← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 162

Sashe 89

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zahra cikin jin dad’in Ta sami hanyar rabuwa da Jakadiya a sauk’ak’e tace dashi “Karka damu Uncle na bar maka Jakadiya, zan samu d’aya cikin Hadimaina tai min rakiya...!”

Jakadiya na son cewa umarnin mahaifin Zahra ne babu hali haka tanaji tana gani Zahra tasa kai abinta Ta shige bayan tayiwa Jamal sallama....

Tana shigewa ta kirawo Muhibbah ta sanar da ita Uncle Jamal ya rik’e Jakadiya zatai masa wani aikin....

Muhibbah ta murmusa, a fili ta furta “Perfect..!!” Cikin zuciyarta kuwa fad’i take Jakadiya kema tak’i Ta sameki....

SameenaAleeyou📚*MUHIBBAH*

*56*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Ba tareda rakiyar ko wacce Hadima ba Zahra tai ficewarta kaman dai yanda suka tsara da Muhibbah... A farfajiyan asibitin Ta umarci driver ya ijeta, tana fitowa daga motar ta soma dialing layin Muhibbah... Juyowar da zatai ta ganta tsaye gefenta, Zahra ta d’an zaro idanu tace “Yaushe kika iso..?”

Hannunta Muhibbah ta kamo tana mai sanar da ita bata jima da isowa ba dan tin fitarsu itama ta fice ta shiga motar haya hasalima biyedasu Zahran suke a baya...

Zahra tace “Toh what next.. Mai zamuyi yanzu..?!”

Muhibbah tace “Zamu shiga ki duba Uncle Fu’ad d’in kaman yanda kikaceda Paa d’inki..”

Zahra ta jinjina kai a hankali kana suka nufi psychiatric ward... Suka zauna a wajen da visitors Ke zama, d’aya daga cikin mai kulada marassa lafiyan ya k’araso yana tambayarsu wajen wanda sukazo.. Babu b’ata lokaci sukace dashi ga wajen wanda sukazo, Zahra tace ita niece d’insa ce...

Nurse d’in ya jinjina kai yace amma saidai Fu’ad bai cikin majinyatan da ake fitowa dasu sabida hauka tuburan da yake, duk mai son ganinsa saidai ya shiga ya gansa a d’aure da sark’ok’i jikin gadonsa...

Koda suka shiga wajen Fu’ad ba Zahra kawai ba harta Muhibbah saida ta tausayawa Fu’ad... Irin d’aurin mahaukata da mahaifiyarsa taima mahaukaciya Izzatu irinsa akaima Fu’ad cikin sark’ok’i sannan yanda mahaifiyarsa Ta yanke harshen Izzatu babu magana haka nan shima gadai harshe cikin bakinsa amma kaman an d’aureta Bai iya cewa komai saidai yana iya sauraron magana...Bai cewa um bai cewa a’a sai kallon mutane da ido... Zahra na hawaye daga nan yanda take tsaye Ta kasa ci gaba da kallonsa... Cikin kuka Ta k’unshe bakinta Ta fice ta bar d’akin dan bazata juri ganinsa a haka ba...

Fu’ad yana ganin Muhibbah ya bar dik wani bige bige da yake yana binta da kallo, Muhibbah tasa bayan hannunta ta goge hawayen da suka gangaro mata... A hankali take takowa har Ta iso kusan jikin gadon, Fu’ad bai daina dubanta ba....

Saida tai k’ok’arin saita kanta kana ta soma fad’in “Wasu lokuta a rayuwa mukanji cewa inama mukeda ikon tsara k’addararmu yanda muke so... Saidai Allah bai hukunta hakan ba a tsakaninmu, shikeda cikakken ikon tsara mana rayuwa yanda duk tazo mana... Wasu k’addaran sukan faru damu ne domin su zamto iznah a garemu, wasu kuma sukan faru ne domin su zamto jarabawa a garemu... Rayuwar gaba d’ayarta jarabawa ce, da dad’i ko Babu dad’i...Mai hak’uri da d’aukan k’addara shi yakeda riba... Ina fata wannan ciwo da kake ciki ya zamto iznah ga ire iren mutane masu tunani irin naka wanda basa d’aukan k’addara su maida la’amaransu ga mahaliccinsu, saidai su jefa kawunansu cikin shaye shayen miyagun k’wayoyi don a nasu k’aramin tinanin wad’annan miyagun k’wayoyin sune zasu zamto makawar damuwarsu da suka tsinci kansu ciki... Watak’ila kuma hakan ya zamto hukuncinka ne bayan abinda kuka aikata ma wancan yarinyar shekarun baya... Fu’ad I’m quite certain you’re not like your two brothers, kaso yin abinda ya kamata tuntuni amma bakada courage... Sabida ‘yanuwanka da mahaifiyarku da suke maka barazana... Ko dan dalilin wannan zan yafe maka dikda cewa akwai jinin mahaifina a hannunka... Jinin mahaifina yayi staining hannunka Fu’ad... Kai ka kashe Abbah na, amma na yarda bada son ranka bane ka aikata hakan....! Na yafe maka Fu’ad kuma ina rok’on Allah ya sassauta maka... Ya baka lafiya, ya kuma inganta rayuwarka..!!” Ta k’arashe idanunta na kuma kad’awa...

