Sashe 28
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya jinjina kansa a hankali yana mai ci gaba da karantar yanayin d’iyar tasa... Har Ta gama had’a masa shayin ta koma mazauninta ta zauna Yarima Mahmood bai daina karantarta ba, yasan dole akwai abinda Ke damunta... Sai yai k’ok’arin danganta hakan da rashin amsar tayinta da Muhibbah batai ba....
Yana son d’iyarsa sosai, a Duniyarsa baison ganin b’acin ranta haka yaita k’ok’arin cheering d’inta, ita kaw Zahra har yanzu wayan dataji mahaifin nata nayi take tinani....
***
Tafe suke hanyar da zai sadaka da b’angaren Yazeed wata kuyanga Ta k’araso cikeda risinawa ta gaidasu kana ta dubi Umaima taceda ita Yarima Fu’ad ke son magana da ita...
Umaima ta d’anyi still tana dubanta kana tace “Ina Yarima Fu’ad d’in yake...?”
Kuyangar Ta kuma sadda kanta kana tace “Yana bayan lambun dake b’angaren sashen Giwa, yana jiranki a cen Rankishi dad’e..!”
Jinjina kai Umaima tai kana tace “Ki sanar dashi Ina zuwa...”
Kuyangar ta jinjina kai cikeda ladabi irinta babban gida had’ida amsawa kana tasa kai ta shige...
Umaima ta dubi Muhibbah kafin tai magana Muhibbah tace “Just go your Highness, ni zan k’arasa sashen Gimbiya Zuhra idan yaso sai ki sameni a cen...!”
Umaima ta jinjina kai murmushi saman fuskarta dan tasan kiran da Fu’ad Ke mata bazai shige akan Muhibbar ba kana tace “Da fatan dai bazaki b’ata a hanya ba...!”
Murmusawa Muhibbah tai kana tace “Tinda ban b’ata cikin duhun dare ba ai ina tinanin banzan b’ace cikin hasken rana ba ranki shi dad’e..!” Suka kuma murmusawa a tare kana Umaima tace “Haka fah... Kinyi gaskiya, I’ll see you later...”
Muhibbah Ta jinjina mata kai kana Ta nufi sashen Yarima Yazeed...
Tana isowa sashen ta tadda Kuyangi daga waje sai risinawa suke suna gaidata, ita kaw taita jinjina masu kai alamun amsawa, a haka Ta nufi cikin gidan...
Shiru ta tadda parlorn saidai tana shiga tai arba da k’atoton hoton Yazeed wanda akai masa daga sama har k’asa yai tsayuwa irinta masu mulki, yana sanye da kaya irinta mulki da sarauta, komai na jikinsa na sarauta ne har zuwa takalmin kufta dake k’afafunsa...
Kansa nad’e cikin Farin rawani mai kunne biyu, idanunsa rufe da bak’ar tabarau wanda ya dad’a fito da hasken fusakarsa, yana sanye da alkyabba fara k’al haka nan hannunsa na dama rik’eda doguwar sanda irinta masu mulki... Kaman ka kirasa ya amsa....Sosai zuciyarta ke tafarfasa tana duban wannan hoto na Yazeed... Ji take kaman ta janyo hoton k’asa tai rugu rugu dashi wala’alla zataji sauk’in zoginda zuciyarta ke mata... Da k’yar Tai k’ok’arin saita kanta kana ta nufi cikin parlorn...
Ganin babu kowa cikin parlorn ya sanyata d’an waige waige... Nan ta hangi hanyar upstairs... Take taji zuciyarta na raya mata ta haura saman... Ta kuma d’an waigawa kana ta nufi hanyar da zai sadaka da upstairs....
A hankali takejin kaman sautin kuka na tashi... Ta kuma kasa kunnuwanta had’ida mak’alewa jikin k’ofar kad’an...
Tana iya sauraro muryar Zuhra cikin kuka tana fad’in “Wlhi Raheema na ga sark’ar buduwar tasa da idanuna kuma a nan cikin drawer na ajiye shine da nai masa yamin wulak’ancin da ko kare bazai ci ba...”
