yaba kyaun da mahaifin nata yayi... Ta saki murmushi a hankali kana ta maidoda da dubantaga Rahima wacce Ta kafe mata Paa d’inta da idanu tamkar zata lashesa, take annurin fuskar Zahra ya d’auke....
Jakadiya da sauran bayin tuni suka zube suna gaidasa....

Rahima kam gaba d’aya Ta shagala da kallon Yariman nata, har saida Jakadiya ta d’an tab’ata kad’an alamun ta sadda idanunta kana Rahima tai k’ok’arin saita kanta had’ida sadda idanunta k’asa, ta d’an janyo hular Alkyabban nata zuwa goshi kad’an....

Cikin tafiya irinta wanda jinin Mulki da sarauta Ke Yawo a jinin jikinsa Yarima Mahmood ya k’araso parlorn, gaba d’ayansu risinawa suka kuma yi suna masu gaidashi cikeda girmamawa kana bayin nan guda biyu suka k’arasa saman tampatseten carpet d’in suka aje trays d’in dake hannayensu wanda Ke rufe da k’yallaye masu ruwan zinari saman darduma mai taushin gaske dake a saman carpet d’in, tuni suka kuma risinawa suna masu komawa cen k’arshen parlorn kansu a k’asa...

Jakadiya ce ta bud’e murya kana ta soma fad’in “Allah ya taimaki Dan Sarki jikan Sarki, Allah ya taimaki babban Yariman Yarimomi a fad’in Masarautar nan, Madallah da samuwarka a wannan masarauta, hasken annurinka ya haskakaka illahirin wannan masarauta, D’awisu kake Sarkin Ado, Farin wata kake sha kallo... Jakadiya tana maraba da sauk’arka Yariman Yarimomi...!!”

K’asaitaccen murmushi saman kyakkyawar fuskarsa ya d’anyi gyaran murya kad’an kana ya furta “Madallah da wannan yabo naki Jakadiya....”

Jakadiya Kai a k’asa take furta “Godiya nake Yariman Yarimomi.... Idan kamin izini zan gabatar maka da isowar Gimbiya Raheema,Zinariya k’wara d’aya tak a masarautar k’asar Akwanga...!” Ta k’arashe tana nunida Raheema wacce kanta ke kife k’asa sai faman murmusawa take....

Jinjina mata kai yai ba tareda ya kuma furta koda kalma ba kana Jakadiya ta soma matsawa da baya.... Kanta a k’asa take furta “Na barku lafiya Allah shi taimakeka...!” Ta k’arashe tana mai ficewa daga parlorn

Lokaci guda Mahmood Ke takowa zuwa gaban Raheema da Farin cikinta Ke ninkuwa.... Tana jin sanda ya iso dab gabanta ta kuma sadda kanta k’asa tana furta “Barka da sauk’a your royal highness...!”

Murmushi yai da gefen bakinsa had’ida jinjina kansa alamun amsa gaisuwar nata, lokaci guda yake nuna mata kujera kana yace “Bismillah..!”
Babu musu ta isa zuwa kujerar da yai mata nuni dashi ta zauna...
Zahra Ta d’an dubesa tana son ta soma zuba masa shagwab’a saidai sam bataga wannan fuskar ba dan gaba d’aya mahaifin nata ya juye mata babban mutum ne yau d’in tamkar wani babban basarake, saikace ba Paa d’inta data saba tsalle jikinsa ba, ita wannan na d’aya daga cikin abinda yasa bataso suka dawo Nigeria ba dan tasan dole wannan sarautar ya zama shamak’i tsakaninta da Paa d’inta, bazasu tab’a zama kaman yanda suke a baya ba...
Nuni yai mata itama da kujerar dake gefen Raheema yace ta zauna... Babu musu ta isa ta zauna dikda cin magani da take....

Raheema ta d’ago tana dubanta fuska d’aukeda murmushi, Zahra dai batako tankata ba saima dad’a d’aure fuska da tai, duban da mahaifinta yai mata ya sanyata sakin fuskarta kad’an kana ta gaida Raheema...
Raheema ta amsada sakin fuska tana k’ok’arin creating guntun conversation tsakaninsu....

A taka’ice kawai Zahra Ke amsata, shid’inma sabida mahaifinta ne dikda rabin hankalinsa naga wayar salulansa ne.... Suna nan a haka Uban Doma ya shigo cikeda risinawa had’ida zubewa yana mai furta “Allah shi taimaki Babban Yarima... Gimbiya Umaima tana neman izinin shigowa...”

Jinjina kai kad’an Mahmood yai alamun bada izini...
Godiya Uban Doma yai kana ya fice ya sanar da Umaima cewa anyi mata izini....

Cikeda risinawa Umaima Ta shigo ta gaidasu kana tace “Yaya inaso na kamin izini na d’auki Zahra dan ta tayani tantance kalolin abincin da zan sauk’i bak’uwata dashi... K’awata zata iso Masarautar nan a yammacin yau da yardar Allah...” Ta k’arashe fuska d’aukeda murmushi...

Zahra da kaman akan k’aya take zumbur Ta mik’e had’ida shagwab’e fuska tana fad’in “Paa please...!”

Murmushi ya d’anyi kad’an kana ya jinjina masu kai alamun suna iya tafiya... Umaima Ta risina had’ida masa godiya, itama Zahran godiyar tai masa cikeda risinawa kana Umaima ta janyo hannunta suka fice...

A b’angaren Raheema kaw ma iya cewa hakan yafi mata dan dama bawai San zaman yarinyar take a wajen ba kawai dai dan babu yanda ta iya ne...
Tuni ta soma zak’ewa tana sanar dashi kalolin abincin data girka masa, tai alamu da hannuwa bayin cewa suzo su bud’e farantan da suka shigo dashi... Shi dai gogan daki daki kurum yake dubanta yana karantar wasu halayya da d’abi’u nata dikda hirar tasu ma iya cewa Raheema ce keyin akasari

***
Chapter 4 · 0% Book details