← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 162

Sashe 80

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana shigewa da wasu ‘yan dak’ik’ai Muhibbah ta fito ta nufi jikin ginin tana shafawa a hankali.... Sosai ta k’urawa ginin idanu nan ta hangi wani dogon layi jikin ginin yasha kwalliya da fenti irinta gidan sarautar wanda sam bazakai zaton ba ado ne kawai na gine ginen gidajen sarauta ba... Dukda gabanta dake tsananin fad’uwa hakan bai hanata saka ‘yar tsarta tsakankanin wannan ginin ba... Ga tsananin mamakinta saiji tayi kaman ginin na motsi... Ta kuma yin basmalah ta tura yatsarta taji tabbas motsi yake.... Allah mai iko Wato ashe k’ofa ce aka yita cikin gini wanda sam ga wanda bai sani na bazai fahimci hakan ba... K’irjinta yaci gaba da fad’uwa tana tunanin mai zata gani bayan wannan gini idan ta bud’e... Lumshe idanunta tai tana k’arfafawa kanta gwiwa da fad’in zata iya da yardar Allah... Ta kuma ambato sunan Allah kana ta d’an bugi ginin da hannunta.. Ga tsananin mamakinta sai gani tai ginin ya soma bud’ewa d’aki mai tsananin duhuwa ya bayyana... Mamaki ya kuma cikata, tabbas d’aki ne a wannan waje.... Toh miye a ciki..? Bata kaiga samo amsa ba ta hango mutum daga can k’uryar d’akin tana ci gaba da karjan gini alamun bataji shigowarta ba....

Dukda bayanta kawai take iya hanga bataga fuskarta ba dashike Ta bada baya ne ma k’ofar, hakan bai hana Muhibbah ci gaba da takowa cikin d’akin k’irjinta naci gaba da bugawa ba, addu’o’i kuwa duk wanda yazo saman harshenta shi takeyi....

A hankali take takawa har ta isa taga abinda matar take.... Cak Izzatu Ta dakata da abinda take dan taji kaman mutum ne a bayanta... Aiko take ta juyo da zummar capko mutumin dake bayanta, Muhibbah ta rintse ido tana jiran mai auka ya auku tinda ta gane matar mahaukaciyar nan ce da Ta kirawo sunanta.... Bata auka mata ba saima tsayawa da tai tana binta da kallo...

Muhibbah ta bud’e idanunta a hankali tana duban matar da tai mata K’uri, cikin d’an tsoro tsoro take takowaga matar wacce tuni Ta soma sakar mata murmushi... Muhibbah taji k’warin gwiwa na zuwa mata.... Murmushi itama ta sakar mata kana tace “Mai kikeyi a nan... Wa ya canza miki d’aki...?!”

Bata bata amsa ba sai nuna mata ramin da take tono datai jikin gini wanda tuni yayi zurfi.... Muhibbah ta dubi ramin da mamaki Ta kuma duban matar... Jinjina mata kai matar tai k’walla tab idanunta... Lokaci guda take kuma janyo hannun Muhibbah ta zaunarta jikin ramin tana mata alamu da hannu kan ta tayata suci gaba da tonon ginin....

Ita dai Muhibbah duk bata kawo komai ba, duk a nata zaton cikin haukar wannan matar take ceda ita su karje gini... Ta k’ak’aro murmushi ta sakar mata kana Ta mik’e ta shiga janyo hannunta tana fad’in “Zo mu tafi... Zan fitar dake daga Masarautar nan, bazan bari su kuma zaluntarki ba... Zo muje..!” Ta k’arashe tana mai kuma janyo hannun mahaukaciyar wacce tak’i koda motsa k’afarta ne...

Muhibbah ta juyo ta dubeta da mamaki kana tace “Bakiso ki kub’uta daga hannun wad’annan azzaluman ne...?”

Matar ta girgiza mata kai alamun a’a kana ta kuma mata nuni da ginin da take karja.... Muhibbah ta dubi ginin ta d’an murmusa kad’an dan tasan duk cikin gushewar hankali ne kana ta matso kusanta tace “Kar ki damu ni nasan k’ofar da zamubi mu fice ba sai kin karje gini ba... Idan kika tsaya yin wannan har zasu cimma Ki su kuma kamaki... Zo muje kafin ya dawo...!” Ta k’arashe tana mai kuma janyo matar wanda wannan karon sosai ta b’ata fuska tana duban Muhibbar... Lokaci guda ta finciki hannunta daga rik’onda Muhibbar tai mata ta koma jikin ginin taci gaba da karjewa ba tareda Ta kuma bin takan Muhibbah ba...

