← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 162

Sashe 138

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zahra ta sauk’e huci a hankali tana mai kuma juyowa tana duban Muhibbah dake duk’a gaban Gimbiya Turai cikeda mamaki, ita gani take idan Muhibbah tak’i Paa d’inta sam bata kyauta ba..

Su Zahra suna ficewa Gimbiya Turai ta saka hannayenta biyu ta kamo Muhibbah ta d’agota had’ida zaunarta gefenta, saida Ta bari natsuwa ya d’an kuma sauk’a mata kana Ta soma fad’in “Mahmood shine ya aureki Muhibbah..! Amma ki sani akwai sharad’inmu dashi, sharad’in kuwa shine idan baki so zaa warware wannan aure kafin ai masa nad’i...”

Muhibbah Ta saka hannunta ta goge ragowar hawayenta jiki a sanyaye take duban Gimbiya Turai wacce itama itad’in take duba... Janyota tai cikin jikinta tana shafa bayanta a hankali alamun lallashi...

Suna a haka Hadimar Muhibbah Ta shigo Ta risina, ta mik’a gaisuwarta kana tace “Ki gafarceni Rankidad’e.. Mai Martaba yayo aike.. Kinada sak’on kira daga garesa..”

Zuciyarta yai wani irin tsinkewa, Ta d’ago tana duban Gimbiya Turai.. Jinjina mata kai tai tace “Maza tashi kije, kuma kar kisa wani damuwa ma ranki... Bazan bari wani basarake ya miki dole ba, share hawayenki maza ki tafi ki amsa kiran nasa..!”

Ta mik’e da k’yar tana mai gyara zaman alkyabbarta.. Lokaci guda tasa kai Hadimar tata na biyeda ita..

**

Tinda Ta shigo sashen nasa gabanta Ke tsnananta fad’uwa, tana k’arasowa Barde ya soma mata kirari da jinina yana mai sanar da ita Rankaidad’e yana farfajiyan samansa yana jiran isowarta..
Batareda ta amsashi ba ta haye sama jikinta a matuk’ar sanyaye ga zuciyarta dake ci gaba da bugu...

Yana zaune saman Darduma ta alfarma wanda aka k’awatasa da manyan pillows na alfarma irinta gidajen masu Mulki... Kanta a k’asa take takowa tanajin bugun zuciyarta na k’aruwa lokaci guda tanajin kalaman Ansar suna kuma Yawo a cikin kanta da kunnuwanta suna neman tarwatsa mata kwanyarta... A haka take had’e hanya dan wani irin fuzga takejin zuciyarta na mata... Ji tai kaman wacce ake turata da k’arfin gaske, taji wani irin jiri na k’ok’arin kaita k’asa... K’iris ya rage bata zube k’asa ba sai tsintar kanta da tai cikin hannun Rankaidad’e..
Ta bud’e idanunta tana dubansa, shid’in ita yake duba fuskarsa dab nata kaman tsinin hancinsu zai had’e... Dukda kyaun halitta da k’warjini da fuskarsa nasa kedashi hakan bai hanata tuno abinda yayi mata ba, ya auorta zuwa Masarautar a wulak’ance domin cikar burinsa.. Hawaye suka gangaro mata lokaci guda tana mai kauda fuskarta gefe...

Ya jima sosai yana dubanta cikin hannunsa kafin ya mik’arta tsaye yana tambaya a hankali “Are you hurt..?”

Ba tareda ta dubesa ba ta girgiza kai alamun a’a... Hannunsa guda taji saman nata ya kamo hannun nata ya nufi saman shimfid’ar da ita... Ta dubi hannun nasa yanda ya rik’o nata hannun cikin nasa... Ta kasa janye idanunta har saida yai masu masauk’i saman Dardumar ta alfarma...

Zamansu yai daidai da shigowar wayan Turaki, ya mik’e ya d’an taka kad’an zuwa jikin fence ya bata baya yana amsa wayar wanda bazai shige kan sak’on da ya bawa Turakin bane

Sai lokaci ta sami zarfin d’agowa ta dubesa, sanye yake cikin tufafi irinta masu mulki, Riga da wando na kufta mai ruwan k’asa wanda suka sha kwalliya da surfani mai ruwan zinari, kansa babu hula sai kwantattun sumarsa bak’i wuluk Sai shek’i suke...
Ta kauda fuskarta a hankali tana k’ok’arin nitsa zuciyarta, lokaci guda tana mai kuma aminta da batun Ansar ko kusa kar ta yarda da wannan wulak’antaccen auren,..
Tayi nisa duniyar tunani bama tasan ya k’araso ya zauna ba sai muryarsa ta sinkayo yana furta “I need all your attention here your Highness..” Ya fad’i daga nan yanda yake a kishingid’e yana murza zobban hannunsa...

