← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 162

Sashe 67

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Babu shiri Giwa da Hadimanta harmada Jakadiya suka take masu baya, saiga Giwa na kuka sharhsar da hawaye... Cikin zuciyarta take furta Jamal d’inta bazai mutu ba dan muddin ya mutu ko shakka babu itama binsa zatai... Tabbas wannan shine ma’anar bayyanar Izzatu... Jamal d’inta ne ashe.... Wani sabon kuka ya kuma kufcewa Giwa sai had’e hanya take suka nufi asibitin cikin Masarauta, Jamal bai daina damk’e k’afarsa dake tsananin masa zogi ba yana fad’in Giwa ta yafe masa mutuwa zai...

A b’angaren Mahmood kaw tinda Majidad’i ya ida fad’in abinda d’an uwansa na jini Yazeed yai masa bai kuma sanin meke wakana wajen ba... Yanajin hayaniyar mutane daga can nesa nesa.. He couldn’t believe his own brother can do this... Turaki ne ya taimaka masa ya zaunarsa saman kujera...
Turaki cikin Washe baki yake fad’in “Allah ya wanke ka abokina... Allah ya wankeka a idon duniya.... Mahmood d’ago kaji gashi nan ana sanarwa kaine Sarki, ka zama Sarkin Masarautar nan your Highness...!”

Siririyar hawaye ne ta gangaro masa sanda yaji Tambura da algaita na tashi ga zigazigi yana wasashi yana ambato sunansa anai masa kirari irin na Saraki “D’an Toron Giwa... Gaba salamun baya salamun... Allah ya baka... Allah yaja zamanin Sarki Mahmooda d’an AbdulJabbar jikan Mahmooda...!!”

Siririyar murya ce ya katse shagalin tana fad’in “Ku dakata shid’in bai cancanta ya zama Sarki ba...!”

Da tsananin mamaki illahirin jama’an cikin Zauren suka juyo suna dubanta da tsananin mamaki....

Mahmood ya furta “Zahra!!!” A hankali... Lokaci guda Zahra taci gaba da takowa cikin tapkeken parlorn hawaye na gangaro mata... A haka ta isa gaban mahaifin nata....

**

Haka Muhibbah ta dinga bin bayan Fu’ad har suka shige sashensa yanda ya fad’a bedroom ya janyo wata drawer ya jawo k’wayoyi cikin hannunsa yana k’ok’arin afasu cikin bakinsa yake fad’in “No no no please... Please forgive me... I was forced to do it.... Please just leave alone..!!” Ya k’arashe yana mai kuma tak’urewa jikin gini daidai lokacin Muhibbah ta shigo jiki a matuk’ar sanyaye take dubansa.... Yana k’ok’arin afa k’wayoyin tai saurin bige hannunsa suka watse k’asa....

Fu’ad ya d’ago yana dubanta lokaci guda yaci gaba da matsawa jikin gini yana furta “Please forgive me...Please please please.. I don’t want to.. Please...!!” Tamkar mai tab’in hankali haka yake sunbatu yana kuma matsawa jikin gini....

Muhibbah tai zaman rak’umi gabansa tace “Fu’ad meke faruwa... Please tell me wane laifi ka aikata kake neman afuwa...?!” Ta k’arashe cikin d’an d’aga Murya....

Dubanta yai da idanunta masu zuban hawaye lokaci guda yake furta “Please forgive me Muhibbah... Baki cancanceni ba... I’m a monster a killer... A ra....!!” Ya kasa ci gaba da magana sai hawaye dake kuma ambiya a fuskarsa....

Lokaci guda yanayinta ya sauya, idanunta sukai jazir, cikin dakewa take ci gaba da fad’in “If you truly love me, you tell me what exactly you’re hiding Fu’ad... Idan ba haka ba ka mance dani dan bazan tab’a kasancewa da mutum irinka ba... Now go ahead and tell me what really happened...!!”

Cikin wane irin yanayi yake furta “I cant Muhibbah... Mahaifiyata da ‘yanuwana zasu disowning d’ina muddin maganan ya isaga Ya Mahmood...!!”

Cikin wane irin sanyin jiki had’ida bugawan zuciya tace “I don’t get you Fu’ad... Meye kake b’oyewa Yarima Mahmood..!?”

Fu’ad na kuka sosai yake furta “Wani babban laifi da muka aikata nida ‘yan uwana guda biyu... Yazeed Jamal da kuma ni Fu’ad... Wani laifi ne da muka aikataga wata ‘yar talikan yarinya shekaru goma sha hud’u baya... Mun aikata laifin ne a bisa umarnin mahaifiyarmu... A cewarta idan har bamu hakan ba bazamu tab’a tabbata akan Karagar mulkin Masarautar nan ba... Na aikata laifin ne dan sadaukarwa ga ahalina Muhibbah... Amma tun bayan wancan lokacin ban kasance cikin kwanciyar hankali ba har yau...!!” Ya k’arashe hawaye na kuma ambaliya a fuskarsa...

Muhibbah da tuni duniyar ya soma juya mata, cikin tsananin sanyin jiki had’ida rawar murya take furta “Mai kuka aikatawa yarinyar da ahalinta..?!” Ta k’arashe siririyar hawaye na gangaro mata..

