← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 162

Sashe 47

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Maami inada manufata da shirina...!”
Ya fad’i kansa tsaye...

Giwa ta had’iyi miyau da k’yar zatai magana kenan Jamal ya shigo da sallama... Dubansu yake da alamun tambaya saman fuskarsa dan tuni ya karanci halinda mahaifiyarsu Ke ciki...Shid’in ya santa sosai wanda idan tana cikin tashin hankali zai iya fad’i haka idan tana cikin Farin ciki da annashuwa zai iya fad’i... Shid’in yasan ko wane motsi na Mahaifiyarsu...

Jamal na shigowa Mahmood yai sallamada Giwa ya fice... Sukabi bayansa da kallo har ya b’ace masu daga ita har Jamal...

Yarima Mahmood na ficewa Jamal ya k’araso da sauri yana tambayarta meke faruwa

Giwa ta k’arasa ta zauna saman kujeranta na alfarma “Gwarzo..!” Ta ambato sunan Jamal cikin kakkausan Murya...

Ya k’araso ya duk’a gabanta yana dubanta cikeda kulawa

“Inaso kaja hankalin d’an Uwanka Mahmood ya amince ya amshi sarautar nan idan ba haka ba munaji muna gani sarautar nan zata kubce daga gidan nan duk abubuwan da muka jima munayi zai tashi a banza, zamu fice daga gidan nan cikin k’ask’anci da tozarci... Nasan bazakaso haka ba d’ah na...!” Ta k’arashe tana aika masa wani irin duba...

A hankali ya shiga jinjina kansa “Maami Karki damu zanyi duk yanda zanyi Yaya ya amince ya amshi sarautar nan... Bayan abinda ya faru yau cikin Fada ya zama dole Yaya ya amshi sarautar nan ko dan ya kare Martaban Ahalinmu a kuma gidanmu...!”

Giwa ta jinjina kai su duka biyun suna masu duban juna...

***

Tafiya mai nisa Majidad’i yai tamkar masu barin gari, saida sukeje wajen gari yanda babu mutane sosai yaja yai parking... Ya kaikaito yana duban Yazeed dake zaune gefensa...

“Ina saurarenka, mai kake nema wajena kana jinin AbdulJabbar...?!”

Murmusawa kad’an Yazeed yai “Abinda kake nema shi nake nema... The THRONE...!!”

Majidad’i ya dubesa da mamaki, lokaci guda ya saki murmushin rainin hankali “Toh mai kakeso nai maka..? Ai d’anuwanka Mahmood ya kamata kaje ka samu da wannan batu amma bani ba...!”

Murmusawa Yazeed ya kumayi yana mai gyara zamansa cikin kujeran “Kana tunanin nida kai zamu samu sarautar ne muddin Mahmood na tsakani...?”

D’an rage girman idanunsa Majidad’i yai yana mai girgiza kai “Ban fahimceka ba... Go straight to the point...!”

Yazeed ya shafa hab’arsa kad’an “Abu guda nake nufi muyi tarayya akai dan cikar burinmu...Let’s take my brother down....!!”
Yai maganar yana tsare Majidad’i da idanu shu’umin murmushin bai bar saman fuskarsa ba...

SameenaAleeyou📚
[7/12, 4:21 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*032*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Bazawarin murmushi Majidad’i yai a karo na biyu, ya kuma gyara zamarsa sosai yana duban Yazeed da ya kafesa da idanu babu alamun wasa a tattaredashi...
“Ni zaka rainawa hankali...? So kake kai amfani dani wajen cimma burinka...? Kai d’in kana tinanin ni zan barka kai amfani dani ne... Har abada bazan tab’a amincewa da wani cikin zuri’ar AbdulJabbar ba..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci...

