← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 162

Sashe 116

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gimbiya Turai taci gaba da fad’in “Muka rufe wannan batu nida Fattu babu wanda yaji tinda dama Sarki baisan da labarin juna biyun ba, bayan wani lokaci mai tsawo Mai Martaba ya waiwayeni, baida labarin ya barni da ciki har na haihu kuma har na rasa abinda na haifa...Ashe a wannan lokacin juna biyun da Izzatu kedashi shine ya janye hankalinsa har ya mance da ni ya bada hankalinsa kacaukam akan Izzatu da cikinta...Bansan ya akayi ya kuma waiwayoni ba, nadaiga yana zuwa wajena akai akai, dukda babu wani Sabo a tsakaninmu yakan bani labarin d’ansa mai suna Mahmood wanda matarsa Basarakiya ta haifa masa... Saidai nayi murmushi amma bana iya cewa komai...

Bayan wasu shekarun yaci gaba da ziyartata, amma ban sake koda b’atan wata bane sannan da alama Izzatu ma bata kuma haihuwa ba tin d’anta mai suna Mahmood da yace ta haifa masa, ya kasance Mahmood shine kad’ai dan Sarki AbdulJabbar wanda ya d’auki son duniya ya d’aura masa, a nan a haka kwatsam ya sanar dani matarsa ta haihuwa ta kuma haifa masa wani d’ah ya saka masa suna Yazeed, Yazeed ya taso ya fara wayo shima, saidai har lokacin magana Mai Martaba bai wuce Mahmood, da matuk’ar wahala kaji ya ambato k’aramin d’ansa mai suna Yazeed, nikam har na mance da haihuwa domin kuwa shekarun da d’an yawa tun bayan dana rasa abinda na haifa daga farko, a tsakanin wannan lokacin nima kwatsam sai na soma laulayi... A lokacin da yazo min da labarin Gimbiya ta haifa masa d’ah namiji ya kuma saka masa sunan mahaifinta Sarki Jamal a lokacin ashe nima inada ciki k’arami ba tareda na sani ba... Naci kuka sosai jin Izzatu ta kuma haihuwa an sakawa yaron sunan mahaifina Sarki Jamaluddeen saidai banida ikon fad’iwa Sarki AbdulJabbar komai... A ‘yan kwanakin da Mai Martaba yayi wajena nan ya fahimci nima ina d’aukeda juna... Toh sai yayi dogon zango wajena bai koma masarauta ba, ashe hankalin Izzatu ya tashi matuk’a ganin Sarki bai waiwayeta ba dukda sabon jariri da take dashi, koda Mai Martaba ya koma sai ya sanar da ita juna biyu gareni da alama Allah ya amshi addu’arsa gashi bayan duk tsawon shekarun nan Izzatu ma zata haifo masa Magaji Wato Izzatu ni kenan kaman yanda ya sanni... Giwa Ta shiga damuwa ashe ciki ne dani kuma har ya fito sam bata kawo zan kuma haihuwa da Sarki ba dan rata ne sosai tsakani tinda da ace jaririn dana rasa yana raye da ya kusa isa munzanin k’aramin matashi, lokacin jaririnta yayi k’wari sosai dan yakai watanni kusan takwas, ta barsa wajen masu kula dashi tazo ta ga halinda nake ciki, saidai wanann zuwan da zatayi batazo da rakiya matsafinta ba, ga dai ciki jikina har ya fito babu halin ta salwantar da cikin tinda Mai Martaba ya sani... Sosai na hango tashin hankali tattareda ita, ta tanbayeni komai gameda cikin, babu abinda na b’oye mata harta asibiti da Mai Martaba ya kaini da kansa saida na sanar da ita, ta dinga sakin huci jin irin kulawa na musamman da Sarki Ke bani sabida cikin... Ta tambayeni yaushe akace zan haihu a asibiti..? Babu musu nan ma na sanar da ita...! Duk wannnan abinda ake Hadimata na tsaye bayan k’ofa rik’eda yarinyarta mai suna Aliya ‘yar shekaru uku a duniya, dan lokacin Hadimata Fattu Allah ya azurtasu d samun yarinya d’iya mace kuma har Ta shekaru hud’u a duniya...!”

