← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 162

Sashe 136

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turaki ya d’anyi jim kansa a k’asa yake furta “A dai duba lamarin Rankaidad’e.. A basa wannan damar duba da matsayin da ahalinsa kedashi wajen Muhibbah.”

Ya tsare Turaki da idanu na wasu dak’ik’ai kana yakai dubansa gefe, a hankali ya jinjina kansa yana mai furtawa da k’yar “Send him in..”

Turaki ya murmusa yana duban Mahmood d’in “Godiya yake Rankaidad’e..” Ya k’arashe yana mai d’ago masa babban yatsarsa guda alamun jinjina...

Bai kuma bi takan Turaki ba ya k’arasa saman kujerarsa yai zama irinta masu mulki yana jiran shigowar Ansar...

Kan Ansar a k’asa ya shigo Barde na biyedashi yana kod’a Sarki Mahmood mai jiran nad’i , Ansar ya k’arasa ya zauna saman Darduman dake gaban Mahmood had’ida masa gaisuwa irinta masu mulki... Da kai kurum Mahmood ke amsawa yana karantar Ansar d’in da idanu, sam shi bai yarda dashi ba...

Barde ne Ke amsa gaisuwar da fad’in “Sarki ya amsa maka Likita Bokan Turai.. Jaaa zamanin Sarkin Sarakuna...”

Ansar yaci gaba da furta “Godiya nake Rankaidad’e.. Akan hanya nake yau in sha Allah zan koma gida shine nace b’arin shigo nai maku sallama.. Allah shi taimakeka..!” Yai maganan yana dunk’ule hannunsa guda had’ida mik’a jinjina ga Mahmood d’in...

Shiru ya ratsa tsakani sai sautin kirari kawai da Barde keyiwa Mahmood “D’awisu Sarkin kwalliya.. Kaga d’an jimina gagara d’aukan shaho..! Girgije sa gabanka yanda kake so.. Dogon Sarki mai dogon zamani.. Allah shi jaa zamaninka...”

Ansar ya zaci Mahmood d’in bazai kuma fad’in wata kalma ba har saida ya d’an d’ago ya dubesa.. Ya soma k’ok’arin mik’ewa yana furta “Idan Sarki yamin izini ni zan wuce...Na barku lafiya your Highness..”
Yai maganan yana mai risinawa...

Ya kuma jinjina masa kai ba tareda ya furta koda kalma guda ba...

Barde ya soma k’ok’arin rakiyawa Ansar yana furta “Sarki ya maka izini Likita..”

Gyaran Muryar Mahmood da suka sinkayo ne yasasu dakatawa Barde na k’ok’arin k’arasowa cikin d’an gudu gudu ya zube gaban Sarkin...

Murya can k’asa yake furtawa Barde a zab’awa Ansar doki mai kyau cikin Bargan Fada sannan ai masa rakiya wajen Gimbiya Muhibbah..

Barde ya jinjina masa yana mai furta “An gama Rankaidad’e.. Godiya yake..”

Ansar Wanda a gabansa akai maganan amma tsaban mulki ba’ayi direct to shi ba sai ya dawo da baya ya risina yana fad’in “Godiya nake Rankaidad’e.. Amma da dai an bar dokin..”

Baikai aya ba Barde ya katsesa da fad’in “Hattara Bokan Turai, Sarki baya kyauta a dawo masa..”

Ansar ya had’iyi abinda ya tsaya masa a mak’oshi... “Godiya nake Rankaidad’e..!” Ya fad’i tareda jinjina..

Har sun soma tafiya suka sinkayo muryarsa mai amo ya amsa illahirin parlorn cikin yin gyaran murya, babu shiri Barde ya koma da baya ya zube..
Mahmood ya d’ago yatsarsa yayi alama guda d’aya biyu zuwa uku, kaman wanda baison magana ya furta “Minti uku kacal..”

Barde ya jinjina kai yana mai furta “An gama Rankaidad’e...”

Barde ne kawai ya fahimci Sarki na nufin minti uku kacal aka baiwa Ansar yayi sallama da Gimbiya... Shikam Ansar d’in bai fahimci komai ba dan ba wani gane yaren sarakunan yake ba...

