← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 162

Sashe 151

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka rungume juna itada Mommy, Ta d’ago tana duban Mommy tace “Mommy ashe dai zaki zo..?”
Murmusawa kad’an Mommy tai tace “Kin tab’a ji anyi biki babu uwar Amarya.. Kuma da irin wannan karramawa da Mai Martaba yayi min ai dole na amsa gayyatarsa koda kuwa Uwar Amarya bata zuwa Bikin d’iyarta... Sannan ni da kaina zan sakaki a lalle Hibbah am..”
Kunya ya d’an kamata sai kuma tace “Mommy Rankaidad’e ne ya tura maku katin gayyata..?”
Mommy ta murmusa tana kuma duban fuskarta tace “Komai ma ya tura Muhibbah, duk wasu abinda kika sani na al’ada na aure ya tura an raba kaf unguwa dangi na kusa dana nesa, inaga idan akwai wad’anda basu shaida ba bazai shige Yawale da iyalansa ba dan ni da kaina na hana a tura masa ko dan abinda yayi miki..”
Muhibbah ta d’anyi shiru tana mai sadda idanunta k’asa sanda Mommy ta ambaci sunan Yawale.. Lokaci guda Mommyn taci gaba da fad’in “Yanda yaso ya tozartaki Sai Allah bai nufi hakan ba.. Ashe ma Sarki ya aurar dake ba tareda ya sani ba.. Yanzu kaf unguwa labarin irin kayan bajinta na gani a fad’i da aka aika daga Masarauta ake ni kaina darajata da kimata ya k’aru a idanun mutane sabida ke Muhibbah.. Ga karramawa da aka min Sarki ya d’aga tawaga tun daga Masarauta suka tafi har can Masarautar Bauchi suka kuma yin wani zugan kana suka nufo gidana.. Shin mai yafi wannan dad’i Muhibbah.. Karkiso kiga d’aukakan da Allah yamin duk a dalilinki.. Allah dai ya baku zaman lafiya da zuri’a d’ayyiba..! Hak’ik’a kinyi dacen miji mai k’aunarki da ganin k’imanki d’iyata... Wanda har zai girmama Uwar rik’onki irin haka bama mahaifiyar data haifeki ba irin wannan miji abin alfahari ne,abin a rik’esa hannu bibbiyu ne Kinji koh.. Domin kuwa duk wanda zai daraja iyayenki shine mijin aure... Ki rik’i aurenki da kyau kinji d’iyata..!” Ta k’arashe cikin rawar murya yayinda Muhibbar ma hawaye ke ziraro mata... Kalaman Mommy duk Sai ya sanya jikinta yin sanyi...
Suka kuma rungume juna suna hawaye Mommy na fad’in zatayi kewarta sosai

Muryar Gudidi suka sinkaya tana duk’e wajen take furta “Rankidad’e nidai gafararki nazo nema.. amin aikin gafara.. Ki yafeni Gimbiya Muhibbah, wllhi duk abinda na miki sharrin shaid’an ne da kuma sharrin zuciya.. Hassada muguwar ciwo ce.. Hassada itace tamin jagoranci na aikata abinda na aikata... Nayi miki hassadan auren d’an k’awata wanda a baya naso ya auri d’iyata bai aureta ba har tayi aure.. Naji hassadan ya auri tsintacciyar mage irinki wacce batada asali balle tushe ashe ba haka abin yake ba.. Sai gashi hassadan da na miki na taya Yawale wajen ganin mun durk’usar da rayuwarki ashe d’aga darajarki mukayi ba tareda mun sani ba.. Na yarda da hausan nan da ake cewa Hassada ga mai rabo taki ne.. D’an hakin daka raina wataran shi zai tsone maka idanu.. zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ko ana shaho sai yayai... Idan rana ta fito tafin hannu bata tab’a kareta..! Tabbas mun miki hassada ya kaikiga alkhairi.. Munso nisantaki da Duniyar ahalinda kika girma taredasu suka maye gurbin ahalinda kika rasa daga farko ashe mun mik’aki ma ahalinki na jini ne bamu sani ba... Munso ki k’ask’anta da muka aura miki wannan mutumin ashe darajarki muka d’aga ba tareda mun sani ba.. Gimbiya ki yafe ni kimin rai ki yafe ni... Murja taso hanani zuwa amma na dage sai nazo na nemi afuwarki..! Ki yafeni Gimbiya Muhibbah..!” Ta k’arashe tana k’ok’arin kamo k’afar Muhibbah wacce tuni ta duk’a ta kamo hannayen Aunty Gudidi, tana girgiza kai take fad’in “A’a Aunty ni ban tab’a rik’eki cikin zuciyata ba.. Ked’in tamkar uwace a gareni domin kuwa ked’in k’awar Mommy ce.. Allah ya yafemu gaba d’aya...”

