Sashe 156
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A haka suka nufo babban Gwani Ja’afar da Turaki sun saka shi a tsakiya ... Dogarai suna biye dasu suna ci gaba da kod’a Mahmood d’in wanda gaba d’aya ji yake jikinsa na wane irin tsuma Wai yau shid’in zai taka k’afafunsa cikin Fadan mahaifinsa Babban Gwani, ya shiga tuno rana na k’arshe da yaga mahaifinsa saman Karagar wani zuwa Nigeria da yayi a lokacin yana can k’asar Spain.. Ya tuna mahaifinsa yace dashi duk daren dad’ewa akwai ranan da zaizo ya gaji wannan Karagar... A lokacin ya dai saurari mahaifin nasa ne amma yafi bada k’arfin Yazeed shine wanda zai gaji mahaifin nasu tinda ya fisa jib’antuwa da al’amaran sarauta... Ja’afar dake gefensa shima wani irin fuzga yakeji zuciyarsa na masa ya shiga tuno abubuwa da dama ciki harda rayuwa k’ark’ashin Inuwar Bayi da yayi cikin Masarautar.. Yau sai gashi nan zai taka cikin Babban Gwanin Mai Martaba kuma shid’in yana daga cikin ahalin gidan... A hankali ya lumshe idanunsa hawaye suka gangaro masa...
Sanda suka isa cikin Babba Gwani gaba d’aya King makers suka mimmik’e tsaye suna bud’e manyan garensu suna furta “Lafiya D’an Toron Giwa... Gaba salamun baya salamun... Ka shigo cikin aminci.. Karagar taka ce..!”
Saida ya isa daidai saman darduman nad’in sarautar mai tambarin masarautarsu yaja ya tsaya yana duban Ja’afar.. Hannun Ja’afar ya kamo suna fuskantar juna, lokaci guda Mahmood Ke furta “Shin zaka iya...? Zaka iya zama saman Karagar nan ka tsare Martabar gidanmu...?”
Cikin tsananin sanyin jiki Ja’afar Ke girgiza kai yana furta “No Yaya.. Bazan iya ba, amma inada yak’inin kai zaka kwatanta da taimakon Allah... We’re all here for you Yaya kai ka cancanci ka d’ale Karagar.. Hawaye suka taru can cikin idanunsa ba tareda sun gangaro ba.. Mahmood ya dafa kafad’ar Ja’afar yace “You spent all your life serving this Palace.. An mai dakai Bawa a cikin Masarautarka.. Bata baka dama ka rayu matsayin d’ah a cikin gidan nan ba, Sabida haka ka cancanci rik’e ragamar jagorancin gidan nan... A yau inaso kai ka gaji mahaifinmu....!” Ya k’arashe hannayensa guda biyu dafe da kafad’un Ja’afar d’in.
Girgiza kai Ja’afar yake yana furta “A’a Yaya kai ka fini cancanta da ka gaji mahaifinmu I’m sure da ace yana raye da abinda zaiso kenan... Sarautar taka ce Your Highness... Mu muka zab’eka ba kai ka zab’I kanka ba... Munbi cancancanta kuma duk munyi mubaya’a cewa kaine kafi kowa cancanta...!”
Kaman daga sama suka sinkayo wata murya...
SameenaAleeyou 📚
[10/9, 1:10 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*87*
*©️Sameena Ameeyou...✍🏽*
A tare Mahmood da Ja’afar suka juyo suna duban Fu’ad dake takowa gaba garesu, hawaye Tab idanun Fu’ad d’in yake ci gaba da takowa cikin Babban Gwanin, cikin wata irin murya mai gauraye da rauni da k’warjini yake furta “Kai kafi kowa cancanta Yaya... Ja’afar yayi gaskiya, kaine ka cancanci ka gaji Abbah..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya a daidai lokacinda ya k’araso gabansu...
Yai tsaye gaban Mahmood suna duban juna, lokaci guda Mahmood Ke furta “Fu’ad kai nake gani a gabana...?”
Fuad ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Ni ne Yaya.. I’m out of the mental facility..!” Yana kaiwa aya Mahmood ya rungumesa sosai yana furta “Naji dad’i Fu’ad.. Naji dad’i da Allah ya baka lafiya... Alhamdulillahi..!”
