← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 162

Sashe 131

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mahmood yana fad’awa d’akin ya hango Jamal haihuwar uwarsa yana k’ok’arin duk’awa ga Muhibbah..! Cikin wane irin daka tsalle ya isa ya kai masa wata jahilar naushi wanda saida ya watsar dashi da sandarsa gefe guda..! Ya kuma janyosa ya shiga kai masa naushi ta ko ina kaman wanda aka aikosa, yana tokarinsa hawaye na tsartowa daga idanunsa... Bai daina tokarinsa yana kai masa bugu ta ko ta ina ba a haka ya dinga naushinsa yana cillosa waje da tsananin bugu gashi babu k’afa balle ya tashi ya gudu..! Ja’afar ne ya k’araso ya dafa Mahmood yace “Yaya Kaji da matarka..! I’ll take it from here..!!”
Duban Ja’afar kurum yake da rinannun idanunsa yanajin idan bai kauce masa ya kashe Jamal ba zai iya had’awa dashi... Ja’afar na k’ok’arin kuma tausan Mahmood da Ko kalma guda ya kasa furtawa har lokacin sai wani irin tsima da jikinsa keyi yana fidda gumi kaman wani rikitaccen zaki wanda ya birkice cikin garken Giwaye..! A d’an wannan tsakanin Jamal ya samu yake rarrafawa ya nufi wajen mahaifiyarsa.. Da lalume Giwa ke fad’in “Jamal..! Gwarzona ka cire min wannan tukunyar azabar..!” Inaa tsaban bugun da Jamal yaji hannun Mahmood bai iya furta koda kalma sai nishi.... Ana haka Giwa taji ana janye Jamal daga cikin hannunta..! Taci gaba da kuruwa tana fad’in kar Jamal ya tafi ya barta ya cire mata wannan tulun azaban da ya manne mata fuska..!
Fad’I take “Gwarzona ka taimakeni..!” Saidai Gwarzo ma takansa yake..!

Ashe Tal’udu ne Ke janye Jamal yana fad’in shid’in daga tsatsonsa yake bazai tafi ya barsa ba..!! Manna hannun da Tal’udu zai jikin Jamal wuta ta kama tin daga Kwankwason Jamal har zuwa cinyarsa... Haka wuta tai masa sutura ta zamto wandonsa domin kuwa wuta ce ta rufe al’auran Jamal gaba d’aya ta zamto sitira garesa..! Ihun azaba da ya saki ya maidoda hankulan su Ja’afar..! Giwa na ihun Fuska cikin Tulu Jamal yana ihun wuta na cin iyakacin al’aurarsa ta masa sutura bata bari al’aurarsa ta bayyana ba, mummunan jan wuta taita ci yana ihu yana neman agaji..

A d’ari Mahmood ya koma cikin d’akin yanda Muhibbah Ke kwance har lokacin idanunta kaman a kakkafe suke..!A hankali cikin wane irin murya mai rarrabewa ya furta sunanata, jikinsa har wani irin rawa yake ya janyota cikin jikinsa, ya shiga jijjigata yana ambato sunnanta... A hankali yaga idanunta suna dubansa kaman zatayi magana..! Yaci gaba da jijjigata yana ambato sunanta.. Saidai lokaci guda idanun nata suka kuma rufewa ruf jikinta ya kuma sakewa cikin jikinsa...! Yai saurin d’agota yai mata irin rik’on da akema jarirai ya fice da ita daga wajen hankalinsa a matuk’ar tashe..!

Giwa na ihu Jamal na ihu, a haka Giwa take takawa tana lalumen wajen tsira har ta nufi d’akin da Muhibbah ta kub’uta daga ciki, tana shiga da shike ba gani take ba fuskarta na rufe cikin tulu nan taji k’afarta ya cakki wani abu kaman allura..Aiko nan ta fad’i k’asa ta tuma da k’arfin gaske domin kaw gaba d’aya ji tayi jikinta ya sake kaman babu wani jijiya da ya kuma rik’e gab’ob’inta.. Aiko tana fad’uwa tulun ya fashe fuskarta da ya gama melewa ya koma kaman jan gauta ya bayyana, tulun tsafin na fashewa wani d’oyi ya kuma gauraye wajen, ashe allurar paralyze da Jamal ya aje zaiywa Muhibbah bayan ya ida cin zarafinta a karo na biyu shine Giwa Ta taka tayi takalmi dashi ya cakketa a k’afarta..!
Haka Giwa Ta zube a wajen tana fitar da wani irin turiri had’ada gurnani na azaba ga fuskarta baka hango komai sai alamun melewar fata..!

Shi kaw Jamal saida wuta ta ci al’aurarsa sosai kafin Ja’afar ya samu ya k’araso ya rufa masa rigar kuftarsa da yake sanye da ita Dan sanda wutar ke gauk’in ci tsaban turirin da take da huci Babu mai iya kusantarsa balle ya basa agaji.... Shid’inma sakin hucin azaba kurum yake... Can bayan wutan ya lafa suka hango Jakadiya itama wuta sosai yaci b’angaren jikinta gefe da ita Mushirinki mutumin ne wanda da alama shikam ma kaman babu rai jikinsa, ya k’one sosai baka hango komai tattar dashi sai wannan jan banten da a kullum yake d’aurawa..!