Raheema da k’irjinta Ke tsananin bugu tace “Toh yanzu ina sark’ar...?”
Zuhra ta kuma goge hawayen dake idanunta kana tace “Ya d’auka yana wajenshi.. Na d’aga sark’an ne da niyyan na nuna miki evidence cewa ba sharri nakewa Yazeed ba, wllhi yana cutar dani...!”
Raheema data sauk’e ajiyan zuciya a hankali jin Yazeed ya d’aga sark’ar, kamo hannun Raheema tai kana tace “K’awata you don’t need to show anything for me to believe you K’awata,nasan zaman hak’uri kike da wannan azzalumin mijin naki.. But Zuhra dole haka zaki ci gaba da hak’uri don kare martabarki da na yaranki... Nasan maybe wataran zai kaiki bango da wannan d’abi’u nasa har kiyi tinanin komawa masarautarku, Toh ki sani yin hakan na nufin tonon asirinki ne Zuhra... Kici gaba da hak’uri akan wanda kikeyi... Kuma Ki d’auke idanunki kan abubuwan da mijinki keyi balle ya saka miki wani ciwon kinji koh....!”
Zuhra ta jinjina kai tana mai godiya wa Raheema da kyawawan shawarin da take bata...
A hankali Muhibbah ta nufo downstairs bayan Ta gama jin komai....Daidai tsakiyar stirs ta hangesa tsaye ya kafeta da mayun idanunsa....
SameenaAleeyou 📚
[6/19, 9:22 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*020*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Kallo yake binta dashi daga sama har k’asa, wannan karon sai yafi samun daman k’are mata kallo fiyeda wancan lokacin da yai arba da ita a cikin duhun dare...
Ala dole tai k’ok’arin saita kanta dikda tsananin zogi da zuciyarta Ke mata musamman ganin irin duban da Yarima Yazeed yake mata.... Bazata bari ya zargi wani abu daga gareta ba... Dan haka lokaci guda tai k’ok’arin d’aura murmushi saman fuskarta “Barkada safiya Your Highness...!” Ta fad’i daga nan yanda take tsaye kyakkyawan murmushi saman fuskarta...
Bai amsata ba saima duba na k’urilla da yake mata... Ganin haka ya sanya Muhibbah soma takowa cikin salo na yaudara da d’aukan hankali.... Saida ta k’araso dab kusa da Yazeed kana ta d’an risinar da kanta tana mai furta “Idan Yarima yamin izini zan sauk’a k’asa....!”
Ga tsananin mamakinta karkacewa taga Yazeed yayi yana k’ok’arin bata hanya...
Ta k’araso zata rab’a ta gefensa ta shige dikda tsananin bugu da k’irjinta keyi...
Dab saitin kunnenta dake b’angarensa Ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Looks like destiny wants us together...!” Yai maganan yana mai aika mata wani irin duba shu’umin murmushinsa saman fuskarsa....
Batakaiga Koda motsa ‘yar yatsarta ba Ta kuma jiyo muryarsa yana fad’in “Be careful what you’re getting yourself into... You might get trapped in the middle..!”
Tai saurin d’agowa tana dubansa, shid’inma ita yake duba babu ko alamun gizau a tattaredashi, lokaci guda ya sakar mata wannan murmushin nasa maras kyaun gani... Muhibbah tai saurin kauda fuskanta gefe tana mai ci gaba da tafiya har ta sauk’a k’asa... Sauk’anta Keda wuya Umaima suka shigo tareda yaran Yazeed da dawowarsu kenan daga islamiya....
Noor ta taho da gudu ta rungume Muhibbah tana k’ok’arin biya karatun da Ta koya a islamiya... Shikaw Sultan sakai yai ya shige abinsa ba tareda yabi takansu ba dan dama hakan nan yaron yake ga k’asaita ga miskilanci... Kana ganinsa Kaga jinin sarauta....
