← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 162

Sashe 91

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Raheema ta rausayar da idanu tace “Ai kama kasan nid’in bata wasa bace na d’ara matarka sau babu iyaka, kuma duk cikin matan da kake Mu’amala dasu babu wacce takaini... Aini bari kaji Yazeed duk d’ah namijin da ya riga ya shiga hannuna toh fah zai wuya ya iya manceni... Haka nan nake da tsayuwa a zuciya, ko shi Mahmood d’in da yake wani jin kansa yana ganin ba auren soyayya zai dani ba auren jeka nayika ne kawai to save his daughter da zaran ya shigo hannuna Ina mai tabbatar maka zai sauk’e wannan jin kan nasa ya susuce akaina... Daga nan sai yanda nayi dashi nayi da d’iyarsa, kai k’arewa wannan shegiyar d’iyar tasa da ya samota Ta gurb’ataccen hanya sai na rabasa da ita dan bana buk’atan bastard child d’insa a gidana... ‘Ya’yan sunnah zan haifa masa...!!”

Yazeed bai daina shafa hab’arsa ba idanu a kannare yake dubanta, lokaci guda yaci gaba da furta “Allah Sa Ki jure rashina kusanki dan Yaya na bazai iya dake kaman yanda ni na iya dake ba...!”

Raheema Ta kuma murmusawa tace “Haka kake tunani.. Ai ba’a sanin maci tuwo sai miya ya k’are... Kai ko a ido kasan Yarimana Gwarzo ne ba rago ba... Wani abin ma sai mun d’aga zuwa k’asar Spain na kashesa da kissa da makirci tinda na kula asiri bai tasiri akansa... Da kissa zalla zan rabasa da wannan shegiyar d’iyar tasa muci soyayyarmu a k’asar Spain...!”

Yazeed ya kuma murmusawa yace “Toh Nidai kar a cikani da zancen Mahmood, tinda yau d’in gaba d’aya nawa ne..!” Ya k’arashe yana mai kuma janyota kusansa...

Raheema na murmushi take furta “Karka damu ai yau d’in gaba d’aya takace dan ko masarauta babu wanda zai San nazo... Till down za...!!” Bai juri k’arasa sauraren maganganun nasu ba yai saurin juyowa idanunsa na kuma kad’awa... Saidai d’aga idanun da zai yaga Zuhra tsaye tana hawaye...

Mahmood ya dubeta da mamaki sai kuma ya juyo yana duban k’ofan parlorn, bazaiso ta shiga taga wannan mummunan cin amana da k’awarta da mijinta sukai mata ba...
Ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali dan baisan da mai zai soma ma Zuhra ba...

Zuhra na hawaye take girgiza bata tsaya sauraren Mahmood dake k’ok’arin dakatar da ita ba ta finciki k’ofar parlorn....

A wane irin firgice Raheema ta mik’e zuciyarta na kuma tsinkewa...

Hawaye na gangaro mata take dubansu... Take Raheema tai saurin kame bakinta had’ida d’aura hannu aka... Lokaci guda ta silale saman gwiwoyinta tana duban Zuhra dake zuban hawaye... “Zuzu wllhi ba yin kaina bane... Zuzu dan Allah Ki yafe min...!!”

Yazeed ne ya katseta da fad’in “Ke dallah shut up... Kar Ki ishe mutane... Uban mai akai mata...?!”
Ya dubi Zuhra dake tsaye wajen idanunta sun kad’a sunyi jazir yace “Ke Uban mai ya kawoki wajen nan..? How did you get here..? Da izinin wama kika fito...?! Zaki bud’e baki kiyi magana ne Ko sai na K’araso wajen na faffalla miki mari..!!”

Cikin tsananin huci Zuhra Ke furta “Try it please...! Ka kwatanta marina Yazeed, yau ni kuma zan nuna maka jinin mulki da sarauta na nan na Yawo jikina... Azzalumi macuci maci amana... Ka cuceni ka zalunci yaranmu tirr ace kaine mahaifin ‘ya’yana... Nayi nadaman had’a zuri’a dakai, amma ka saka a ranka daga yau ni Zuhra na gama zaman aure dakai... Kuma ka jira hukuncin da zan yanke..!!!”
Tana ida fad’in haka tasa kai zata juya... Raheema tai saurin rarrafawa ta kamo bakin zaninta... “Aminiyata dan Allah Ki yafe min, wllhi sharrin shaid’an ne kuma tilasta min Yazeed yayi... Wllhi ba halina bane... Dan Allah karki bari Yarima Mahmood yaji wannan batu nayi imani fasa aurena zai... Dan Allah Zuhra kimin rai kimin wannan alfarmar kinji k’awata...!”