**

Tsaf Ta shirya cikin wani lallausan leshi da akai masa d’inkin riga da skirt, sosai ya amsheta, Ta jima tana duban kanta jikin full-length mirror abubuwa da dama suna zuwa zuciyarta, kaman anyi ruwa an d’auke Wai yau babu su Giwa cikin Masarautar.. Allah kenan Buwayi gagara misali... Ta tako a hankali tana mai tuna daren jiya da abinda suka faru, zama tai bakin gado tana mai kuma nanata lamarin cikin zuciyarta..Tana nan a haka Hadimarta ta nemi izinin shigowa kana ta shigo kanta a k’Asa bayan Muhibbar ta mata izini..

“Ki gafarceni Rankidad’e, Barde yace in sanar dake kinada bak’o a waje...”

“Bak’o.!” Ta nanata a hankali tana tunanin waye ma Barden.. Ta dubi Hadimar kad’an tace “Wanene Barde..?”

Hadimar ta kuma risinawa tace “Amintaccen Hadimin Sarki Mahmood mai jiran nad’i kenan Allah shi taimakeki..”

Muhibbah tai shiru kaman mai tunani sai kuma ta jinjina kai a hankali tace “Kije ki tambayo ko wanene bak’on..”

Hadimar ta kuma jinjina kai had’ida bin umarnin uwargijiyarta..

Jim kad’an ta dawo ta risina tace “Allah shi taimakeki kaman yanda Barde ya sanar dani, Maimartaba Sarki Mahmood ne ya turosa..”

Tai still tana duban Hadimar, jinjin kai tai a hankali tace “Kije ki sanar dashi ina tafe..”
Hadimar ta amsa cikeda girmamawa kana ta fice...

lokaci guda Muhibbah Ta mik’e had’ida janyo alkyabbarta ta rufa bisa kanta, A parlor Ta tadda Hadimar tana jiran fitowarta lokaci guda tai mata jagoranci zuwa wani madaidaicin parlor a k’asa...

Ga tsananin mamakinta Ansar ta gani, ta saki murmushi a hankali shid’inma murmushin ne saman fuskarsa...

Yana hangota ya mik’e tsaye yana jin zuciyarsa na fuzga kaman zai fasa k’irjinsa ya fito waje...

Tana K’arasowa ya silale k’asa hm had’ida d’ago babbar yatsarsa alamun jinjina gareta “Rankidad’e..!”

Dariya yaso bata amma sai ta murmusa kawai ta k’araso ta zauna saman kujera tana mai furta “Ka tashi ka zauna idan ba so kake nima na duk’a gaba gareka ba..”

Ya mik’e da sauri yana murmushi ya koma saman kujera ya zauna had’ida furta “Wane ni Gimbiya Ta zauna k’asa gabana.. Ai sai kisa na koma garinmu da k’afa guda..”

Nan ma murmushi kawai tai wanda da gani na k’arfin hali ne..

Shiru ya ratsa tsakani zukatansu saiko bugun zukatansu, gaba d’aya sai tana jin wane irin nauyinsa..

Muryarsa Ta sinkayo yana furta “Cant I talk to my sister in private..?” Yai maganar yana duban Hadimar dake tsaye gefen kujerar da Muhibbah Ke zaune bisa kanta a k’asa...

D’agowa Muhibbah tai Ta dubi Hadimar tai mata alama da hannu kan cewa Ta fice daga parlorn.. Hadimar ta risina tayi yanda Muhibbah ta umarta...

Shiru ya d’an ratsa tsakani kana Ansar yai gyaran murya ya soma fad’in “I know by now kinada masaniyar cewa ba’a d’aura mana aure ba..”

Ta d’an d’ago a d’an firgice tana dubansa, Ansar ya jinjina mata kai alamun Tabbatarwa yace “Muhibbah ba’a d’aura mana aure ba kaman yanda mukaci buri.. Sun mana fin k’arfi... Sun rabamu da k’arfin mulki da dukiya.. Ko Kinsan wanene ya aureki..?” Yai tambayar cikin rawar murya yana duban Muhibbah da tuni k’walls sun ciko idanunta... Ansar yaci gaba da furta “Muhibbah Yarima Mahmood shine ya aureki... Kuma ba don yana k’aunarki ba sai don yayi amfani dake ki zamto bakin zaren da zai warware masa duk wani k’ulli dake cikin Masarautar nan... Hibbah Mahmood sayenki yayi da mak’udan kud’ad’e daga wajen Yawale... Nasan shid’in d’an uwanki ne... Nasan bai kamata naita fad’in kalamai irin haka ba, but is the truth Muhibbah... Shid’in ba Auren soyayya yayi dake ba.. Satoki yayi daga wajen masoyinki na asali..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya..