Fu’ad yace “Zalunci mafi muni... Mun mata fyad’e dukanmu uku... Muka kashe mahaifinta sannan muka cinna wuta cikin gidan ta k’one da ita da mahaifiyarta suna cikin gidan... Wuta ya cinyesu a gaban idanuna... I couldn’t do anything to stop the fire... Yazeed da Jamal sun janyeni sun hanani taimakon yarinyar da mahaifiyarta... Haka muka k’yalesu suka k’one k’urumus cikin gidan... Bazan tab’a yafewa kaina ba Muhibbah...!!” Ya k’arashe cikin tsananin kuka...

Muhibbah da hawaye Ke ambaliya a fuskrta cikin tsananin rawar murya tace “Kana nufin ku kuka aikata laifin banda Mahmood...?!”

Fu’ad ya jinjina kai yace “Idan Yaya ya sani tabbas zamu rasashi bazai tab’a yarda ya rayu cikin ahali azzalumai ba... Mahaifiyarmu zata rasashi amma a cewarta duk abinda mukai sadaukarwa ce gareshi dan tasan shi bazai tab’a aikatawa ba shiyasa mu Ta umarce mu muyi... Ranan bukin wata sallah ce... Mun fita mu dukanmu hud’u akan dawakanmu dan zaga gari, saiko bawanmu Ja’afar dake rik’eda linzami na sabida a lokacin ni k’arami ne sosai ban wuce sha uku ba shisa Jafar ke rik’e min linzami ko fita kilisa zamuyi... A can wajen gari muka tsinci yarinyar tanata kuka da alama tabi ‘yan kallon dawakai da wasan sallah masu zaga gari shine ta b’ace... A lokacin almuru ya k’arato... Yaya shine ya soma hango yarinyar ya umarci Ja’afar ya k’arasa ya duba dan yaji kaman kukan mutum... Jafar yai kaman yanda Ya Mahmood yace....!” Ya d’anyi fasali hawaye naci gaba da gangaro masa... Lokaci guda yaci gaba da fad’in “Akai sa’a Jafar yasan yarinyar a bayan masarauta gidansu yake kaman yanda Jafar ya sanar da Yaya... Yazeed yace mu tafi mu barta bai kamata a ganmu da k’ask’antattun mutane irin wad’Annan ba... Yaya yace koda wasa baza’ai haka ba... Yaya da kanshi ya d’auketa ya azata saman dokinsa da yake bisa tana gaba yana baya ya bata apple d’in da yake ci, kallo guda zakai masa ka fahimci tsantsan tausayin yarinyar da ya kamasa...”

Muhibbah Ta lumshe idanunta a hankali hawaye suka gangaro mata tana mai tuna tabbas anyi haka, wannan kyakkyawan murmushin nasa shine saman kyakkyawan fuskarsa... Ta sinkayo muryar Fu’ad naci gaba da fad’in

“Ga dukkan alamu yarinyar da Jafar sunsan juna sosai dan na kula da irin duban da sukewa juna tana daga saman doki Jafar na janye da linzamin doki na.. Hasalima sanin Jafar da tai yasa Ta amince damu...”

“A Haka muka iso har masarauta, dan lokacin da muka iso har yarinyar tayi bacci jikin Yaya sabida tafiya ne saman doki dole akwai gajiya musamman ga yarinya mace irinta... A lokacin da muka iso masarauta d’an aike ya taremu ya sanar damu mahaifinmu Wato Mai Martaba Amale yana kiran Ja’afar kirata gaggawa... Yaya Mahmood yace maza Ja’afar yaje ya amsa kiran Amale shi zai kula da yarinyar zai kaita Gida sannan zai sauk’o ya rik’e linzamin dokina dan kar na fad’i...Ja’afar yai masa kwatancen gidansu yarinyar kana ya tafi Fada amsa kiran Mai Martaba... A daidai lokacinda Ja’afar ya tafi amsa kiran Amale ita yarinyar ta farka daga baccinta... Tabi bayan Ja’far da kallo tsoro sosai saman fuskarta, da alama Ta razana sosai damu tinda dama sabida Ja’afar ta yarda ta bimu gashi shi kuma ya tafi....”

“Mun kula tunda Ja’afar ya tafi hankalin yarinyar bai kwanta damu ba... Sosai tsoronmu ya bayyana a tattareda ita musamman dataji Yazeed yanata mitan maiyasa zamu taimaka ma k’ask’antacciya irin wannan yarinyar...! Ya Mahmood shi ya sakar mata murmushi ya tambayeta zata gane gidansu daga nan bayan Masarauta, tai saurin girgiza kai cikeda tsoro tace dashi ita bazata gane ba dan basu jima da dawowa garin ba kuma a lokacin akwai duhun dare..! Mukaita dariyarta muna daga saman doki Yaya ya tsawatar mana yace mu daina mata dariya, ya kwantar mata da hankali da fad’in cewa zamu kaita har gida....!Ana haka muna tafe Yaya ya rik’e linzamin dokina da kuma dokin da ita yarinyar ke bisa d’an aike ya kuma zuwa yayi kiran Yaya inji mai Martaba... Yaya ya bar mana amanan Yarinyar ya janyo Yazeed gefe yaja masa kunne kan cewa mu tabbata mun kai yarinyar har gidansu, shi zai jeshi ya amsa kiran Mai Martaba....
Chapter 67 · 0% Book details