← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 162

Sashe 86

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jamal ya jinjina kai yace “In sha Allah Yaya, dama nima goben inada zuwa ganin Dr na...” Ya d’anyi fasali kana yaci gaba da fad’in “ Yaya akwai maganar da nakeso muyi... Idan bazaka damu ba...Allah shi taimakeka...! Allah shi ja zamaninka..!!” Ya k’arashe yana kirariwa Yayan nasa...

Giwa ta had’iyi miyau da k’yar kana tace “Jamal ka k’yale Yayanka yaje ya huta yayi tafiya ya gaji...!”

Mahmood ya girgiza kai yace “A’a no... Family first, Ka tafi sashe na ka jirani a can, I’ll check on Zahra idan na fito sai muyi maganan koh...!” Ya k’arashe cikeda tausayin Jamal d’in duba da lalurar da yake fama dashi a yanzu...

Jamal ya jinjina kai cikeda jin dad’i yana mai masa godiya had’ida kwad’a masa kirari har ya haye sama... Ya maidoda dubansaga Giwa wacce Ke muzurai ya danna mata wata muguwar harara kana yasa kai yai shigewarsa, tana kiran sunansa ko tsayawa baiba balle ya amsata... Muguwar haushi take basa sabida bata goyon bayan aurensa da Umaima..!
Giwa tai saurin bin bayansa ta kamo sandar crutches d’insa hakan yasa ya dakata ba tareda yaci gaba da tafiya ba...

Fuska babu walwala yace “Let go... Ki k’yaleni na tafi Maami, I’m not in the mood for your lectures..!”

Giwa ta kuma had’iyan miyau da k’yar tace “Jamal ka saurareni please... Ba abinda kake tinani bane, ba maganan hanaka auren Umaima zanyi ba..!”

A hasale yace idan ba haka ba mai zakiyi... Mai zaki cemin...?!”

Giwa ta kuma marairaice fuska tana mai k’ak’aro murmushi yawa mutumiyar arziki tace “Ce maka zanyi na amince ka auri ‘yaruwarka Umaima.. Na amince ka fad’awa Yayanka a saka maku rana tare..!”

Da mamaki yake dubanta murmushi saman fuskarsa “Da gaske Maami...! Kin amince na auri Umaima..?!”

Giwa ta jinjina masa kai murmushi saman fuskarta... Baisan sanda ya rungumeta yana furta “Thank you..! Thank you Maami.. Kin gama min komai...Na miki alk’awari zan rik’e Umaima da amana, zan d’aura daga yanda kika tsaya.. Tin tana k’arama rik’onta a hannunki yake dan haka ni zanci gaba da rik’eta bisa gaskiya da amana..!”

Giwa Ta kuma murmusawa ta shafi gefen fuskarsa kad’an “Nasan zaka iya Gwarzo... Na gama iyaka tunanina idan ba kaiba babu wanda zai rik’e min Umaima bisa gaskiya da rik’on amana... I trust you Gwarzona..!”

Shima murmushin ya sakarwa mahaifiyar tasa su duka biyun suna duban juna...
**

Mik’ewa Muhibbah tai ta dubi Zahra tace “Princess zan wuce, zan koma masauk’i, Ina fata zakiyi duk abubuwan dana fad’a miki...”

Zahra ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali had’ida jinjina mata kai baki a ture kad’an...Muhibbah Ta sakar mata murmushi kana ta d’an dafata kaman zatace wani abu sai kuma tasa kai ta shige cikin tsananin kariyar zuciya, ta sani Raheema bata dace da Rankaidad’e ba amma yaya zatayi idan zab’insa kenan, bayan abubuwan da suka faru dashi bata fata ta kuma ganinsa broken, kuma tayi imani duk randa yasan abinda mahaifiyarsa da ‘yanuwansa sukai zai zama broken, bazataso Ta k’ara masa akai da matsalar Raheema ba...Zatai masa addu’an Allah yasa alkhairi a cikin aurensa da Raheema ya kuma shiryeta ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ahalin da yake k’ok’arin ginawa tareda ita...Tana fatan aurensa da Raheema zatai ya zamto silan shiriyarta domin shid’in mutumin kirki ne ya cancanci mace Ta k’warai....A hankali Ta saka hannunta ta murd’a handle d’in k’ofar.... Idanunta dake duban k’asa suka soma hango had’add’iyar takalmin kufta da k’afafunsa Ke rufe ciki, gabanta ya yanke ya fad’i.. Ga wani musulmin k’amshi da yai sallama ma k’ofofin hancinta, k’amshin nan dai da ya cika motar abokinsa sanda suka maidata gida...Cikin d’ak’ik’a zuciyarta Ke harbawa da sauri da sauri... A hankali take k’ok’arin d’ago k’wayar idanun nata zuciyarta bai daina harbawa ba har ta d’ago sosai suka dubi juna... Gani tai idanunsa k’yam akanta hannayensa hard’e waje guda fuskarsa d’aukeda alaman tambayar ya akai kika dawo..?!

