Sashe 53
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yarfe gumin da ya keto mata tai sanda ta doka kiran Jakadiya..! Nan kuma ta tuna ashe Jakadiya bata warware daga bugun da Izzatu tai mata ba... Taja gajeren tsuka a hankali sanda hadimarta guda ta shigo tana mai risinawa... Giwa ta fatattaketa tace tajeta tai mata kiran Jakadiya bata damu ko ta warke ko bata warke ba, dik yanda za’ai tazo Ta tana nemanta... Babu shiri Baiwar ta mik’e cikeda girmamawa ta fice... Giwa sai faman safa da marwa take tana huci....
***
Sauri sauri ta fito da niyyan bin bayan Jamal amma saidai mai, tana fitowa suka kusan karo da Fu’ad zai shige sashen Giwa.... Fu’ad ya tsaya cak yana mai dubanta kyakkyawan murmushi saman fuskarsa...
Dukda k’atutun bak’in ciki da ya tokare mata mak’oshi hakan bai hanata k’ak’aro murmushin yak’e ta sakar masa ba....
“Your Highness... Barka da rana...!” Ta fad’i murmushin bai bar saman fuskarta ba...
Saida ya rage girman idanunsa kad’an sai kuma yace “Bazan amsa irin wannan gaisuwar ba Hibbah... Mu gaisa a cen..!” Ya k’arashe yana mai duban sliding door dake gefe yanda zai fitar dake madaidaicin wajen shak’atawa... Bayi masu kaikomo kaw idan suka Zo shigewa sai Sun risina Sun gaidasu...
Muhibbah da gaba d’aya ranta ya gama jagulewa sabida plan d’inta da Fu’ad ya b’ata mata k’ok’arin saita kanta tai tace “But your Highness ka mance sharad’ina, banso kowa yasan alak’ar for now a Masarautar nan... Gudun k’anan maganganu irinta gidan sarauta... Nafiso mu fahimci junanmu sosai and... to be sure of what we feel for each other..!”
Fu’ad ya d’an kuma takowa kusanta kad’an had’ida rage muryarsa “And you think zan iya jure wannan sharud’an Naki Hibbah... Is not as if we are doing anything wrong.... So banga abin damuwa ba... And one more thing...!” Ta d’ago tana dubansa jin yayi fasali
Fu’ad yaci gaba da fad’in “My feelings for you are real Muhibbah... Bana buk’atan yin wani tunani gameda soyayyarmu... Unless kuma kece baki so na...!” Ya k’arashe yana mai tsareta da idanu...
Tamkar takai masa naushi a fuska haka takeji jin yanda yake furta mata kalaman Soyayya wanda tayi imani da yasan ko wacece ita bazai soma hakan ba... Badon karta ruining plans d’inta ba data masa kaca kaca tun daga nan amma saidai hakan ba mai yuwa bane...
Tai k’ok’arin d’aura fake smile saman fuskarta “Ba haka nake nufi ba your Highness..”
Fu’ad ya katseta da fad’in “Idan har ba haka kike nufi ba, then prove it...!” Bai jira cewarta ba ya shige k’ofar...
Ta fuzar da fuci a hankali badon taso ba tabi bayansa zuciyarta gaba d’aya a cunkushe..
Shiko Fu’ad ganin ta biyo bayansa sai zuciyarsa ta aminta tabbas Muhibbah k’aunarsa take... Toh wata mace ne ma zata k’isa, baijin akwaita...
Kyakkyawan murmushi saman fuskarsa yake dubanta cikeda jin dad’i, tuni ya sakankance yaci gaba da jero mata kalaman k’auna...
Shigowarsa sashen kenan ya hangesu, kanta a k’asa tana faman sakin murmushi ga Fu’ad tsaye gabanta yana kasheta da wane irin kallo wanda ko ba’a fad’i maka ba kasan abinda irin kallon Ke nufi... Da gani suna matuk’ar jin dad’in zancen da suke.... Cikin sakanni zuciyarsa Ke harbawa....
SameenaAleeyou 📚[7/24, 6:11 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*36*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
A hankali yake murza hannunsa dake rufe cikin bandage wanda sam baisan yana yin hakan ba, ya kasa janye idanunsa daga barin duban nasu bai kuma daina murza hannun nasa ba wanda da alama ko zogin ciwon baiji... Ji yake tamkar zuciyarsa zata b’allo daga cikin k’irjinsa ta fito waje.. Kan kace mai jini ya soma d’iga a wajen...
