← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 162

Sashe 103

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zobban dake hannunsa yake murzawa a hankali yana mai furtawa a fili “Whatever you’re hiding nasan dole zai fito... Sannu a hankali zan fahimci wacece Ke da kuma abinda kike b’oyewa...!!” Yai shiru yana nanata kalamanta ga Baiwar _Ni Amarya ce ki taimaka ki fitar dani, mijina na can yana nemana... kasheni zasuyi.._
Kalmar zasu kasheni data fad’i yaketa nanatawa, kenan tabbas akwai wani k’ulli da take dashi cikin Masarautar.. Ko menene wannan k’ullin... Sannu a hankali zai fahimci haka.. Ya k’arashe tunanin nasa yana mai warware zanen ginin gidan sarauta da ya samu a hannunta... Lokaci guda yake kuma karantar zanen...
A hankali ya mik’e ya fito sararin waje daga nan saman benen nasa yana k’arewa fad’in Masarautar kallo...

Can ya hangi motoci ‘yan kawo Amarya Raheema suna tururuwar shigowa... Ya saki murmushi da gefen bakinsa a hankali kana ya nad’e hannayensa ta baya yana mai kallon yanda motocin Ke shigowa sahu sahu...

Yana ganin aka fito da Raheema rufe cikin Alkyabba aka nufi b’angaren Giwa da ita.. Bai kuma bi takansu ba sai ma sauk’owa parlornsa na k’asa da yayi ya kunna labaru...

**

A can Fadar Giwa kaw ana tsaka da bukin al’ada Amarya Umaima na tsakiya an rufa mata alkyabba ana raye raye da kid’i kid’i kaman yanda yake a al’adarsu ranan d’aurin aure akanyi irin wannan bukiga amarya kwatsam sukaji isowar su Raheema da masu kawota...dama tuni labari ya iso masu cewa auren Yazeed da Raheema aka d’aura... Hankalin Giwa da Waziri idan yayi dubu ya tashi dukda k’ok’arin danne hakan da Giwa take dan a halin yanzu abubuwan dake kanta sun sha k’arfinta k’iris ya rage su tarwatsa mata kwanya, ga takaicin shikenan shirinsu na d’aura alhakin mutuwar Mahmood kan Raheema da Zeenatu ya tashi a aiki tinda ba’ayi auren da Mahmood d’in ba, Gashi tinda abin ya faru ko idanun Mahmood basu gani ba dan su duk a nasu zaton shima can wajen Auren Raheemar ya tafi hakan yasa Giwa bata ko yi tunanin nemansa ba... Har sai yanzu da aka shigo mata da Raheema matsayin matar Yazeed..! Yanzu ne suke kuma tabbatarwa Yazeed aka aurawa Raheemah ba Mahmood ba.. Tirk’ashi..!

Kuka sosai Raheemah take cikin dandatson taron ‘yan biki tana fad’in itafah sai an canza wannan aure an maida kan Sarki Mahmood... Ita ba Yarima Yazeed bane mijinta...Gimbiya Zeenat na gefenta tana lallashinta...

Abinka da gidan biki cike gidan yake da ‘yanuwa da abokan arziki dikda cewa sabida tsaban mugun hali irin na Giwa bata cika tara mutane ba amma an cika kam abinda da gida na sarauta...
Matayen masu madafan ikon cikin Masarautar duk suna nan, kama daga matan Waziri Galadima Matawalle Liman Sardauna da dai sauransu duk Sun hallara a Fadar Giwan dashike yau d’in ranan shagalin buki ne

Giwa ta dubi tawagan ‘yan tawagan kawo Amarya tace “Ku kwantar da hankalinku za’ai komai a tsanake irinta babban Gida...!”

Muryar Zuhra ne kaman daga sama suka sinkayo tana fad’in “Ina girma a gidan da babu wani Girma..!”

Gaba d’aya kallo ya dawo kan Zuhra harta Giwa saida ta kaikaito tana duban Zuhra dake K’arasowa cikin Fadar...!

Zuhra ta K’araso tsakiyan taron ta isa har gaban Raheemah... Gimbiya Zeenat na k’iftawa Zuhra idanu kan tayi shiru amma inaa ko kallo bata ishi Zuhra ba...