Fu’ad ya d’an murmusa kad’an yana duban Mahmood d’in wanda shine favorite d’insa gaba d’aya cikin ‘yan uwan nasa... Take kuma ya sadda kansa k’asa bayan yakai dubansaga Ja’afar yana tuno abubuwan da Jamal ya sanar dashi bayan ya kai masu ziyara a cikin asibitin kafin ya nufo Masarauta... Ja’afar ya d’an dafa Sa kad’an yana sakin murmushi.. “It shall all be well... Brother.. Im glad you’re finally home.. Allah ya k’ara maka lafiya...!”
A tare Mahmood da Fu’ad suka amsada Ameen Mahmood d’in na duban k’annen nasa... Lokaci guda ya rungumosu gaba d’aya ya k’ank’amesu cikin jikinsa.. Su duka ukun suka rungume juna gaba d’aya hawaye na gangaro masu... Tausayinsu ya cika zukatan mutanen dake wajen..
Kaga yanda masu rawani Ke matsan k’walla.. Allahu Akbar dole ka koka ma wannan ahali wanda suka sha fama da gwagwarmayar rayuwa... Bayan lafawan komai Algaita yaci gaba da tashi.. Aka soma gudanar da cika ciken nad’in sarauta kaman yanda yake a al’adance... Mahmood yai zama irin zaman da ake idan za’a ci abinci nan saman darduman, Dogarai sukaci gaba da kod’asa sanda ake fesa masa turaren mulki.. Galadima da Talba suka d’auko Alkyabba fara k’al wanda akai mata kwalliya da zare mai kalar zinari suka rufa masa basmala saman harshensu... Shima Mahmood d’in bai daina tsarkake mahaliccinsa ba Sarkin da babu ya shi... Yanaji wani irin babban al’amari ne Ke aukuwa dashi... Gaba d’aya Sai yanajin zuciyarsa tana wane irin fuzga daga cikin k’irjinsa.. Sanda akazo za’a d’aura masa hular Kambin sarautar Galadima ya umarci Ja’afar da ya d’aurawa d’anuwansa Mahmood Kambin Mulkin a saman kansa... Jafar ya k’araso hawaye da murmushi gauraye saman fuskarsa ya amshi hular hannun Galadima.. Har ya soma k’ok’arin d’aurawa saman kan Mahmood sai kuka ya dakata, gaba d’aya suka tsaya suna dubansa, Sunan Fu’ad ya ambata wanda yasa Fu’ad d’in d’agowa cikin fad’uwar gaba, Ja’afar na sakin murmushi yace dashi a hankali “Come here Brother.!”
Saida ya d’an d’ago yana duban mutanen dake wajen kaman mai tsoron motsawa, Mahmood ya sakar masa murmushi yana dubansa, a hankali Fu’ad ya mik’e ya k’arasa gaban Ja’afar d’in.. Lokaci guda Ja’afar ya kamo hannunsa ya aza saman Kambin yace “Lets do this together Brother..!”
Cikin tsananin sanyin jiki Fu’ad ke dubansa, lokaci guda ya shiga girgiza kai yana furta “No Ja’afar, I can’t do this.. Banida matsayin da zan d’aura Kambi saman kan Sarki..!”
Ja’afar ya dafa hannunsa yace “But you’re our brother Fu’ad, it doesn’t matter idan ba Matar Sarki bace Ta haifeka.. Kuyangar Sarki ce ta haifeka, kai d’in d’an mahaifinmu ne .. Ko ka mance Mahaifiyarmu ta bama mahaifinmu Mai Martaba kyautar Baiwarta mahaifiyarka, kai d’in d’ansa ne Fu’ad.. Kai d’in d’an K’wark’wararsa ce.. Ka amince da haka mu d’aurawa Yaya Kambin mulki akansa...!” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa..
