← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 162

Sashe 124

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

**

Haka Zahra Ta mak’ale jikin wani gini ta k’unshe bakinta tana jin kuka na zuwa nata sosai, sai taji kaman sautin tafiyarsa ta wani wajen sai ta canza wajen b’uya a hankali tana mai kuma toshe bakinta da duka hannayeta biyu gudun kar kukan da take ya kufce ya fito, Ta rintse idanunta da k’arfin gaske wasu irin hawaye suka zubo nata sanda taji alamun gadan gadan ya nufo ta yanda take... Yana gab da cimmata dan har ya soma k’ok’arin tura k’ofar zanan da take mak’ale bayansa taji sautin murya kaman na Giwa tana fad’in “Jamal bamuda sauran lokaci Ina yarinyar take.. Ina Saudatu..!?”

Jamal yace “Maami tana kulle a d’akinta... Yanzu zan k’arasa nai mata alluran..!!”

Giwa Ta girgiza kai tace “Ka bar batun allura Jamal, dama itace gudan jinin da K’addarar Masarautar nan Ke wuyanta, itace wannan gudan jini tol da k’ofarta Ke bud’e a Fadan Sarauniya Tamuna, idan a yau d’in nan Tal’udu yayi abinda bai yi da ita a baya ba shikenan k’ofar zai rufe kaida ‘yan uwanka dole ku tabbata akan Mulkin gidan nan.. Mulki bazai tab’a kufce mana ba... Muje muyi sauri mu mik’ataga Tal’udu ya cika aiki Kaga matarka Umaima ta tsira..!!”

Jamal na girgiza kai yake furta “But Maami Zahra tana nan a wajen nan, Ta b’ace min ban ganta ba, yanzu haka ita nake nema..!!”

Giwa Ta zaro idanu waje tace “Jamal Zahra kuma..! Zahra fah kace..? Mai ya kawota nan.. Ya akai tazo nan..?!”

Girgiza kai yake yana furta “I don’t know Maami..! She followed me..!”

Giwa tace “K’yale batun Zahra ka shige muje kafin damarmu na k’arshe ya kufce mana..!”

Jamal ya girgiza kai yace “Maami don’t underestimate that girl.. What if taje ta fad’awa Mahmood..?!”

Giwa Ta buga Uban tsaki tace “Idanma ta fad’a masa bazai samemu ba dan muna Fadan Sarauniya tareda ita yarinyar, sannan abu ne mai matuk’ar sauk’i yanzu da muka samu k’ofar makullin Mulkinmu zai rufu ruff sai mu kashe Mahmooda harma da d’iyarsa kaga mun cire bare cikinmu tinda daga shi har d’iyar tasa ba jina bane.. Dama na gaji da pretending..! Shige muje.. Muyi sauri bamuda lokaci..!!” Ta k’arashe tana turasa Jakadiya na biye dasu...

Hankalin Zahra yakai k’ololuwa wajen tashi...! Tana jin Sun wuce ta bud’e bakinta data toshe Ta fitar da kukan da ya kuma taso mata tin daga k’irji..! Kuka take tana mamakin badak’alan zalunci da aka jika anayi cikin Masarautar su... Babu abina yafi tsaya mata kaman jin muryar Giwa da tayi tana fad’in Mahmood da d’iyarsa ba jininta bane..! Ashe ba ita ta haifi Paa d’inta ba shisa tun can basa wani son juna irin yanda jika da Kaka Ke son juna... Wasu hawayen suka kuma gangaro mata tsananin tausayin Paa d’inta na kuma kama Ta....! Tunowa da halinda Muhibbah Ke ciki ya sanyata Saurin mik’ewa Ta nufo waje babu shiri tana kuma neman hanya... Allah kurum take ambato tana rok’onsa ya fitar da ita ta isa ga mahaifinta..!!

**
K’iris ya rage bai had’ada masu tsaron k’ofar Masarautar ba, saida ya shige har tsakiyar farfajiyan Masarautar kana yaja wani irin burki... Zuciyarsa bata daina bugawa ba ya finciki marfin motar ya fito... A guje ya nufi b’angaren da ya ajeta, jama’an masarauta sai zubewa suke suna basa hanya cikeda mamakin yanayin da suka gansa ciki... Turaki da Barde harmada Ansar suka k’araso cikin Masarautar suma hankali tashe...