Wutan duniya kenan taci wad’annan bayin Allah cikin ‘yan mintoci da basu shige a k’irga ba amma suka k’one irin haka, inaga wutan lahira wanda baida misali... Tun daga duniya Fuskar Mushirika Giwa wanda bata sujada wa mahaliccinta dashi sai Bokanta da sarauniyar tsafinsu yaci wuta ya mele ya koma abin tsoro da k’yama, shi kuwa Jamal al’aurar da yake sab’on Allah dashi yake cin zarafin ‘ya’yan mutane dashi ana tsafi dasu yaci wuta ya mele ya k’one k’urumus..! Allah kasa mufi k’arfin zukatanmu kayi mana mai kyau duniya da lahira Ameen..!

A can b’angaren Mahmood kuwa yanda ya fito da Muhibbah saman hannunsa yana gudu cikin Masarautar duk yanda ya gifta sai Sun zabura Sun kuma dubansa...
Can ya hango Turaki da Ansar suna tsayuwar jiran fitowarsu ne daga cikin ginin da alama..! Cikin wane irin murya yake sanar da Turaki ya kawo mota..!
Gaba d’aya Turakin ma ya rikice, sai ya rasa wace hanyar zaibi saida Ansar yai directing nasa..! Mahmood bai daina jijjigata cikin hannunsa yana ambato sunanta ba.. Turaki na isowa da motar Yarima Mahmood ya bud’e baya ya shimfid’ata, take shima d’in ya shige ya aza kanta bisa cinyarsa har lokacin bai daina jijjiga fuskarta yana ambato sunanta ba..! Shi kuwa Ansar da yake likita ne sai ya k’araso yana k’ok’arin dubata..!

Mahmood da bai daina sakin huci ba cikin wane irin darara tsawa yaceda Ansar “Don’t touch her..! Don’t you dare touch her..!!” Yanda yake maganan zai tabbatar maka bai k’aunan yaga hannun wani namiji kusanta..!

Ansar da tsawar ta shigesa sosai, girgiza kai yake yana duban Mahmood d’in yake furta “Ni likita ne, zan duba na gani ne if she’s still breathing..!”

Baikai aya ba saiji yayi Yarima Mahmood ya shak’o wuyarsa ya janyosa kusan fuskarsa yana furta “She’s breathing..! She’s alive..! Kada ka sake tunanin Ta mutu..! Idan na kuma jin irin wannan kalma daga bakinka zansa Dakarun Masarautar nan su fille wuyarka..!!” Yana ida fad’in haka yayi jifa da Ansar gefe guda..!

Turaki yai masa K’uri sanda yake fad’i da Turakin ya tada mota su fice..!

Turaki bai kunna motar ba sai duban Mahmood d’in kurum da yake da idanu..!

Mahmood ya d’ago a zuciye yana tambayan Turaki mai yake jira..!

Har lokacin Turaki bai amsasa ba bai kuma tada motar ba sai k’arasawa da yayi ya d’aga Ansar daga k’asa..!
Cikin tsananin tafarfasan zuciya ya fito daga motar ya isa ya Turaki yana fad’in ya basa keys..! Turaki bai basa sai ma duban Ansar da yayi yace “Dr please check on her..!”

Cikin huci Mahmood ya janyo Turaki da wuya ya maidasa gefe ya kuma tare gaban Ansar yana furta “Wannan mutumin bazai tab’a min mata ba..!!”

Turaki ya dafe kansa yace “Your Highness please..! Ba maganar matarka ake a nan ba..! Maganan ceton rayuwar Muhibbah ake a nan..! What if tana buk’atan wani taimako na gaggawa before we make it to the hospital, what if akwai abinda ya kamata a mata kafin mu tafi asibitin wanda zai taimaka..! Mahmood idan Muhibbah ta mutu yanzu a nan zai zamana kai k’arasata, kishinka ne ya k’arasa kasheta..! Please let him check on her , ka bari ya dubata don ko asibtin kaje wani likitan ne zai dubata..!”

A hankali Yarima Mahmood ya janye jikinsa ya baiwa Ansar hanya ba don yaso ba, yana mai aikawa Turaki muguwar kallo, idanunsa k’yam akan Ansar d’in yana duban yanda yake k’ok’arin kai hannunsa saman fuskar Muhibbah da zummar d’aga marfin idonta..! Cikin sauri Mahmood ya mik’a hannunsa ya d’aga masa marfin idon nata yana furta “Duk abinda zakayi ka fad’a min ni zan maka..!”

Turaki dai girgiza kai kurum yayi yana kallon wannan drama na Rankaidad’e..!

Ansar ya d’anyi gyaran murya yace “Rankaidad’e da ka kaita d’aki ka kwantarta saman gado, inaga ba wani abin tashin hankali bane, Shock d’in data tsinci kanta ciki had’ida girman abubuwan da suka faru da ita that’s the reason she passed out, you can take her to her room your Highness..! Idan yaso sai ka kirawo likitan daka yarda dashi ya dubata..!”
Idanunsa na kan Ansar bai daina fitar da huci ba yake furta “You don’t tell me what to do..! Musamman Abinda ya shafi matata..!! Now get lost..!” Ya k’arashe yana mai kuma d’aukota saman hannunsa.. Har ya soma tafiya ya kaikaito ya dubi Turaki yace “I need a female Dr..!”
Bai kuma furta komai ba ya nufi sashensa da ita..

Turaki ya sauk’e fuci a hankali, kafin yayi magana Ansar ya girgiza masa kai yace “Kar ka damu I understand where he’s coming from, yanzu da ya fahimci abinda ya faru da Muhibbah bazai aminta da ko wane namiji kusanta ba koda kuwa likita ne..!”

Turaki ya jinjina kai a hankali yana fuzar da wani hucin, lokaci guda ya ciro wayarsa ya shiga kiran asibiti..!
**
Chapter 131 · 0% Book details