← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 162

Sashe 66

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Majidad’i da a yau d’in harda tozali ya shafa cikin idanunsa k’uri yaiwa Jamal kana ya tintsire da wata irin bahaguwar dariya, yana nuna Jamal da Takobin yake fad’in “Sai na fille wuyanka, na fara dakai kafin na isa kan d’anuwan naka Kaga sai ayi gawa biyu a take ku hutasar da mahaifiyarku da yin kuka biyu... Zatai kuka d’aya ma mutuwa biyu...!!” Ya k’arashe yana mai d’aga Takobin sama da niyyan sarawa Jamal... Daidai nan Giwa ta K’araso cikeda tashin hankali zuciyarta na zillo cikin k’irji... Hankalinta bai ida tashi ba saida ta hango Majidad’i na yunk’urin sauk’ewa d’anta mafi soyuwa a gareta Takobi a wuyansa... Giwa ta k’walla kiran sunan Jamaal da wane irin k’aran gaske daidai lokacinda Jamal d’in ya kauce Takobin ta samesa a kafad’a ya keta masa hannun riga had’ida kuskuran fatarsa kad’an, ji kake kyaaat....

Dukda zuciyarta dake tsananin bugu hakan bai hanata k’arasowa cikin parlorn ba tana fad’in waye ya baiwa wannan mahaukacin izinin shigowa cikin Fada...!

Kallon k’ask’anci Majidadi ya rakata dashi a daidai kokacin da aketa zubewa ana faman gaisheta....

Dariya ya kuma fashewa dashi kana yace “Madallah da isowarki Rankidad’e... Idan kin mance na tuna miki nine nan wanda ba’a sakani ba’a hanani kuma ajalin mulkin ahalin Sarki AbdulJabbar... Yayi daidai da kikazo nan ki gani da idanunki yanda basai ankai miki labari cikin Fada ba... Kiga yanda zan murk’ushe wuyan ‘ya’yanki musamman wannan babban maci amanan...!!” Ya k’arashe yana mai nuni da Yazeed da har lokacin bai daina binsa da ido yana sakin huci ba....

Dikda tsananin shakkarsa da Dogarai keji hakan bai hanasu yunk’urin dakatarda Majidad’i ba ganin yana k’ok’arin wuce gona da iri har Giwa ce zai dinga fad’i mata kalamai haka....!

Takubba biyu ya rik’e a duka hannayensa yana mai nunasu da Takobin yake fad’in dik wanda ya fasa tunk’arosa bai haifu ba... Ko step d’aya bazai k’ara ba amma duk wanda yai wauwautan k’arasowa gabansa ko shakka babu saidai uwarsa ta haifi wani amma bashi ba dan har lahira zai cire wuyan mutum... Ya k’arashe zancen nasa yana mai kuma d’ago Takubban....

Yazeed da ya kula ya maida hankalinsa ga dogarai tsalle yai ya tokari Majidad’i saida ya kaisa k’asa kana finciko Takobi guda dake hannun Majidad’in...

Majidad’i ya rakasa da kallon mamaki dan bai zaton Yazeed zai iya koda motsa Takobi hannunsa ba balle har ya k’wace.....

Lokaci guda Yazeed ya sakar masa murmushin nan nasa had’ida d’aga gira guda... Ya k’arasa gaban Majidad’i dake zube wajen yana juya Takobin dake hannunsa yasa k’afarsa guda ya take k’irjin Majidad’i lokaci guda yake nuna k’wayar idanunsa da tsinin Takobin, murmushin bai bar saman fuskarsa ba yake furta “Ina Jarumtar naka..? Kodai dama a baki ne ba’a fagen daga ba...?!” Shiru ya d’an ratsa tsakani kana Yazeed yaci gaba da fad’in “Zan iya fille kanka a nan idan naso, idan kuma naga dama muka kara naci k’arfinka sai na maidaka bawa har k’arahen rayuwarka... Ka rayu cikin yimani bauta... Na tabbata bazakaso hakan ba... Partner..!” Ya k’arashe muguwar murmushi saman fuskarsa...
Lokaci guda ya kuma d’agowa yana bin illahirin mutanen dake wajen da ido ciki harda mahaifiyarsa da tsananin tashin hankali ya nuna saman fuskarta... Fuskar nan nasa a matuk’ar d’aure ya bud’e murya yana fad’in “Inaso kowa ya bud’e idanunsa da kyau yaga yanda zan gama da wannan d’anta’addan kuma sannan hakan ya zamto izna da ishara ga duk wani mai yunk’urin ta’addanci irin nasa... Masarautar nan bazata lamunci ta’addanci ba..!!” Ya k’arashe cikin tsananin karaji