D’aya daga cikin Kuyangi masu kulada b’angaren Muhibbah itace Ta soma hango Rankaidad’e cikin wane irin yanayi da bata tab’a ganinsa ciki ba...! Ta shige a guje tana fad’in “Hasiya..! Hasiya ki shirya ga Rankaidad’e..!!”

Gaba d’aya Kuyangin sun rikice duk sun zuzzube a k’Asa zukatansu naci gaba da tsinkewa...

Babu kaman Hasiya wacce Ke zaune saman gadon Muhibbah ta janyo alkyabba ta rufe fuskarta da ita, zuciyarta sai tsinkewa yake sanda taji Rankaidad’e ya turo k’ofar d’akin ya sako k’afafunsa ciki...

Kai tsaye ya nufeta zuciyarsa bata daina tsinkewa ba, lokaci guda yakai hannunsa ya janye Alkyabban... Zuciyarsa tai wani irin tsinkewa sanda yaga ba Muhibbah bace..!! Fuskarsa Ta kuma rinewa zuwa ja haka nan idanunsa... Ga wane irin gumi da ya wanke masa fuska gaba d’aya sai d’iga yake...
Ita kaw Kuyangar sai karkarwa jikinta keyi sabida tsananin tsoro tamkar zata had’iyi ranta...

Mik’ewa yayi ya dafe kansa da duka hannayensa biyu dai dai lokacinda sauran kuyangin suka shigo kawunansu a k’asa... Shugabar tasu ce ta soma duk’awa tana furta “Rankaidad’e kai mana aikin Gafara...!”

Cikin wane irin yanayi yake dubanta kana yace “Where’s my wife..?! Ina matata nace..?!!”

Kuyangar jiki na rawa take furta “Allah shi taimakeka.. Munyi iyaka k’ok’arinmu ganin mun dakatar da ita amma tak’i tsayuwa..!”

Bai daina huci ba yake dubanta lokaci guda yake furta “Wannan shine umarnin da aka baku..?! Nace wannan shine umarnin da aka baku..?! Wacece take nan sanda hakan ya faru..?!”

Hannu na rawa d’aya ‘yar matashiyar ta nuna Hasiya da tuni ta silalo ta zube k’asa daga saman gadon..!

Tana jin ya soma takowa zuwa gabanta Ta soma fad’i cikin tsananin rawar murya “Rankaidad’e kai min gafara wllhi babu yanda banyida Gimbiya ba amma ta had’ani da Allah tace rayuwarta na cikin had’ari a Masarautar nan ya zama dole ta gudu shiyasa mukayi musayen kaya ta saka nawa na Bayi gudun kar azzaluman da suke nemanta su kamata..! Rankaidad’e Gimbiya tayi nisa da Masarautar nan dan tun jiya bata nan..!”

Zuciyarsa taci gaba da tsinkewa, kenan da gaske su Giwa suna nemanta zasu halak’ata..! Ina Ta tafi..?!
Bai tsaya nemo amsa ba ya nufo waje yanda ya tadda Ansar da Turaki.. Ansar na ganinsa ya k’arasa yana tambayarsa Ina Muhibbah.. Ko kallon arziki Ansar bai samu daga Mahmood d’in ba.. Saima duban Barde da yayi yace a rufe Kuyangin nan har sai an sami Muhibbah... Hakan yasa suka fahimci Muhibbah bata a cikin gidan...!

Bai kuma bin takan kowa ba ya nufi b’angaren Giwa kaman zai kifa k’asa..! Saidai koda ya nufi b’angaren Giwa bata nan babu Jakadiya babu Zahra ma sai taron ‘yan karb’an gaisuwa irinsu matan Waziri Talba Madaki da dai sauran masu sarauta harda iyalan Wambai...!

Cikin sauri ya fito ya nufi b’angaren Jamal tinda harda shi a case d’in..!

Nan ma bai tadda kowa ba, yayi tunanin ko yana waje can wajen maza su Talba da su Liman da dai sauran masu sarauta dake cike a Fada dan karb’an gaisuwa da jajen abinda ya sami Yarima Yazeed...

Yana k’ok’arin sa kai da niyyan ficewa ya sinkayo muryar mace daga upstairs alamun tana neman taimako...

A hankali ya furta Muhibbah... Babu shiri ya nufi saman yana bud’e k’ofofi yake ambato sunanta...!