Muhibbah ta bita da idanu cikeda mamakin yanda ta koma ta duk’a gaban garun tana ci gaba da k’walk’walewa... Sauk’e ajiyan zuciya tai a hankali wata zuciya na cewa bazaki Iya da matar nan ba Ke kad’ai, Ki fice Ki karya Giwa kafin ki dawo ki ceci matar nan idan ba haka ba kema in suka kamaki haka zasu maisheki, kinga baki taimaki matar nan ba gashi kema an kamaki.... Da wannan tunanin Muhibbah tasa kai zata shige ta k’yale Mahaukaciya Izzatu...

Har takai k’ofa sai kuma ta tsaya cak tana tunanin anya lafiya mahaukaciyar nan Ke karjan gini haka kurum... Anya bazata duba abinda mahaukaciyar nan keyi ba...? Take taji tana son ganin abinda mahaukaciyar keta k’ok’arin nuna mata tai zaton cikin haukarta ne... Dawowa da baya Muhibbah tai ba tareda taceda mahaukaciyar komai ba ta duk’a a hankali tana duban abinda take... A hankali Muhibbah ta saka idanunta tana duban cikin ramin wani irin yanayi da bazatace gashi ba yana fuzgarta, zuciyarta na bugawa cikin nastuwa... Tai k’ok’arin janye hannayen Izzatu daga jikin ginin kana ta saka k’wayar idanunta tana lek’awa.... Duhu ne iyaka ganinka amma taji wani irin yanayi kam... Toh nan d’in kuma inane... Wata zuciyar tace k’ila mahaukaciyar tayi zaton ta nan d’in zata sami hanya...! Hakan yasa Muhibbah waigowa da niyyan k’ok’arin shawo kan mahaukaciyar nan Ta amince Ta bita su fice... A yunk’urin da zatai da zummar waigowa kunnenta guda ya tsaya daf jikin ramin da Izzatu ta karje yayi zururu... Kaman wanda iska ya koro sautin haka ta jiyo sauk’an numfashin mutum cikin kunnenta... Zuciyarta ta kuma tsinkewa.. Tabbas akwai bil’adam bayan wannan gini... D’agowa tai Ta dubi Izzatu da tai mata K’uri kana tace “Akwai mutum a bayan ginin nan..!”

Izzatu Ta jinjina mata kai a hankali alamun tabbatarwa... Cikin sauri Muhibbah ta mik’e tana duban Izzatu take furta “Wannan gini bazamu iya turasa ba, koda zamuyi kwanaki muna tono... Amma da izinin Allah zamu kub’utar da mutumin nan dake rufe a wannan fursuna mai tsananin duhuwa...”
Ta kamo hannayen Izzatu duka biyu tace “Kin tuna Taswiran da kika bani..?”

Izzatu ta jinjina mata kai alamun eh.. Muhibbah taci gabada fad’in “Zanen dake cikin Taswiran yayi yanayi da ire iren wad’annan gine gine na sarauta, yau d’in na tabbatar da haka... Idan muka fice a nan zamu zaga ta baya ko Allah zaisa mu sami k’ofar da zata cimmamu da d’akin da aka rufesa... Muje bamuda sauran lokaci...!” Ta k’arashe tana mai janyo hannun Izzatu suka fice cikin sauri....

Saidai koda suka fito babu wata alamu da zasu iya gane akwai hanya da zai sadasu da wata d’aki a wajen... Muhibbah tai K’uri tana kallon dogayen gine ginen... Waigowa tai Ta dubi Izzatu da itama gine ginen take duba... Fuzar da fuci kad’an Muhibbah tai kana ta nufi wata hanyar dake nan b’angaren hagu da ginin... Nan ma shiru babu alamun hanya...
Magana Izzatu take mata saidai maganar bata fita baka fahimtar komai sai gwalamniya... Muhibbah tai mata K’uri cikeda tausayawa, lokaci guda ta matsoga Izzatu ta kuma dafe hannayenta tace “Banjin zamu samu hanyar da zamu kub’utar da mutumin dake wancan d’akin amma mu koma cikin wancan d’akin muga idan zamu iya karje ginin cikin gaggawa...!”
Ta fad’i hakan ne Dan baiwa mahaukaciyar da a yanzu take tantaman haukarta k’warin gwiwa.... Muhibbah ta kamo hannunta suka saka kai zasu koma cikin d’akin... Kaman daga sama suka sinkayo murya yana furta “Ina kuke tunanin zakuje..!!!”

