← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 162

Sashe 75

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Meenatu an tab’o chapter da take so... Ta murmusa kad’an had’ida rausayar da idanu, harda su sauk’e ajiyan zuciya tace “Toh ita dai soyayya wata aba ce da Allah ya kana halitta a zukatan ‘yan adam... Idan kina son mutum zakiji kin damu dashi sosai kuma kin damu da al’amransa gaba d’aya, sannan kina son kasancewa dashi...Idan ya shiga damuwa zakiji kema kin shiga damuwa... Haka idan yana cikin Farin ciki kema zaki tsinci kanki cikin Farin ciki...Kina gudun duk abinda zai b’ata masa sannan kina muradin duk abinda zai faranta masa... Na tak’aice maki soyayya is all about CARE...Kalman Kula da ita soyayya ke farawa kafin komai ya biyo baya.... Kin gamsu...?!” Ta k’arashe tana Ware idanunta gaba d’aya hab’arta saman hannayenta...

Muhibbah dake kallonta tamkar wata d’aliba gaban malama ta jinjina kanta a hankali had’ida sauk’e ajiyan zuciya tace “Na gode k’awata... Bara na tashi naje kafin dare yayi..!”

Meenatu tace “Kai k’awata da wuri haka... Ki tsaya kici cake gaya can Ummati na baking mana...”

Muhibbah na daidaita mayafinta akanta take fad’in “Aiko ga k’amshin duk ya cika min hanci amma dai bazan iya jira ba, ku ajiye min nawa share d’in da safe ku kawo min.. Ina Mama ban gaisheta ba, kodashike barta kawai dare ma yayi na shigo gobe mu gaisa tinda yanzu na dawo...!”

Meenatu tace “Toh bara na taka miki...!” Tai maganar tana janyo mayafinta suka jera suka fito a tare...

Suna tafe suna hira har saida suka hango ‘yan masallaci na fitowa kana Muhibbah taceda Meenatu ta koma kawai gaya can ‘yan masallaci sun fito ma... Meenatu tace Ok sai goben, sukai sallama kowa ta nufi gidansu...

A daidai gate ta had’u dashi ya fito masallaci...
Da sauri tayi niyyan shigewa ya tare k’ofan “Ina kika fito a daren nan..?” Ya tambaya yana dubanta..

Fuskarta naga wane b’angaren tace “Ina ruwanka da yanda na fito, ko har yanzu zargin nawa kake baka yarda dani ba...?!”

Dafe kansa yai kad’an yace “Wai har yanzu maganan zargin nan bazai fita daga bakinki ba... Hibbah why are you acting like this.. This isn’t you, gaba d’aya kaman an canzaki, yaushe kika soma maida min magana anyhow...!”

Wannan karon galala ta dubeta kana ta kuma kauda kai gefe tace “Dan Allah ka matsa min na shige bazan iya jure tsayuwar nan ba...!”

Ansar yai shiru yana dubanta, lokaci guda yace “Alright, naji zan matsa ki shige amma sai kin tabbatar min kinyi hak’uri kuma bazaki sake maganan zargin nan ba... Only then zan baki hanya ki shige...

Ta d’an cizi leb’en bakinta kad’an tana mai duban wani gefe tace “Naji shikenan ya wuce... Ka matsa min na shige...”

Ya d’anyi mata K’uri na dak’ik’ai kana ya matsa mata tasa kai ta shige... Bayanta ya biyo yana mai fad’in idan Mommy bata parlor ta jirasa a nan zai d’auko wayarsa a d’aki ya k’araso... Ko amsasa bata iya yi ba saima shigewa da tai cikin sauri...

**

MASARAUTA

Shi kad’ai a d’aki yana neman mafitar hanyar da zai b’ullowa Mahmood, bazai yuwu ya k’yalesa yaita cin kashinsa a ransa yanda yake so ba, har shi ne Mahmood zaice zai dank’asa ga Hukuma.. Toh ma su waye hukumar..? Ai Fada itace hukuma mai zaman kanta... He needs to take Mahmood outta his way completely... Toh amma ta yaya zai hakan...?! K’aran da wayar salulansa tai ne ya katse masa tunanin nasa... Zayyad ne mai kiran.. Ya d’aga kaman baison d’agawa..
Daga d’aya b’angaren Zayyad yace “Allah shi taimaki Sarki mai jiran Gado...!!”

