← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 162

Sashe 104

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda Zuhra ta koma sashenta rungume yaranta tayi tana kuka sosai, sai kuma taji sam bata kyauta ba... Komin yaya ne halin Yazeed he’s still her children’s Father, Ji take kaman Ta muzanta yaranta ne a idon duniya... Gaba d’aya sai tausayin yaran nata ya rufe ta... Tana kuka ta rungumesu sosai tana furta su yafe mata dukda cewa yaran bama su fahimci nufinta ba sudai kawai sunga mahaifiyarsu na kuka sosai... Ta macen tasa hannu tana sharewa mamarta hawaye suna masu ci gaba da bata hak’uri....

Hadimarta Ta K’araso ta risina tace “Rankidad’e an gama shirya kayyakin gaba d’aya...!”

Zuhra ta jinjina kai tana mai k’ok’arin saita kanta tace “Ki sauk’o da kayan k’asa gobe idan Allah ya kaimu fitan sassafe zamuyi...!”

Hadimar ta jinjina kai had’ida risinawa tana mai amsawa... Sultan ya dubi nahaifiyarsa yace “Momy tafiya zamuyi..? Ina zamuje..? Ba’ayi hutun sch ba..!”

Ta k’ak’aro murmushin k’arfin hali ta shafi kan yaron tace “Masarautar su Deedah zamuje baka so..?!”

Jin an ambaci Deedah kakarsa sai ya soma murna yana cewa eh yana son zuwa...! Suna a haka Yazeed ya shigo tagajan magajan tamkar wanda aka jefosa... Sultan ya tafi ga mahaifinsa da gudu yana fad’in “Daddy zamu tafi Masarautar su Deedah kaima zaka bimu...?”

Baki sake Yazeed Ke duban yaron cikin rashin yarda da abinda yakeji daga bakin yaron, ya dubi Zuhra wacce tai kaman bata San yana wajen... Bai ida mamaki ba saida ya hango Kuyangar taba sauk’owa da suitcases nik’i nik’i...

Ya kuma maida dubansaga Zuhra wacce Ke k’ok’arin mik’ewa... Tamkar zautacce ya isa gareta yana fad’in “Can you tell me what’s the meaning of this..?!”

Zuhra ta bud’e murya ta kirawo Hadimar tace ta haura da yaran upstairs..

Babu musu Hadimar ta k’araso ta risina ta gaida Yazeed Wanda ko kallo bata ishesa ba kana Ta janye yaran suka haura sama...

Zuhra tasa kai kaman zata shige Yazeed yai saurin rik’ota da k’arfin gaske yana sakin huci yake fad’in “I think I asked you a question..?!”

Murmushi tai wanda kai tsaye za’a iya cewa na takaici ne kana tace “Abinda idanunka ya gane maka Toh haka ne..!”

“I’m still your husband Zuhra..! You’re not going anywhere.. Dan haka ki cire ranki... Kina nan a Masarautar nan tareda ni da yaranmu... Bazan tab’a barinki ki tarwatsa ahalinmu ba... Sultan zai gaji sarautar wannan masarauta dan haka bazan barki ki b’ata min shirina ba kin fahimta..!” Ya k’arashe yana sakin huci...

Wulak’antaccen kallo take aika masa kana tace “Wane ahali kake magana..?! Ahalin da ka riga ka gama tarwatsawa.. Tausayin yarana nake ace sunada Uba irinka.. Shiyasa sam bazan barsu su girma cikin wannan Masarautar ba wanda koba jima ko ba dad’e sai an goranta masu halin mahaifinsu da abun kunyar da ya jawo masu..! Yazeed ka mance da batun aurenmu dan ka sami wacce zata maye gurbina a yanzu, yarana kuma bazan barsu hannun azzalumar matarka ba dan bansan wane irin tarbiya Zata basu ba, idan sun girma sun mallaki hankalin kansu zasu iya dawowa Masarautar mahaifinsu amma ba yanzu ba... A halin yanzu yarana ni sukeda buk’ata bakai ba...!” Tana ida fad’in haka tasa kai zata shige...

Yazeed yai saurin shan gabanta yana mai ci gaba da huci... Sallaman mutane ne da suka sinkaya daga k’ofar Parlorn ya karkata hankalinsu....