Cikin tsananin kuka Gudidi ta rungumo Muhibbah tana fad’in ta cika mai kyakkyawan zuciya.. Mommy da Aunty Salma suka share hawayen da ya gangaro masu suma.. Daga bisani Muhibbah ta samu ta gaisa da Aunty Salma itama ta nemi yafiyarta dukda cewa duk abinda sukayi ba yin kanta bane Gudidi ce ta tilasta mata.. Daga nan kuwa suka k’ume a d’aki itada k’awarta Meenatu tana labarta mata yanda abubuwa suka kasance bayan aurenta da Bak’on Buzu... Gashi yanzu tinda labari ya karad’e unguwa Sarki take aure kowa har son sake ganinta yake, harta ita kanta Meenatun a halin yanzu wani matsayi ta samu wajen K’awaye dashike itace aminiyarta.. Rayuwa kenan, duniya rawar ‘yanmata na gaba Sai ya koma baya, na baya ya dawo gaba... Yau ga Muhibbah da har cikin k’awaye ana k’yamatar sabida rashin cikakken asalinta sai gashi yanzu har ana tsere tseren rab’an makusanta ta bama ita kanta ba.. Shiyasa sam raina d’an adam baida alfanu bakasan mai Allah ya aje wajenba shi da ya halicci kayansa.. Allah kasa mu dace duniya da lahira.. Ameen!

**

A can Bauchi kuwa tun bayan ficewarsu Mommy Ansar ya shirya tsaf ya nufi gidan surkinsa Yawale bayan gudanar da sallar la’asar, Sosai yaci gayu cikin shiga Ta kamala, jampa harda hula shida ba gwanin saka manyan kaya ba... Baffah Yawale ya fito yana Washe baki yake furta “A’a Yakubu dama kaine tafe..?”
“Eh Baffah ni ne.. Mun sameku lafiya..?” Ya k’arashe yana duk’awa cikeda girmamawa yau d’in yake gaida Yawale..

Yawale yaci gaba da goga karan asuwakin dake bakinsa ya fuzar da tuk’an kana yace “shine baka shiga daga ciki ba ka tsaya daga nan saikace wani bak’o..”

Ansar ya murmusa yace “A’a Baffah ai nan d’inma yayi.. Ai akan hanya ma nake..!”

Baffah yace “Au toh toh..! Inji dai ba ja’irar yarinyar nan Hameedah ce tai maka wani abin ba..?” Yai maganar cikin fad’a..

Girgiza kai Ansar yai yace “A’a Baffah Hameedah batai min komai ba... Tafiyar dama takace..!”

Yawale ya kuma Washe baki ganin yanda sirkin nasa yaci gayu gashi yace tafiyar tasa ce, toh kodai wani babban kyauta zai masa..? K’ila ma gida ya sai masa... Zai masa irin nasu na yaran zamani yayi masa surprise.. Yaci gaba da Washe baki yana furta “Toh toh toh Allah sarki.. Wato dai tafiyar tawa ce..?”

Ansar ya jinjina kai a hankali yana mai bud’ewa Yawale marfin Mota yake furta “Muje Baffah babu lokaci..”

Yawale ya shiga tofar da tuk’an aswakin da yake goge hak’waransa dasu yana furta “Toh Toh ai kuwa dai Babu lokaci.. Ku likitoci lokacinku ai a k’ayyade yake.. Toh Wai nace ko zan shiga naima Innar taku sallama..?”

Ansar ya girgiza kai yace “za’a Baffah ai ba sai ka mata sallama ba, muje kawai...!” Ya k’arashe yana mai kuma hangame masa marfin motar..

