← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 162

Sashe 148

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_”Yammacin wata Rana ce mai d’aukeda bak’ar hadari wanda ya sanya tsaban duhun hadarin da k’yar mutum Ke iya ganin gabansa.. A wannan yammaci d’iyata Zahra ta shigo rayuwata... Kan hanyarmu muke na dawowa daga garinsu matar abokina Turaki, nayima Turaki rakiya a lokacin yana zuwa neman auren Hidaya.. I was the one driving the car sanda wata mata from no where ta bayyana gabanmu, ban kula da ita ba kasancewar akwai duhun hadari sosai.. Ga sauri da muke dan mu samu mu iso Masarauta kafin wannan ruwan ya sauk’a...”_ Muhibbah ta d’anyi fasali kafin taci gaba da karantawa
_”Sam ban kula da wannan matar ba wacce take rungume da jaririya sabuwar haihuwa, kafin na ankare na buge wannan matar da mota.. Cikin tsananin tashin hankali muka fito muka nufi wannan matar dake kwance gefe tamkar bata numfashi, sam bamu kula da jaririyar da take d’aukeda ita wacce tuni ta fettu gefe, muka nufo kan matar muna k’ok’arin bata agaji na gaggawa tareda tabbacin cewa tana numfashi... Cikin sauri muka d’auki wannan matar muka nufi Mota da ita dan muyi rushing d’inta zuwa asibiti dukda cewa wajen daji ne babu asibiti kusa... Sam bamu kula da jaririyar ba a zatonmu k’unshin tsummokaranta ne marassa amfani.. Bamu takan k’ullin kayan ba dan rayuwarta yafi mahimmanci, sam bamu San cewa ba k’ullin kaya bane d’iyarta ce lullub’e cikin zanin... Nan da nan muka nufi asibitin cikin garin Yalwan Shandam da ita dukda cewa a lokacin garin yana hautsine sabida rikicin ta’addanci da ake a garin a wancan lokacin... Mun samu da k’yar muka samu Likitan da yayi attending wannan matar.. Hankalina sosai ya tashi a wancan lokacin dan ban tab’a buge koda k’aramar dabba bane tinda na soma tuk’i sai gashi na buge mutum sukutum kuma Ta shiga cikin mawuyacin hali na kota ta mutu ko tayi rai dukda cewa a zahiri babu ko k’warzani alamun ciwo jikinta..Muka jira aka dubata ta ta d’an farfad’o kad’an, Likitan yace damu mu shiga mu ganta Ta farfad’o but her heart was very weak, Da alama batada k’oshin lafiya, komai ka iya faruwa.. Likita ya k’arada fad’in kaman akwai abinda take son fad’i.. Aiko muna shiga muka samu tana magana kaman sumbatu tana fad’in yaranta yaranta, Sansanin Yalwan Shandam, akwai jinjirarta a goyo bayanta.. ina jinjirarta..? Daga wad’annan kalaman bamu kuma sinkayo muryarta ba.. Na dubi Turaki cikin tsananin tashin hankali nace matar nan akwai jaririya a tareda ita dole mu koma wajen da muka bugeta.. Turaki yace anya kuwa Rankaidad’e kodai sumbatun zafin ciwo kawai take.. Na girgiza kai naceda Turaki hankalina bazai kwanta ba sai na koma wannan wajen na tabbatar da kalaman matar nan...Haka na fice a cikin sauri Turaki na k’ok’arin dakatar dani kasancewar garin ba’a kwance lafiya yake ba ga dare ya soma shiga.. Naceda Turaki koda zan had’uda ajalina Zanje na duba na tabbata bamu bar wata rai a wannan wajen ba wacce bazata iya yiwa kanta komai ba.. Haka na fice na nufi wannan wajen... Nayita dubawa banga k’ullin kayan ba.. Ga yayyafi da tuni aka soma ga kukan hadari, har na hak’ura zan tafi na sinkayo kukan jaririya... Nai saurin juyawa ina duban yanda nake sinkayo kukan.. Can k’asan wata bishiya na hango