← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 162

Sashe 29

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sand’a take tafiyar nata har saida ta k’araso jikin k’ofar dataji maganganunsu kwanakin baya... Ta tura a hankali kana ta d’an kutsa kanta ta shige cikin sauri ta mak’ale jikin k’ofa... Shigarta keda wuya kuwa ta soma jiyo muryar Yazeed yana fad’i cikin gadara da isa... “Mamee babu wanda ya isa ya hanani neman sarautar nan... I’m sorry to say not even you... Wllhi wllhi na rantse da mahaliccina ko Abbah ne ya taso daga kabarinsa saidai muyi takara dashi muga waye zai kada wani...”

“Yazeeeed!!!” Mahmood ya daka masa tsawa cikin karaji...

Shima Yazeed d’in cikin tsananin karaji yake ci gaba da fad’in “What..!!! Zaka hanani ne... C’mon Yaya, among the two of us kafi kowa sanin ni nafi cancanta da wannan
Mulki , a ijiye maganan cewa ka jima baka k’asar nan, a dawo maganan kamala da cancanta, I’m a family man bacin haka ni inada Magaji kaikuwa fah...? Bakadashi, d’iyarka d’aya ce tol kuma mace kaga bazata gaji Karagar Masarautar nan ba... Aje ma mace zata iya mulki shin taka d’iyar zatai mulki ne..? Ko ka mance cewa....!”

Bai kai aya ba Mahmood dake tsananin huci ya d’ago yatsarsa dake rawa sabida b’acin rai yana mai furta “Kar ka bari na sake maka kashedi Yazeed... Leave my daughter out of this...!!!”

Sai sannan Giwa ta katsesu da fad’in “Ya isa...! Ya isa haka nace..!! Shin wai ku bazaku tab’a zama inuwa guda ba... Haba Haba shin sai kunga bayana... Wannan wace irin masifa ne... Kai Yazeed na riga na gama magana idan bazakaga girman Yayanka ka bar masa wannan Karagar mulki ba ni dana haifeka Ina tsammanin zakaga girma na... Wllhi bazaka tab’a samun albarkana da goyon bayana ba idan dai akan mulkin nan ne..!!!” Ta k’arashe cikin tsananin karaji hawaye na k’ok’arin kawowa idanunta...

Jamal da k’irjinsa Ke tsananin bugu hango hawaye da yai kwance cikin idanun Mahaifiyarsu, a tamanin ya tafi ya duk’a gabanta yana lallashinta yana bata baki cikin tsananin damuwa da nuna tashin hankali...

Wani wulak’antaccen kallo Yazeed ya watsa mata, kana ya murmusa da gefen bakinsa... “I thought I made myself clear Maami... You can’t stop me... I won’t allow you to deny me what’s rightfully mine...!” Yana kaiwa nan yasa kai ya nufo k’ofa cikin sassarfa kaman zai kifa da k’asa...

Jin takunsa ya sanya Muhibbah saurin mak’alewa bayan k’ofa... Tana ganin Yazeed ya fice cikin tsananin huci da b’acin rai...

Yazeed na ficewa Mahmood ya k’araso gaban Giwa ya zuba gwiwoyinsa a k’asa... Lokaci guda ya d’aura hannunsa guda saman nata...
Giwa ta d’ago idanunta masu rauni a yau d’in tamkar ba ita ba tana duban Mahmood dake duk’e gabanta...

Yarima Mahmood yaci gaba da fad’in “Maami Ki yafe min, Ki yafewa d’an uwana Yazeed... Ba nufinmu bane mu sakaki cikin k’unci da bak’in ciki, na sani a koda yaushe Uwa batada burin da ya shige Ta sanya yaranta cikin Farin ciki... Na sani dik wannan fad’i tashin da kikeyi sabida mu ne... Amma Maami abu guda da nakeso Ki sani shine, shifa Mulki Allah Ke badashi ga wanda yaso ya kuma hana wanda yaso a kuma lokacinda yaga dama... So Maami idan Allah ya k’addari Yazeed shine wanda zai d’ale Karagar Masarautar nan inaso ki bashi full support d’inki ki kuma bashi albarkanki da addu’o’inki domin hakan ne zai leading d’insa to what’s right...”