Tawagan ‘yan rakiyar Amarya Raheema ne suka rakota sashen angonta....
Zuhra tana ganinsu Ta saki murmushi mai kyau kana Ta maidoda dubantaga Yazeed tace “Looks like your bride is here already, Allah bada zaman Lafiya ya kad’e fitina..!”
Ta kuma sakar masa murmushi tayi hayewarta sama ya barsu...
Shi kuwa Yazeed dafe da kunkuminsa yake dubansu...
Baiko bi takansu ba yayi ficewarsa... Can spot d’insu ya tafi dan gaba d’aya ji yake duniyar na juya masa, da ace zai sami sararin yin kuka da yayi ko zai d’an ji sanyi cikin zuciyarsa... Haka ya dinga d’irkawa cikin barasa babuji babu gani a tinaninsa hakan ne kawai zaisa ya sami sauk’in abinda yakeji cikin zuciyarsa....
Tin ma’aikatan club d’in na d’aukan abin kaman wasa hardai sukaga abin ya zarce tunaninsu gashi yau d’in babu abokan Yazeed ko guda da suka je, haka dole guda d’aya daga cikin ma’aikatan ya d’aga waya ya kirawo Zayyad ya sanar dashi halinda Yazeed ke ciki... Babu shiri Zayyad ya k’araso ya tadda Yazeed sai layi yake yana sunbatu ma’aikatan club d’in sun hanasa fita bai biyasu kud’i ba... Yazeed ya cakumo guy d’in yana fad’i cikin murya irinta ‘yan maye “Kasan ko ni wanene...! Kasan ko ni wanene da har zaka hana ni fita...? I’m Prince Yazeed AbdulJabbar..! I can buy the whole club including you yourself..!” Ya k’arashe yana mai kuma shak’e masa wuya...

Da k’yar Zayyad ya b’anb’are mutumin hannun Yazeed ya ciro kud’i ya biya bashin da ake bin Yazeed d’in kana ya shiga janyosa yana fad’in su tafi, Yazeed d’in sai tarjewa yake yana sunbatu yana amo da bak’in cikinsa...

Har cikin Masarauta Zayyad ya kawosa a haka, yana shiga sashensa yaci karo da Raheemah cikin d’akinsa saman gadonsa ta baje tana shek’a bacci... Da tangad’i ya isa gareta ya k’ura mata idanu, baice komai ba ya nufi closet ya zaro belt ya nannad’e cikin hannunsa, Raheema da san bataji shigowar mutum ba sai sauk’ar bulala taji cikin jikinta, ta kwand’ara ihu ta mik’e tana fad’in kwarankwatsa ya fad’o mata...

Yazeed yace “Bai fad’o maki ba tukuna somin tab’i ne wannan.... Uban wa ya baki izinin d’ale min kan gado..?!”

Raheemah na hawaye take furta “Yazeed Ina zanje fisabilillahi, Aunty Zeenat ta koroni daga sashenta tace tinda Bazan zama matar Sarki Mahmood ba zamana wajenta baida amfani tace dole na tafi d’akin mijina na bar mata sashenta..!”

Yazeed ya tintsire da dariya yana nunata da belt belt d’in yake fad’in “Itama tasan bakida amfani kenan tinda baki auri Mahmood ba... Toh haka nima babu amfanin da zaki min tinda kika kasa cika min burina na auren Mahmood... Da yanzu kin auri Mahmood da na zama Sarki amma sabida dolanci irin Naki kika bari Zuhra tabi bayanki har Ta gano ina kike zuwa...!”

Cikin kuka Raheema ke girgiza kai alamun a’a tana fad’in “Wllhi Allah ban San Zuhra zataje wajen nan ba, kaima kasan nafi kowa yin taka tsan tsan... The whole thing affects me more, na rasa Aminiyata na rasa masoyina Mahmood, wllhi ji nake rayuwar gaba d’aya ta fice raina..!”