Majidad’i dake kwance k’asa gaban Yazeed da ya take masa k’irji da k’afa guda murmusawa shima yai ba tareda ko gizau ba yace “Tsari mai kyau Your Highness, dad’ina dakai akwai kwanya da kaifin basira... Kai da kanka kake kawo shawarin abinda za’ayi kuma shawarin Naka yayi daidai da tunanin duk wani mai san mulki... Naji dad’in shawarinka a karo na biyu... Mu kara a fafata wanda dik yaci galba kan d’an uwansa sai ya k’arashi rayuwarsa cikin Bauta... Zanso jinin AbdulJabbar ya zamto Bawa mafi k’ask’anci a gareni...Amma saidai kashh banjin zan yafewa duk wani wanda yaci amanata har na bashi daman sake rayuwa... Abu guda nake ma duk wanda yaci amanata shine KISA... Dama guda kake dashi yanzu da nake kwance gabanka ka gama dani tin ina kwance k’asa k’ark’ashin k’afanka dan nayi imani ni kuma idan har ka bari na tashi sai na kasheka...!!”

Yazeed da baisan dawan garin ba dan sam baisan Majidad’i yasha maganin k’arfe ba cikin tsananin huci yake kuma danna k’afarsa saman k’irjin Majidad’i ya shiga k’ok’arin darza masa Takobin da iyaka k’arfinsa, sai faman haki yake yana kuma darza Takobin amma saidai abin mamaki ko kad’an tak’i ratsa fatar Majidad’i balle ta shiga cikin jikinsa... Majidad’i yai masa K’uri saima sakin murmushi da ya soma lokaci guda murmushin nasa na rikid’ewa dariya had’ida shewa...

Jikin Yazeed yai bala’in sanyi... Ya darza ya darza Takobi ta kasa shigewa... Idanunsa suka firfito waje...

Cikin tsananin tashin hankali Giwa Ke girgiza kai tana k’ok’arin fincika daga rik’onda Jamal yai mata take fad’in “Jamal ka k’yaleni na ceci d’an uwanka mahaukacin nan kashesa zai...!”

Illahirin jama’an dake wajen wannan ya dubi wannan wancan ya dubi wancan... Harta Muhibbah dake lab’e daga gefe abin itama tsoro da mamaki ya bata... Ta kuma duban Majidad’i tana mamakin wanene wannan da tsana mai k’arfi yai k’amari tsakaninsa da ahalin sarki AbdulJabbar... Kuma ga dukkan alamu baida tsoro ko gizau a tattaredashi.... Tinaninta ya katse sana Majidadi ya tsagaita da dariyarsa yana duban Yazeed da tuni ya gaji da darza Takobi sai faman haki yake gumi na gangaro masa... Murmusawa yai kana yace “Ka d’auka zanzo wajen nan ne unprepared your Highness.... Ka tapka babban kuskure daka zaci you can outsmart someone like me.... Yanzu ni kuma zan baka abinda kake nema... Zan kashe na cire wuyanka ayi min roman k’wak’walwanka sannan nayi sark’a da k’wayan idanunka na ratayeta a wuyana...!!” Ya k’arashe yana mai daka tsalle daga kwance sai gashi ya mik’e tsaye Yazeed ya zube k’asa... Lokaci guda ya soma nufo Yazeed yana sakin muguwar murmushi Yazeed d’in na faman jada baya daga zaune zuciyarsa naci gaba da tsinkewa yaga mutuwa muraran....

Giwa na kuma fincika take fad’i ma Dogarai su kama wannan d’anta’addan amma ko gizau babu wanda ya matsa sabida tsananin tsoron Majidad’i dan yanda yace d’in tabbas zai kashe rai.. Ta koma gasu Galadima su Hakimi dansauransu tana fad’in haka sunaji suna gani zasu bar wannan mahaukacin ya kashe mata d’a... Suma babu wanda ya motsa saima muzurai da suke, yanda Takobin Majidad’i Ke tsananin k’yalli tabbas tsaf zai fille wuyan mutum....

