Sashe 137
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ansar ya mik’e jiki a sanyaye yana furta “Ni zan koma Hibbah, I hope zakiyi abinda ya dace ... Ki k’wace ‘yancinki daga hannun mutumin da ya sayoki tamkar Baiwa a kasuwa..!” Yana ida fad’in haka Barde ya lek’o yana furta “Lokacinda mai Martaba ya d’ibar maka ya cika Bokan Turai...”
Ansar ya jinjina kai yana mai k’ok’arin saita kansa had’ida mik’ewa “Na barki lafiya Rankidad’e..!” Ya fad’i yana duban k’asa kana yasa kai ya fice yanda ya bar Muhibbah naci gaba da matsan hawaye zuciyarta na tsananin mata zafi...
A hanya Raheemah Ta had’uda Ansar ya fito daga Bargan dawakai ya zab’i doki mai kyau kaman yanda Mahmood yai masa kyauta...
Yai tsaye da mamaki yana duban matar data tsaya gaba garesa cikin tufafi irinta masu mulki ga Hadimarta guda tsaye bayanta...
“Lafiya..?” Ya furta yana dubanta...
Alama da hannu Raheemah taiwa Hadimar don ta basu waje...
Raheemah ta murmusa tace “Lafiya sai alkhairi..”
Shima murmusawan yai kad’an yace “Ban fahimceki ba.. Wacece ke..?”
“Call me solution to your problems..!” Tai maganar murmushi bai bar saman fuskarta ba...
Gajeren murmushi yai yace “I don’t get you..”
“Da sannu zaka fahimta tinda na kula kaima k’arfin mulki da iko aka nuna maka aka rabaka da masoyiyarka kaman yanda nima aka rabani da nawa masoyin aka aura min wanda bana so..”
Ansar ya dubeta da tsananin mamaki yace “Kina nufin yanda aka aura min wacce bana so kema haka aka miki..?”
Ta jinjina kai tace “K’warai kuwa and if you want Muhibbah back ni kad’aice zan taimakeka duk fad’in Masarautar nan..”
Yai K’uri yana dubanta sai kuma yace “How is that possible..?”
Raheemah ta murmusa kana ta mik’a masa wayar salulanta tace “Zuba digits d’inka a nan...”
Babu musu ya amsa ya hau zuba mata lambar wayan salulansa...
Ya amshi wayar bayan ya gama kana tace “Sai kaji daga gareni..” Daga haka sa kai tai Ta shige Hadimarta ta take mata baya..
Ansar yabi bayanta da kallo har ta b’ace masa cikeda mamakin makirce makirce dake cikin wannan masarauta.. Koda shike shi ina ruwansa idan dai zai samu Muhibbah ta dawo garesa, akan son da yakewa Muhibbah babu abinda bazai ba don kawai ta dawo garesa.. Bazai tab’a bari a rabasu haka kurum ba... Ya k’arashe yana mai jin zafin Wai Mahmood da gaske ya aure masa Muhibbarsa... Sabida tsaban an rainasa ma bacci akasashi yayi kafin akai masa wannan rainin wayon.. Yai k’wafa yana mai ayyanawa bazai tab’a hutawa ba har sai ya tabbata auren Muhibbah da Mahmood ya lalace..
**
A can b’angaren Ja’afar kuwa tun bayan da suka baro Bargan dawakai shida Baba Nomau ya nufo b’angaren Yazeed, tsaye yayi yana k’arema sashen kallo yana tuna abubuwa da na wulak’anci da tozarci da ya fuskanta daga wajen wad’annan ahali... A hankali ya soma takowa cikin sashen hannayensa hard’e ta baya yana mai kuma k’arema sashen kallo... Daga k’ofar Parlorn ya tsaya yana duban Yazeed dake zaune dirshan a k’asa hotonsa wanda da ka shigo parlorn zai maka marhaban cikin shiga irinta mulki aje gabansa ya tasa hoton gaba yana cazgan kuka kaman wani k’aramin yaro ga wasu Kuyangi tsartsaye gefensa suna bin umarnin da yake basu ba don sunso ba, harta abinci a baki suka basa da alama...
Suna ganin shigowar Ja’afar suka rirrisina suna kwasan gaisuwa.. J’afar ya amsa masu yana mai jinjina kai... Alama yaima Kuyangin da hannu kan cewa Su fice, babu shiri suka fice kawunansu gaba d’aya a k’asa...
