Sashe 22
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jakadiya ta girgiza kai a hankali alamun a’a...
Giwa Ta jinjina kai cikeda k’asaita kana taci gaba da fad’in “Umaima zata min amfani nan gaba kad’an a shirina Jakadiya... A halin yanzu Umaima ta gama aminta ni d’in Sarauniyar K’warai ce mai kimanta adalci da k’aunan jama’a... Dik abinda zan bijiro mata dashi nan gaba kad’an bazata watsa min k’asa a idanu ba, dan Haka Jakadiya koda wasa kar na sake zartar da hukunci cikin Masarautar nan mu samu sab’anin ra’ayi, duk abinda nayi ko zanyi ki ya zama wajibi akanki ya zama dole Ki aminta dashi... Da ace wata ce cikin bayi tayi wannan magana ba ke ba Jakadiya da yanzu ta jima a barzahu...!”
Jakadiya Jiki na matuk’ar rawa take fad’in “Tuba nake Allah ya taimakeki... Allah ya huci ran Giwar Amale... Jakadiya tana neman afuwanki Allah ya baki yawan rai...!” Ta k’arashe tana mai d’ago hannu daga nan durk’ushe alamun jinjina...
Shigowar Jamal ya sanya Jakadiya mik’ewa Ta basu waje bayan ta gama kwasan gaisuwa wajen Yarima Jamal....
Cen saman kujera na alfarma dake gefe cikin d’akin ya zauna... Mahaifiyar tasa ta dubesa kana tace “Baba na ya haka... Ya na ganka haka, akwai matsala ne...?”
Jamal ya fuzar da huci a hankali kana yace “Maami magana ce kan Ya Mahmood...!”
Ta gyara zama sosai tana duban Jamal kana tace “Umhum Ina saurarenka, mai kuma ya faru da Mahmood d’in...?”
Shafe fuskarsa Jamal yai da duka tafukan hannayensa kana yace “Maami Wai kinsan d’iyarsa Zahra ba Aliya bace ta haifeta... Yarinyar bada aure ya haifeta ba...!”
Shiru Giwa tai tamkar mai nazari tana mai kuma tabbatar da zarginta kan lamarin yarinyar, Toh amma saidai abu ne mai kaman wuya ace Mahmood zai aikata wani abu makamancin wannan, idan za’a saka mata takwabi zata iya rantsuwa d’anta Mahmood bazai tab’a aikata mummunan sab’o irin wannan ba... Ance ba’a shaidan d’an adam amma ita tayi shaidan Mahmood... Toh yaya akai hakan ta kansance...?
Muryar Jamal ya dawo da ita daga Duniyar tunani yanda yake fad’in “Maami abin ya matuk’ar bani tsoro da mamaki... Ya za’ace Yaya ya aikata babban abin kunya irin wannan, Maami bayyanar wannan magana barazanace garemu baki d’aya....!”
Dubansa ta d’anyi kana tace “Babu wanda zai sani, kuma kaima banaso ka nuna masa kasan komai, maganan zai zauna a haka kaman ba’ayi ba....!”
Su duka biyu sukai shiru kowa na sak’awa da warwarewa cikin zuciyarsa....
**
A b’angaren Mahmood kaw tinda aka fito daga masallacin Juma’a ya b’adda kama ya fice ya nufi gidan D’an uwan mahaifinsa Dattijo Baba Wambai, ko Ubandoma baisan ya fice ba, sannan ko motar Masarautar bai d’auka ba, hasalima motar haya ya shige ya nufi gidan Baba Wambai....
Tamkar wani buzu haka yasha rawani ya nad’e fuskarsa, a k’ofar gidan ya tsaya yanda ya tadda wani yaro ya taho zai shige k’ofar gidan..
Yarima Mahmood yai kiransa kana yace “Kai yaro shin kana shiga wannan gidan...?”
Yaron ya jinjina kai alamun eh kana ya k’arada “Amma matar gidan masifaffiya ce tana koranmu idan mun shiga d’iban ruwa....”
Yarima Mahmood da ya b’adda kama zuwa bak’on Buzu yace “Ka shiga ciki kace ana sallama da Baba Wambai.... Idan an tambayeka inji Wanene kace bak’on Buzu ne...”
Yaron ya jinjina kai yana mai amsawa kana ya nufi cikin gidan...
Jim kad’an saiga Baba Wambai ya fito a daddafe yana rik’eda yaron yake fad’in “Kai Muntaqa ka faye wasa gaban famfo shiyasa Innani Ke korinka, muje naga bak’on Buzun....!”