Yawale ya rik’e mota ya shige yana furta “Kai kaji Mota mai taushi kaman a saman auduga nake..!” Yai maganar yana d’an tsalle daga zaune saman kujerar... Sanyin AC ya dake sa yace “Allahu Akbar! Kai kaji Ni’ima kaman a turai.. Yo irin Ni’ima ai bazakso a isa yanda za’aje ba Yakubu.. Kai Yakubu kana hutawa fah..”

Ansar da idanunsa kega kwalta yace “Is the reward of my hard working Baffah..”

Yawale yace “Na’am mai kace Yakubu..?”

“A’a bance komai ba Baffah.. Nace tafiya mai d’an tsawo zamuyi..!”

Yawale ya kuma wage baki yace “Ai babu komai ni dama yau d’in babu yanda zanje... Yau ina mahaifinka yana raye yaga yanda Ka zama.. Allah sarki d’anuwna ba rabon yaga gurmanka ba..”

Gaba d’aya ya cika masa kunne lokaci guda ya murd’a radio yana fad’in “Baffah kaji radio kasan ba’a rabaku da ita..”

Daga haka bai kuma bitakan Yawale ba saima maida hankalinsa ga yuk’i da yayi.. Yawale Sai maganarsa yake shi kad’ai k’arshe dai har bacci ya soma d’aukansa basu isa yanda zasuje ba..

**

Kaman sauk’an aradu haka Raheemah dake asibiti wajen Yazeed ta tsinci zancen, sai huci take tana zagaya d’akin, tanata k’ok’arin neman layin Ansar amma bai shiga.. Ta buga tsuka tana fad’i a fili dole ta tafi Masarauta taje ta tsayar da wannan auren koda za’a mutu ne...
Muryar Yazeed Ta sinkayo cikin tsananin jinya yana fad’in “Please call me Mahmood and his wife... Dan Allah ki kira mun su...!”

Raheemah ta dubesa da mamaki tace “Mai zaka masu... Ina ruwanka dasu.. Ko bakaji cewa bukin aurensu had’eda nad’in sarautar Mahmood ake ba..?”

“Ki kira min su Raheemah..!” Ya kuma fad’in cikin rawar murya..

Raheemah ta girgiza kai cikin rashin yarda da abinda takeji “Yazeed mai zakaida mutanenda sune sanadin kasancewarka a asibitin nan.. Mai zaka ce masu..?”

Idanunsa na duban sama hawaye na ziraro masa yake furta “Just call them, Ina matuk’ar son Nayi magana dasu..Please ki kira min su, kimin wannan alfarmar..”

Raheemah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali had’ida jinjina kai.. “Fine zanyi yanda kace idan haka zai saka Farin ciki...”

Yazeed dake hawaye ya furta “Na gode..!”

Raheemah ta kuma dubansa cikin tsananin sanyin jiki Wai yau Yazeed ne ke godiya.. Ikon Allah kenan..
Tinda ta baro asibitin haka ta nufo Masarauta jikinta a matuk’ar sanyaye, saidai tinda ta iso Masarautar jikinta ya kuma yin sanyi ganin d’imbin Al’umman dake cikin Masarautar, ga algaita nata tashi ga Dogarai sai wasa Sarki da amaryar suke wacce itama amaryar sarkin d’iyar sarauta ce gaba da baya.. Gwiwoyin Raheemah suka kuma yin sanyi, sanda ta isa sashen Gimbiya Zeenat ta tadda ita kanta Gimbiya Zeenat d’in bata k’asa bata sama.. Sai kai komo Kuyangi suke a sashenta ana had’a kyautttuka na bajinta, na sarki daban na matarsa daban na mahaifiyarsa daban.. Baki sake Raheemah Ke dubanta yanda take bada umarnin inda za’a kai kyauttukan wanda aka rurrufesu saman manya manyan parantai masu ruwan zinari an rufesu da manyan k’yalle masu d’aukan idanu kaman yanda sukeyi a al’ada lokutan auratayyansu...

“Aunty kema murna kike da auren..?!” Raheemah ta tambaya jiki a sanyaye..
Chapter 151 · 0% Book details