“K’awa...?!” Zuhra Ta nanata tana dubanta, lokaci guda tai murmushi wanda da gani kasan na takaici ne “Amma lallai na yarda Raheema bakida kunya, kuma baki gaji kunya ba... Anya Ke jinin babban Gida ce... Babu Gimbiya ko Sarauniya da zata watsar da kanta taci mutuncin kanta kaman yanda kikayi... Wllhi ko a haka kin shafawa Masarautarku b’ak’in fenti wanda zai wuya ya shafe.. Bani kika cuta ba Raheema..! Kanki kika cuta.. Kin cuci rayuwarki, kin kwab’ar da duk wani daraja da k’ima da Allah yayi miki a matsayinki na d’iya mace... Kin yaye Hijabin mutunci da Allah ya halicceki da ita... Kin..!”

Yazeed ya katseta da fad’in “Idan kin gama wa’azin naki ki fice kuma kije ki jirani a gida... Ina nan zuwa dan wllhi kinji na rantse sai na hukuntaki..!!”

Zuhra ta d’ago tana watsa masa duban k’yama... Lokaci guda Ta murmusa tace “Zakasha mamaki irin wanda baka tab’a sha ba Yazeed..!!”
Daga haka fincikan mayafinta tai daga hannun Raheema had’ida shureta da k’afarta tasa kai Ta fice abinta... Zuciyarta na tsananin mata zogi...

Tana fitowa ta tadda babu Mahmood alamun ya tafi... Mota ta shige ta kifa kanta tana kuka sosai... Driver d’in da Hadimarta dake jiranta daga nan waje cikin mota abin sai ya masu wane iri ganin shugabar tasu tana kuka..

Hadimar tata ta umarci driver d’in ya fice daga cikin motan ya d’an basu waje taji damuwar Uwargijiyar tata...
Driver yayi yanda tace

Hadimar ta d’an risina tace “Rankidad’e kuka bai kamaci kyakkyawar Gimbiya irinki ba... Ko akwai abinda zan iyayi na tsaida hawayen shugabata masu tsada su daina zuba..?!”

Zuhra ta d’ago Tai k’ok’arin saita kanta “Babu komai Hindu kiyi magana ma driver ya shigo mu koma masarauta...!”

Baiwar data kira da Hindu ta dan jinjina kai sai kuma tace “Ki gafarceni ya Shugabata, Kodai wani abin tashin hankalin kika gani cikin gidan nan..?!”

D’an daka mata tsawa tai da fad’in “Nace miki babu komai Hindu, Ki kirawo Driver mu tafi... Bana son gardama..!!”

Hindu Ta risina tace “Tuba nake Rankidad’e... Kimin aikin gafara..!!” Ta k’arashe tana mai bin umarnin shugabar tata...

Har suka isa masarauta Zuhra bata daina matsan k’walla ba tana tina kalan cin amanar da K’awarta aminiyarta da mijinta sukai mata...
**

A b’angaren Mahmood kaw tinda ya bar wajen yake falfala gudu saman kwalta, clash Turaki yayi da motar tasa yai saurin takewa Mahmood d’in baya... Ganin irin tuk’in da yake kaman wani mai shirin barin gari yasa Turaki umartan mai tasi d’in yasha gaban motar Mahmood...
Haka mai tasi d’in ya k’ure malejin motar saida suka cimma Mahmood d’in... Turaki ya sallami mai tasi kana ya nufo yanda Mahmood d’in ya paka motarsa....

“Rankaidad’e Wai mai ya faru...? Ina Zahran...? Ya na ganka kai kad’ai, badai wani abin sukai mata ba koh...?!” Ya k’arashe cikeda kulawa...

Mahmood ya d’ago rinannun idanunsa yana duban Turaki dasu... Sosai Turaki ya razana da yanayin abokin nasa... Murya na rawa yake furta “Rankaidad’e... Kamin magana dan Allah...!!”

Bud’e masa lock yai ba tareda yace komai ba, Turaki ya shige cikin motar Jiki a matuk’ar sanyaye dan shi dik a zatonsa wani abin ne ya sami Zahra...

