← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 162

Sashe 21

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cen ya hangota tak’ure ta kifa kanta da gwiwa tana cazgan kuka....
Tsaye yai yana dubanta cikeda tausayawa.... A duniyarsa baison yaga mace na kuka irin haka koda kuwa baiwace ba d’iya ba, harga Allah yakanji babu dad’i cikin zuciyarsa... A hankali yaci gaba da takowa zuwa gareta, saida ya k’araso har yanda take kana yai sallama cikin muryarsa mai cikeda aminci....

D’if kukan nata ya d’auke tamkar anyi ruwa an d’auke, dikda k’irjinta dake bugawa a hankali hakan bai hanata k’ok’arin saita kanta ba.... Tai saurin gogewa hawayen fuskarta had’ida d’agowa... A karo na farko da sukai eye contact tin bayan dawowarta Masarautar....

Yau Yarima Mahmood ne tsaye a gabanta, tabbas abubuwan da suka faru wancan lokacin sun shiga dawo mata daki daki, saidai ya zama dole tai k’ok’arin saita kanta ta tattaro duka jarumtarta ta had’e waje guda...
Ta k’ak’aro murmushi a hankali kana ta mik’e tsaye tana mai gyara mayafinta..
“Barka da dare Rankashi dad’e..!” Tai maganar tana mai duban k’Asa...

Yarima Mahmood da har lokacin hannayensa Ke hard’e ta baya jinjina mata kai yai a hankali kana yace “Barkanki...! Ke kuwa mai kikeyi a nan cikin daren nan.....?”

Ta d’an saci dubansa jin tambayar da ya jefo mata kana Ta kuma k’ak’aro murmushi tace “Babu komai rankashi dad’e ni bak’uwa ce a Masarautar... I guess rashin sabo da wajene yasa bacci ya k’aurace min shisa na fito nan na zauna....!” Ta k’arashe tana wasa da ‘yan yatsun hannunta....

Jinjina kansa yai a hankali kana yace “Shiyasa kike kuka...? Ko kinsan sautin kukanki ka iya hana wasu halittu samun nitsatsen bacci cikin Masarautar nan...?”

Wannan karon d’agowa tai tana dubansa sosai kana ta d’an kauda fuskarta gefe....

Ganin tayi shiru babu amsa yasa Yarima Mahmood gyara tsayuwarsa had’ida d’aga kansa sama kad’an....

“Bakiyi kamanni da bayi ba... Shin wacece Ke...?!” Ya k’arashe yana mai sauk’e idanunsa akanta da alamun tuhuma...

Ji tai wani abu ya tokare mata mak’oshi, tai k’ok’arin daidaita natsuwarta
“Bak’uwar Umaima ce ni Rankashi dad’e....!” Tai maganar tana mai sadda kanta k’asa...

Sosai ya kaikaito wannan karon yana dubanta tamkar wanda ya tina wani abu kana yace “Muhibbah..?!”

Ta d’ago itama tana dubansa, lokaci guda ta sami kanta tana mai jinjina masa kai alamun eh....

Yarima Mahmood ya gyara tsayuwarsa kana yace “It was you then...Kece wacce kika taimaki d’iyata Zahra...”

Taji murmushi na zuwa saman fuskarta kana tace “Nayi abinda ya kamata ne your highness...!”

Tinda suka soma magana sai yanzu ya sinkayo wani zak’i cikin muryar nata bayan ya ambaci Zahra....

Yai murmushi for the first time tin bayan had’uwarsu a nan wajen... Lokaci guda kuma ya d’aure fuska kaman wanda ya tina wani abu... Ita kaw Muhibbah zuciyarta sai ci gaba da tabbatar mata take, tabbas weakness d’in Yarima Mahmood d’iyarsa Zahra ce, hanyar da zata sami yardarsa kenan shine ta shiga jikin d’iyarsa sosai... Muryarsa ne ya katse mata tinanin nata
“Kin min laifi...!”

Ta d’an d’ago da alamun firgici wannan karon kana tace “Laifi kuma Rankashi dad’e...?!”

SameenaAleeyou 📚
[6/8, 8:31 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*016*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Yarima Mahmood ya jinjina kai kana yace “K’warai kuwa... Kinmin laifi...”
D’an sadda kanta ta kumayi kana tace “Dikda bansan laifin ba, tuba nake Rankashi dad’e...!” Cikeda risinawa tai maganar...