Shu’umin murmushi Yazeed ya kumayi a karo na babu adadi “A cikin wannan battle d’in you need me more than I need you, zan maka amfani fiyeda yanda zaka min... Kasan ance da d’an gari akanci gari.. Bazaka tab’a samun Karagar nan ba ba tareda taimakon d’aya daga cikin ahalin AbdulJabbar ba... Idan baka amince min ba haka Kanajina kana gani sarauta bazata tab’a komawa gidanku ba, Idan Yayana Mahmood ya gama zamaninsa ni ne nan zan amshi mulkin ba kaiba haka idan na gama Magaji na d’ah na ko d’aya daga cikin k’annena shi zai amshi mulkin... Kaman Yanda Baba Wambai ya tsufa bai gaji gidansu ba tarihin abinda ya faru dashi zai kuma maimaita kanshi akanka kaga har abada jininku bazasu kuma samun wannan sarauta ba... Amma idan ka amince min muka had’a k’arfi da k’arfe muka yak’i Mahmood yak’in neman sarautar zai tsaya ne tsakanin mu biyu... Ni da kuma Kai...!” Ya d’anyi fasali yana duban Majidad’i da tuni ya apka tarkonsa, ya kuma sakin murmushin nasa kana ya mik’a hannu ya d’auki takobin Majidad’i da hannu guda ya d’agata sama yana juyata a hankali yake k’are mata kallo lokaci guda yake ci gaba da sakin murmushi yana furta “Takobi zai maye gurbin Mahmood a tsakaninmu... Domin kuwa shi ne zai fitar da Jarumi cikin mu biyun...Takobi shi zai raba gardama a tsakaninmu sannan ya tantance Jarumi cikinmu...Shi zai tantance waye ya dace da rik’on Sarautar wannan Masarauta...!!!” Ya k’arashe yana mai d’ora bakin takwabin a saitin wuyar Majidad’i murmushin bai bar saman fuskarsa ba...

Murmushi Majidad’in ma yai kana yace “Kana tinanin zaka iya karawa dani...?!”

Hab’ar Majidad’i kad’an Yazeed ya kama daidai sanda yake Yawo da makamin a saitin wuyar Majidad’in, lokaci guda yake furta “Babu alamun ragwanci ga mutuminda ya nuna abokin karawansa da makami har yai nasaran saita makamin a mak’oshinsa... I can cut your throat right this instant amma bazanyi hakan ba dan nafi so mu kara a filin daga yanda babu Dakarun da zasu kawo mana d’auki... Takwabi ce kad’ai zatai magana a tsakaninmu...!” Ya k’arashe yana mai cire takobin daga wuyan Majidad’i...

Wani murmushi renin hankali Majidad’i yai yana mai jinjina kai “Finally jinin AbdulJabbar mai tinani irin nawa... Jarumi shi ya cancanci sarautar wannan masarauta namu, kaman yanda kace Takobi zata raba gardama tsakaninmu a filin daga... Zamu dawo da tsohon Al’adun kakaninmu wanda Jarumi kad’ai Ke yin Sarauta.... Naji dad’in wannan shawari naka Yarima Yazeed... Toh amma wani hanzari ba gudu ba... Shin kana tunanin Masarauta zata amince ta dawo da Al’adar da aka jima da banning d’inta, Al’adar da aka jima da kasheta a wannan masarauta tamu...?!”

Gajeren murmushi Yazeed yai “Kadai muyi k’ok’arin kawar da Mahmood a tsakani duk abinda zaizo daga baya mai sauk’i ne.... Partners..?!” Ya k’arashe yana mai mik’a masa hannu alamun musabaha....

Majidad’i ya mik’o masa hannu sukai masabaha yana mai jinjina kai yake furta “Partners..!!”

Daga nan sallama sukai da Yazeed yanda Yazeed d’in ya kirawo abokinsa Zayyad yazo ya d’aukesa dan tuni Majidad’i yayi tafiyarsa bazasuso a gansu tare ba...

Zayyad na k’arasowa da mamaki yake duban Yazeed sanda ya bud’e marfin mota ya shige “Rankaidad’e Wai mai ya faru ne... What really happened... Why are you here all alone... Ina motarka, Ina Hadiminka...?!”

Ko tambaya guda Yazeed bai amsa ba sai ci gaba da sakin murmushi da yake lokaci guda yake furta “I’ll soon get rid of one of my major problems...!” Ya k’arashe yana sakin murmushin nan nasa....

Zayyad da tuni ya soma driving murmusawa yai kad’an yana furta “WOW! This calls for celebration Your Highness... Fad’a min ina zamuje muyi celebrating...?!”

D’an dubansa da wutsiyar idanu Yazeed yai ba tareda yace komai ba... Zayyad yaci gaba da fad’in “I guess ka sami kan yarinyar nan ne dataci maka mutunci ko kuma ka samo hanyar da zakai ka fitar da Mahmood daga masarauta...!”