Saurin d’agowa Giwa tai tana dubansa, kaman Ta shak’esa Ta huta haka takeji... Fad’i take cikin zuciyarta _”K’arya kake Mahmood, baka isa ka tsallake Karagar nan ba a yanzu... Dole ka d’ale sannan ka mutu kafin d’ah na Yazeed ya k’arb’a yai dogon zango har k’annensa da d’ansa ma suzo suyi... Mahmood kenan, ai nafi kowa son ganin Yazeed saman Karagar nan amma hakan ba mai yuwa bane a halin kana nan da rai.. Sai ka shid’a ka tafi ka tadda iyayenka a cen barzahu kafin Yazeed ya d’ale... Na riga nayi tanadima yarana Mahmood.. Ni ce nan na datse mahaifar matarka donma kar Ta haihu balle ka sami Magaji har ka saka ran wataran zai sarauta, Kaga da zaran ka mutu zuriyarka Ta k’are kenan a Masarautar nan Mahmood, saiko wannan shegiyar d’iyar taka wacce koda namiji ne shege bai gadon sarauta...!”_ Tana ida tinanin taji wani irin sanyi na sauk’a mata cikin zuciya, taji murmushi na zuwa saman fuskarta... Hannu tasa ta shafi fuskar Mahmood tana mai furtawa a fili “Mahmood d’ah na Allah dai shi maka Albarka... Ka cika d’ah mai biyayya da ko wacce uwa zatai mafarkin samu... Kalamanka gaskiya ne Mahmood, Allah shine mai bada mulki, shiyasa nake rok’onsa babu dare babu rana da ya mallaka maka wannan gadon mulki... Ni kaine zab’ina Mahmood, idan baka d’ale Karagar mulkin nan ba zanji kaman ban cika burin mahaifinku bane na ganin cewa kai ka zamto magajinsa... Kullum burin mahaifinku kenan ka gajesa Sadauki...!” Ta k’arashe cikin rau rau da murya...

Daga Mahmood har Jamal saida mahaifiyar tasu Ta basu tausayi, sam rauni ba d’abi’arta bane, idan ta shiga yanayin sai ta baka tausai...

Yarima Mahmood ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Kici gaba da mana addu’a Maami, addu’anki yafi komai... Allah yai mana zab’i na alkhairi...!”
Ta jinjina masa kai a hankali tana mai kuma saka masa albarka kana ya mik’e yana furtawa Jamal zai duba Zahra ya kula da mahaifiyarsu...

Jamal ya jinjina masa kai yana mai furta “Alright Yaya, kaje zan kulada Maami...”

Jinjina masa kai Mahmood yai kana yai sallamada mahaifiyar tasu...

Yana fitowa Muhibbah tabi bayansa da kallo, harga Allah bata San dalili ba amma cen k’asan zuciyarta sai ta sami kanta da jin tausayinsa, wani b’angare na zuciyar nata kuma na waswasi da kokonto kan batun da taji Yazeed nayi akan d’iyar Mahmood d’in... Kaman akwai wani ayan tambaya kan d’iyar tasa... Take taji tana son sanin menene Yazeed yake son fad’i kan Zahra....

Bayan Mahmood ya fice itama ta sad’ad’o ta fito daga mab’oyarta...

Yarima Mahmood na fitowa bai zarce ko Ina ba sai d’akin Zahra....Kwance ya hangota saman gado tamkar mai bacci, ya saki murmushi a hankali kana ya soma takowa cikin d’akin...

Ita kaw Zahra tanajin tafiyar mahaifin nata ta lumshe idanunta tamkar mai baccin da gaske, dan bayan maganganun da taji yanayi a waya bata tunanin zata kuma iya duban idonsa and act like babu wani abindake faruwa....

Tana jin sanda ya zauna a gefenta had’ida gyara mata mayafinda Ta rufa.... Murmushi saman fuskarsa yake dubanta, ya d’an d’auki lokaci yana dubanta kafin ya sumbaci goshinta ya mik’e ya fice daga d’akin gaba d’aya...