Yaron yai masa nunida yanda Yarima Mahmood ke tsaye kana yace “Gashi nan ai Baba...!”
Baba Wambai yakai dubansa ga mutumin saidai duba d’aya yai ma k’wayar idanunsa ya fahimci Mahmood ne...
Ya saki murmushi a hankali kana yace “Mahmuda kaine tafe da tsakar ranan nan...?”
Yarima Mahmood ya d’an murmusa kad’an yana mai jinjina kai yake furta “Ai nayi zaton bazaka ganeni ba Baba...”
Murmushin Baba Wambai ma yayi kana yace “Yo banda abinka Mahmooda dik yanda zaka kai ga canza kamanni ai bazaka b’ace min ba... Wannan idanu nawa da kake gani tarau yake, gashi gidanmu munyi gadon ciwon ido amma ni nawa har yafi Naka mai cikeda k’uruciya.... K’araso daga ciki....!”
Mahmood ya d’anyi still a wajen yana mai rik’o hannun Baba Wambai yake fad’in “A’a Baba Wai da nafiso mu zauna daga waje don banaso wani ma yasan nazo shiyasa na b’adda kamanni....”
Baba Wambai ya jinjina kai kana yace “Kayi gaskiya Mahmuda, hakan da kayi kayi daidai, mu k’arasa k’arkashin bishiyar Gamjin cen....!”
Mahmood ya jinjina kai yana mai taimakawa Baba Wambai har suka isa k’ark’ashin bishiyar, suka zauna saman manyan reshen bishiyar da suka sauk’o k’asa.....
Bayan sun gaisa Baba Wambai yace “Ina saurarenka Mahamuda, meke tafe dakai...?”
Mahmood ya d’an gyara zamansa had’ida kwance rawanin kad’an kana ya soma fad’in “Wato Baba kan mafarkan nan ne da suka addabeni wanda babu daren da zaiyi na kwanta bacci na tashi ba tareda nayisu ba... Abun ya fara damuna sosai Baba....!” Ya k’arashe cikeda kulawa...
Dattijo Wambai yai K’uri yana duban wani gefen kana yace “Mahamuda dik yanda akai wannan mafarkai naka da kake yawanyi sunada manufarsu... Banida ilimin fassarar mafarki amma koma minene Allah shi yasan maiyasa yake nuna maka abu makamancin haka cikin baccinka.... Wasilci na farko da zanyi maka shine kaci gaba da k’ok’arin kwatanta rik’o da addini... Sannan abu na gaba kaci gaba da taka tsan tsan cikin wannan gida D’ah na...! Gidan sarauta gida mai kafi da abubuwa na ban mamaki had’ida tarihi.... Kasa ma ranka babu wanda ya isa ya cutar dakai face da izinin mahaliccinka... Sannan ka tausaya ma wad’anda suke k’asa dakai domin ka samu sauk’in gudanar da al’amara daga wajen mahaliccinka....”
Yarima Mahmood ya jinjina kansa a hankali kana yace “In sha Allah zan yi k’ok’arin kwatanta dik abinda ka umarta Baba...”
Baba Wambai ya jinjina kansa alamun gamsuwa kana yace “Sannan abu na gaba shine tunda yanzu Allah yasa ka dawo, kaci gaba da abinda iyayenmu suka rik’e gidan dashi, don na tabbata tun bayan rasuwar mahaifinmu Sarki Kakanka mai rasuwa aka daina wannan kyakkyawar d’abi’a a cikin gidan....!”
Ya d’an dubi Baba Wambai kana yace “Me kenan Baba...?”
“Duk ranan Juma’a akanyi sauk’an alkur’ani mai girma cikin fada sannan mahaifinmu yakan fita masallacin juma’a ya raba sadaka ma yara da gajiyayyu sannan yakan sauya kama ya zaga ya duba marassa lafiya wasu lokutan harma da gidajen marayu...da kuma kasuwanni domin yaga mai yake wakana a k’asarsa. yakan kuma kai ziyara gidan yari yaga halinda fursunoninsa Ke ciki....Duk wad’annan d’abi’u ne masu kyau wanda shugaba idan ya suffanta dasu tabbas yayi koyi da shugabbannin K’warai.... Tin bayan rasuwar mahaifinmu aka daina gudanar da irin wad'annn al'amara a Fada... Daga nan abubuwa suka rikice, domin kaw duk gidan da ba'a ambaton Allah cikinsa wannan gida tamkar kufai ne....”