Suna tafe a motar babu mai cewa uffan, sai falfala gudu da Mahmood keyi dasu bisa kwalta... Idan ya danna birki saidai Turaki ya dubesa, Turaki ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali har suka iso wani waje mai yawan ciyayi da duwatsu... Shidai Turaki duban Mahmood d’in kurum yake a matuk’ar tsorace da yanayin nasa...

Murya can k’asa yace “Kenan a wannan dajin suka b’oyeta...?!”

Sai lokacin Mahmood yace “Ita wa..?!”

Turaki da mamaki yace “Rankaidad’e Zahra’u nake nufi...!”

Nusawa Mahmood yai kad’an kana ya juyo yana duban Turaki idanunsa na kuma kad’awa, ya fuzar da fuci mai d’umi yana shafe fuskarsa da tafukan hannayensa... Lokaci guda ya zauna saman Dutse guda d’aya had’ida kalmashe k’afarsa guda...

Turaki ma ya k’arasa ya zauna jikina sanyaye “Rankaidad’e...”

Bai bari ya ida fad’in abinda zai fad’i ba yace “Zahra bazatai wannan tunanin ita kad’ai ba... Ta yaya ma zata San cewa akwai wata alak’a mai muni tsakanin Yazeed da Raheemah... Dole akwai wanda ya shirya mata hakan..!” Ya k’arashe yana mai duban Turaki...

Turaki da gaba d’aya ya zama confused yace “Your Highness... Ban fahimceka ba.. Wai meke faruwa ne..?!”

Cikin kalmomi k’alilan Mahmood ya sanar dashi abinda ya faru a gidan da sukai zaton an aje Zahra...

Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un Turaki Ke nanatawa yana jinjina lamarin “Turk’ashi..!” Ya d’an nusa kad’an sai kuma yace “Abokina Allah ne ya soka da alkhairi ya nuna maka hakan tun kafin akaiga aure... Amma kuma maganarka akwai k’amshin gaskiya cikinta Rankaidad’e, Zahra bazata iya tsara wannan abin ba, dole akwai wanda ya tsara mata hakan... Toh amma wa kenan..?!”

Mahmood ya d’an dubesa yace “Na tadda Zuhra matar Yazeed a wajen wanda bansan ya akai taje wajen ba... It might be possible Zuhra tasan komai tuntuni ko tana zarginsu sai ta had’a wannan plan d’in domin ta kamasu red handed..”

Turaki ya jinjina kai yace “Kaji tunani na manya.. Tabbas haka ne Rankaidad’e, kuma ko acan asibiti ma an tabbatar mana Zhara tajeta tareda wata mace... Ko shakka babu hakan ne..!”

Mahmood yai shiru tamkar mai nazari har lokacin ransa a matuk’ar b’ace yake.. Turaki ya d’an sadda kai yace “Hak’uri zakai Rankaidad’e, ita rayuwa...”

Duban da Mahmood d’in ya aika masa ya hana Turaki k’arasa magana.. Lokaci guda Mahmood d’in Ke fad’in “Maiyasa kake bani hak’uri bayan nan tab’a sonta ba... Abinda ya dameni shine involving Zahra da akai... Bai kamata tasan ire iren wad’annan abubuwan ba... Why must she involve my daughter, da ni ta samu da batun yafi Ta samu d’iyata da irin wannan batu...!” Ya k’arashe cikin tsananin nuna b’acin rai...

Turaki ya d’an shafi kansa yace “Haka ne Rankaidad’e amma kasan ba kowa zai iya samunka da wannan batu ba... Watik’ila shiyasa Ta biyo Ta wajen Zahra...!”

Mahmood ya katsesa da fad’in “That doesn’t justify what she did....she shouldn’t have involved my daughter... !!”

Turaki ya risina yace “Allah ya huce zuciyar Sarki... Tuba take Allah shi taimakeka, itama na tabbata tana cikin tashin hankali tinda Yazeed mijinta ne... A gafarceta Rankaidad’e..!!” Ya k’arashe yana risinawa gaban Mahmood d’in...

D’an girgiza kai kurum Mahmood yai yace “Tashi mu tafi...!”

Babu musu Turaki ya mik’e yana fad’in ya kamata suje masarauta suga halinda Zahra ke ciki... Yai maganar yana mai amsar car keys d’in Mahmood d’in....

**
Chapter 91 · 0% Book details