Ta had’iyi miyau da k’yar ganin babu wani walwala saman fuskrsa, tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi wanda kai tsaye zaka kirasada yak’e. “Your Highness..! Barkada sauk’a..!!” Tai maganar cikin rabewar kalmomi...

Zaida ya kuma d’iban wasu dak’ik’ai kaman bazaice komai ba sai kuma yai mata alama da kai alamun amsawa ba tareda ya furta komai ba sai duban tuhuma da yake mata wanda sosai hakan ya haifar mata da tsarguwa... Ta d’an sadda kanta tana k’ok’arin matsawa alamun basa hanya...

Bai janye idanunsa ba har saida yaga tana k’ok’arin d’ago fuskarta.... Yai saurin kauda fuskarsa sabida zuciyarsa data gaza natsuwa... Muhibbah tasa kai Ta shige zuciyarta naci gaba da bugawa... Kaman daga sama ta sinkayo muryarsa na fad’in “Maiyasa kika dawo..?!”

Taji tambayar tamkar sauk’ar aradu..! Ta d’ago da sauri tana dubansa, sosai ya had’e gira... Rasa mai zatace tai sai murza ‘yan yatsunta da take... Da wutsiyar idanu yake dubanta alamun yana jiran amsa...!
Saida Ta had’iyi miyau da k’yar, kana Ta soma k’ok’arin had’o kalamai saman harshenta dikda cewa lokaci guda taji bata k’aunar tai masa k’arya amma babu yanda Ta iya ne... “Amm... Dama lecture free week nake shisa na koma gida... And and Mommy was sick, so sai naje duba jikinta... But she’s ok now shisa na dawo sabida exams..!” Ta k’arashe da k’yar kaman mai laifin da aka titsiye gaban Kuliya...

Ya tsareta da idanu sosai kana yace “Dole sai cikin Masarautar nan zaki zauna..?!”

Maganarsa ya haifar mata da sanyin jiki, dan sam bata fahimci cewa ya fad’i haka ne gudun kada Yazeed ya kuma attempting cutar da ita har dai zasu zauna gida guda... Itakam ji tai maganar nasa kaman hannunka mai sanda yake mata... Batakaiga basa amsa ba ta kuma sinkayo muryarsa yana fad’in “At least you’ve someone to protect you here... It’s not safe out there...!!”

Tai saurin d’agowa tana dubansa dan sai yanzu ta fahimci mai yake nufi, saidai tuni yasa kai ya nufi cikin d’akin ba tareda ya tsaya jiran amsa daga gareta ba...Tabi bayansa da kallo had’ida sakin murmushi kad’an..
Daga nan yanda take tsaye tana iya hango alamu daga yanayin Zahra ko shakka babu Ta d’auki hud’ubar da tai mata cewa Ta nemi yafiyar mahaifinta... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali zuciyarta na mata wane irin sanyi Mahmood da d’iyarsa zasu sasanta... A haka ta nufi masauk’i tai kwance tana tinanin abubuwa da dama... Saidai duk juyi da zatai sai Rankaidad’e ya fad’o mata... Maiyasa tinaninsa ya addabeta..? Toh Kodai dan a baya tanajin guiltiness ne, toh amma yanzu fah..? Ai ya kamata ta yakishesa a zuciyarta tinda ta tabbata Zahra zata d’auki hud’ubarta ta baiwa mahaifinta hak’uri su sasanta tsakaninsu... Ta kuma sakin murmushi a hankali tana tuna had’uwarsu da sukai d’azu... Kalamansa na k’arshe zuciyarta keta nanatawa _You’ve someone to protect you here.._ Ta kuma sakin murmushi a hankali had’ida lumshe idanunta...