Muhibbah ta saci duban upstairs yanda ta bar Yazeed tsaye saidai sam bata hange koda k’yallinsa ba da alama ya shige wane wajen... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali dikda yawo da kalaman Yazeed Keyi a kwanyarta... What if Yazeed ya ganeta ne..? What if ya fahimceta ne... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un! Idan hakan ta kasance ya kenan zatai ita da bata fara komai cikin abinda ya kawota ba... Muryar Umaima ne ya dawo da ita daga duniyar tinaninda ta tafi yanda take sanarda kuyangar dake rik’eda Noor zasu haura sama data sanarwa Gimbiya Zuhra shigowarsu... Kuyangar ta jinjina mata kai cikeda risinawa kana Ta nufi benen rik’eda Noor...
D’an duban Muhibbah Umaima tai Dan Ta lura kaman wani abu na damunta... “Hibbah lafia...? Akwai wani abu ne..?”
K’ok’arin saita kanta Muhibbah tai had’ida girgiza kai kana tace “No babu komai, mai kika gani..?”
Umaima ta d’an murmusa kad’an kana tace “Well, ni inada wani batu da nakeso muyi dake..”
Muhibbah ta d’an zaro idanu waje kana tace “You seems serious... Hope all is well..!”
Umaima ta kuma murmusawa kana tace “K’alau saima alkhairi...!”
Muhibbah Ta d’an kuma yin fari da idanunta kana tace “Now you’re making me nervous... Rankishi dad’e wai meke faruwa ne..?!”
Kashe mata idanu guda Umaima tai kana tace “Idan mun fice a nan zan sanar dake komai in details... Relax K’awata na fad’a maki babu komai sai alkhairi...” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta...
Murmushin yak’e Muhibbar ma tai daidai sanda Zuhura da Raheema suka nufo parlorn...
Raheema na hangosu ta rausayar da idanu had’ida fuzar da huci a hankali, Ta tsani wannan shegiyar Muhibbar, Ta tsani ganinta.. She can’t stand the sight of her... Dafa k’awarta tai a hankali tana mai furtawa cikin sigan rad’a “You take care K’awata... Da dare zan shigo mu k’arasa zancenmu... Ki kwantar da hankalin ki kinji... And think about dik abubuwan da na fad’a miki....!”
Jinjina mata kai Zuhra tai a hankali kana Raheema ta d’agawa Umaima hannu alamun gaisuwa ko takan Muhibbah batabi ba tai ficewarta....
Zuhra ta k’araso garesu da fari’arta tanai masu sannu da zuwa, sai nan nan dasu take gwanin ban tausai, dubanta kurum Muhibbah keyi amma tausayinta ne fal k’asan zuciyarta, shin ya zataji idan taji aminiyarta wacce ta aminta da ita take kawo mata kokenta da dik wani sirri nata da ita mijinta yake cin amanarta... Kai wannan duniya da amana tai k’aranci shin ina zamu kai girman hakki...
Sun jima sosai b’angaren Gimbiya Zuhra Muhibbah na karantarta tsaf, har sai bayan sallan azahar kana suka nufo b’angare Giwa....
Har wannan lokaci Muhibbah dai bata wani saki jikinta ba, sosai kalaman Yazeed ya d’aga mata hankali... Ta yaya ma zata kwantar da hankalinta bayan kalaman da taji suna fita daga bakin Yazeed... Bazata bari Yazeed ya rusa mata dik wani shirinta ba, dole tasan yanda zatai Ta tabbata hankalinsa baikaiga yanda take tinani ba....
Basu samu ganin Giwa ba Jakadiya ta sanar dasu Giwa na sama tana ganawa da yaranta, hakan yasa suka yada zango nan b’angarensu Umaima...
Hango Fu’ad daga k’asan bene da Umaima tai ya sanyata fasa shigewa parlorn dole ta nufo k’asa tana fad’iwa Muhibbah ta jeta tana nan tafe....
Muhibbah ta jinjina kai kana tasa kai kaman zata nufi b’angaren benen da zai sadaka da sashen su Umaima....
K’uri taiwa b’angaren Giwa dan tinda taji ance Giwa na ganawa da yaranta taji tana son jin kan mai suke tattaunawa... Ta d’an waiga gefe da gefe bataga kowa ba, hakan ya bata daman kutsa kai ta nufi sashen matakalan Giwa....