← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 162

Sashe 113

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Can d’akin da ya ganawa Jakadiya azaba suka aje Muhibbah.. Saman kujeran da ya d’aure Jakadiya saman Kujeran ya d’aureta itama, saidai ita d’aurin da ya bada igiya bane kaman yanda yayiwa Jakadiya da handcuffs ya d’aureta yanda ko motsi mai kyau bata iyawa...!
Giwa ta Washe idanu tana duban yarinyar zuciyarta naci gaba da tafarfasa..! Duk itace silan komai, Ta tabbata itace Ta janyo duk halinda suka tsinci kansu cikin Masarautar.... Ta dubi Jakadiya dake tsaye rik’eda ruwa cikin bucket tace “Jakadiya..!”

Jakadiya ta risina tana mai furta “Allah shi taimakeki..!”

Giwa taci gaba da fad’in “shek’a mata ruwan nan ta bud’e idanunta..!!”

Babu musu Jakadiya tayi yanda Giwa tace, ta watsawa Muhibbah ruwan mai matuk’ar sanyi tun daga tsakar kanta har zuwa k’afafunta tana mai furta “Tashi Munafuka..!”

Aiko nan tayi wani irin jan dogon numfashi ta bud’e idanunta da suka mata matuk’ar nauyi da k’yar tana jinta gaba d’aya a tamke...!

A hankali Ta ida ware idanun nata yanda taga Giwa, Jamal da kuma Jakadiya tsartsaye gabanta dukansu Uku sun zuba mata idanu....

SameenaAleeyou📚*MUHIBBAH*

*69*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Cikin tsananin huci Giwa Ke furta “Da kyau..! Da kyau d’ahnah..! Kai d’in ka cika jinina, ka cika min alk’awari ka kawo min wannan ‘yar lek’en asirin har tafin hannuna...!!”

Jamal dake dafe da sandarsa idanunsa naga Muhibbar shima yake furta “Maami I told you so.. Na fad’a miki zan kawo miki ita har yanda kike, ban tab’a disappointing d’inki ba Maami...!”

Giwa ta jinjina kai tace “Ina matuk’ar alfahari dakai...!” Ta kuma duban Muhibbah wacce Ke sakin huci tana dubansu da idanunta wanda tuni sun rikid’e sun koma jazir ga ruwan da Jakadiya ta watsa mata sai faman d’iga yake a fuskarta...
Take Giwa ta soma takowa gabanta cikin tsananin huci, saida ta k’araso har gaban kujerar da Muhibbah ke d’aure bisa kana ta bud’e murya tace “Ke k’aramar alhaki, ki sanar damu waye ya turoki Masarautar nan..! Ma waye kike lek’en asiri cikin Masarautar..?! Wacece Ke..?! Su waye shuwagabanninki..?! Daga wace masarautar kike..?!”Ta k’arashe tana mai kamo hab’ar Muhibbah ta d’ago fuskarta da k’arfin gaske...

Muhibbah bata daina huci ba tana aika ma Giwa kallon k’yama take furta “Maiyasa kike tunanin zan sanar da azzaluma irinki ko wacece ni..?!”

Take Giwa ta d’auketada wani irin jahilin mari wanda saida ya tsaga mata leb’en bakinta jini ya fito... Muhibbah ta rintse idanunta sabida azaba, Giwa zata kuma kai mata wani marin Jamal ya dakarta da ita da fad’in “Haba Maami just mari won’t make her talk, har yanzu ita d’in ji take wata babbar k’waro ce tinda har ta Iya shigowa cikin Masarautar nan ta tashi duk wani bomb data dasa ba tareda wani ya fahimceta ba, har Ta iya Sa k’afa Ta tsallake ta gudu, hakan bai isheta ba ta zabi ta kuma dawowa...! Zaifi kyau idan kika mik’a min ragamar hukuntata, Ina mai tabbatar miki nan bada jimawa ba zata bud’e baki tai magana harda abinda ba’a tambayeta..!”