Ya d’an gyara tsayuwarsa a karo na UKU had’ida yin gyaran murya kad’an “Baki San laifin ba....?”
Ta d’ago kad’an tana duban fuskarsa da security light ya haske tarau... Lokaci guda ta kuma maida nata fuskar k’asa tana mai furta “Tuba nike Rankashi dad’e...!” Yanda tai maganar sai yai masa tamkar ya tab’a sanin mai irin wannan muryar shekaru da jimawa...
Ya d’an d’auke idanunsa daga dubanta kana yace “Umaima bata sanar dake sak’o na ba...?!”

Sai yanzu ta tina ashe fah Wai tin jiya Umaima ta sanar da ita Yarima Mahmood na kiranta... Ta d’an daburce kad’an kai kace har cikin zuciyarta hakan ne kana tace “Allah ya huci zuciyarka Rankashi dad’e...!”

“Baki amsa min tambayata ba... Sannan cikinku waye zan hukunta Ke ko Umaima...?!” Ya k’arashe Murya a dake...
Dubansa kad’an tai kana ta shiga girgiza kai a hankali “Ta sanar dani Rankashi dad’e... A gafarceni laifin nawa ne... And please kar a hukunta Umaima batada laifi... !”

Bai amsata ba sai jefo mata tambaya da yai.. “Kinada alak’a da gidan sarauta ne...?”
Taji tambayar a bazata...
Gyara tsayuwarta ta d’anyi alamun gajiya da tsayuwa kana tace “A’a Rankashi dad’e wannan shine karona na farko a gidan Sarauta...!”

Ya jinjina kai a hankali yana jinjina d’abi’u irinta babban gida da take dashi, lokaci guda yana karantar ta da alama ta soma gajiya da tsayuwar..
Shiru ya gifta tsakaninsu har kaman babu mai yin magana cikinsu kana Yarima Mahmood yace “Baki sanar dani ba.. Kukan mai kike a nan...?”

Ta k’ak’aro murmushi kana tace “Kewar gida nake Rankashi dad’e... Kaifa mai ya fito dakai cikin daren nan....?!”
Saida tai tambayar sai kuma taga rashin dacewar tambayar tata, musamman da ta hangi irin duban mamakin da yake mata...
Lokaci guda ta kuma risinawa tana mai furta “Tuba nake Rankashi dad’e... A gafarceni....!”
Yanda tai maganan ya sanayasa sakin k’asaitaccen murmushi a hankali kana yace “Na kasa bacci ne kaman yanda kema kika kasa....”

Mamaki ya cikata ganin ya amsata Kai tsaye, Ta d’an jinjina kai a hankali kana tace “Kai hak’uri Rankashi dad’e, not being nosy, har kuma masu mulki kunada damuwar da take hanaku bacci....?”

Dariya taso basa wannan karon jin kalamanta tamkar ta k’aramar yarinya, saikace Zahra ce tai maganar...
Gyaran murya ya kumayi kad’an bayan ya murmusa a tak’aice kana ya isa gefen dakali ya d’an zauna...
Ganin tai tsaye wajen ya sanyashi nuna mata d’aya dakalin dake gefe kana yace “Bismillah..!”
Babu musu ta isa ta zauna...

Mahmood yaci gaba da fad’in “Baki San masu mulki sukeda damuwa ba... Shin baki San duk wanda Allah ya jarabcesa da jagoranci wasu Al’umma ya d’aura masa babban nauyi bane...? Ta yaya shugaba zaiyi bacci hankalinsa kwance bayan baisan halinda d’aukacin al’ummarsa suka kwana ba..?”
Tai shiru ba tareda ta iya amsa masa tambayar ba...
Yarima Mahmood ya jinjina kansa kana yace “Dik yanda bawa yakai da samun wani d’an Kaso na mulki daga cikin mulkin duniya da Allah ke rabawa tsakanin bayinsa bazai tsallake matsaloli na rayuwa ba... In one way or the other dole yanada matsalarsa... Cikan d’an adam kenan...!”