So yake yayi magana amma babu hali sai hawaye dake gangaro masa fuskarsa d’aukeda alamun tambaya...Muhibbah dake zuban hawaye ta jinjina masa kai alamun tabbatarwa, lokaci guda take furta “Yes... Yes Fu’ad... I’m that girl that you and your brothers abused... Ni ce Saudatu...!!” Ta k’arashe hawaye na kuma gangaro mata...

Fu’ad yaci gaba da tsareta da idanu hawaye naci gaba da gangaro masa... Muhibbah taci gaba da fad’in “Na dawo cikin rayuwarku ne domin na tarwatsa ahalinku, saidai tun kafin nakaiga tarwatsaku da alama zunubanku suna hunting d’inku d’aya bayan d’aya...I’ve never loved you Fu’ad... Kawai nayi amfani da damar ne to ruin you, saidai kaida kanka tuni ka tarwatsa kanka Ta hanyar d’irka ma kwanyarka miyagun k’wayoyi...Ina fata Allah ya kawo maka sassauci Fu’ad... Sannan Ina maka bankwana na k’arshe watak’ila bazamu kuma had’uwa ba... Allah Ubangiji ya sassauta maka....!” Ta k’arashe tana mai ficewa daga cikin d’akin....

Fu’ad yabi bayanta da kallo har Ta b’acewa ganinsa wasu irin hawaye na kuma gangaro masa... A hankali ya lumshe idanunsa wasu hawayen suka kuma gangaro masa...

A nan kujerun da visitors ke zama ta tadda Zahra tai zaune damuwa fal zuciyarta... Daga gefenta Muhibbah ta zauna ta d’an dafata kad’an, Zahra Ta d’ago idanunta masu rauni tana dubanta lokaci guda take furta “He’s my favorite you know... it breaks me seeing him like this... Uncle Fu’ad yanada kirki, he might have his own faults a matsayinsa na d’anadam but I can assure you he’s a good person...!”

Jinjina mata kai Muhibbah tai tace “Na yarda, yanada zuciya mai kyau... Kiyi mishi addu’a Zahra Allah ya bashi lafiya...!”

Zahra Ta jinjina kanta hankali had’ida fatan samun sauk’iga Fu’ad... Saida suka d’an b’ata lokaci a asibitin kafin suka saci wata hanya suka fice yanda driver d’in bazai gansu ba... Shiru shiru yana jiran fitowar Zahra hardai ya yanke shawarin sauk’a ya duba ta ina Zahran take...

Tin yana d’aukan abin wasa hardai ta tabbata babu Zahra babu dalilinta.... K’ololuwar tashin hankali ya shiga... Haka ya dinga karad’e ward d’in yana furta Rankidad’e amma babu ita babu alamunta... Koda ya tambayi nurses d’in dake wajen sai ce masa sukai eh wata ‘yar matashiyar budurwa ta shigo ta duba Yarima Fu’ad amma Ta fice tuntuni... Kuma Bafajen dake gadin k’ofan d’akin Fu’ad akai rashin sa’a ya fice Sayen goro har Muhibbah da Zahra suka shigo suka fice...

Cikin tsananin kid’ima driver ya kirawo layin Hadimin Yarima Mahmood....

**

Jakadiya ta had’iyi miyau da k’yar tana duban sunk’urun d’akin da suka shigo itada Yarima Jamal wanda babu komai cikinta sai wata kujerar katako k’wara d’aya tak...Ta risina kad’an tace “Allah shi taimakeka ko wani abin zanyi maka cikin d’akin nan..?!”
Yanda ta hango fuskar Jamal d’in ya sanyata had’iye sauran kalaman nata... Sai kuma taga ya sakar mata murmushi lokaci guda... Yai mata nuni da wata ‘yar akwati mai kaman briefcase yace Ta d’auko ta kawo gabansa... Babu musu Jakadiya ta isa ta d’auko Jakan ta aje gaban Jamal cikeda risinawa...