Ubandoma da gumi Ke ci gaba da tsartsafo masa yace “Fattu da d’iyarta, Dama Fattu Hadimarki ce..?!”

Gimbiya Turai ta jinjina kai tace “Fattu Hadimata ce wacce Mai Martaba ya ijeta da mjinta matsayin masu kula dani...!”

Gimbiya Turai ta nusa taci gaba da fad’in “Fattu taga duk abinda ya faru kan idanunta yanda Izzatu ta tasani gaba da tambayoyi kuma ban b’oye mata komai ba na sanar da ita... Hankalin Fattu sosai ya tashi daga nan yanda take lab’e... Kukan yarinyarta shine ya janyo hankalin Izzatu ta dubeni tace wacece wannan..? Nace da ita Hadimata ce mai Martaba ya bani...! Giwa ko ince Izzatu ta tsare Fattu da d’iyarta Aliya da idanu... Bata masu dai komai a wannan lokacin ba saidai Ta gargad’eni cewa kada Mai Martaba yasan ta kawo min ziyara..! Na jinjina mata kai nace bazai sani ba... Toh ko bayan data tafi Fattu taso mu sanar da Mai Martaba cewa matarsa ta kawo min ziyara amma na gargad’i Fattu nace da ita kada ta sanar da mai Martaba ko mijinta ma kada ta sanar dashi.. Abin sosai ya dami Fattu dan haka nan kawai bata aminta da ziyaran da Giwar Amale ta kawo min ba na bazata... Toh a haka Mai Martaba yakan kawo min ziyara har dai lokacin haihuwata yazo, a lokacin haihuwata banga Mai Martaba ba, baizo ba saidai kwatsam naga Izzatu tace min Mai Martaba ya turota ta amshi haihuwata... Ta bani wani ruwan magani tace nasha shine zai d’aga min nak’uda..! Babu musu na amsa ruwan maganin na shanye kaman yanda Ta umarceni, ai kuwa Ina shan ruwan nan nak’uda ya tashi gadan gadan, na haihu ban haihu ba ban sani ba, tin daga wannan lokacin ban kuma sanin wacce duniya nake ba sabida tsananin azaba, bani a cikin hayyaci na, farkawa kawai nayi na ganni gefen Fattu dake kuka rungume da jariri... Cikin d’imauta naceda Fattu ina jaririna..! Fattu na hawaye ta mik’o min shi tace dani jaririna baizo da rai ba...! Naci kuka sosai, na rungume gawan jaririna ina hawaye.... Giro da wasu mutanen gari su sukaima jaririna sutura aka rufesa... Bayan faruwan wannan al’amari da kad’an Mai Martaba yazo ya tadda na haihu yaro baizo da rai ba... Sosai shima ya shiga damuwan rasa jaririn da mukai... Ashe abinda ya hanasa zuwa ya kwanta jinya ne na d’an wani lokaci wanda har bai fita koda Fadarsa ne, yana warkewa kuwa ya taho gareni dan duba halinda nida Jaririna muke ciki...! Tin daga bayan wannan lokaci ban kuma samun haihuwa ba, tun bayan rasa jaririna da nayi...!”

Muryar Ubandoma suka sinkaya yana fad’in “Ki yafeni Rankidad’e..! Kimin aikin gafara Ranki dad’e..!!” Cikin kuka yana mai zubewa saman gwiwoyinsa yake furta wad’annan kalamai...
Gaba d’aya kallonsu ya koma kan Ubandoma dake duk’e gaban Gimbiya Turai yana kuka yana neman gafara....!

Baba Nomau ne ya dafa Ubandoma yace “Kar ka katseta ka dakata ta ida sanar damu dukkan abinda ya faru gudun kada mu fad’a wani labarin..!”

Ubandoma ya jinjina kai har lokacin yana duk’e yana hawaye...

Gimbiya Turai taci gaba da fad’in “Bayan kaman shekaru biyar da faruwan wannan al’amari wasu fatake suka tsaya a garinmu suka nemi a taimaka masu da ruwan sha a nan gidan da aka ajeni...! Sun razana sosai sanda sukayi tozali dani a cikin gidan...
D’aya daga cikin rundunar fataken ta saki Kwanun shan da aka kawo mata ruwa ciki ya zube sabida tsananin tsorata da tai da ganina... Cikin rawar murya ta ambato sunana “Gimbiya Turai..!” A razana nake sanar dasu bani bace...! Nayi saurin guduwa d’aki ina kuka... Fattu Ta bisu da kallon mamaki tana kuma mamakin jin sun ambaceni da Gimbiya Turai...

