Sashe 114
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
D’aki Jamal ya dawo domin shiryawa dan shima dole ya nufi asibiti yaga halinda Yazeed Ke ciki...!
Sauri sauri ya kwab’e k’anan kayan dake jikinsa ya zira jampa, Umaima da tun shigowarsa idanunta biyu kikimau ta kumayi tamkar har lokacin bata farfad’o ba.... Tana jin sanda ya ida shirinsa ya k’araso gareta ya manna mata peck a goshi yana mai furta “I’ll be right back my love...! Zan dawo na d’aukeki muyi nesa da wannan Masarautar... Na tanadar mana rayuwa mai kyau sweetheart... You just need to trust me Umaima, zan baki rayuwar data dace dake..! I Wait for me kinji love..!” Ya k’arashe yana mai gyara mata kwanciyarta dukda cewa d’aure take da jikin gado...!
Jamal na ficewa wasu irin hawaye masu tsananin d’umi suka gangaro mata, Ta bud’e idanunta da sukai matuk’ar mata nauyi tana k’arema d’akin kallo... Wani irin d’auri yayi mata hannu da k’afafu yanda zai matuk’ar wahala tai escape...! Take ta kuma fashewa da wani irin kuka wanda bata San na menene ba, na kasancewar wannan azzalumin mutumin a matsayin mijinta ne ko kuwa na tausayin halinda ta tsinci kanta ciki ne..! Maiyasa bata saurari Muhibbah ba tin daga farko k’ila da yanzu daga ita har Muhibbar Sun kub’uta, gashi bata San duniyar da yakai Muhibbah ba, koma tana raye ko ya kasheta sai Allah..! Ta kuma rintse idanunta wasu hawayen masu matuk’ar zafi suka gangaro mata... Tana tsaka da kukan ta hangi wani abu Can k’asa saman rug, kaman waya kaman kwali.. Saidai bazama Ta iya mik’ewa ba balle ta isa ga abun... Ta shiga k’ok’arin janye jikinta tana yunk’urin d’aga kanta, nan Ta hangi tabbas waya ce.. K’ila k’aramar wayar Jamal d’in ce ta fad’i garin sauri da yake don shiryawa...! Ta shiga k’ok’arin jijjiga hannayenta da k’afafunta ko Allah zai bata sa’an kwance d’aurin... Inaa ko motsawa batayi, gadai waya tana hangowa nan k’asa kusan k’afarta amma bazata iya janyowa ba sabida d’aurin da aka mata.. Ta kuma rintse idanunta hawaye naci gaba da gangaro mata...
**
Tashin hankali maras misaltuwa Giwa ta tsinci kanta ciki sanda taga halinda Yazeed yake ciki, da gaske dai Yazeed d’in dataci masa burin zama Sarki shine kwance saman gado babu hannaye...
Yazeed ya rasa hannayensa ya kuma rasa ‘ya’yensa duk a sabida bak’in zuciya irin nasa... Wannan rayuwa da mai yayi kama, abin bazai kuma masa ciwo ba har sai randa ya bud’e idanu ya gansa a halinda yake ciki kuma shine yayi silan faruwan komai, shine yayi silan rasa hannayensa da mutuwar yaransa gaba d’aya... Lallai tashin hankali na gaba gareshi...
Jamal ma sosai hankalinsa ya tashi da ganin halinda Yazeed ya tsinci kansa ciki, dukda ya rasa k’afarsa gani yake nasa mai sauk’i ne tinda gashi har za’ai masa wata k’afar, shi kuwa Yazeed babu hali ayi masa hannaye haka zai k’arashe rayuwarsa babu hannaye bazai iya yiwa kansa komai ba saidai ayi masa dukda kuwa pride da jin kai da isa irin nasa...
Cikin tashin hankali Giwa ta isaga Mahmood da tin shigowarsu asibitin kallon kirki bai shiga takaninsu ba saima kai komo da yake da likitoci suna updating nasa halinda Matar Yazeed da Handimarta Ke ciki... Ga dukkan alamu Hadimar nata itama Allah ya amshi rayuwarta amma matar Yazeed ta rayu, anyi gwaje gwaje akanta kuma babu wani internal injury data samu saidai wad’anda idanu ka iya gani, babu wani fracture data samu saiko buguwar k’ashi, a halin da ake ciki Zuhra tana d’akin hutu tana ci gaba da samun kulawa dan har kawo zuwa lokacin bata farfad’o ba bayan gwaje gwaje da akai mata...