Fu’ad da tuni kansa ya soma juyawa waya ya ciro ya kirawo Yayansa Mahmood amma bai d’agawa... Kansa taci gaba da sara masa... Sosai ya kame kansa dake tsananin sara masa ya fice daga cikin wajen gaba d’aya cikin wane irin sauri kaman zai kifa k’asa...
Muhibbah tana ganin ficewarsa tai saurin bin bayansa dan babu sauran abinda zata tsaya kallo ko shakka babu wannan D’angundan zai kashe Yazeed kisan wulak’anci a sauk’ake sakayyanta data ahalinta na bibiyan wannan ahali... Koda wannan tashin hankalin aka k’yale Giwa tasan ta sami nata ajalin kenan...
Gwara tabi wancan mahaukacin Fu’ad taga shi kuma mai yake shiryawa....
**

Kafin kace wani abu cikin Masarauta gaba d’aya ya yamutse, hargitse ne ta ko ina, Isowar Ubandoma da Waziri ya hana Majidad’i sarawa Yazeed Takobin wanda tuni ya sadakar Majidad’i ya fille wuyansa....

Ubandoma yace “Ku dakata zan fad’i gaskiya..!!”

Kallo ya dawo kan Ubandoma da Waziri..
Waziri ya jinjina masa kai alamun yayi magana....

Ubandoma ya soma fad’in “Yarima Mahmood baida laifi... Kawai na fad’i hakan ne dan ceton rayuwata da Yarima Yazeed yayi kuma shima Yarima Yazeed baida laifi duk abinda na fad’i ni ne nan na k’ago na fad’a babu laifin ahalin Marigayi Sarki AbdulJabbar ko d’aya..!!” Ya k’arashe yana mai duban Majidad’i..

Dariyar rainin hankali Majidad’i ya fashe dashi yace “Ni ne nan zaku rainama hankali ku maisheni dolo wanda baisan mai yakeyi ba... Kunje kun kitsa yanda zakuyi... Nayi imani ku kuka kashe min mahaifina dan ku d’in ba’a aminta daku nayi kuskure da na yarda dakai Yazeed bayan kaid’in kaci amanan d’anuwanka... Gashi nima kaci amanata... Kaid’in ba d’an halas bane dan haka yanzu zan gama dakai bayan na sanar da d’inbin al’umman dake wajen nan irin cin amanar dakaiwa d’an uwanka Mahmood kaso d’aura masa gagarunin sharri...!!”

Daidai lokacin Mahmood da Turaki suka shigo... Muryar Mahmood suka sinkayo yana fad’in “Mai kake cewa Majidad’i... Meye kuka k’ulla min kaida Yazeed..?!”

Giwa ta k’ara so ga Mahmood tana fad’in “Sadauki kada ka yarda da zancen wannan mahaukacin so yake ya raba tsakaninku.. So yake ya tarwatsa ahalinmu shid’in D’anta’adda ne... Kar ka yarda da kalma guda da zai fito daga bakinka....!”

Dariyan da Majidad’i ya fashe dashi ne ya sanyata dakatawa tana mai rakasa da wani irin duba...

Mahmood ya d’an dafata kad’an yana mai furta “Maami Kiyi hak’uri, Ina son jin abinda Majidad’i Ke son fad’i...!”

Majidad’i ya kuma fashewa dariya kana yace “Da kyau Rankaidad’e, ni kuma yanzu zan sanar dakai abinda wannan k’Aramin maras kunyan yaso shirya maka..!” Babu b’ara lokaci Majidad’i ya fad’I duk wani shirinsu da Yazeed a bainar jama’a... Yana ida fad’i ya kuma d’aga takobin zai dab’a masa Jamal ya isa a guje da zummar taimakawa d’anuwansa Yazeed ya janyesa daga wajen dan har lokacin Yazeed zube yake wajen gaban Majidad’i ya kasa koda motsa ‘yar yatsansa sabida hanjin cikinsa da suka gama kad’awa.... Saidai akayi rashin sa’a duk’awan da Jamal zai da niyyar taimakawa d’anuwansa Yazeed Takobin mai d’aukeda guba mai muni ta sauk’a kan k’afar Jamal... Ta yanki Jamal a k’afarsa na dama... Wane irin k’ara ya saki had’ida zubewa wajen yana mai kama k’afarsa... Sara Takobin da Majidad’i zai Dogarai suka sami chance d’in rufe kansa cikin buhu sukai masa caa suka cafkesa, D’angundansa zai arce shima aka capkosa... Tuni aka fice da Jamal neman agaji na gaggawa dan tuni ya had’a gumi sabida tsananin guba da Takobin Ke d’aukedashi, da ace a ciki ko wuya yankan ya samesa tabbas da tuni ya shek’a lahira...
Chapter 66 · 0% Book details