**

Washe gari Zahra Ke sanar da ita yanda sukai da mahaifinta, sosai taji dad’in hakan, saidai a cewar Zahran duk sabida Muhibbar tai haka... Aje dai a hakan taji dad’i sosai da suka sasanta tsakaninsu... Zataso komawa gida tinda tayi Major abinda ya dawo da ita saidai alk’awarin da ta d’aukarwa Ubandoma da mahaukaciyar matar nan harmada Jafar shine kawai zai iya zaunarta a Masarautar bacin haka bataga kuma mai zata zauna tai ba tinda tayi abinda ya dawo ita...A bakin Zahran take jin cewa mahaifinta ya sanar da ita an saka bikinsu da Raheema nan da sati biyu kuma ta basa goyon bayanta dikda cewa bata k’aunar alak’arsu da Raheemar amma tinda yana so zatai hak’uri ta accepting d’inta muddin hakan zai faranta masa rai....

Take jikin Muhibbah yai sanyi tamkar an tsoma a k’ank’ara... Ta d’ago idanunta masu rauni tana duban Zahra dasu “Kikace an saka auren Paa d’inki..?!”

Zahra ta jinjina mata kai tace “Haka Paa yace min an tsaida aurensu nan da sati biyu dan masu mulki basa jira... Amma na gaya masa dan dai kawai yana sone idan ta ni ne bana son ya aureta... But I guess I don’t have a choice then..!” Ta k’arashe cikin sanyin murya tana mai zama saman koren ciyawan da yaima lambun shak’atawan k’awanya...

Muhibbah ta zauna a sanyaye tana mai jinjina lamarin, in the next two weeks Rankaidad’e zai auri matar nan... Ta had’iyi miyau da k’yar tana mai ayyanawa cikin zuciyarta, tabbas bazata jira sati biyu yai mata a wannan masarauta ba gwara kawai ta tafi dan Allah ya gani bazata juri ganin auren Rankaidad’e da matar nan ba... Zataji kaman taci amanarsa ne tinda ita tasan mai zai aura shi kuma bai san mai zai aura ba... Duk surutun da Zahra ke mata bata d’aukan komai tuni tai nisa cikin duniyar tunani...

Yarima Mahmood da Turaki kaw daga can saman bene suke hangan Zahra da Muhibbah, hannayensa hard’e ta baya yake dubansu zuciyarsa naci gaba da raya masa wasu abubuwa...

Turaki dake tsaye gefensa sauk’e ajiyan zuciya yai kad’an kana yace “Your Highness har yanzu kana nan akan bakan ka na barin k’asar... Dan Allah think your decision through, wacce kake shirin yin wannan abu domin ita gashi ta kwantar da hankalinta, a tunanina Rankaidad’e you don’t need to leave anymore...!”

Ba tareda ya dubesa ba har lokacin idanunsa naga Muhibbah yake furta “I’m sure this is all her doing... Inada tabbacin cewa ita ta shawo kan Zahra, she’s a good influence to my daughter... Saidai ita d’in ba mai zama cikin Masarautar nan bane, akwai randa zata gama abinda ya kawota Ta tafi... I’m afraid idan ta tafi Zahra zata iya komawa ruwa, musamman akwai ire irensu Yazeed cikin Masarautar nan masu poisoning zuciyarta da gurb’atattun tinani... Zaifi kyau idan na d’auketa daga cikin Masarautar nan...!”

Turaki yayi shiru yana dubansa, lokaci guda ya girgiza kai yace “I’m sorry Rankaidad’e but ya zama dole na fad’a maka gaskiya hardai kana nan a matsayinka na Abokina.... Mahmood bari na maka magana da siga ta abokantaka mu aje mulki da matsayinka a gefe.. Ina maka magana ne a matsayina na abokinka ba a matsayinka na Sarki ba...Wannan hukunci da kake k’ok’arin yankewa akwai ranan da zakai nadamar yinsa... Your life is right here, cikin Masarautar nan... Bakada sauran rayuwa a Spain...!”

Cikin karaji yaceda Turaki “I don’t remember asking for your opinion...!”
Chapter 86 · 0% Book details