Yana ficewa, hawayen da Zahra ke mak’alewa suka gangaro mata, lokaci guda Ta mik’e Ta zauna sosai kana ta d’auki family picture d’insu dake aje saman bedside d’inta.... A hankali take shafa hoton, hawaye na gangaro mata lokaci guda take furta “Paa why... What’s that you’re hiding from me... What’s that that you don’t want me to find out... Does it have to do with my Maama’s death... ¿Tienes algo que ver con la muerte de mi mamá? (Shin kanada sa hannu ne a mutuwar magaifiyata.) Paa I love you, I love you so much... And I don’t want our relationship to be ruined...Pero Paa, si me entero de que tienes algo que ver con la muerte de mi Maama ... no sé si alguna vez podré perdonarte Paa (Idan na fahimci da saka hannun ka a mutuwar mahaifiyata, Bana tinanin zan tab’a yafe maka Paa..)”
Ta k’arashe tana mai rungume hoton cikin k’irjinta hawaye na kuma gangaro mata...

Muhibbah dake lab’e tana duban yarinyar a hankali ta saka hannu ta d’anyi knocking... Zahra ta shiga goge hawayenta da sauri tana mai juyowaga k’ofan...

Ganin Muhibbah ce ya sanyata sakin murmushi... Muhibbar ma murmushin take kana tace “May I...?”

Jinjina mata kai Zahra tai tana mai furta “Please come in....”

Fuskarta d’aukeda murmushi ta shigo kana ta zauna a gefen Zahra... Lokaci guda ta k’ura mata idanu tamkar mai karantarta....
Saida ta d’an muskuta kad’an kana tace “Are you alright mi Amiga...?”

Jin Ta ambaceta da Amiga ya sanyata sakin murmushi kana tace “Did you just call me your friend..?”

Jinjina mata kai Muhibbah tai kana tace “Of course I did... Ko mu ba k’awaye bane...?”

Murmusawa Zahra ta kumayi kana tace “Yeah, haka ne... You’re my only friend here... After all..!”

Muhibbah ta kuma murmusawa kana takai dubanta ga hoton da Zahra ke rik’eda... Ta d’an dubi Zahran wacce itama ita take duba

Lokaci guda Muhibbah Ke furta “You really miss your mom, right...!”

Jinjina mata kai Zahra tai tana mai kuma goge ragowar hawayen dake idanunta “So terrible... I miss my Maama... Ina kewarta sosai...!” Ta k’arashe wasu hawayen na gangaro mata...

Tausayin yarinyar ya kuma kama Muhibbah, lokaci guda ta matso kusanta sosai had’ida bata warmed hug... Lokaci guda take lallashinta had’ida kwantar mata da hankali...

“Ki kwantar da hankalinki Zahra, kuma kisa a ranki duk mai rai mamaci ne... Wataran muma duka babu mu, and be thankful you still have your Father who adores you very much... Ganinki haka cikin damuwa I’m sure it will break him.. So instead ki d’agawa mahaifinki hankali ki kwantar da hankalinki kici gaba da yiwa mahaifiyarki addu’a kinji koh...!” Ta k’arashe cikeda kulawa...

D’agowa Zahra tai tana dubanta kana Ta shiga jinjina mata kai alamun amincewa, lokaci guda take furta “You still have your mother, right.?”

K’uri Muhibbah tai mata, tana tina sanda mahaifinta da ‘yanuwansa sukai tarayya wajen kassara mata rayuwarta... Idanunta suka kad’a sukai ja lokaci guda....

Zahra ta d’an matsa daga jikin Muhibbah tana mai furta “Oh... I’m sorry, I’m sorry please...!”

Girgiza mata kai Muhibbah keyi had’ida k’ak’aro murmushi ta d’aura saman fuskarta “No is okay dear... Yeah, I still have my mom... But I lost my father when I was your age....!”

Zahra ta dubeta cikeda tausayawa kana tace “Kin rasa mahaifinki ni kuma na rasa mahaifiyata...!”

Muhibbah ta jinjina mata kai tana mai k’ok’arin saita kanta, lokaci guda taci gaba da furta “It’s part of life... Samu da rashi, wasu lokutan mu rasa mutanen da muke matuk’ar so sukeda mahimmacin a rayuwarmu... But babu yanda muka iya da hukuncin Ubangiji.. Saidai mu karb’e k’addararmu a yanda yazo mana...!”

Zahra ta jinjina kai kana tace “Yeah.. You’re right..!”
Chapter 29 · 0% Book details