← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 162

Sashe 26

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Giwa da gaba d’aya ta soma jin kaman wani abu na mintsilinta, gaba d’aya kasa sukuni tai a wajen... Take hannunta na hagu da ko yaushe rufe yake cikin wani bak’ar safa ya soma mata k’aik’ayi.... Takai dubantaga Jakadiya wacce tuni Ta fahimci halin da Uwargijiyar tata ke ciki.... Tai saurin k’arasowa gareta had’ida kwanto da kanta alamun jinjina da gaisuwa a zahiri... Saidai su biyu d’in saiko mahaliccinsu ne suka san abinda suke tattaunawa....

Cin abincin da ba’a ida taredasu ba suka bar wajen....
A b’angaren Gimbiya Zeenatu kaw K’uri tai masu sanda suke k’arasowa, tabbas gabanta ya fad’i sanda Ta hangi Yarima Mahmood tace da wannan budurwa, sai yanzu take ganin ashe ba laifin Raheema bane da ta tada hankali kan yarinyar... Tin yaushe ake jajen isowar Yarima Mahmood sai gashi ya k’araso tareda wannan yarinyar... Ita data tura Raheema taje ta nemo Mahmood yanda ya shiga ya fita su taho tare, gashi tana cen tana sakarci wannan shu’umar ta samosa... Waima ina Raheema ta tsaya...? Amsar data kasa samowa... Cen kuma ta hange mazaunin Yazeed babu kowa, fuci ta saki a hankali tana mai girgiza kai... Sarai ta sani wajen d’an iskan cen Yazeed ta makare... Tabbas sai ta koyawa Raheema hankali yau d’in nan basai gobe ba... Cikin tsananin k’unan rai ta mik’e tai tafiyarta itama Kuyanginta na biyeda ita....

Yayinda Zahra dasu Sultan su Noor yaran Yazeed suka kewaye Yarima Mahmood kowa yanaso ya sauraresa hakan ya baiwa Muhibbah daman silalewa ta isa gefen Umaima ta zauna tana hango tsananin k’aunan yaran gaba d’aya a fuskar Mahmood....
Maiyasa takeji cen k’asar zuciyarta shid’in yanada wani kyakkyawan hali cikin mutane gaba d’aya wanda ba kowa Keda irin wannan halin ba...? Maiyasa takejin tsira da kwanciyar hankali a duk sanda ta kasance tare dashi... Daren jiya bayan tattaunawarsu sosai ta sami natsuwa cikin zuciyarta, sannan yanzu datai zaton su Yazeed zasu kamata bayyanarsa sai ya jefata cikin nastuwa da kwanciyar hankali.... Bugu da k’ari alak’arsa da mutanen Masarautar gaba d’aya ko shakka babu yanada kyau....Toh maiyasa ya kasance azzalumi daga fari...? Kasa samun amsar tai sai wani b’angare na zuciyarta dake raya mata.. Ba’a canza wa tuwo suna... Watak’ila wannan nasa salon kenan na yaudara... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tanajin tsanarsa na kuma taso mata daga cen k’asar zuciyarta lokaci guda....
Saurin kawar da fuskarta tai Daga barin dubansa hakan yai dai dai da hango Raheema da tai tana k’ok’arin k’arasowa wajen sai waige waige take kana ganinta Kaga maras gaskiya....

Muhibbah ta kafe Raheema da idanu yanda take bin Yarima Mahmood da Mayen kallo, ko ba’ace ba so take taje wajensa saidai hakan ba mai yuwa bane kaman yanda yake a tsarin gidan... Idan d’an sarki na neman aurenki koda kina rayuwa cikin gidan kai tsaye bazaku keb’e ba har sai Jakadiya tai iso an shirya had’uwar ta musamman kafin ku gana...

Lokaci guda Raheema Ta maidoda dubanta ga Umaima da Muhibbah dake cakalan fruits d’in gabanta tamkar wata mai tausayinsu....

Cikeda k’asaita Ta soma takowa garesu... Umaima ce ta tarbeta da fari’a yayinda Muhibbah ke binta da kallon k’yama bayan abinda Ta gani tsakaninta da Yazeed....

Murmushi saman fuskar Raheema take duban Muhibbah, nan taga hankalin Muhibbar naga Zahra da mahaifinta yanda take serving d’insa abinci ba tareda ta bari wata baiwa tai masa ba....