Muhibbah dake jin batun tamkar wani sauk’an aradu duban Ansar take hawaye na gangaro mata “Kace ya auroni ne domin na zamto bakin zare a garesa..?”

Ansar ya jinjina kai yace “K’warai domin yayi amfani dake ki warware masa duk wani k’ullin dake cikin Masarautar nan, Don’t you find it strange yanda yazo ya ajeki ba tareda wani bayani ba, sannan saida aka drugging d’inki aka kawoki cikin Masarautar nan, nima kuma akai drugging d’ina aka hanani halartar aurenmu... Mahmood da Baffah Yawale planed everything Hibbah.. Harta Mommy batasan da wannan shirin nasu ba.. Tana can hankalinta tashe da tunanin wanene mijin da aka aura miki..Hibbah Mommy bata cancanci haka ba.. None of us deserve this..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya..

Izuwa lokacin kukan da Muhibbah keyi ya k’aru, Wato wannan shine dalilin Rankaidad’e na bibiyanta, she was right sayota yayi tamkar wata baiwa ya ajiyeta babu wani bayani, shin ta ya ma za’ai mata irin wannan auren kawai dan yana basarake.. Har abada bazata aminta da wannan auren ba.. D’ago idanunta masu zuban ruwa tai tana mai jinjina kai take furta “Ina mai tabbatar maka wannan auren won’t last, ban amince ba kuma bazan tab’a amincewa ba...!”

Har cikin ransa yaji dad’in kalamanta, shawo kanta bazai masa wahala ba... Bazai bar masarautar ba har sai ya tabbata ya d’auke abinda aka sace daga garesa.. Wannan dalili shiyasa ya sauk’ar da kansa ya saye zuciyar Turaki da d’abi’u masu kyau tinda ya fahimci duk duniya babu wanda Yarima Mahmood yake d’aukar maganansa irin Turaki shiyasa ya biyo ta jikin Turaki dan ya sami amincewa e Ammar Mahmood cewa shid’in mutumin k’warai ne kuma baizo dan ya lalata aurensa ba.. Ya saki murmushi a hankali yana mai duban Muhibbah yanda take cazgan kuka mai tab’a zuciya, Ya jinjina kai a hankali kana ya soma furta “Don’t ever agree to this marriage Muhibbah..! Baffah Yawale sold you, martabanki da kimarki ya wuce a aurar dake a wulak’ance just like that...You’ve been through a lot, you deserve happiness... Ke Sarauniya ce, Martabarki ya wuce a aurar dake a wulak’ance...!”
Muryarsa ya soma rawa sanda yake ci gaba da furta “Mahmood doesn’t love you Muhibbah.. Kawai k’arfin mulki ya gwada akanki...Da ace yana sonki bazai auroki a wulak’ance ba, he kidnapped you, satoki yayi Hibbah... Na sani d’anuwanki ne but I’m sorry to say he’s just like them.. Shima d’in d’an ta’adda ne tin da sayenki yayi wajen Yawale ya kawoki nan sabida baki cikin hayyacinki.. Hibbah please don’t agree to this marriage, do it for me.. For the love we have for each other.. Muhibbah kar ki bari su k’wace min ke... I still love you, so much..!” Ya k’arashe yana mai silalowa daga saman kujera ya duk’a gwiwoyinsa gabanta had’ida had’e hannayensa biyu waje guda alamun rok’o..

Hawayene kurum Ke ziraro mata d’aya na bin d’aya... Ansar ya mata hallaci a rayuwa, kuma sud’in masoyane basu cancanci haka daga Rankaidad’e ba.. Dama dangin sayenta yayi, tayi gaskiya da tace sayota yayi tamkar Baiwa.. Kenan yajesa ya saye Yawale da kud’i ya saida masa ita... Ta yaya zai aikata haka..?! Ta yaya zai sayota tamkar wata Baiwa, dole mana ya kulleta a d’aki ya hanata fita.

Raheemah dake lab’e jikin window wani irin murmushi ne saman fuskarta, Wato abinda ya faru kenan, idan kuwa haka ne dole tayi amfani da wannan damar su had’a k’arfi da k’arfe itada wannan mutumin su raba Mahmood da Muhibbah, itama ta sami chance da zata rama abinda Mahmood d’in da Muhibbah sukai mata...
Chapter 136 · 0% Book details