Sauk’owar Zahra kenan Ta hangi mahaifinta ya k’urama waje guda idanu ga jini na kuma d’iga daga cikin hannunsa... Cikin sauri Zahra ta k’araso tana duban hannun nasa take fad’in “Paa... Paa you’re bleeding again....!!”
Muryar Zahra da Muhibbah ta sinkayo ya sanyata saurin waigowa tana duban wajen... Ido suka had’a da Mahmood saidai tuni yasa kai ya juya ya fice gaba d’aya daga sashen yana mai tamke hannunsa mai d’igan jini, lokaci guda yake ceda d’iyarsa it wasn’t serious she shouldn’t worry...
Zahra tuni tabi bayansa yayinda Muhibbah kacaukam hankalinta ya koma garesu... Ta dubi Fu’ad daketa faman duba abu cikin waya da alama baisan wainar da ake tuyawa ba...
D’an dafa kanta tai kad’an had’ida tamke idanunta...
Fu’ad ya d’ago yana dubanta had’ida daina abinda yake “Are you alright..?!” Ya tambaya yana dubanta...
K’ak’aro murmushi tai tace “Kar ka damu just a headache...!”
Cikin nuna kulawa Fu’ad Ke fad’in “Headache.! Subhanallah, do you want to see a Doctor... Should I call one...!”
D’an girgiza masa kai tai tace “No kar ka damu, idan nai bacci zai daina, na gode da kulawa...!”
Ya sauk’e fuci a hankali sai kuma yace “Are you sure..?”
Ta jinjina masa kai ba tareda tace komai ba...
Daidaita tsayuwarsa ya kumayi sai kuma yace “Muje na rakaki..”
Ta girgiza masa kai a hankali “Ka mance conditions d’ina... We shouldn’t be seen together..”
Ya d’an ware idanunsa kad’an kaman zaice wani abu sai kuma yace “Alright fine... But promise me one thing..!”
Ta d’ago tana dubansa.. Fu’ad yaci gaba da fad’in “You’d take good care of yourself for me..!” Ya k’arashe cikin kwantar da murya..
Dariya yaso bata amma sai ta gimtse tace “I’d in sha Allah... I promise..!”
Fu’ad ya murmusa kad’an yana mai bata hanya alamun ta shige... Ta tako zata shige, Daidai k’ofa Ta sinkayo muryarsa yana fad’i tamkar mai rad’a “I love you..!”
Murmushi kurum ta sakar masa ba tareda tace komai ba ta shige...
**
A b’angaren Mahmood kuwa suna tafe shida Zahra Raheema ta hangosu, cikin sauri ta take masu baya tana tambayan Zahra meke faruwa...
Shi kuwa Mahmood cikin sassarfa kurum yake tafiyar nasa ba tareda yabi takan Raheema dake tambayar Zahra abindake faruwa ba...
Hannunsa a tamke sosai yake tafiyar zuciyarsa naci gaba da bugawa, suna shigowa parlorn ya shiga warware bandage d’in k’arfi k’arfi wanda har saida yaso baiwa Zahra tsoro...
Raheema ta k’araso cikin rawar jiki take fad’in “Yarima mai ya sameka... Ina ka sami wannan k’aton yankan...?” Ta dubi Zahra dake tsaye gefe tana duban mahaifin nata cikin kid’ima tace “Zahra get the first aid let’s treat his wound...!”
Muryarsa suka sinkayo yana furta “No..!”
Raheema Ta dubesa tace “But you’re bleeding..”
Katseta yai cikin tsananin d’aga murya “I said no... Ko bakiji bane..!!”
Raheema ta koma gefe tana duban ikon Allah yayinda Zahra Ke furta “Paa should I call Aunty Muhibbah tunda itace tai maka treating, na kirata ta sake..”
“Whattt..!!” Raheema ta furta cikin zuciyarta, ina take har akai wannan iskancin... Wannan shegiyar mayyar yarinyar ta wanke ciwon mijinta... Eh lallai Aunty Zeenatu tayi gaskiya da tace wannan yarinyar karuwanci kawai take sonyi da Princes d’in Masarautar nan.... Toh wllhi tayi k’arya ta fara da Mahmood d’inta..