Mahmood yai shiru yana mai jinjina kansa kana yace "Haka ne Baba, in sha Allah za’aci gaba da sauk’an alk’ur’ani mai Girma duk juma’a cikin gidan kaman yanda akeyi a baya....”
Baba Wambai ya jinjina kai yana mai furta “Masha Allahu... Hakan yayi kyau Mahmuda, Ubangiji ya maka Albarka ya tsareka da tsarewarsa daga dikkan sharri da zai tunk’aroka...”
Mahmood ya amsa da Ameen kana ya jefowa Baba Wambai tambayar da ya sanyashi d’agowa sosai yana dubansa...
“Baba nikam nace ba, shin kasan lokacin da Ja’afar ya tafi ya bar Masarautar nan..? Shin dama Bawa na iya tsallake Masarautar su ne ya tafi wani wajen....? Shin Baba mai yasa Ja’afar ya tafi rana tsaka yabar Masarautar nan...? Kanada wata masaniya akai ne Baba....?”
SameenaAleeyou 📚*MUHIBBAH*
*017*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
A hankali Baba Wambai ya sauk’e ajiyan zuciya kana ya kuma duban Yarima Mahmood a karo na biyu....
“Baba akwai wani abu ne...?” Mahmood d’in ya bid’a..
Baba Wambai ya girgiza kai a hankali alamun a’a kana yace “Banida masaniyar abinda ya fitar da Ja’afar daga Masarautar nan... Kaman yanda ka dawo ka tarar baya nan, nima kwatsam na fahimci baya nan, Mahmuda abubuwa da dama cikin Masarautar sai ayi ban sani ba... Inaga idan akwai wanda yafi cancanta ya amsa maka wannan tambaya taka toh ba kowa bace face mahaifiyarka, sai ko kuma Waziri....!” Ya k’arashe yana duban Mahmood d’in....
Shiru ya d’an gifta tsakani ba tareda ya kuma cewa komai ba, tabbas yana so ya nemo Ja’afar yanda ya shiga ya fita.... Ya kuma d’agowa ya dubi Baba Wambai kana yace “Na gode Baba, ni zan wuce...!” Yai maganar yana mai k’ok’arin mik’ewa tsaye...
Baba Wambai ma k’ok’arin mik’ewan yake saidai tuni Mahmood ya taimaka masa ya mik’ar dashi tsaye had’ida rik’e hannunsa guda.... Lokaci guda suka nufi k’ofan gidan Baba Wambai a haka, yayinda Dattijo Wambai yaci gaba da fad’in “Sarkin gobe bazaka sha ko ruwa gidan Baban naka ba...?”
Murmushi saman fuskarsa yake fad’in “A’a Baba na gode k’warai, Allah ya k’ara maka lafiya.....!”
Baba Wambai ya amsada Ameen yana mai ci gaba da sakawa Mahmood Albarka, a daidai sanda suka iso Gate d’in gidan...
Baibar k’ofar gidan ba har saida ya tabbata Baba Wambai ya shige ciki lafiya kana ya matsa daga wajen ya ciro wayarsa a aljihu yana neman layin Turaki...
**
Giwa dake tsaye tana huci had’ida aikama Ubandoma dake duk’e gabanta jahilin kallo, lokaci guda Ta ambato sunan Ubandoman cikin wane irin kakkausar murya...
Ubandoma ya risina yana mai amsawa had’ida kirariwa shugabar tasa...
Giwa da kanta Ke sama tana duban wani gefen cikin tsananin k’unan rai taci gaba da fad’in “Zaka amshi horon mari daga hannun Jakadiya..!”
Jakadiya da Ubandoma suka dubi juna a tare cikeda firgici....
“Jakadiya..!!!” Giwa Ta kuma ambato sunan Jakadiya cikin kakkausar murya...
Babu shiri Jakadiya ta risinawa tana mai furta “Angama rankishi dad’e, Ubandoma godiya yake...!”
yayinda Ubandoma ya baje babbar riga yana mai kuma neman gafara wajen Giwa, Jakadiya ta mik’e tana nad’e hannun rigarta su duka biyun duban juna suke itada Ubandoma... Yana k’yafata mata idanu had’ida had’e hannayensa biyu waje guda alamun neman afuwa...
Gigirza masa kai kurum Jakadiya takeyi alamun batada zab’i...
Ubandoma ya kuma risinawa yana fad’in “Rankishi dad’e a duba lamarin nan dai.. Ai mani aikin gafara bazan sake ba Allah shi taimakeki....!”