Zuhra ta tsaya sosai gaban Raheemah.. Ta saka hannu ta d’aga alkyabbar da aka rufa mata, fuskarta ya bayyana.... Murmushi Zuhra ta saki kana tace “K’awata ko ince kishiyata...Haba Amarya miye na d’aga jijiyar wuya kan cewa sai an canza aure ya koma kan Mai Martaba Sarki Mahmood..? Karfa ki mance kowa da daidanshi Allah yake had’asa kuma shi Sarki taimakonku kawai yayi ya rufa maku asiri gashi Ke kina neman tonawa kanku asiri..!”

Gimbiya Zeenat ta katseta da fad’in “Ke Zuhra ya kike abu kaman ba d’iyar manyan mutane ba... Kaman ba jinin sarauta ba...!”

Zuhra ta murmusa tace “Tuba nake Rankidad’e..! A gafarceni amma gaskiya nake fad’i... kuma Ita wacce aka d’aurama auren ta fini sanin gaskiya nake fad’i..!”
Ta juyo tana duban Raheema da Hawaye Ke kuma gangaro mata tace “Da bakiyi bore kin tonawa kanku asiri ba kika bar abin a rufe kaman yanda Sarki mai adalci da halin Dattako yayi maku abin a sutirce da ya fi miki... Amma kika zab’i Ki tona kanku.. Toh nidai babu abinda zance saidai nace Allah ya bada zaman hak’uri dan idan a baya anyi zaman sharholiya da shagala yanzu kam saidai Ayi hak’uri... Ayita hak’uri da juna ana kai zuciya nesa dan shi maci mana baya fasa hali.. Sai ki gani ki kauda kai kiji kiyi kaman bakiji ba shawarita kenan...”

Katseta Gimbiya Zeenat tayi da fad’in “Amma dai ke bakida kunya, dik yanda akai ke ba ‘yar babban gida bace... Kishi ne kawai yasa kike fad’in haka dan Raheema ta aure mijinki..!”

Zuhra ta katseta da fad’in “Wazai b’ata lokacinsa ya tsaya kishi kan wanda baisan k’imar d’iya mace ba balle har yasan sadakar Aure.?! Rashin kunya yasan yanda ya samo asali... Auren Sarki Mahmood da kike k’ok’arin k’ullawa tsakaninsa da k’anwarki ba sabida komai bane sai don kinaso ku shanye Sarki Mahmood ya koma sai yanda kukayi dashi, dan bakida burin da ya wuce ki mallaki matsayin Giwa cikin Masarautar nan.. Shin gaskiya na fad’i..!” Ta k’arashe tana dubanta...

Gimbiya Zeenat Ta soma muzurai tana tattare tabarmar kunya da bori... Ita kaw Giwa batai mamakin jin haka ba tinda har Waziri ma ya tasamma cin amanarta,kowa ba abin yarda bane a wannan Masarauta...

Ita Giwa tana k’ok’arin k’ulla tugguwa Raheema da Zeenatu bayan Raheemar Ta aure Mahmood ashe suma su Raheemar da nasu k’ullin akan Giwan... Tirk’ashi Mahmood dai da baida hakkinsu gaba d’aya Allah ya tsallakar dashi, shiyasa duk abunda mugu ke k’ulla maka idan baka da hakkinsa sai Allah ya maida masa sharrinsa kansa... Gashi dai Allah ya tsallakar da Mahmood tsakanin k’ullin wad’annan mugayen mutanen...

Taro ya hargitse mata aka soma ‘yar k’usk’us ana kame baki... Kayan kunya dai bazasu daina faruwa cikin wannan masarauta ba... Matar Wambai kaw da nata tawagar suka sami abinyi...
Iyakacin kunya dai Giwa ta gama shansa a bainar jama’a... Haka aka dinga silalewa ana ficewa daga Fadar Giwa... Umaima kaw kuka Ta dinga yi ganin wannan kayan tashin hankali dake faruwa ranar aurenta... Haka Zahra da Hadimanta suka janyota d’aki suna lallashi...

Giwa ma dai da taimakon Hadimanta ta bar cikin Fadar dan har yanzu Jakadiya jinya take bata warware ba da itace zatai jagorawa Giwa...

Aka bar Raheema da tawagarsu nan wajen, sai kuma jinjina lamarin suke, masu k’usk’us daga gefe nayi.. Lallai sun sami labarin komawa masarautarsu dashi...