Likita da Mahmood suka gama tattaunawa, Mahmood ya saka hannu a takardan amsan gawawwakin ya kuma yin sallama da likita...!
Tinda Giwa taga Mahmood bai ko bi takanta ba tasha jinin jikinta tasan duk yanda akayi wani babban al’amarin ya faru...
Dakatar da Jakadiya tai kana tabi bayan Mahmood d’in kafin ya b’acewa ganinta, can daidai wani lobby yanda babu mutane Giwa ta cimmasa, sunansa ta kira amma bai tsaya ba saima ci gaba da tafiya da yake... Ta d’an kuma d’aga k’afa tana mai furta “Sadauki ka saurareni..!”
Cak ya tsaya ba tareda ya juyo ba zuciyarsa naci gaba da tsananin zogi, Allah ya gani dukda ta kasance mahaifiyarsa ko fuskrta bai k’aunar gani... Giwa ta k’araso tana furta “Haba Sadauki..! Ya ina maka magana kana kuma tafiya.. Sadauki ba kai kad’ai bane halinda Yazeed da ahalinsa suka tsinci kansu ciki ya d’aga ma hankali, dukkanmu nan hankalinmu a tashe yake.. Kai d’aukacin masarauta hankali a tashe yake...! Ni fah mahaifiyarsa ce har kana tunanin zaka fini shiga damuwa Mahmood..?! Mahmood anya babu wani abinda ke damunka d’ah na.. Ka sanar dani.. Haba Mai Martaba Sarki mai jiran gado..!” Ta k’arashe cikin kwantar da murya...
Juyowar da zai, yanda Giwa taga k’wayar idanunsa da yanayin fuskarsa ba k’aramin firgitata yayi ba, yau d’in sai ya koma mata tamkar AbdulJabbar ranan da asirinta ya tonu a idanunsa, domin kuwa wani kamanni ne na musamman ya kuma fitowa tsakaninsa da Mahaifin nasa...
Cikin kakkausar murya Mahmood ke furta “Sarki..! Sarki..! Mai za’ayi da Sarautar da aka gina kan zalunci...? Mai za’ayi da sarautar da akaci zarafin wad’anda basuda hakki dan a tabbatar da samuwar wannan sarautar..! Ki fad’a min Maami mai za’ayi da irin wannan sarautar..?!”
Ba Giwa dake rarraba idanu gabansa ba harta Jamal dake daga can bayan Giwan saida yasha jinin jikinsa ya tsaya cak ya kasa ci gaba da dogara sandarsa..!
Zuciyar Giwa na bugu take furta “Sadauki ban fahimceka ba... Mai kake nufi...?!”
Sosai ya kaikaito wannan karon yana dubanta, jijiyoyin jikinsa na kuma mik’ewa yake furta “Ina nufin babu abinda zanyi da sarautar da kika nemawa ahalinki ta hanyar Malamai ‘yan tsubbu mushurikai masu kaikuga halak’a...! Maami how could you..! How could you do something like this..? How could you turn your children into criminals..!!”
Cikin rawar murya Giwa Ke furta “Mahmood ban fahimce ka ba... Mai kake nufi..?!”
Girgiza kansa kurum yake cikeda tsananin takaici, lokaci guda yake ci gaba da furta “Fu’ad told me everything... Abubwan da suka faru fourteen years back, Fu’ad ya sanar dani how you ruined our family and destroyed the life of an innocent child....! Shin Maami ina zaki kai girman zunubin da kika d’auka, kin saka yaranki sun lalata rayuwar k’aramar yarinya akan son zuciya... Kin maida yaranki ‘yan ta’adda..! Fyad’e fyad’e Maami..! Shin wace uwa ce zatai jagoranci ma yaranta su aikata mummunan laifi irin wannan... Wace irin uwace zata aikata haka Maami, Fu’ad was only a kid then amma da k’arfi saida kukasa ya aikata laifin... Ki fad’a min ina zaki kai girman zunubin nan..?!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya irin na wanda ransa yakai k’ololuwa wajen b’aci...