Can saman gado ya hango Umaima ta gama jigata maganan ma da k’yar take..! Cikin tsananin sanyi jiki had’ida mamakin ahalinsa ya isaga Umaima ya hau kwanceta..!

Yana kwanceta yake tambayar “Who did this to you.?!”

Cikin kuka take sanar dashi duk abinda ya faru tin daga kan abubuwan da Muhibbah ta sanar da ita gameda Jamal har kamasu da Jamal d’in yayi ya d’aureta.. Bata kuma San ina yakai Umaima ba... Har kawo kiran Zahra da tai a waya duk saida Ta sanar dashi..!

Cikin kuka daidai sanda ya ida kwanceta take fad’in “Yaya please you need to go after Zahra..! You need to save them both.. I’m sure idan Jamal ya ganta itama bazai barta ba..!!”

Umaima bata ida magana ba Mahmood ya mik’e ya soma jada baya zuciyarsa na barazanar fitowa waje... Mutane biyu da sukeda matuk’ar mahimmanci a rayuwarsa suna hanun mahaukacin k’aninsa... Matarsa da kuma d’iyarsa suna hannun Jamal..!

Lokaci guda yake girgiza kai yana kuma jada baya..! Take ya nufo downstairs yana ambaton sunan Jamal da k’arfin gaske..!

Duk wanda yaci karo da Mahmood cikin Masarautar sai yasan babu lafiya.. Hanya kurum ake basa ana risinawa, duk wanda ya giftasa kuwa sai ya bisa da kallo....

Yana fitowa babban haraban Masarautar yayi wani irin k’ara cikin muryarsa mai amon gaske yana ambato sunan Jamal...! Can ya hangi Zahra ta nufosa a guje sai layi take alamun Ta jigata.. Fsukarta shar shar da hawaye take furta “Paaaa!!!”

“Zahra..!” Ya furta zuciyarsa naci gaba da tsinkewa..!
Zahra tana isowa ya tarota ta fad’o hannunsa dan k’iris ya rage bata zube k’Asa ba sabida tsananin tangad’i da take..!

Mahmood ya shiga jijjigata yana kiran sunanta yana tambayarta Ina Jamal da Muhibbah..!

Cikin kuka Zahra Ke. Furta “Paa you need to save her..! Her life is in great danger Paa..! Maami and Uncle Jamal zasu kasheta..! Paa I don’t want to lose her..!”

Cikin tsananin rawar murya yake furta “No Zahra bazamu rasata ba kinji.. Tell me ta ina suke..! Talk to me Zahra... Fad’a min yanda suke..!!” Ya k’arashe yana jijjiga Zahra da har lokacin bata gama dawowa daidai ba..

“Paa bazan iya ganewa ba...! All I know kawai daga ta can ne yanda na fito..! Paa you need to hurry..!”

Bai kuma tsayawa sauraren Zahra ba ya nufi yanda take nuna masa.. Turaki dasu Barde harma da Ansar da k’arasowarsu kenan sukabi bayansa... Turaki yaceda Barde yaje yazo da Dakaru a bazama nema cikin Fada...!

Umaima da itama bata jima da k’arasowa ba suka rungume juna itada Zahra suna kuka sosai..!

**

Bata kuma sanin meke faruwa ba tinda taga Giwa da Jamal a gabanta sai bud’e idanu tayi ta ganta cikin wani d’aki a wane irin waje... Ta ware idanunta da sukai matuk’ar mata nauyi tana k’arema d’akin kallo..! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Ta fahimci wannan d’aki, bayan shekaru goma sha hud’u da suka shud’e Ta fahimci d’akin.. Shine d’akin da ta farka ta tsinci kanta ciki bayan yaran Giwa sun lalata mata rayuwa.. Allah ya taimaketa Ta kub’uta daga hannun wani azzalumin mutumi mushiriki mummuna wanda sam baida kyaun gani...! Yau Gata nan Ta kuma tsintar kanta cikin d’akin bayan duka wad’annan shekaru..! Ta yuwu wannan shine K’addararta.. Koda ta gudu a baya yanzu gashi ta kuma dawowa bayan shekarun nan..! Ta lumshe idanunta a hankali hawaye suka gangaro mata..! Ta yunk’ura zata tashi taji inaa gaba d’aya a zarge take, irin d’aurin da akema abin yanka idan za’a yanka irin d’aurin akai mata..! Aka had’e hannuwanta da k’afafunta aka d’aure waje guda..!
Chapter 124 · 0% Book details