Giwa na sakin huci take furta “Na baka wuk’a da nama Jamal, kayi mata duk wani nau’i na azaba da kakeda tabbacin zaisa ta bud’e baki ta fad’i ko wacece ita da kuma abinda ya kawota cikin Masarautar nan...!!”

Jamal ya murmusa kana yace “Godiya nake Rankidad’e Giwa, hukuntata zai bani pleasure sabida ta shiga gonata..!” Ya kuma kai dubansaga Jakadiya yace “Jakadiya..!”
Jakadiya ta yada kai tana mai amsawa da “Rankaidad’e..!”

Jamal yaci gaba da fad’in “Ki mik’o min jakan kayan aiki na..!”

Babu musu Jakadiya ta jinjina kai tana mai furta “An gama Rankaidad’e..!”

Jakadiya ta tafi mik’o kit d’in Jamal tana mai furta “Yarinya yau ranar ki ce, bayan bani mayafi da kikayi kika k’ala min sharri banci miki ba ban sha miki ba gashi nan zaki girbi irin ukuban da kika sakani ciki..!!”
Ta k’arashe tana mai aje kit d’in gaban Jamal wanda har lokacin bai janye idanunsa daga kan Muhibbah ba..!

Tsoro da firgici suka cika Muhibbah ganin irin takarcen mugunta da zalunci dake cikin jakan da Jamal yai umarni ta mik’o masa... Tana gani ya soma ciro allurai da wasu k’arrafa saikace wanda zaiyi aikin kanikanci...!
A idonta ya soma had’a wasu ruwan allurai yana zira su cikin doguwar syringe irin wanda ake amfani wa dabbobi dashi.. Ta tina ire iren syringe d’in da suka gani a d’akin da ya rufe Jafar, badai itama tura mata wad’annan ruwan bala’in zai ba.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Abinda zuciyarta Ke iya nanatawa kenan dukda k’irjinta dake tsananin bugu, gashi ko motsi mai kyau bata iya yi dan d’aurin handcuffs Jamal yayi mata, harta k’afafunta suma ya d’aure cikin k’araffa yanda ko kusa bazata iya tunanin guduwa ba... Allah kawai take ambato ya ceceta daga hannun wad’annan azzaluman bayi nasa dan tasan shi kad’ai ne zai ceceta..!

Jamal ya nufota da alluran muguwar murmushi saman fuskarsa..! Girgiza kai Muhibbah take tana hawaye bakinta bai daina ambaton Allah ba..! Giwa kuwa fad’i take “Danna mata alluran Jamal, nace kada ka ragar mata ka danna mata ya shiga tin daga kwanyarta har izuwa k’afafunta..!”

Jamal yai wata murmushi na mugunta yana tsaye gaban Muhibbar yake fad’in “Kinga wannan alluran, Ina miki ita shikenan gab’ob’inki Sun tashi a aiki...! Ban tab’a yiwa kowa irin wannan alluran ba a kanki zanyi lunching d’inta..! Allura ce wacce idan na miki ita shikenan kin koma saidai kallo da idanu, babu wani joint na jikinki da zai kuma motsawa, komai saidai ai miki.. Idan har kika sake allurar nan ta huda jikinki shikenan you’ll be paralyzed for the rest of your life...! So I’ll still ask you nicely... Who are you..?! Wacece Ke...?! Wane ganganci ne ya shigo dake cikin Masarautar nan..?!”

Dukda tsananin tsoron abinda ka iya zuwa yazo gameda ita hakan bai hanata murmusawa ba tana mai furta “I’d definitely tell you who I’m Dark Prince..! Mai kake ci na baka na zuba..!? But before then, kafin na sanar dakai ko ni wacece sai na tabbata rayukan da suke cikin had’ari a Masarautar nan sun kub’uta... Ka fahimta..!”

Jamal bai daina huci ba yake dubanta da tsananin mamaki, rashin tsoronta sosai ya basa mamaki tana a matsayin mace, kodashike abinda tayi ko mazan ma ba kowa ne zai iya kasadan da tayi ba, ta tsallaka ta shigo Masarautar ta kuma shiga jikin ahalin Masarautar ba tareda sun fahimci motive d’inta ba...