Yai tsaye gaban Yazeed har lokacin hannayensa hard’e suke ta baya... Daga k’afafu Yazeed ke duban Ja’afar har izuwa Fuskarsa take yaji kaman an luma masa mashi a k’ahon zuciya, yai saurin rintse idanunsa dan bazai iya jure ganin wannan kayan bugawar zuciyar ba..
Ubandoma dake biyeda Ja’afar ganin yayi shiru yana k’arewa Yazeed d’in kallo ya sanyashi fad’in “Rankaidad’e mai kake so ayi dashi, a fattatakesa daga cikin Masarauta ne ko kuwa a fatattakesa ya koma can yanda aka fito.. Ma’ana b’angaren Bauta..!”
Hannu yasa ya d’an sosa kunnensa guda kana yace “Kasan idan mutum nada zuciyar musulunci duk yanda yaso rama mugunta bazai jura ba.. Kuma wad’annan ahali duk abinda zamu masu bazamu rama zalunci da sukaima Al’umma ba, ko a haka Sun amshi sakamakon duniya.. Right Yazeed..!” Ya k’arashe yana mai duban Yazeed dake zaune dirshan gabansa..
Yazeed bai iya amsawa ba saima dad’a kifa kansa da yayi...
Ubandoma ya kai masa shura da k’afa yana mai furta “Hattara D’an Bayi..! Tashi ka duk’a da kyau ka amsa Yarima... Yarima baya jiran amsa daga wajen k’ask’antacce Bawa irinka...”
Cikin tsananin huci Yazeed yake furta “I rather die akan na risina gaban wanda yake a matsayin Bawa na a baya...!” Ya k’arashe Wasu irin hawayen d’acin rai suna gangaro masa...
Ubandoma ya nufosa zai kai masa damk’a Ja’afar ya dakatar dashi ta hanyar d’aga masa hannu, murmushi saman fuskarsa ya kwanto da fuskar tasa dab kusan na Yazeed d’in “We shall see..! Bawa d’an Baiwa..!!”
Ya kuma murmusawa kad’an lokaci guda ya shiga zagaye tampatsetsten parlorn Yazeed d’in na alfarma, yana k’arema kayan alatu da aka k’awata Parlorn dashi kallo... Ya iso gaban family Picture d’in su Yazeed wanda yake manne cikin parlorn gwanin ban sha’awa... Yai K’uri yana k’arema picture d’in kallo, lokaci guda yake furta “How Pity..! You’re all alone now, they all left you..” Ya d’an girgiza kansa kad’an yana mai yin wani salo irinta tausayawa, lokaci guda yaci gaba da furta “Babu izza..! Babu sarauta..! Babu asali..! Babu mata..! Babu ‘ya’ya..!” Daidai lokacin ya kaikaito sosai yana duban Yazeed kana yaci gaba da fad’in “And what is worse, kaga wannan luxury d’in da kake cikin zakai bankwana da ita a yau domin kuwa angulu zata koma gidanta na tsamiya.. Za’a koma yanda aka fito.. Yankin bayi da Bauta...!” Ya k’arashe idanunsa tar kan Yazeed d’in wanda ya kasa gaskgata abinda yakeji daga bakin wulak’antaccen Bawan da ya raina a baya irin Ja’afar wanda ko yanda ya taka bai isa ya taka k’asar wajen ba, cikin wane irin yanayi yace “Ja’afar..! B’angaren Bayi fah kace.. Ni Yazeed ne zan koma rayuwa cikin Bayi..?!”
Ubandoma ya katsesa da fad’in “Hattara D’an Baiwa.. Ba’a jayayya da Yarima..!”
Yazeed ya had’iyi miyau da k’yar yace “Yarima..!” Yai maganar da k’yar kaman mai koyon magana..
Ja’afar ya kaikaito yana dubansa yace “Eh b’angaren bayi zaka koma Yazeed domin kuwa nan ne ya kamaceka..! Da ace ka zamto d’ah ga Maimartab watak’ila da an ajiyeka a gidan tsoffin k’wark’warorin Sarakuna wanda suke rayuwa da ‘ya’yensu amma martabarka da darajarka batakai nasu ba, sabida kaid’in ba ahalin gidan nan bane... Jinin k’ask’antacciyar Baiwa ce wacce taci amanan Ubangidanta... A b’angaren bayin ma yankin da zaku zauna kaida sauran ‘yanuwanka idan sun fito daga asibiti bazai kai na sauran bayi daraja ba domin kuwa kud’in maciya amanan masarauta ne...!” Ya k’arashe yana mai maidoda dubansaga Ubandoma... Murya a dake yaceda Ubandoma aima Yazeed rakiya zuwa sabon sashensa..