Giwa na girgiza kai take furta “Mahmood Fu’ad mahaukaci ne mai yasa zaka yarda dashi...! Ko a kotu ne mahaukaci baya bada shaida..! K’wayarsa ce ta sanar dashi hakan shiyasa ya sanar dakai duk wannan k’arerayi marassa asali balle tushe..! Yanzu kai a naka tunanin zan aikata laifi makamancin wannan..? Haba Mahmood ya kake abu kaman ba Babba ba..!”
Katseta yayi da fad’in “I tried not to believe him amma zuciyata ta k’i aminta da hakan...! Na yarda Fu’ad ya fad’i gaskiya sabida bayan duka wannan shekarun bai mance komai ba..!”
Sai sannan Jamal ya k’araso yana fad’in “Yaya Fu’ad was lying to you... How can you believe a psychopath like him..!”
Cikin tsananin huci Mahmood ya katsesa da fad’in “Shut up..! Rufe min baki...!! That’s because kun tilasta masa yin hauka.. You and our mother tormented Fu’ad.. Ya sanar dani yanda kayita drugging d’insa kana injecting d’insa dan kawai ku mantar dashi komai ku hanasa magana.. You’re the real psychopath here Jamal... Na zaci gaba d’aya cikinku ka fisu hankali, kullum ina maka zato mai kyau dan kafi Yazeed hankali a fuska Ta d’abi’a ashe ba haka bane, you’re the worse..! Ta yaya zaka halak’a kwanyar d’an uwanka da strong drugs, Kai kayi introducing k’wayoyi masu gusar da tunani ma Fu’ad tun yana k’arami baisan illan abunba... kawai dan ku hanasa fad’in laifin da kukayi tarayya wajen aikatawa... How could you do this to your own brother...! I can’t believe this, I can’t believe my on family can be this heartless..!!”
Kan Jamal na k’asa yawa mutumin arziki yake furta “Yaya wllhi Fu’ad cikin haukarsa ya sanar dakai haka, duk abubuwan da ya sanar dakai none of them is true..!”
“Nace kamin shiru kafin na k’araso wajen na k’arasa karya d’aya k’afar taka mutumin banza kawai...!”
Giwa na k’wak’ulo kukan k’arya take kuma k’aryata zancen...
Girgiza kai kurum Mahmood yake kana yai saurin sa kai ya fice daga asibitin dan idan yaci gaba da tsayuwa wajen zai iya mance ita d’in mahaifiyarsa ce wanda baya fata a isa peak d’in....
**
K’AUYEN GALAMBI
Jafar da Ubandoma zaune daga can wani b’angare na tsakar gidan sun kunna k’irare suna shan d’umi dashike tsakar gidan akwai yalwan fili... Ko wannen su rik’eda gasasshiyar masara suna ci suna shan d’umin wutan dan anyi ruwa garin ya d’auki sanyi sosai, Ubandoma na kuma labartawa Ja’afar abubuwan da sukaita faruwa cikin Masarautar a lokacinda yake rufe...!
Jafar sai faman murza masaran dake hannunsa yake yana hango k’uran da zai tashi idan ya saka k’afarsa cikin Masarautar... Dan yayi imani koda ace shi bawa ne duk wanda suka cuzgunawa rayuwarsa cikin Masarautar sai sun biya abinda suka masa... Ko zafin k’una hannunsa da masarar keyi bayaji sai kuma mutsuk’ata yake cikin tafin hannunsa.. Hasken Farin wata ya haske kyakkyawar fuskarsa wanda a ‘yan kwanakin da sukayi wannan K’AUYEN har ya sauya kamaninnsa na asali ya kuma bayyana... Gaban Ubandoma ya yanke ya fad’i domin kuwa harta zaman da Ja’afar yayi irinta masu mulki ne... Kardai jinin Saraki ne Giwa ta basa ya canza da d’an Bawa...! Idan kuwa hakan ne baijin Jafar zai yafe masa musamman da yaga irin tanadin da Jafarun yayiwa wad’anda suka zaluncesa randa duk ya saka k’afarsa cikin Masarautar...
Bai ida tunanin ba suka sinkayo muryar Tabawa matar Baba Nomau ta fito tana furta “Malam..! Malam kazo kaga abin mamaki...!”
Jafar da Ubandoma suka dubi juna, cikin sauri suka mik’e suka nufi yanda Mama Tabawa ke kira...