← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 162

Sashe 44

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida ta isa masauk’i kuma ta soma tuhumar kanta, maiyasa ma zata taimaki Mahmood... Maiyasa bazata K’yalesa ya fad’a tarkon Raheema ba..? Wata zuciya tace hakan da kikai shine daidai dan idan kika bari asirinsu Raheema yai tasiri akansa toh fah zaki rama abinda yai maki ne bashi a cikin hayyacinsa... Gwara yana cikin hankalinsa yanda zaifi jin zafin duk abubuwan da zaki masa... Abinda kikai kinyi daidai Muhibbah ba taimakon mak’iyinki kikai ba... Ta k’arshe tinanin tana mai zama cikin sofa lokaci guda tunanin abinda taji Raheema na fad’i ya dawo mata... Wato binciken k’wak’wafa Raheema zata saka ai akanta... Idan kuwa haka ne toh fah zama bai ganta ba... Ya zama dole ta toshe duk wani hanya da real identity d’inta zai bayyana... Bazata bari Raheema Ta kawo mata cikas a shirinta ba... Toh ya zatai mai zata farayi... Ta ina zata b’ullowa Al’amarin...? Tai zaune tana tinani... Idan har Raheema zatai bincike kanta Toh fah saidai Ta tafi makarantarsu ta soma binciken don ta nan ne kawai zata iya yin bincikenta cikin sauk’i tinda ita ba ‘yar gari bace...! “Ansar...!” Ta furta a hankali... Shine kawai mutumin da zai zamto mata cover... Tai saurin janyo wayar salulantar da zummar dialing layin Ansar sai kuma taji jikinta yai matuk’ar yin sanyi ganin rabuwarsu Ta k’arshe da Fad’a suka rabu... Ta kuma ce masa bazata sake tambayar komai daga garesa ba koda shawari ne...Ta lumshe idanunta a hankali tana mai ije wayar gefe guda...

***

A can babban gwani kuwa masu sarautar sunyi zaune gaba d’aya... Su Waziri Galadima Hakimi da Talba da dai sauransu, Sun zagaye Karagar Mulki dake daga center... Mahmood na gefen Waziri Talba yaci gaba da fad’in “Bazai yuwu mu zauna haka nan babu sarki ba har yanzu... Kundai ga abinda ya sami Wambai, kai tsaye bazance wanine ke nufinsa da sharri ba amma mu munsan gida irin namu... Tinda cikinta aka haifemu muka kuma yi wayo cikinta har kawowa girmanmu... Idan muka zauna muka zuba idanu toh haka kaf sai anbi kanmu d’aya bayan d’aya an illatamu.... A ajiye maganan b’angaranci da son Mulki a gefe kowa yayi hak’uri a baiwa wanda ya cancanta mulkin nan... Kuma ni nan na janye neman mulkin nan da nake na mik’a wuyaga d’ah na Mahmooda dan shine ya cancanci wannan sarauta...!”

Su Waziri gaba d’aya suka shiga jinjina kai suna furta “Wannan gaskiya ne Mai Girma Talba....!”

Dogarai dake tsartsaye gefe suka soma wasa Mahmood suna fad’in Allah ya bashi dama gadon gidansu ne...

Talba yaci gaba da fad’in “Alhamdulillahi tinda duk munyi na’am sai a tsayar da ranan da za’a nad’a Sarki Mahmooda na biyu... Idan kuma akwai wanda bai amince ba sai muji dalilinsa..!!”

Kaman daga sama suka sinkayo murya cikeda iko da gadara yana fad’in “K’warai kuwa akwai wanda bai amince ba..!!!”

Gaba d’aya suka kaikaito suna duban k’ofar had’ida da mamakin wanda yai maganar....
Waziri ya kifa kansa kurum yana girgizawa a hankali....

SameenaAleeyou 📚[7/8, 10:10 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*030*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

“Majidad’i...!!!” Hakimin gari ya furta cikeda mamaki sanda Majidad’i yaci gaba da kutso Kai cikin tampatstetsen parlorn...

Shamak’i ya zube yana kwasan gaisuwa yake furta “Ku gafarceni Majidad’i yak’i sauraro na saima nuna min takwabi da yai a wuyana.!” Ya k’arashe yana muzurai alamun har lokacin tsoro ne dabaibaye dashi...

Masu sarautun gargajiya suka soma mik’ewa tsaye babu shiri ganin zarkwad’ed’iyar takwabin dake rik’e hannun Majidad’i sai faman shek’i take tana k’yalli....