Gajeren tsaki Yazeed yai yace “Zayyad this place is a complete chaos...But trust me I’d never give up... The word losing is not even in my vocabulary... I was born to become a King..!!” Ya k’arashe cikin tsananin karaji...

Daga d’aya b’angaren Zayyad ya murmusa yace “Gaskiya ne Your Highness, nasan bazaka tab’a giving up ba my King... The throne is surely yours... Allah shi ja zamaninka... Ai yanzu ma nake jin rad’e rad’i cikin gari kan abin kunyar da d’iyar Yarima Mahmood tai masa cikin d’inbin jama’an masarauta...!”

Yazeed da baisan da wannan zancen ba, mik’ewa tsaye yai sosai yana furta “Ban fahimceka ba Zayyad.. Yimin bayani yanda zan fahimta, mai ya faru..?!”

Zayyad yace “She creates a scene there... Apparently tana kokonton mahaifinta na b’oye mata wani abu, something very big da ta danganta da mutuwar Mahaifiyarta... Na tak’aice maka zance your Highness bayan abinda d’iyar Mahmood tayi bana zaton za’ai nad’in sarautarsa a matsayin Sarki..!”

Baisan sanda ya bushe da dariya ba wanda ya jima baiyi irinta ba “At last labari mai dad’i... Zayyad kaci kyauta, Madalla da wannan labari naka...!” Bai kuma jiran cewar Zayyad ba ya katse kiran yana mai ci gaba da darawa shi kad’ai cikin d’akin... Ya akai Hauni Hadiminsa bai labarta masa wannan batu ba mai dad’i haka ba, kodashike gaba d’aya yau d’in shi ya hana Hauni kusantar yanda yake sabida tsananin b’acin rai da bak’in ciki da yake ciki... Zuciysrsa tayi wasai yanzun... Zahra itace greatest weakness d’in Mahmood... What if yaje ya k’yank’yasa wa Zahra wani abu gameda ko wacece ita...? Yai murmushi a fili yana mai jinjina kai lokaci guda yake d’an buga kafad’arsa kad’an yana mai ziga kansa da fad’in “You’re genius Prince Yazeed... Great..! Good..! Kaid’in na daban ne...!!” Ya kuma sakin murmushi yana mai furta “Sarautar taka ce Yazeed.!” Ya k’arasa jikin k’aramar fridge ya ciro kwalban barasarsa ya d’aga sama had’ida furta “Cheers to you victory..!” Lokaci guda ya kuma fashewa da wata irin dariya kana ya shiga kwankwad’a...

**

Giwa zaune gaban Tal’udu ga wani bak’in tulu akanta mai tsananin nauyin gaske sai haki take gumi na tsartsafowa daga ko wane sak’o na jikinta... Tal’udu yaci gaba da sumbatu cikin wane irin yare maras dad’in ji... Take cikin bak’in tulun dake bisa kan Giwa ya kama da wuta bal bal... Tal’udu ya daka tsalle ya jada baya yana duban cikin tulun...

Giwa kuwa k’ara Ta saki sabida azaban zafi da takeji daga tsakar kanta har zuwa k’asanta... Fad’i take “Ka cire min wannan azaban kai Tal’udu... Kar ka barni na halak’a..!!”
Sai ihu take tana jin kaman ana dafa naman jikinta har zuwa b’argonta cikin wuta mai k’unan gaske... Take wutar ta kuma ruruwa sosai Giwa na kuma sakin k’ara har saida tulun ta tsage wutan ya soma k’ona sumar Giwa... Birgima ta shigayi a wajen tana ambaton Tal’udu ya taimaketa ya cire mata wutan dake k’onata... Da k’yar wutar ta daina ci amma kam ya k’one rabin sumarta... Ta koma gefe tana haki bak’in hayak’i ya b’ata mata fuska kaman wata dodanniya...

Tal’udu ya tako gabanta ya kirawo sunanta cikin wata irin kakkausar murya “TURAI..!!”

Giwa ta d’ago da k’yar tana kallonsa... Tal’udu yaci gaba da fad’in “Garin yaya kikayi sake Izzatu ta kufce daga hannunki..?!!”