Jamal ya kuma sakin murmushi yace “Dad’ina dake Jakadiya akwai bin umarnin iyayen gidanki... Shiyasa zanji mamaki matuk’a idan akace kinci amanar iyayen gidanki...!”

Jakadiya ta Washe baki had’ida risinawa tace “Ai Rankaidad’e bana fata wannan rana tazo... Ranan da zan juya ma ahalin gidan nan baya... Duk abinda kuka umarceni sami’ina wa’ad’ana ne a matsayina na baiwa mai biyyaya.. Allah shi taimakeka..!!” Ta k’arashe tana mai kuma d’ago masa hannu alamun jinjina...

Kansa a karkace yake dubanta, lokaci guda ya kuma sakin murmushi kana yai mata nuni da wannan kujerar k’wara d’aya tak dake cikin d’akin yace ta k’arasa ta zauna a samansa...

Jakadiya ta soma shan jinin jikinta, ta d’an d’ago tana dubansa kad’an “Rankaidad’e ina baiwa ina zama kan kujera a gaban Ubangidanta...?!”

Jamal ya kuma murmusawa yace “So nake yau ki zamto Sarauniya cikin d’akin nan... Sabida ke kikeda mulkin wannan d’akin a yau.. Na tabbata zakiso kiji yanda Iyayen gidanki sukeji koda na rana guda ne..!”

Jakadiya ta had’iyi miyau da k’yar tana washe baki wanda yafi kama da yak’e “Toh Rankidad’e idan kace haka.. Ni umarninka nake bi...!”

Jakadiya ta isa saman kujerar ta zauna tana mai daidaita saman kujerar a hankali lokaci guda tana mai ci gaba da wage baki yawa an mata alk’awarin kujerar Makkah... Sai bud’e kafad’a take saman kujerar tana jinta tamkar Sarauniya...

Yai tsaye jikin sandar crutches d’insa daga nan yanda yake tsaye yana dubanta, murmushi bai bar saman fuskarsa ba...
“Ya kikaji Jakadiya..? Ya kikaji zak’in ‘yanci da Mulki..?!”

Jakadiya tace “Ba’a magana Rankaidad’e... Duk yanda zanso fasaltawa bazan iya ba..!”

Ya jinjina kai a hankali kana ya isa gefe ya d’auko wata igiya... Itadai Jakadiya duk bata ankare ba sai juyi take saman kujera tana jinta yawa Sarauniya.... Bata ankara ba sai ganin Jamal tai duk’e gabanta...

Cikin kid’ima take furta “Allah shi taimakeka kai min rai ka tashi a gabana kar wani ya shigo ya ganmu haka tsire kaina za’ai... Kai min rai ka tashi Rankaidad’e...!!”

Duk surutun da take Jamal Bai tankata ba har saida ya ida abinda yake tsaf kana ya dafa sandarsa ya mik’e yana sakin murmushi...

Jakadiya ta yunk’ura zata tashi amma mai..? Saiji tai k’afunfunta gaba d’aya an d’aure jikin kujerar...
Ta d’ago a firgice tana duban Jamal da ya koma tamkar bai tab’a dariya ba...

Murya na rawa take furta “Rankaidad’e... D’aureni Kai.. Rankaidad’e idan wani laifi nayi ka yafeni, tuba nake..!!”

“Karki damu yau Sarauniya kike... Mulki zaki baza amma a saman kujerar nan...” Ya ida maganar yana mai d’aure hannayenta biyu jikin kujerar...

Izuwa lokacin hanjin cikin Jakadiya sun soma kad’awa... Taga irin azaban da wannan mahaukacin yayiwa Jafar har suka zaci Jafar mutuwa yayi tsawon shekara guda wannan mugun ya kullesa yana azabtar dashi...bata fata ya kwatanta hakan da ita...

Jiki na matuk’ar rawa take furta “Rankaidad’e... Wayyo ni Talle... Wayyo Allah na... Rankaidad’e kamin rai na tuba...!!” Yanda Ta rikice gaba d’aya sai ta zamto Tamkar mai laifi abinka da wacce bata k’ulla gaskiya da alkhairi tsawon rayuwarta...

Gabanta ya k’araso bai daina sakin murmushin ba yace “Relax Jakadiya, ke ai yau Sarauniya ce... Har yanzu sai wasan kwaikwayon muke...!!”

Jin haka yasa Jakadiya Ta d’an sauk’e ajiyan zuciya kad’an kana ta saki murmushi tace “Rankaidad’e ai ka bani tsoro ne...!!”
Chapter 89 · 0% Book details