Waziri yai azama yana mai furta “Kai Majidad’i lafiyarka... Meye haka nake gani... Ka kuwa San mai kake aikatawa..? Ka kuwa San ko ina kake... Ko kuwa hankalinka ne ya gushe...?!!”

Cikeda izza had’ida rashin tsoro Majidad’i yace “K’warai kuwa Waziri babu wanda ya isa ya d’ale Karagar nan muddin ba’a zak’ulo mutumin da ya illata min mahaifina ba... Sannan sanin kanku ne muddin Wambai na numfashi a doron k’asa sai da yardarsa da amincewarsa a nad’a Sabon sarki a Masarautar nan.... Oh Wato kunzo nan kun had’e kawunanku zaku nad’a sabon sarki mahaifina nacen kwance... Toh ina mai tabbatar maku babu wanda zai hau Karagar nan har sai an zak’ulo wad’anda Keda alhakin kasancewar mahaifina a haka... A shirye nake na fafata da dik wani wanda yace zai jayayya dani....!!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da sakin huci...

Cikin tsananin b’acin rai Waziri Ke furta “Kayi kuskure Majidad’i.. Ka wulak’anta gidan nan kaci mutuncin ahalinta dan haka dole ka amshi horo... Sarkin Gidaaa...!!! Yai maganar cikin d’aga murya yana mai ci gaba da fad’in “A d’auke Majidad’i a tafi dashi Gidan Yarin Wutin gadi....!!!”

Take Majidad’i ya bada balance ya d’aga takwabinsa yana fad’in dik wanda ya nufo yanda yake sai ya fille kansa...

Mahmood ne ya tako gabansa ba tareda shakku ko tsoron makamin dake hannun Majidad’i ba... Gaba d’aya sukai K’uri suna duban ikon Allah...

Majidad’i yana duban Mahmood take ci gaba da sakin huci yana kuma d’aga takwabin nasa sama.... Cikin tsananin huci yake k’ok’arin kaiwa Mahmood d’in sara ganin bai daina takowa yanda yake ba... Saidai ga tsananin mamakinsu tuni Mahmood yakaiwa takwabin damk’a ya rik’e sosai cikin tafin hannunsa dukda tsananin kaifi da takwabin kedashi.... Majidad’i yaci gaba da huci yana k’ok’arin cire takwabin daga cikin hannun Mahmood amma abu yaci tura... Su kansu saida sukai mamaki ga kuma jini dake gangarowa daga cikin tafin hannun Mahmood d’in alamun yanka... Su Galadima su Waziri sukai K’uri suna duban ikon Allah dan gaba d’aya sai Yarima Mahmood ya juye masu mahaifinsa Sarki AbdulJabbar.... Galadima da Waziri suka dubi juna a tare idanunsu na firfitowa waje sosai....

Sarkin Yak’i kuwa tuni ya daka tsalle ya zaro takwabin dake mak’ale gefen d’amaransa wanda dama dik sanda za’ai taro cikin Fada da d’amararsa ta yak’i yake halarta.... D’aga masa hannu guda Mahmood yai alamun dakatarwa kana ya maidoda dubansaga Majidad’i dake ci gaba da sakin huci har lokacin bai iya k’wace takwabin daga cikin hannun Mahmood ba....

Ga tsananin mamakinsu k’asaitaccen murmushi Mahmood ya sakarwa Majidad’i saikace baijin zafin yankar wuk’an na ratsa sa, lokaci guda yake furta “Ka kwantar da hankalinka D’anuwana, kaman yanda kace babu wanda zai hau Karagar nan har sai an binciko musabbabin ciwon Baba Wambai... Idan don ni Mahmood ne na amince da haka d’in... Ka sani Babu wani Sarki da zaiso a zubar da jini a mulkinsa, kuma babu wani sarkin da zaiso yaga an zubar da jinin Al’ummansa kafin ya d’ale Karagar mulki.... Zamanin yanzu yasha bambam da wancan zamanin, kasan ance Sarki goma Zamani goma..!” Ya k’arashe yana mai jifa da takwabin dake damk’e cikin hannunsa guda wanda ko motsata Majidad’i ya kasayi...

Waziri ya had’iyi miyau da k’yar wanda tai masa k’ebebe a mak’ogoro... Lallai yau yaga jarumtar Mahmooda, sam bai tab’a kawowa shid’in zai jarumta irinta mahaifinsa ba sai gashi yana nema ya zarce AbdulJabbar... Anya bokan Turai bai shera mata k’arya ba kuwa... Anya idan suka sake Mulkin nan ya fad’o hannun Mahmooda zasu cimma burinsu cikin sauk’i kuwa...? Gaba d’aya Waziri ya zama lost, gaba d’aya yama rasa abinyi... Tsoro da tashin hankali sun cika zuciyarsa sosai...