Yazeed yace “Munafuka rufe mun baki... Duk kece kika janyo halinda na tsinci kaina ciki, kuma yanzu basai anjima ba zaki fara nadaman aurena da kikayi..!” Yana kaiwa nan ya shiga janyota tana tarjewa tana fad’in mai zai mata.... Ko amsata baiba saida ya d’auko sellotape d’in da yake manne bakin Zuhra dashi idan zai jibgeta danma kar tayi ihu aji... Haka Raheema tana ji tana gani tana zaro idanu waje cikeda mamakin abinda Yazeed ke k’ok’arin yi... “Yazeed no...What are you doing..? Please no..!” Inaa ko saurarenta baiba ya manne bakinta da sellotape d’in ya kuma janyota ya d’aure jikin gado ya shiga jibganta tamkar wanda aka turosa, baiji bai gani dukan Raheemah yake tana runtse idanunta masu zuban hawaye babu hali tayi ihu dan bakinta a rufe yake... Duk wani takaici da bak’in cikin da Yazeed ke ciki akan Raheema ya sauk’esu tass da bugu... Saida yaga kaman numfashinta na neman d’aukewa kana ya sarara mata da bugu .. Yana nunata da bulalar yake fad’in “A nan zaki kwana a d’aure kuma babu mai shigowa balle ya ceceki...

**

A b’angaren Muhibbah kuwa sosai taci kuka har Ta gode Allah, tayi tunanin tashi ta gabatar da salloli ko zata sami sauk’in halinda ta tsinci kanta ciki amma sai taci karo da al’adarta tazo mata... Tai saurin mik’ewa tana duba bayan skirt d’inta yanda yayi stain... Ga dare gashi bama tasan ya za’ai ta sami sanitary pads ba, gashi Kuyangin duk basa nan... Ta isa k’ofa tana bubbugawa ko za’ajita amma shiru alamun babu kowa gajeren tsaki tayi Ta komo cikin d’akin tana tinanin abinyi... Closet ta bud’e yanda taga kayyaki ne na alfarma jere cikin closet d’in na kwalliyan mata amma saidai babu alamun sanitary pad a wajen... Ta d’an tab’e baki kad’an ta nufi bathroom d’in dan dole tayo wanka a halinda ta tsinci kanta ciki....

Komai na band’akin abin burgewa ne, ga wani ni’imtaccen k’amshi da yake tashi... Harda Sabon toothbrush da toothpaste aje saman sink Wato dai duk an aje mata kenan, ko wane salo Giwa tazo dashi kuma yanzu oho...
Can sama da jacuzzi ta hango k’aton tambarin heart mai furanni ciki an rubuta M&A... Taita nanatawa cikin zuciyarta M&A ko mai hakan yake nufi oho... Batayi using ruwan k’amshin da aka had’a mata ba Sabida yanayin da take ciki, koma bata a wannan yanayin bazata shiga ruwan da bata San wane tsidsabaru bane Giwa ta saka mata ciki... Wa ya sani ma ko ta haka zatai mata nata kisan gillan, ta nufi cubicle dake gefe nan cikin bathroom d’in abinta ta sakar ma kanta shower.... Tana jin ruwa mai d’umin na ratsa cikin kanta da jikinta hawaye na kuma gangaro mata... Ansar kurum take hangowa tasan duk yanda yake yanzu hankalinsa yakai k’ololuwa wajen tashi... A daidai lokacin da take wannan tunani tana hawaye Ansar yana can gadon asibiti yasha drip guda an d’aura masa na biyu yana kuma sha...

Mommy da Hameedah zaune gefensa an rasa mai lallashin wani cikinsu....

**
Da mamaki Turaki yake bin wayar nasa da kallo, k’arfe shabiyun dare har ta gauta... Allah yasa yana parlor yana kallo bai shige d’aki ba tukuna... Ya d’aga wayar Rankaidad’e suna gaisawa , daga d’aya b’angaren Mahmood yace “Sanitary pads nake so...!”

Turaki ya gyara zama yana nanatawa “Cikin daren nan Rankaidad’e...?!”

Mahmood ya jinjina masa kai yace “Eh cikin daren nan...!”

Turaki yace “Amma Rankaidad’e baza’a bari zuwa safiya ba...?!”

Cikeda k’osawa Mahmood yace “It can’t wait till morning... Yanzu nake so..!”

Turaki ya murmusa kad’an yace “Toh an gama Rankaidad’e..!” Mik’ewa yayi ya zari car keys d’insa ya tsaya a manyan store’s da yasan zai samesu a bud’e komin daren, ya saya ya nufi Fada dashi....
Chapter 104 · 0% Book details