k’ullin kayan.. A hankali na duk’a na shiga warwarewa.. It was a baby girl.. A beautiful baby girl wacce kallo guda nai mata naji wane irin shauk’i had’ida tausayi.. Hannayena suna rawa nasa na d’auko jaririyar wacce taketa kuka sabida yunwa da jigata, Na soma jijjigata a hannuna amma batayi shiru ba, nai saurin shigewa da ita mota tsoron kar ruwa ya jik’ata ya k’ara mata fever, nan da nan muka bari wajen dukda cewa ana iya tareni a tuhumeni a ina na samu jaririya musamman sabida halin rashin tsaro da ake fama dashi.. Haka tana hannuna Ina jijjigata Ina driving har Allah ya taimakeni tayi bacci... Kasancewar motata lambar emirate council ne shiyasa van sami wani matsala da Jami’an tsaro ba... Haka na nufo asibtin rungume da jaririyar saidai a lokacinda na iso na tadda Turaki yayi jigum yana jiran k’arasowata.. Na k’arasa da fari’ata rungume da yarinyar ina fad’ida Turaki gashi na samo jaririyar ina mahaifiyarta take...? Jiki a sanyaye Turaki yake girgiza kai, na tsaya ina dubansa cikin tsananin sanyin jiki.. Lokaci guda na fad’a d’akin da matar take rungume da jaririyar a hannuna.. Saidai ga dukkan alamu lokaci yayi Allah ya amshi ran matar nan kafin na kawo mata jaririyarta... Na k’arasa cikin sanyin jiki na ajiye mata jaririyar a gefenta ina furta ga d’iyarki na kawo miki.. Ki tashi ki ganta... Ina maganan hawaye suna gangaro mun.. Likita ya shigo ya dafani yace Rankaidad’e Allah yayi mata cikawa, Ina ‘yanuwanta suke..? Daga ni har Turaki babu wanda yasan inda dangin wannan matar suke amma saidai munji ta ambaci Sansanin Yelwan Shandam.. Muka fito nida Turaki muna tunanin abinyi ga jaririya rungume hannuna.. Turaki yace Rankaidad’e yanzu meye abinyi..? Nace dashi sassafe idan Allah yasa muna cikin masu rai zamu tafi Sansanin Yelwan Shandam mu bincika ahalin matar nan, Turaki ya dubeni yace yarinyar fah..? Sai sannan na tuna da jaririyar dake rungume cikin hannuna..! Nai mata k’uri Ina dubanta ba tareda na iya furta koda kalma ba.. Bamusan a ina sansanin yake ba hakan yasa muka soma tambaya cikin daren.. Nan ake sanar damu ai ‘yan tadda Sun tashi wannan Sansanin Sun k’oneta babu wanda yasan yanda Refugees d’in suka koma... Wani sabon tashin hankali, kenan bazamu samu sauran ahalin matar nan ba, Turaki ya kuma dubana rik’eda yarinyar yace Rankaidad’e yaya zamuyi da yarinyar nan..? Na kuma dubanta k’walla Tab idanuna, lokaci guda naceda Turaki I won’t give her away.. She’s mine Turaki, Zan zama mahaifinta..! Batada kowa bayan ni.. She lost the only family she had left, which’s her mom.. na zamto sanadiyan rasata da tayi, zan zama gatanta in sha Allah... Zan bata duk wani kula da mahaifi yake baiwa d’iyarsa.. Har abada bazata tab’a sanin cewa bani na haifeta ba..! Turaki ya dubeni sosai yace Rankaidad’e are you sure about this.. This is a serious decision your Highness..! Naceda Turaki k’warai ni ne mahaifinta, kuma matata Aliya itace mahaifiyarta...Zamu binne hakan dani dakai yanzu a nan wajen.. Kamin alk’awari babu wanda zaiji wannan batu..? Turaki yai shiru yana nazarin girman alk’awarin da zai d’auka..! Na kuma dafa kafad’arsa nace ka min alk’awari brother..? A hankali Turaki ya jinjina kai yace nayi maka alk’awari amma ta yaya zaka b’oye hakan daga mutane..? Nace dashi yazo a daidai