Bud’e murya Raheema tai kana tace “Sun burgeki koh...?”

Da mamaki Muhibbah ta kaikaito tana duban Raheema dake ci gaba da sakin shu’umin murmushi....

Lokaci guda Muhibbar ma ta d’aura murmushi saman fuskarta kana tace “Duk wanda ya dubesu dole su burgesa sannan kuma yai masu fatan su tabbata a haka ba tareda wani ya shiga tsakaninsu ya zamto sanadiyan lalacewar wannan kyakkyawan alak’a dake tsakaninsu...!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta tana duban Raheema da tuni kalaman Muhibban sun sanyaya mata jiki...
Murmusawa Raheema ta kumayi kana tace “Muhibbah koh...? I hope you know your place... Ya kamata ki rage shigewa Zahra..!”

Muhibbah ta kuma murmusawa tana duban Zahra dake cen wajen mahaifinta kana tace “I’m sorry your Highness, but I think that’s for her to decide... You can’t choose her friends... Am I right...?!”

Raheema tai murmushi da yafi kama da yak’e kana tace “What Zahra needs is a mother, and not a friend..Kin fahimta..!!”

Wannan karon daga sama zuwa k’asa Muhibbah ke duban Raheema, murmushin bai bar saman fuskarta ba take furta “And wa kike tinanin ta cancanta da zama mahaifiya ga Zahra... You..?!” Lokaci guda ta kuma sakin murmushi kana tace “Ki kwantar da hankalinki your Highness, Yarimanki bai gabana, bashi bane a gabana... Karatun da ya kawoni garin nan shine gabana... So Ki kwantar da hankalinki kinji, I’m not an enemy here Princess...Kema idan kinaso mu k’ulla k’awance zamu iya zama k’awaye kinji koh....!!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin wani murmushi kana ta furta “Na barki lafiya your Highness... Have a good evening...!!” Har ta juya zata wuce sai kuma ta juyo tana kuma duban Raheema kana Ta kuma sakin murmushi tace “Oh... Nice earrings tho...!” Tana ida fad’in haka tasa kai tai shigewarta ko sallama da Umaima ma bata sami zarafin yi ba aka bar Raheema baki sake tana bin bayanta da kallo...

Shiko Yarima Mahmood lek’en ta yanda zai hangota yake kan faman yi amma bai hangota d’in ba... Ba dan yaso ba ya kuma maida hankalinsa ga yaransa....

***

Yamutsettsen tsoho mummuna abin tsoro da k’yama da Giwa Ke kirada Tal’udu shine ya kuma mik’ewa tsaye gaban Giwa cikin tsananin k’unan rai ga hayak’i da ya gauraye wajen gaba d’aya lokaci guda yake furta “Turai..!!! Kina Ina d’anki ya had’o kan Malamai suna cikin Masarautar nan suna k’ona min dakaruna dake ko wacce kusurwa ta cikin gidan nan....!! Idan har hakan yaci gaba da faruwa toh fah dole ya wargaza duk wani sauran shirinmu....!”

Giwa ta soma girgiza kai tana furta “Bazan tab’a barin Mahmood ya wargaza min shirina ba...Kafin ya wargaza min ni zan gama dashi...!!” Ta k’arashe cikin tsananin huci..

Tal’udu yai wani irin dariya mai mummunan sauti kana yace “Kina gab da makara Turai domin kaw wannan yaro naki da shirinsa ya dawo... Kuma ya dawo ne domin ya yak’eki ya bankad’o duk wasu sirrikanki...!!!”

Giwa ta d’ago tana huci lokaci guda take furta “Bazai yuwu yaron dana rik’esa matsayin d’anda na haifa shekara da shekaru ya zama silan rugujewata ba... Dannewa da nai da rik’onsa da nai tsawon shekarun nan ya isheni uk’uba, ya isheni k’unci... Kai da bakinka ka fad’a min Mahmood bazai k’argo kan gadon Mulki ba... Da zaran ya mutu kuma d’ah na ne Yazeed zai d’ale Karagar....!!!” Ta k’arashe cikin tsananin huci....

Tal’udu ya kuma fashewa da wata irin dariya kana yace.....

SameenaAleeyou📚
[6/15, 7:17 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*019*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Tal’udu yaci gaba da fad’in “Ai kin makara tinda kika sake wannan yarinyar ta kufce miki.... Fitilar tsafi ta nuna min gudan jinin na tattareda ita...!!”