Fu’ad dake zuban hawaye lokaci guda ya shiga jinjina kai kana yakai hannunsa saman kambin....A tare suka mik’e suka rik’e hular hawaye na gangarowa daga idanunsu.. Shi kansa Mahmood d’in hawaye ne ya mak’ale cikin idanunsa ya kasa gangarowa sai wane irin tsuma da illahirin jikinsa keyi... Bayan sun d’aura masa Kambin Baba Talba da Galadima sune suka soma d’aura masa farar rawanin akansa wanda take fara k’al sai d’auke idanu take... Take aka nad’a masa rawani mai kunne biyu akansa, Wali ya k’araso da d’amaran Mulki sanda Mahmood zai mik’e Dogarai suka baza babban garensu suna furta gyara kimtsi da kyau.. Saida har ya mik’e tsaye kana Wali da Maga yak’i suka k’araso suna d’aura masa d’amarar... Bayan sun ida d’aura masa d’amaran Mulkin Shattima ya k’araso da Takobin hannunsa... Ya mik’awa Magayak’i.. Magayak’i ya amsa ya sakama Mahmood Takobin cikin damararsa... Had’ida mik’a masa Sandar Mulki ya rik’e yana duban d’imbin Al’umman masarautarsa...Allahu Akbar kallo guda zaka masa kace ga Sarki nan wanda zai amsa sunansa Sarki... Babban Gwani Ta kacame da kalaman yabo.. A hankali Mahmood ya soma takawa sanda ya nufi Karagar zai d’ale.. As he was walking towards the Throne Abubuwan da suka faru cikin gidan sai zuwa masa suke, kama daga canza identity d’in da Giwa tayi har zuwa duk wasu abubuwa da suka faru.. Ya jima sosai yana duban KARAGAR hawaye tab idanunsa.. Take ya nemi tsari daga mahallicinsa daga sharrin dake tattareda wannan Karagar ya kuma rok’i mahaliccinsa da ya tabbatar masa da dukkan Alkhairi dake tattareda Karagar sannan yayi masa jagoranci bisa jarabawar da ya jarabcesa dashi na shigabancin Al’umma... Sanda ya d’ale saman Karagar da basmala daidai nan hawaye guda d’aya ta d’igo daga cikin idanunsa.. Allahu Akbar nan kaji Babban Gwani ya kacame da ambaton Allah... Bakunansu sai furta alkhairi suke.. Algaita yaci gaba da tashi.. Take aka buga masa Tambura guda sha biyu na Masarautar.. Yana jin jikinsa na wani irin Karma alamun da gaske sai dai yau shi Mahmood ya d’ale Karagar.. Bayan tsawon shekara guda da watanni da akai babu Sarki a Masarautar sai iftila’i da k’alubale da sukaita faruwa sai gashi yau Allah ya tabbatar da ikonsa ya d’aura Sarki a wannan Masarautar saidai muce Ubangiji yayi masa jagoranci...
Ko wanne Tambari guda Goma sha biyun nan da za’a buga sai an ambaci ma’anarta.. Haka saida aka buga masa shabiyu russ ana fad’in ma’anarsu... Daga bisani Masu sarauta suka soma k’arasowa suna zubewa suna kwasan gaisuwa... Galadima ya fara yin nasa Barde yana amsa masa da fad’in “An gaisheka Galadima..! Mai Martaba ya amsa..! Matawalle ma yayi nasa Barde ya kuma amsa masa da “An gaisheka Matawalle..! Mai Martaba ya amsa..!” Haka duk masu sarauta kowa saida ya kawo nasa caffan ga Sarki Mahmooda d’an AbdulJabbar...
Turaki na hawaye ya k’araso ya mik’a gaisuwarsa da taya murna ga abokinsa yana mai furta “Long live the King..!”
Ja’afar ma ya k’araso yai masa haka Fu’ad ma... Ko wannensu hawayen Farin ciki kwance cikin k’wayan idanunsu...
Shagulgulan bukin nad’in sarauta sukaci gaba wakana... Zigazigai naci gaba da yin kirariwa Sarki “Allah shi jaaa zamaninka..! Lafiya Baya goya marayu... Lafiya cika sarari..! Lafiya mai sulken yak’i..! Lafiya mai Tambura goma sha biyu... A laaaaafiya azurfa babu gauraye...!” Ire iren kirarin da ake tayiwa Mahmood kenan ana fad’in Allah ya bashi gidansu...
Yinin ranan Masarautar taci gaba da karb’an kyauttuka daga masarautu daban daban.. Yammacin ranan masu mulki suka hau Dawakai sukayita kawo caffa (gaisuwa) saman dawakai ma Sarki dan nuna Farin cikinsu...
Ja’afar ya dubi Fu’ad da har lokacin Bai wani saki jikinsa ba, kana ya dafasa kad’an yace “Kana so mu hau Doki muyi wasan doki..?”
Fu’ad ya dubesa hawaye kwance cikin idanunsa yake furta “You know, to be honest I still can’t believe my own Mother can do all those horrible things.. How can someone be so inhuman...!”
Ja’afar ya dafasa kad’an yace “Fu’ad wasu lokutan mukanso abubuwa su kasance yanda muka tsarasu amma saidai ba muda ikon yin hakan sai abinda Allah yayi... Mutum baya wuce k’addararsa, na sani da ciwo amma kayi hak’uri sai kaci jarabawarka..!”