Hannu ya d’aga zai kwad’a mata mari sai kuma ya dakata yana murmushi, lokaci guda yace “Kafin ki zuk’i ruwan allurar nan ya kamata a soma cire wasu parts na jikinki dan idan kinyi paralyze abin bazai maki wani ciwo ba, gwara kinaji kina gani da lafiyarki a soma rabaki da wasu sassa na jikinki, zan kuma fara da bakin ki, I’ll cut off your tongue sai muga da bakin da zakiyi tsaurin ido...!” Ya k’arashe yana ciro wasu k’araffa cikin akwatin nasa...

Giwa ta katsesa da fad’in “Ai idan ka yanke harshenta bazamuji mai ya kawota ba, ka dai soma da wasu sassa na jikinta kaman yatsun hannayenta zuwa k’afafunta, na tabbata idan taji zogi da azaba zata yi magana..!”

Jamal ya jinjina kai yace “Zan iya farawa da murafen kunnuwanta Ta yanda zataji abinda zamu sanar da ita da kyau...!” Ya k’arashe yana ciro wasu k’araffan...

Zuciyar Muhibbah bata daina tsinkewa ba ganin da gaske wannan mugun yanka sassan jikinta yakeda niyya... Allah kawai take ambato had’ida kauda fuskarta gefe, ta tamke idanunta sosai zuciyarta naci gaba da tsananin bugu tana jira taji ya kama marfin kunnenta guda kaman yanda yace....
Kaman daga sama wayar salulansa ta soma ringing.. Aje k’araffan yayi ya soma k’ok’arin lalumo wayarsa cikin aljihun wandonsa, number ce mai kiran nasa, yana d’agawa aka sanar dashi halinda Yazeed da kuma ahalinsa Ke ciki a asibiti...!

Zuciyar Jamal ya tsinke, ya d’ago yana duban Giwa... Ganin irin duban da yake mata ya sanyata maida hankalinta kacaukam garesa tana tambayarsa meke faruwa...

Hankali tashe Jamal Ke sanar da ita abinda aka sanar dashi a wayar... Take jikin Giwa ya d’auki rawa, cikin yanayi na tashin hankali take furta “Yazeed..! Yazeed.. Yazeed d’ah nah, zanje na gansa yanzun nan... Ina son ganinsa...!” Bata kuma tsayawa bi takan kowa ba Ta nufi k’ofa hankali tashe...
Tuni Jakadiya ta take mata baya, Shiko Jamal duban Muhibbah yayi yace “Allah ya ceceki for now, amma ki sani ina nan dawowa, sai kin d’and’ani azabata..! No one messes with me...!!”

Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice yana cangwala sandarsa...

Muhibbah da hawaye Ke zubo mata sauk’e ajiyan zuciya tayi wasu hawayen na muma kwaranyo mata, ta soma jijjiga kujeran ko Allah zaisa cuffs d’in su b’alle.. Inaa ko gizau batayi, wasu hawaye masu d’umi suka kuma zubo mata... Toh kenan basu ne suka ajeta wancan d’akin ba... Kenan babu saka hannunsu a dawowarta Masarautar..! Toh waye ya dawo da ita idan har ba Giwa bace ba kuma d’aya daga cikin azzaluman yaranta bane..?! Tambayar da zuciyarta tai mata... Toh amma taga Yarima Mahmood a wannan d’akin da aka ajeta..! Toh mai ya kaisa d’akin..? Kodai shine ya satota..? Toh amma mai zaisa ya sato ta ya dawo da ita cikin Masarautar ranan aurenta idan dai har baiyi tarayya dasu Giwa wajen yunk’urin cutar da ita ba... Shin waye zai iya warware mata k’ullin dake cikin kwanyarta..?! Ta kuma lumshe idanunta a hankali wasu hawayen suka gangaro mata, tasan duk yanda akayi Mommy da Ansar suna can suna nemanta, ta sani hankulansu ba’a kwance yake ba kaman yanda nata ma bai kwance... Allah taci gaba da ambato domin ya kawo mata d’aukin halinda Ta tsinci kanta ciki....

**
Chapter 113 · 0% Book details