Tai shiru tana jinjina kalamansa lokaci guda tana jin natsuwa na sauk’ar mata cikin zuciyarta a hankali... Sai takejin kaman she’s safe around him....
Lokaci guda taga ya mik’e hannayensa hard’e Ta baya kana yace “Kije kwanta dare yaja sosai, kokuma Ki tausashi zuciyarki da ambaton mahaliccinki, zaki samu natsuwa a cikin yin hakan....!”
Daga haka bai kuma cewa komai ba sai sa kai da yai ya soma takawa a hankali....

Muhibbah tabi bayansa da kallo tamkar mai tinanin wani abu.... Cikin sauri ta mik’e tabi bayansa kana tace “Rankashi dad’e.... Na gode....!”

Bai juyo ya dubeta ba saima sa kai da yai yaci gaba da tafiya...
Muhibbah tabi bayansa da muguwar kallo cikeda tsana da k’yama har ya b’acewa ganinta, lokaci guda hawaye na kuma gangaro mata... Tasa bayan hannunta tana goge hawayen da suka wanke mata fuska... Zuciyarta naci gaba da mata zogi.... Lokaci guda kuma ta tsinci kanta tana mai bin shawarin Yarima Mahmood, Ta nufi d’aki ta d’auro alwala kana ta fito ta tada sallah kaman yanda ya bata shawarin yin hakan..
**

Washe gari Ta kama juma’a babban rana, sannan a wannan ranan Muhibbah ta sami ganawa da Giwa tun bayan zuwanta Masarautar... Wani ikon Allah had’uwa ta farko da Giwa da Muhibbah sukai Allah ya jefa k’aunar Muhibbah cikin zuciyar Giwa... K’awayen Umaima sunsha zuwa Masarautar amma bata tab’a gamo da wacce jininsu yazo d’aya irin Muhibbah ba, har tambayarta take gameda rayuwarta musamman da taji makaranta ya kawota garin...

Giwa ta kuma gyarawa daga kishingid’en da take tana duban Muhibbah dake risine gabanta a k’asa kana tace “Kikace ke ‘yar asalin garin Bauchi ne...?”

Muhibbah ta jinjina kai kana tace “Eh Allah shi taimakeki, ni ‘yar asalin garin Giad’e ne dake nan jihar Bauchi amma cikin Bauchi muke zama, mahaifina Alhaji Iro Datti ya kwana biyu da rasuwa....” Ta k’arashe cikeda girmamawa...

Giwa ta jinina Kai tana mai furta “Allah sarki ashe ked’in Marainiya ce... Toh ki saki jikinki kinji koh domin kaw kinzo gidan goya marayu... Ki zauna a Masarautar nan har iyaka lokacinda zaki kammala karatunki kinji koh...!”

Muhibbah Ta d’ago cikeda jin dad’i tana duban Giwa dake ci gaba da sakin murmushi a hankali kana tace “Godiya nake Rankishi dad’e... Na gode na gode K’warai Allah ya k’ara girma...!”

Giwa ta girgiza kai a hankali murmushi bai bar saman fuskarta ba take ci gaba da fad’in “Babu komai Muhibbah ki saki jikinki tamkar Umaima nan gidanku ne kinji koh...!”
Muhibbah Ta kuma risinawa tana godiya yayinda Umaima Ke tayata godiyan cikeda jin dad’i...
Har Giwa tai masu izinin ficewa Jakadiya bata daina jifarsu da muguwar kallo ba...

Suna fita Jakadiya Ta gyara zama tana duban Giwa “Allah shi taimakeki anya baki gaggawan maraba da wannan yarinyar ba, bansan dalili ba amma sam bata kwanta min ba....Allah shi baki yawan rai a duba lamarin...!”

“Jakadiya yaushe kika fara samun ra’ayin kanki a gidan nan banida labari”Giwa tace tana mai aikata mata wulak’antaccen kallo...

Jakadiya yada kai k’asa tana neman afuwa da tuba...

K’asaitaccen murmushi saman fuskar Giwa kana taci gaba da fad’in “Jakadiya kenan... Kaman baki san ko ni wacece ba har yanzu... Duk abinda nayi Jakadiya yanada manufansa... Kin tab’a tambayata Maiyasa dik abinda Umaima zatayi ko zatazo dashi cikin Masarautar nan bana dakatar da ita...?!”
Chapter 21 · 0% Book details