Dubansa da wutsiyar idanu kana yace “Abokina na yarda ka sanni sosai yanzu kam... Idan na zama sarki komai mai yuwa ne sannan ne zan rama abinda tai min don bataci banza ba... No one messes with Prince Yazeed AbdulJabbar..!” Ya k’arashe yana sakin murmushi sanda yake tuna kalan wulak’ancin da zaiwa Muhibbah muddin ya zamto Sarki... Sai ta gwammaci dama batazo duniya ba da irin wulak’ancin da ya tanadar mata...
Zayyad na tambayarsa destination ko answer sa bai ba sai sakin murmushin mugunta da yake ci gaba da yi a hankali.... Sanin Yazeed d’in bazai amsasa ba ya sanyashi yin shiru da bakinsa ya nufi shisha spot d’insu da suka saba zuwa...

**

Waziri ya gama had’a kan ‘yandabansa cikin dare ya basu umarnin su shiga Gidan Wambai su nemo k’undin nan yanda ya shiga ya fita, idan ta kama su tone k’asan gidan ne su tone su ciro masa k’undin nan duk yanda za’ai....
Ya kwance bakin rawaninsa ya nunawa shugaban exactly kalan jakar fata da k’undin ke ciki Wanda zasu d’auko masa....

Shugaban ‘yandaban ya amsa ya juyata ya k’are mata kallo kana ya risina yace “An gama mai girma Waziri... Idan cikin tandu take sai an d’auko maka ita...!!”

Waziri yace “Yauwa haka nake sonji... Kuyi dik yanda zakuyi ku d’auko min wannan jaka sannan Koda wasa kar ku bari a kamaku, kuma kada ku bar wata alama da zata nuna cewa Waziri ne ya turoku...!”

Suka jinjina kai suna masu furta an gama Mai Girma Waziri..!

Ubandoma dake lab’e bayansu murmushi yai dan yasan tinda wad’annan ‘yandaba ba ma’abota sarauta bane bazasu fahimci yanda Wambai zai aje wannan k’undi cikin sauk’i ba, dan haka zai k’yalesu su gama dube dubensu har su fice sannan ya shiga ya d’auko k’undin cikin tsanaki yakaiwa Giwa da sharad’in mallaka masa ‘yanci...! Ya saki murmushi yana mai gyara zaman layarsa da zai danna dan ya b’ace da zaran yaji alamun za’a kamasa...

Hakan ce kuwa ta kasance tuni ‘yandaban Waziri sun isa gidan Wambai Ubandoma na biye dasu ba tareda saninsu ba....

Gidan babu kowa sai ma’aikata, ba tareda b’ata lokaci ba suka kame ma’aikatan gaba d’aya suka d’auresu suka kullesu a nan D’akin Maigadi... Tuni suka shiga suka soma bincikensu... Sun kwashe kusan awanni biyu suna wannan bincike babu k’undi babu alamunsa... Haka suka wargaza gidan gaba d’aya sukai d’add’aya da komai amma babu k’undi babu alamun k’undi...

K’arshe haka suka hak’ura suka fice, ogansu ya kirawo Waziri yana mai sanar dashi Rashin sa’an da sukai...

Suna ficewa shi kuwa Ubandoma ya shigo ya soma nasa binciken musamman da yaji basu dace ba...

Waziri ya sanar da shugaban ‘yandaban nasa da suyi maza su fice daga gidan kafin azo a kamasu, daga nan Fada ya nufa wajen Giwa dan dole taji wannan batu cewa dik yanda akai Bak’on Buzu ya rigasu isa wajen Wambai, ya tabbata wannan mutumi bak’on Buzun shine ya amshe k’undin nan daga wajen Wambai.. Ya zama dole su zak’ulo waye Bak’on Buzu kafin Mahmood ya rigasu sanin ko wanene Bak’on Buzu....!!

Majidad’i yasha mamaki sanda ya shigo gidan Mahaifinsa ya tadda mai gadi da ma’aikata rufe nan d’akin Maigadin sunsha d’auri... Take tunanin Bak’on Buzu ya fad’o masa... Babu shiri ko takan mai gadin da ma’aikatan baibi ba ya fad’a cikin gidan a guje, yasan duk wanda ya shigo gidan ba b’arawon gaske bane akwai abinda ake nema ne wajen mahaifinsa kuma ta haka ne kawai zai capke wanda keda alhakin ciwon mahaifinsa....!
Chapter 47 · 0% Book details