Ta d’ago ta d’an dubesa hawayen mak’ale cikin idanunta, ji tayi wani irin k’warin gwiwa na zuwa mata dukda wani irin abu da yake fuzgar zuciyarta wanda bazatace ga abin ba...Cikin murya mai rauni had’ida zafin nama take furta “Why your Highness..? Maiyasa..? Sabida kayi amfani dani ka toni asirin Giwa da ‘ya’yanta cikin Masarautar nan shiyasa ka sayoni daga wajen Yawale..? To fulfill your own mission...? Maiyasa ku masu mulki kukeda zalunci..? Maiyasa baku duba buk’atan kowa sai kanku..?! Maiyasa kanku kawai kuka sani..?! Mai yasa baku damu ba who’ll get hurt..? Maiyasa baku damu ba..!”

Mahmood dake murza hannunsa kad’an yana jin kalamanta suna tsananin masa zogi cikin zuciyarsa, cikin wane irin daka tsawa ya katseta da fad’in “Enough..! Ya isheki haka..! You don’t know anything, so you better hold it right there..!” Ya k’arashe yana sakin huci...

Kukan da take rik’ewa ya kufce mata, Ta shiga girgiza kai tana hawaye.. Lokaci guda take furta “This isn’t fair..! It isn’t fair..!” Ta yunk’ura zata mik’e Ta fice cikin sauri rik’eda bakinta wanda kuka ne kawai ciki...Bata ankara ba saiji tai ya fuzgota Ta fad’o cikin jikinsa...
Sosai take kuka tana k’ok’arin cire jikinta daga nasa, bai saketa ba saima dad’a matseta da yayi har saida yai tunanin kar ya karya mata wani k’ashi... Saitin kunnenta yake maganar cikin fuci mai yanayi da rad’a “Ba’a tashi gaban Sarki sai yaba da izini.. You lack manners... Ki koyi yanda zakike magana dani idan har kina son samun amsoshinki... Kin fahimta..?!” Ya k’arashe yana mai sassauta rik’on da yai mata...

Wani k’arfin hali ne taji yana zuwa mata, ta shiga b’anb’are hannun nasa daga cikin jikinta take furta “Ban amince da wannan auren fin k’arfin ba kuma bazan tab’a amincewa ba... Your Highness..!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin cire jikinta... Tsam ya rik’e yatsun hannun nata, yai amfani da d’aya hannunsa ya janyota ta kuma fad’owa cikin jikinsa, hab’arsa ya aza kad’an saman kafad’arta, cikin sigan rad’a yake ci gaba da furta “Haven’t they informed you yet.. Sarki baya saki, idan kika shigo kin shigo kenan.. Prepárate para convertirte en mi reina (Kiyi shirin zama Sarauniyata) Y prepárate para realizar todos los deberes de una mujer casada.” (Sannan kiyi shirin sauk’e duk wani nauyi da ya rataya bisa matar aure)

Bata fahimci kalamansa ba kasancewar cikin harshen spanish yayi, saidai ta tsinta kalmomi da baza’a rasa ba... Tana jin sanda ya sakar mata hannu ba tareda ya kuma bin takanta ba ya koma saman darduman yai zamansa lokaci guda yana mai saka apple cikin bakinsa... Tai tsaye tana mamakin k’arfin hali na wannan Basaraken... Kaman bashi bane ya ida magana ko kallon b’angaren da take bai kumayi ba kaman bashi a wajen...

Kanta a k’asa ta juya ta fice daga wajen wasu hawayen na kuma gangaro mata.. Ba ma kanta take wannan yak’in ba wa Ansar take domin kuwa sam bai cancanci haka ba.. Rankaidad’e k’arfin Mulki kurum ya nuna masa ya samu Baffah Yawale mutum ne mai son duniya shiyasa yai sauk’in shawo kansa, sannan babu riba cikin auren da babu soyayya tinda ba sonta yake ya aurota ne kawai dan wani buk’ata ne nasa... Tana tafe taji ta bangi mutum, ta d’ago tana dubanta ba kowa bace face Raheemah...