Wani irin mummunan fad’uwan gaba ne ya dirarwa Giwa lokaci guda... Ta d’ago idanu tana duban Tal’udu dake tsaye gabanta daga shi sai wata ‘yar bante kalan ja, yamutsattsen fatarsa babu kyaun gani......
Giwa Ta shiga girgiza kai tana furta “Wacce kenan... Wace yarinya ce wannan Tal’udu....?!!”
Ya kuma fashewa da wata irin dariya kana yace “Yarinya Ta farko da ya kamata na tara da ita, ban tarada ita ba Allah ya bata sa’an tserewa.... Tabbas itace gudan jinin...!!”

Gaban Giwa ya kuma bugawa... Batasan sanda Ta mik’e tsaye ba tana fad’in “Kana nufin kace ba’a sami gudan jini tsakanin duka wad’annan ‘yanmatan da suke wajen nan ba...?”

Tal’udu ya kuma fashewa da dariya kana yace “Ai na fad’a miki gudan jinin ka iya tsayawa akanta ita d’ayanta... Kuma idan har ya tsaya akanta ita d’aya toh fah ko shakka babu K’addarar Masarautar nan na rataye ne a wuyanta....!!”

Giwa na tsananin huci take furta “Amma yarana sun tabbatar min cewa wannan yarinyar Saudatu ta jima da mutuwa sun kasheta..!!”

Tal’udu yai wata murmushi mai mummunan sauti kana yace “Tin a lokacin na fad’a miki yaranki k’arya suke maki Allah bai basu sa’an kashe wannan yarinyar ba kaman yanda suka sanar dake Sun kasheta...!!”

Giwa Ta soma ganin jiri duniyar na juya mata, ta dafe kanta da ya shiga sara mata lokaci guda.... Meke shirin faruwa da ita, idan Saudatu tana raye toh tana ina... Kai ina ita bata yarda ba, bata yarda Saudatu na raye ba... Bata kuma yarda k’addarar Masarautar Ta na rataye a wuyarta ba... Lokaci guda ta d’ago tana duban Tal’udu cikin wane irin fuci take furta “Hakan ba mai yuwa bane Tal’udu... Babu yanda za’a ce k’addarar Masarautar nan na rataye a wuyar wannan k’ask’antacciyar yarinyar d’iyar k’ask’antattu... Idan duk baka sami gudan jinin cikin wad’annan ‘yanmatan goma sha hud’u da suke a matsayin mallakinka a yanzu dole a sake nemo wata budurwa a jarabba da ita... Ni bazan tab’a yarda da fad’uwa ba Tal’udu....Na riga dana bisne sirrinka da babu wani mahaluk’i da ya isa ya bincikosu.....!” Ta k’arashe tana tsananin huci

Juya mata baya Tal’udu yai kana yace “Turai ina gargad’inki dik randa Mahmuda yai nasaran bud’e kurkuku dake k’ark’ashin k’asan Masarautar nan.... Ki tabbata daga wannan rana daga ni har Ke k’arshemu yazo....!!!” Yana ida fad’in haka hayak’in dake cikin d’akin ya kuma turnuk’ewa hannun Giwa dake lullub’e cikin bak’in safan shima ya soma hayak’i... Ta zaro ido tana duban hannun nata cikeda firgici... Cen kuma hayak’in ya soma gushewa, a haka itama hayak’in dake fitowa daga cikin hannun nata ke tafiya har dai hayak’in ya k’are gaba d’aya... Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya tai kana Ta sauk’a daga saman jan darduman su ta tsafi mai d’aukeda Tambarin Masarautar tasu....

Tana fitowa ta tadda Jakadiya na jiranta, tai tsaye tana k’arema ‘yanmatan dake kai komo wajen kallo... Ta hangi wannan d’aki da kullum yake a bud’e... D’akin da ya kamata ace Saudatu ce a ciki amma an bar d’akin da gib’i... Wannan yarinya ba k’aramin cutarta tai ba, da ace bata gudu daga wajen Tal’udu ba da yanzu babu wani barazana gaba gareta... Ta yaya Tal’udu zaice k’addarar wannan Masarautar na rataye a wuyan tsinanniyan yarinyar nan wacce itada iyayenta suka tasamma kawowa mulkinta sanadi...
Chapter 26 · 0% Book details