Daga haka bai kuma tsayawa jiran komai ba yasa kai zai shige abinsa Ubandoma yana fad’in “An gama Rankaidad’e..! Yazeedu godiya yake Rankaidad’e...!”
Da tsananin mamaki Yazeed ya koma tamkar an dasa a wajen yake duban Ja’afar har ya b’acewa ganinsa, ya nemi hawayen da suke zubo masa ya rasa, Ashe kuka ma rahama ne... Ji yayi inama zai iya ci gaba da kukan da yake da sai yafi masa sauk’i... Yanaji Ubandoma ya kamo hak’ark’arinsa ya mik’ar dashi tsaye yana fad’in “Maza a koma tushe, a koma yanda aka fito...”
Wai yau shi Yazeed, shi Prince Zeed ne aka maidosa sashen Bayi na cikin Masarautarsu... Masarauatr da yaci burin Mulka kowa ya zamto yana k’asa dashi sai gashi kowa ya zamto sama dashi, harta bayin da yake ganinsu k’ask’antattun yau sun fisa daraja a cikin Masarautar sa... Giwa itace Ta jawo masa wannan k’ask’anci wanda gwara ya mutu da yaga irin wannan rana...Gwara ya kashe kansa da yaga irin wannan takaici..
**
Jiki a matuk’ar sanyaye ta nufi sashen Gimbiya Turai tana ganin hanya na had’e mata kalaman Ansar suna kuma buga kwanyarta
_Ked’in sayoki yayi, satoki yayi, bakida wani daraja a idanunsa kuma bazaki tab’a yin daraja a idanunsa ba, k’arfin mulki ya nuna akanki, don yayi amfani dake kawai wajen cimma burinsa ya dawo dake cikin Masarautar.. Kuma burin nasa ya cika tinda kika taimaka masa ya fidda Giwa da ahalinta daga cikin Masarautar_
SameenaAleeyou 📚
*MUHIBBAH*
*79*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
A parlor ta tadda Gimbiya Turai taredasu Umaima da Zahra, Hadimai sai sintiri suke tsakanin sashen ana kawo mata kyauttutuka daga matayen masu muk’amin gargajiya kaman yanda yake a al’adance...
Yanayin da sukaga Muhibbah ciki sosai ya basu tsoro, Umaima ta mik’e da sauri ta isa ta kamo hannunta tana tambayarta meke faruwa.. Duban Umaima takeda idanunta masu zuban ruwa, lokaci guda Ta rungume Umaima kuka na kuma kufce mata...
Zahra da Umaima suka dubi juna yayinda Gimbiya tai alamawa Hadiman da hannu cewa su fice su basu waje...
Hannun Muhibbah Umaima ta kamo suka k’araso saman Darduman da suke zaune bisa itada Zahra kana ta zaunar da Muhibbar...
Zahra ta matso had’ida mata k’uri murya a hankali take furta “Tia.. Is all well..? Lafiya kike kuka haka..? Kodai Giwa ce ta dawo cikin Masarautar..? Talk to us please..!”Ta k’arashe fuska fal damuwa...
Umaima Ta kamo hannun Zahra tana mata alamu da ido kan tai shiru ta daina jerowa Muhibbah tambayoyi irin haka...
Gaba d’aya sukai mata K’uri suna duban yanda take k’ok’arin daidaita kanta tana share hawayen dake mak’ale cikin idanunta...
D’agowa tai ta dubi Gimbiya Turai, muryarta na tsananin rawa tace “Ummi da gaske Rankaidad’e ne ya aureni..? Da gaske shine mijina..?!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya..
Zahra da Umaima suka dubi juna suna masu shan jinin jikinsu...
Gimbiya tai masu umarni su fice su basu waje itada Muhibbah..
Jiki a sanyaye Umaima ta janyo hannun Zahra suka nufi k’ofa, Zahra na fad’i k’asa k’asa “Kina tunanin bazata amince da auren Paa d’ina ba.. But I thought they loved each other.. And they’ll make a perfect couple together...!” Ta k’arashe cikeda kulawa..
Umaima ta girgiza kai kad’an tace “Just shut up Zahra, and stop meddling...”