Raheemah tai mata K’uri murmushi saman fuskarta lokaci guda take furta “Muhibbah... Ko ince Rankidad’e.. Long time no see.. Kodashike ku matan sarakuna dama da kulle aka sanku..!”

Muhibbah dake tsananin huci tana duban Raheemar bud’e baki tai da niyyan magana Raheema Ta dakatar da ita da fad’in “A’a’a no.. Don’t you dare..! Bakida wani excuse Muhibbah.. Kin tona mana asiri nida Yazeed dan kawai ki mallaki Mahmood ma karan kanki... Good burinki ya cika kin zama matar Yarima Mahmood kuma Sarki mai jiran Gado...!” Ta d’anyi fasali tana mai murmusawa, lokaci guda taci gaba da fad’in “Ashe dai ba ni kad’ai maci amana ba... Ni k’awata naci amana kekuwa amanar soyayya kikaci.. Amanar mutanen da suka zamto fitila ga rayuwarki... How shameful ba’a San jinin babban gida da cin amana ba..!” Ta k’arashe tana yatsina fuska...

Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Koda wasa kar ki kwatanta kanki dani, balle abunda Kika aikata.. Ked’in kinci amanan mahaliccinki ne bayan ya baki amanan kanki, kinga kuwa cikin mu biyun kinfi dacewa da akiraki da maci amana..!”

Dukda kalaman Muhibbah sun mata zafi hakan bai hanata furta “Admit son Mahmood kike.. Ai dama na fad’a tun farkon zuwanki idonki akansa suke...Kin yaudare mutumin da ya shafe shekaru yana dakon soyayyarki... Kin cika butulu Muhibbah..!”

Cikin sauri Muhibbah tasa kai zata shige sabida zuciyarta dake tsananin tafarfasa, Raheemah tai saurin tare gabanta tana furta “Fuskarki ya nuna komai Muhibbah... Idan har bada biyu kika toni asirinmu da Yazeed ba, idan har ba don ki mallaki Mahmood kikayi haka ba, idan har ba don kici amanan masoyinki na gaskiya kikayi haka ba.. Toh kisa Mahmood ya sawwak’e maki kafin ai masa nad’i kafin ayi bukin tarewarku domin kuwa muddin akai masa nad’in sarauta bazai sakeki ba sannan ko da ace ya sakeki zaki k’are rayuwarki ne gidan tsaffin matayen sarakuna bazaki tab’a auren wanda ranki yake so ba. Bazaki tab’a auren masoyinki ba har abada domin kuwa haka k’a’idan sarautar yake..! Idan har kin cika jinin sarauta d’iyar masu mulki, idan har jinin yana Yawo a jijiyoyin jikinki bazaki tab’a zama mayaudariya maci amana ba, idan har kin cika duk abubuwan dana zayyano Yo kiyi proving... ki nuna min ba sabida amfanin kanki kika tozartamu nida Yazeed a idanun duniya ba.. Kiyi abinda ya kamata kafin wa’adi ya cika miki Muhibbah..!” Ta k’arashe tana mai gyara zaman alkyabbanta kana ta nufi b’angaren Yazeed zuciyarta na mata wani irin sanyi, don tasan ko shakka babu kalamanta zasuyi tasiri a zuciyar Muhibbah...

Ga tsananin mamakin Raheema a gark’ame taga k’ofan sashen... Ta dubi wasu bayi dake zaune gefe tai alama wa guda d’aya ya k’araso cikeda risinawa “Yarima Yazeed fah..?!”

Ta tambaya tana dubansa, Bawan yace “Allah taimakeki ai Yazeedu zakice, yanzu bashida maraba damu k’ila mun fisa..”

Raheemah ta katsesa da fad’in “Ba wannan na tambayeka ba.. Shin ina yake..!”

“Tuba nake Rankidad’e, Wato Yazeed dai ya koma b’angaren can..!” Yai mata alama da hannu Ta sashen Bayi..

K’irjinta yai wani bugawa, Ta dubi hannun nasa da mamaki tana mai girgiza kai cikeda shakku take furta “Ban fahimceka ba.. B’angaren Bayi fah kake nuna min..!”

Hadimin ya kuma jinjina kai yace “Haka ne Allah shi taimakeki... Can ya koma b’angaren Bauta da bayi..”
Chapter 138 · 0% Book details