**

Hankali kwance yake kallon tashan labaru na Aljazeera, hayaniyar Yazeed ya somaji da alama dogarai masu tsaron k’ofarsa sun hana Yazeed d’in shigowa... Can kuma saiga Yazeed d’in ya kutso yana fad’iwa Hadimin Mahmood koda wasa kada ya k’araso kusa dashi...

Hannu Mahmood ya d’agawa Hadimin alamun ya fice ya k’yalesu...

Barde ya risina alamun girmamawa kana ya fice...

Yazeed na huci yake duban Mahmood lokaci guda yake furta “Yaushe Bayi k’ask’antattu suka samu ‘yanci cikin gidan nan da har zasu hanani shiga yanda duk nakeso a fad’in Masarautar nan... Waye ya baiwa Bawa k’ask’antacce ikon dakatarda ‘yantacce...!?”

Daga yanda yake kishingide ya lank’wasa k’afarsa guda had’ida d’aura hannunsa guda saman k’afar yana murza zobensa a hankali, kyakkyawan murmushi saman fuskarsa ya baiwa Yazeed amsa da fad’in “Ba ma kowa na saka shamak’i cikin ahalin gidan nan ba... Wa mutum d’aya na saka kuma kaine... So umarnina suke bi da sukayi yunk’urin hanaka..!”

Yazeed na sakin huci yake furta “Ka daina yin wani abu kaman kaid’in ka zama Sarki... Karka mance har yau ba’ai bikin nad’aka matsayin Sarki ba, ba’ai maka wankan sarauta ba, ba’a mallaka maka sandar Mulki ba, ba’a d’aura maka rawanin Sarki ba, ba’a d’aura maka d’amaran Sarki ba, ba’a rufa maka alkyabbar sarauta ba, ba’a kuma buga maka Tambarin Saraki ba... Har yau baka d’ale Karagar ba suna suke baka a baki...So komai ka iya faruwa...! You never know mai zai faru anjima ko gobe... Everything is possible... Ta yuyu wannan karaga da kake ganin k’iris ya rage ka d’ale ba Naka bane..!!” Ya k’arashe yana sakin muguwar murmushi....

Murmushin Mahmood ya mayar masa kana yace “Allah shike bada Mulki ga wanda yaso ya kuma hana wanda yaso a kuma lokacin da yaga Dama...! Zuciya da ta aminta da tayi imani da hakan bazata tab’a damuwa don ta samu ko ta rasa ba... Komai a rubuce yake tuntuni..!!”

Yazeed yaci gaba da sakin huci yana duban Mahmood d’in yana ayyanawa cikin zuciyarsa ranan da Mahmood d’in zai San cewa ba Giwa ce ta haifesa ba k’ask’antacciyar Baiwa ce ta haifesa...

Har ya sa kai zai fice sai kuma ya dawo da baya yace “Kayi gaggawan warware auren wasan yaran daka d’aura min dan ban amince da wannan auren ba kuma bazan amince ba...!”

K’asaitaccen Murmushi kwance saman fuskar Mahmood yake fad’in “ Wuk’a da nama a hannunka suke dear brother..! Kayi yanda Kaso da Matarka taka ce..! She is all yours... Igiyar aurenta a hannunka yake ba’a hannuna ba sai yanda kaso kayi..!”
Daga haka maida hankalinsa kacaukam ga talabijin yayi ba tareda ya kuma bi takan Yazeed dake tsaye nan waje takaici na neman kashesa ba... Ji yake kaman ya k’arasa ya lumawa Mahmood d’in wuk’a a ciki kowa ma ya huta... Ya tsani Mahmood ya tsanesa, baida babban mak’iyi a duniya sama dashi..!
Fuuu yasa kai ya fice kaman zai kifa k’asa, duk ya fice hayyacinsa ko buttons d’in wuyar rigarsa bai iya had’awa duk ya koma kaman wani zaucecce lokaci guda....

**

Safa da Marwa kurum Giwa take nan k’uryar d’aki, takai mari Takai gauro... Ya zama dole taga Tal’udu dan yanda take tunanin al’amaran sun kai har sun zarce nan...

SameenaAleeyou 📚
*MUHIBBAH*

*64*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Chapter 103 · 0% Book details