Cak suka tsaya yayinda Izzatu ta finciki hannunta ta soma jada baya tana nok’ewa had’ida yin wasu abubuwa na marassa hankali.... Muhibbah kaw rintse idanunta tai a hankali Dan ta tabbata yau kam shikenan an kamata....

Mutumin yaci gaba da takowa yanda suke har lokacin idanun Muhibbah a rintse suke, ya bud’e murya yace “Juyo Ki kuma nuna kanki..!”

Bata juyo ba sai addu’o’i da take jerowa cikin zuciyarta.... The more tana add’ua the more tana jin k’warin gwiwa na zuwa mata tsoro na yaye mata... Ji tayi zata iya fuskantar koma wanene idan ta kama su kara ne ma sai su kara d’in...

Fuska a matuk’ar murtuk’e Ta waigo cikin dakewa...
Ubandoma yai mata K’uri yana son gane ina ya santa... Ya saki murmushi yana nunata da yatsa yace “Kece.!! Haba ai biri yayi kama da mutum, Jakadiya tayi gaskiya da tace bata yarda dake ba... Ashe ked’in kin jima kina k’ulla abubuwa cikin Masarautar nan.. Akwai babban dalili da ya shigo dake... Zaki gane kurenki yarinya... Zaki d’and’ani kud’arki, zaki gane cewa ba’a diran mik’iya ma Masarauta irin wannan... Kin tapka babban kuskure yarinya.. Kin hak’i kabarinki da kanki... Yanzu ba tareda b’ata lokaci ba zan d’aukeki ga Giwar Amale... Na tabbata zan samu babban rabo...!!” Ya k’arashe yana mai fashewa da dariya...

Yayinda Muhibbah tai masa K’uri tana duban yanda yake dariya... ita kaw Izzatu gefe ta koma ta mak’ale jikin gini tana girgiza kai... Ubandoma na k’ok’arin takowa yanda Muhibbah take Izzatu ta k’arso a guje ta rungume Muhibbah tana hawaye take Girgiza wa Ubandoma kai alamun a’a...

Ko gizau Muhibbah batai ba saima ci gaba da duban Ubandoma da take da idanunta wanda babu alamun tsoro ko sarewa cikinsu... Cikin dakakkiyar murya Ta soma furta “Shin wace riba da ka samu daga wajen Uwargijiyarka idan ka bari aka cutar da rayukan da basuda alhakin kowa..? Shin wace riba zaka samu a wannan ta duniya wacce ita d’in ba matabbatace face GIDAN ARO... Shin wace riba ka samu a iyaka shekarun da kai kana ha’intar mutane da basuda hakki... Ka dubi tsawon shekarun da kai a baya, ka d’auki tsawon rayuwarka kana bauta ne ma wacce bata ganin darajarka balle kimarka saima d’inbin wulak’anci da tozarci da kake fuskanta daga gareta... Shin mai zai ragu jikinka idan ka zab’i ka aiwatar da abinda ya dace... Na tabbata tsawon rayuwarka ka yisu ne a matsayin bawa maras ‘yanci wanda sai abinda aka umarcesa...!”

Katseta yayi da fad’in “Ke yarinya hattara, kar Ki bada shaida akan abinda bakida masaniya... Wannan abu da kikaga nakeyi nima ba son raina bane... Kaman yanda kika ce tsawon rayuwana na shafesa ne wajen bauta tabbas haka ne.. Kuma wannan abu da nake yanzu inada tabbacin shi zai bani ‘yanci da na jima ina nema sabida duniyar nan yanzu babu abinda za’a baiwa Giwa Ta shiga nishad’i tamkar wannan matar..!” Ya k’arashe yana nuni da Izzatu, lokaci guda yaci gaba da fad’in “Wannan mahaukaciya da kike gani itace tikitin samun ‘yanci na da zuri’ata..!”
Chapter 80 · 0% Book details