Tayi nisa cikin tunani har batama San sanda Mahmood yai hayewarsa sama ba Zahra kuma ta fice tuni ta barta nan tsaye...
Ta d’aga Kai tana duban matakalan bene zuciyarta naci gaba da harbawa... Toh maiyasa har yanzu maganin bai soma aiki ba, maiyasa gaba d’aya bata gabansa, tama kula tamkar yanzu yafi yin watsi da ita unlike before, dik tsiya da yakan aika ai kiranta koda ba wani zancen arziki zasuyi ba amma yanzu ko takanta baiyi, jibi har ciwo yaji duk bata sani ba tana can baki sake wata ‘yar banza na neman k’wace mata Mahmood d’inta... Toh wllhi da sakel hakan ba mai yuwa bane... Ta k’arashe tunanin nata tana mai ficewa fuuu tamkar zata tashi sama...
**
Yana haurawa sama shirin fita yai kana ya fito waya manne kunnensa yana magana da Turaki...
Turaki yace “You can’t drive like that your Highness ka bari nazo na kaika...!”
Cikin kakkausar murya yake fad’in “Mai ka d’aukeni, kan wannan k’aramin ciwon kake cewa bazan iya driving ba... Banida lokacin jiranka Turaki, and I don’t trust anyone cikin Masarautar nan...!” Yana ida fad’in haka bai ko jira cewan Turaki ba ya katse kiran had’ida jefa wayar cikin aljihu... Turaki na kiran sunansa inaa ko amsa sa baiba ya isa ma’ajiyan mitocinsa ya shige guda d’aya yayi ficewarsa...
Yana ficewa Waziri ya lek’o daga mab’oyarsa yana wani muzurai da idanu, take ya ciro waya cikin babban rigarsa ya k’ara a kunnensa “Ya fito, kabi bayansa... Kuma ka tabbata bai b’ace maka ba....!” Daga haka katse kiran Waziri yai kana ya nufi sashen Giwa...
Duba d’aya Giwa tai masa ta kauda kanta gefe... Waziri ya saki murmushi mai taushi yana mai duban yanda Giwa Ke sakin huci...
Da kirari ya soma mata, ya wasata sosai yai mata kirari da yabo sosai kana ya k’arada “Muddin Waziri na numfashi bakida damuwa, idan akan Mahmuda ne kisaka ma ranki Mahmood a tafin hannunki yake domin koda Ubandoma ya munafuncemu ya had’e kai da wani cikin Masarautar nan na aje mutum guda wanda zai dinga bibiyan al’amaran Mahmood da kuma duk yanda yake zuwa zai sanar damu...!”
Giwa Ta d’an dubesa kad’an har lokacin fuskarta babu walwala.. “Allah yasa gaskiya kake fad’i...!”
Ya kuma murmusawa yana mai takowa gabanta kad’an “Burinki k’iris yake da cika, Ina mai tabbatar miki..!!”
Sai wannan karon ta murmusa kad’an kana Ta mik’e cikeda k’asaita, fuskarta na duban wani b’angare take furta “Waziri akwai sauran rina a kaba... D’azu Yazeed yazo min da wani zance kuma na duba maganganunsa sosai na aunasu, tabbas akwai kuraye da dama cikin Masarautar nan... Idan har Ubandoma nada k’arfin halinda zai iya cin amanamu toh ko shakka babu zai iya tona mana asiri.. Ubandoma yasan sirrikanmu da dama bazai yuwu mu k’yalesa haka nan ba..!”
Waziri ya tako kad’an yace “Mai kike so Ayi....?”
Giwa ta waigo tana dubanasa lokaci guda take d’an buga hannunta dake rufe cikin bak’ar safa... “A sakashi yayi shiru na har abada... A b’atar dashi kaman yanda aka b’atar da sauran..!!”
Waziri ya kuma takowa kad’an, shiru na d’an dak’ik’ai suka gifta “Ba abu bane mai sauk’i duba da cewa Mahmood yana nan cikin Masarautar nan a halin yanzu, amma bakida damuwa Allah shi taimakeki... Zan kula da wannan..!!”
Giwa ta juyo tana dubansa murmushi saman fuskarta, lokaci guda ta tako daidai gabansa su duka biyun suna duban juna cikin idanu murmushi kwance saman guskokinsu....