Giwa na haki take furta “Banida masaniya... Kayi duk abinda zakayi ka zak’ulo matar nan... Wannan shine aikinka dama...!!”

Sandar hannunsa ya buga k’asa kana ya d’aga Kai sama yana girgiza kai yake fad’in “Na fad’a miki, duk randa mahaukaciyar nan ta bayyana tashin hankali ne gareki, sannan idan har kika sake ta kufce miki gaba d’aya hakan ka iya zamtowa bayyanar sirrikanki gaba d’aya... Kar ki mance na fad’a miki ita kad’aice zata iya sanar dake yanda yarinyar nan Saudatu take...!! Sannan abu na gaba d’anki Jamalu zai karya lak’anin da muka d’aura kansa cewa bazai tab’a yin aure ba... Kin mance kin sadaukar dashi ga Aljana Tamuna wacce duk ‘yanmatan da yake masu fyad’e k’wark’warori ne gareta... Duk macen da zai tara da ita dole ta na kusanceta kuma dole ta zamto k’wark’wara ga Sarauniya Tamuna... Kinga hakan na nufin Matar da zai aura dole ta zamto tamu... Sarauniya kuma bata tarayya da wata mace wani yaci gaba da tarayya da ita hakan na nufi D’anki Jamal zai iya mutuwa kenan idan har hakan ta kasance..!! Tun a fari ke kika janyo muka rasa wannan yarinyar Saudatu... Da ace Sarauniya Tamuna ta sameta da shikenan d’anki bazai shiga halinda yake ciki yanzu ba... Idan har kina son dawamammiyar Mulki irinta Sarauniya Tamuna dole d’anki yaci gaba da kawo mata k’wark’warori ta hanyar fyad’e wa k’anan ‘yan mata... Babu aure a tsarin mu Turai... D’anki Jamalu bazai tab’a aure ba... Wannan itace dokar..!!”

Cikin rawar jiki Giwa Ke fad’in “A’a a’a Jamal Bazai tab’a aure ba... Alk’awari na maka... Shid’in bazai aure ba... Bazan rasa d’ah na ba...!!”

Tal’udu ya kuma buga sandarsa yace “Turai fitilan tsafi ya hasko tashin hankali gaba gareki... Idan har baki nemo Izzatu cikin kwanaki UKU ba... Zaki iya rasa komai na rayuwarki, Mulkinki da kuma ‘ya’yayenki..!!” Ya k’arashe yana mai buga sandar tasa guguwa ya kaure b’att ya b’ace cikin d’akin....

Giwa ta shiga doka masa kira tana fad’in duka wanann iftila’in da take ciki yana nufin akwai wani gaba gareta...!
Gefe ta koma tana shafa gefen kaita yanda wuta ya kwashe sumar... Da farko ta rasa hannunta guda da ya k’one k’urumus yanzu gashi ta rasa wani b’angare na sumarta... Shi haka wuta zaita cinye b’angarori na jikinta har ta k’one gaba d’aya kafin burinta na kafa ‘ya’yanta kan mulki ya tabbata..! Inaa bazata bari hakan ya kasance ba... Dole Waziri yasan yanda za’ai ya zak’ulo Izzatu duk yanda ta shige a fad’in k’asar kuwa... Da wanann tunani ta mik’e ta rufa alkyabbarta ta fito ta tadda Jakadiya..

_Sak’on ta’aziya ga d’aukacin members na Sameena Aleeyou novels sakamon rashin member guda d’aya da ya riskemu... Umm Jafar Muna addu’an Allah ya karb’i shahadarki... Allah ya baki Aljannah mad’aukakiya ya kuma d’ayyaba bayanki... Ameen thumma Ameen..! Dan Allah muna rok’onku da bakunanku masu albarka duk wanda yaga wannan yai mata add’ua.._

*MUHIBBAH*

*49*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Jakadiya na ganinta tai saurin zabura kaman taga wani abin tsoro sai kuma ta zube tana kwasan gaisuwa cikeda tsoro, dan harga Allah uwargijiyar tata ta bata tsoro a yanayin data ganta ciki...

Giwa ta watsa mata muguwar kallo tace “Dodanniya kika gani ko mai...?!”
Chapter 75 · 0% Book details