tinda dama shirye shiryen barin k’asar muke nida matata Aliya a lokacin sabida tak’urawa matata da Giwa tayi a cewarta Baiwa ce bata kamaceni ba.. Nace dashi zamu tafi da ita K’asar Spain zamu raineta a can, a lokacin da zamu dawo zamu Zo da ita matsayin d’iyarmu da muka haifa can k’asar Spain.. A wannan daren na kawowa matata Aliya d’iyata wacce na sanya mata suna Fatima Zahra... Yanda Aliya taimin alk’awarin cewa zata rufa wanann sirrin itama, Zahra ta zamto d’iyarta.. D’iyarmu nida ita... Washe gari muka koma wannan garin muka had’a jama’a akaiwa Mahaifiyar Zahra sutura da sallah kaman yanda yake a addini muka kaita makwancinta na gaskiya.. Na kuma d’aukan alk’awari saman k’abarinta cewa zan rik’e d’iyarta bisa gaskiya da amana...! Wannan shine Labarin d’iyata Zahra.. Zahra k’anwarki ce Muhibbah..! Zahra itace jaririyar k’anwarki wacce kuka rabu da ita da mahaifiyarku a Sansanin Yalwan Shandam..!”_
Tana ida karantawa ta saki takardan ya fad’i k’asa tana mai shessh’ek’ar kuka.. Zahra wacce itama tana durk’ushe wajen tinda Muhibbah ta soma karantawa tana fitar da wane irin kuka mai ban tausayi.. Da rarrafe Muhibbah ta K’araso yanda Zahra ke duk’a lokaci guda ta janyota cikin jikinta suka rungume juna cikin wane irin shauk’i, su duka biyun kuka suke mai tab’a zuciyar mai sauraro.. Illahirin mutane dake wajen hawaye suke da jin irin wannan al’amari... Cikin kuka Zahra Ke fad’in “My sister..! You’re my sister..!!” Tsananin kuka ya hanata ci gaba da magana..

K’ank’ameta Muhibbah ta kumayi tana mai kuma kwantar da kanta cikin k’irjinta take furta “Yes Zahra.. I’m your sister.. Your big sister... Allah ya kuma had’amu bayan mun rabu na tsawon shekaru..!”

Zahra ma cikin muryar kuka take ci gaba da furta “Since the I first saw you... I felt something very special about you, like we’re connected somehow..!” Muryarta ya carke sai kuka...
Muhibbah ta kuma rungumarta tana furta “Likewise Zahra... I felt the same, mu d’in ‘yan uwa ne..!” Ta kasa ci gaba da nagana itama sai kuka... Umaima ta k’araso ta duk’a gefensu tana kuka itama, lokaci guda ta dafa hannayenta saman kafad’unsu.. Suka d’ago suna duban juna su duka ukun... Lokaci guda suka rungume juna gaba d’aya su ukun suna wane irin kuka mai tab’a zuciyar mai sauraro.. Gimbiya Turai ta taso ta had’esu gaba d’aya ta rungume tana matsan hawaye itama.. Lokaci guda take furta “Alhamdulillah..! Alhamdulillah..!! Allah na gode maka daka had’e kan ahalinmu waje guda.. Bayan duk k’ok’arin da wasu sukayi suga Sun tarwatsa kan wannan ahali sai gashi ka had’emu waje guda cikin labaru da k’addarori na rayuwa daban daban.. Wa zaiyi tunanin wad’annan ‘yanmata guda uku tsatso guda ne.. Sai gashi cikin hikimarka da buwayarka ka had’esu waje guda.. Allah na gode maka daka had’e kan ahalin Alfah waje guda..!” Kuka yaci k’arfinta ga tsananin rawa da muryarta yake...
Mommy dake gefe sai matsan k’walla take tana duban wannan al’amari mai cikeda al’ajabi ga kuma tab’a zuciya.. Allahu Akbar Allah mai iko... Ashe wannan masarauta k’unshe yake da ahalin Muhibbah shiyasa taji duk yanda zatayi sai tazo wannan Masarautar.. Ashe dai Allah ne ya dawo da ita cikin ahalinta.. Kai wanann kayan Farin ciki da yawa yake.. Ubangiji ya cika abin godiya...!
Chapter 148 · 0% Book details