Mahmood nayin jifa da takwabin Dakaru suka K’araso a tamanin suka capke Majidad’i Waziri na fad’in a tafi dashi fursuna....

Mahmood ne ya dakatar dasu da fad’in “Ku sakeshi, ku k’yaleshi yai tafiyarsa... Amma wannan zai zamto gargad’i na k’arshe da zai kutso cikin Fada da takwabi tsirarta alhalin masarauta na cikin lumana.... Ubandoma..!!!”

Ubandoma ya k’araso had’ida zubewa gaban Mahmood yana mai furta “Rabkaidad’e..!!!”

Mahmood yaci gaba da fad’in “Ka raka Majidad’i har zuwa bakin k’ofar Masarauta, a tabbata Majidad’i ya fice daga cikin Masarauta cikin lumana da aminci....!!”

Ubandoma ya kuma risinawa yana mai amsawa kana ya tasa k’eyar Majidad’i yana fad’in “Godiya Majidad’i yake Allah shi baka yawan rai...!!”

D’anmaliki da Talba suka dubi Mahmood cikeda jin dad’in abinda yayi yanzu, hakan ya kuma tabbatar masu da cancantar Mahmood na zama Sarkinsu na gaba... Haka aka san Sarki da jib’antan lamuran Al’ummansa had’ida jarumta da kuma rangwame da sassauci ga wad’anda Allah ya hukunta masa zamtowa shugaba a garesu... Abinda Majidad’i yayi yaci a tafi dashi gidan Yari amma Mahmood yai masa afuwa ya kuma ce ai masa rakiya har k’ofar Fada a tabbata ya fita lafiya cikin aminci sannan ya janye sarautar da aka basa har sai an warware wasu al’amara a Masarautar kaman ciwon Baba Wambai dan shi bai yarda Bak’on Buzu nada alak’a da ciwon Wambai ba tinda dai yasan shid’in shine bak’on Buzu... Baisan dalili ba amma jikinsa na basa akwai wata k’ulleleliya a al’amarin....

**

Bayan an watse a Fada ne Waziri ya k’araso yana kuma ingiza Mahmood cewa lallai ya d’ale Karagar nan a yanzu, dan hakan ne kawai zai basa daman aiwatar da al’amara yanda suka kamata... Ya k’arada “Rankaidad’e Kaga dai yanda maras kunyar yaron nan d’an wajen Wambai ya shigo yai abin kunya da Allah wadai cikin Fada, na tabbata Mahaifiyarka bazataji dad’i ba muddin taji cewa Kingmakers sunyi ma’am gaba d’aya cewa ka zamto Sarki harma ana k’ok’arin tsaida ranan rantsar dakai matsayin Sarkin wanann nahiya tamu mai babban daraja amma kak’i kace a sarara zuwa wani lokaci... Rankaidad’e da dai an duba lamarin... Wanann sarauta dama gadonka ne Allah shi taimakeka...!” Ya k’arashe yana mai kuma k’ank’an dakai...

Shiru tamkar mai nazari Mahmood yai hannunsa mai d’igan jini na dunk’ule yake furta “Waziri..!!”

Waziri yai saurin mik’o masa jinjina yana mai amsawa...

Mahmood yaci gaba da fad’in “Ina labarin neman Jafar da na wakiltaka.... Shin a ina aka tsaya...?!”

Waziri ya had’iyi miyau da k’yar kana ya soma fad’in “Allah shi baka yawan rai, ai shi Bawa idan ya samu wata ‘yar k’ofar da zai tsere sam bazai tsaya gari kusa ba... Allah shi taimaki Saraki Babban Sarki a wannan daula tamu Jafar babu shi babu labarinsa... Babu hanyar da bamubi ba harta hanyoyin bincike na zamani dana gargajiya duk munbi amma shiru babu wani labari gameda Bawa Jafaru...!!”

K’uri Mahmood yaima k’ofa yayinda Waziri yaci gaba da muzurai yana k’ok’arin had’iyi tuk’in goro da ya tsaya masa a mak’oshi...

Bai kuma furta komai ba sai sa kai da yai ya fice daga parlorn hannayensa hard’e ta baya...
Chapter 44 · 0% Book details