Fattu ta k’arasa garesu tace “Bayin Allah ko akwai wani abu ne..?!”

Matar data ambaceni da Gimbiya Turai tace “Mu Fatake ne daga can Nahiyar Benin, wannan matar data gudu d’aki d’iyar Sarkin k’asarmu ne wanda bayan aurenta da kad’an mahaifinta Sarki ya mutu, dangin dangau sukai qaqa gida suka haye gadon mulkin mahaifinta sabida d’an uwa d’aya tak gareta, kuma a lokacin da Sarki mahaifinta ya rasu d’anuwanta yana k’arami bazai iya yak’in neman mulki ma kansa ba, dangin mahaifiyarsa suka d’aukesa sukai nesa dashi, kwanakin baya ya dawo k’asar Benin yana tambayar Sarkin wane nahiya ne ya auri ‘yar uwarsa dan a halin yanzu ya girma har ya zamto Magidanci.. Ashe ‘yaruwasa tana nan a wannan Nahiya, tabbas zamu koma masa da labari..!”

Fattu dai saurarensu kawai tayi har suka gama shan ruwan da zasu sha suka d’auki hanya....

Bayan sun tafi Fattu ta shiga k’wank’wasa min k’ofa tana sanar dani Sun tafi... Na fito illahirin jikina rawa yake... Na mance inada d’an uwa sunansa Alfah...! A lokacin da wad’Annan Fataken suka ambaci Alfah sai na tuna shi, take naji ina son sanar da Mai Martaba duk abinda ya sameni, take naji kaman an sauk’e min wani dutse mai nauyi a k’irjina, tsoron sanar da Mai Martaba halinda Izzatu ta jefani ciki duk sai naji kaman an yaye min lokaci guda... Na sanar da Fattu komai duk abinda ya faru..! Fattu ta dinga aljabi tana mamakin yanda Izzatu ta canza kanta dani.. Nan naga kukan Fattu ya kasa tsagaitawa..! Na dafa Fattu nace “Fattu akwai wani abu ne..?!”

Fattu na kuka take cedani “Rankidad’e tabbas na yarda matar nan zatayi duk abinda kikace domin kuwa Jaririn da kika tashi kika gani matsayin d’anki ba naki bane... Ina lab’e akan idanuna Ta canza jaririnki da gawa.. Naji tsoron yin magana ne a matsayi na na baiwa tinda banida shaidu babban magana ne da ya shafi matar Sarki wanda ban isa nayi jayayya da ita ba... Shiyasa kika tashi kika ganni rungume da hajaririn ina kuka... Rankidad’e duk yanda akayi jaririnki yana nan a raye.. Watak’ila Giwa ta b’oyesa a wani wajen... Kuma zai iya yuwuwa cikinki na fari kin haifa.. Zai iya yuwa itace ta salwantar da jaririnki na farko..!”

Ubandoma dake hawaye jinjina kai yake yana furta “Tabbas inada masaniyan kan jaririnki na biyu kuma yana nan a raye..!” Yayi maganar cikin rawar murya...

Gimbiya Turai ta share hawayen da suka zubo mata kana taci gaba da fad’in
“Nida Fattu muka yanke shawarin idan d’iyar Fattu ta dawo daga makarantar Allo Giro ma ya dawo daga Kasuwa zamu tattara mu d’unguma mu tafi Masarauta dan mu sanar da Mai Martaba halinda ake ciki tunda yanzu Allah yayi na dawo hayyacina..! Da wannan shawari muka nufo tsakar gida dan soma shiryawa....Wani ikon Allah muna fitowa tsakar gidan muka tadda Izzatu cikin bak’ak’en tufafi Alkyabba da rufin kai, hannunta rik’eda fitila jan wuta naci a cikin fitilar, Ta kafe mu da idanu cikin yanayi na ban tsoro ga wani k’aton bak’in tulu gabanta bak’in hayak’i na fitowa daga cikin tulun....!”
Chapter 116 · 0% Book details