← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 162

Sashe 129

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A hankali Mahmood Ke takowa yanda take zaune Ta bada baya tana duban fad’in Masarautar da irin rayuwar da tayi ciki... Al’amarin mahaifiya ya wuce wasa, tabbas shiyasa yaji wani al’amari mai girma a tattareda matar sanda suka soma had’uwa a lokacin tana cikin halin hauka wanda Giwa tai sanadiyar kasancewarta ciki..! Rauni sosai ya bayyana tattare dashi, dole ma yaji rauni domin kuwa mahaifiya ba abin wasa bace..! Tsawon rayuwarsa yayi ne yana yima wancan azzalumar matar biyayya.. Ashe ba itace Ta haifesa ba rabasa tayi da mahaifiyarsa..! Ko mai zai ma Giwa baijin zai huce domin kuwa Ta masa abubuwa da dama wanda duniyar nan tayi kad’an yace zai rama a cikinta saidai ya barwa wanda ya haliccesa ya kuma hicceta yayi hukunci tsakaninsu domin shi kad’ai ne zai iya hukunci ma wannan azzalumar matar wacce babu d’igon imani ko rahama cikin zuciyarta..!

Ya duk’a a hankali gijif saitin k’afafunta yana jin wani irin kuka mai k’arfin gaske na zuwa masa..! A hankali ya saka yatsun hannunsa yana shafa yatsun k’afafunta dasu.. Hawayensa na d’iga saman k’afafun nata..! Baisan sanda ya kifa fuskarsa saman k’afafun nata yana kuka sosai..! Itama kukan take tana dafe dashi..!!

Ta kasa aminta shid’in d’anta na fari ne data rasa tsawon shekaru... Su duka biyun babu mai iya cewa komai sai kukan rahama da suke, hak’ik’a Ubangijinsu ya cika rahamarsa a garesu, bayan d’ebe tsammani na tsawon shekaru yau sai gashi ya kuma had’e fuskokinsu matsayin d’ah da uwa..! Allahu Akbar komai yayi tsanani yana tare da sauk’i, duk tsananin da ka tsinci kanka ciki, kada ka karaya, ka yarda da Ubangijinka kayi imani cewa zai kawo maka sauk’i...!

Hannayenta na rawa ta d’ago fuskarsa dake jik’e sharkaf da hawaye wanda ya rine zuwa ja sabida tsananin kuka..!

Turaki da Ansar dake gefe guda suna kallon wannan kayan Farin ciki da Al’ajabi duban juna sukai had’ida sakar ma juna murmushi lokaci guda Turaki na labartawa Ansar d’in wanene Mahmood, d’abi’unsa tsakanin mutane kama daga ahalinsa har zuwa al’ummarsa..!

Ansar na duban reunion d’in Mahmood da mahaifiyarsa yake furta “Ban tab’a cin karo da labari irin na wad’Annan bayin Allah ba..! Hak’ik’a an masu zalunci mafi muni a doron k’asa..! Daga k’arshe Allah ya kuma had’e fuskokinsu.. Sun cancanci farin ciki a sauran rayuwar da Ta rage garesu..!!”

Turaki ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Wannan haka ne..!”
Ubandoma ne ya k’araso yana kuma sanar dasu yanda al’Amara suka kasance..! Nan su Turaki ma Ke sanar dashi yanda al’amaran suke a Masarauta, sosai hankalin Ubandoma ya tashi jin Muhibbah na hannun Giwa, ya tuna sanda suka rabu tai masu sallama..! Tabbas idan Giwa ta gane itace Saudatu bazata barta da rai ba...! Hankali tashe yake tambayar su Turaki ina ake zaton Giwa takai Muhibbah..!

Turaki yace ai babu irin neman da basuyi ba cikin Masarautar, har dai Sun soma tunanin ko ta fice da ita daga cikin Masarautar ne..!

Ubandoma ya nusa kaman mai tunani sai kuma ya girgiza kai yace “Giwa bazata tab’a fitar da Saudatu daga cikin Masarautar nan ba, ita d’in ta jima da k’udirin tsafi akan yarinyar..!”

Turaki da Ansar suka dubi juna suka kuma duban Ubandoma cikeda mamaki lokaci guda suka maida dubansu gaba d’aya ga su Mahmood..

Hannayen Mahmood ta shiga warwarewa kaman tana neman wani abu, nan tsakanin yatsun hannunsa na dama ta hango irin alaman dake nata hannu Wanda ashe shima yanada irinta, take ta ware hannunta itama Ta jera da nasa hannun, alaman tabon ya bayyana saman tafukan hannayensu, su duka biyu sukai K’uri suna duban irin alama guda da Allah ya halitta masu, ko shakka babu su d’in d’ah ne da mahaifiya..! Wani sabon kuka ya kufce mata.. Take Ta rungume d’anta tana kuka sosai..! J’afar da k’arasowar kenan shika cikin tsananin sanyin jiki ya isa ya rungumesu gaba d’aya..! Su duka ukun suka rungume junansu kaman masu tsoron kada a kuma raba tsakaninsu.. Sosai suke kuka mai ban tausayi da tab’a zuciyar duk wani mai imani...

Dattijo Baba Nomau dake zaune daga gefe shima saida ya kamo bakin babbar rigarsa yana tsane k’wallan da suka gangaro masa..!

Toh daga nan fah bayan wanann ya lafa aka sako batun neman Muhibbah..!

Yasu yasu ne zaune k’asan Rumfar yanda suke tattauna ta inda zasu b’ullowa al’amarin tinda an bincika ko ina ba’a sami su Giwa ba..!

Gimbiya Turai ta dubi Mahmood tace “Izzatu bazata tab’a fitar da Saudatu daga cikin Masarautar nan ba, domin kaman yanda na baku labari ita d’in ta jima da k’udirin yin tsafi da d’iyar d’an uwana..! Amma saidai akwai abinda nake tunani shine zai kaimu ga yanda Izzatu Takai Saudah..!”

Mahmood ya d’ago a firgice yana dubanta duk ya jigata a d’an tsawon yini guda da wannan al’amari Ke faruwa..!

Gimbiya taci gaba da fad’in “Wambai ya bani wani Taswira yace na adana shine zai toni asirin Izzatu duk daren dad’ewa..! Kuma na baiwa Saudah wannan Taswiran..!!”

Zuciyar Mahmood bata daina bugawa ba yake tuno abubuwan da suka faru... Sai yanzu zanen ginin gidan sarauta da Wambai ya basa da kuma wanda ya tsinta hannun Muhibbah ya fad’o masa..! Ya mik’e babu shiri yana furta “Nasan yanda Taswiran suke nima Wambai ya bai guda d’aya kafin ya bar duniya..! Amma fallen zanen guda uku ne.. Bazamu iya gane inda zanen ya dosa ba da abinda yake nufi sai mun cika guda ukun... Ina zuwa..!!” Bai kuma tsayawa sauraren kowa ba ya shiga cikin sassarfa ya nufi d’akin da aka aje Muhibbah..! Saidai babu zanen babu dalilinsu..!

Hankali tashe ya dawo ya sanar dasu babu zanen bai gansu ba...!!

Kaman daga sama ya sinkayo muryar Zahra ta nufosa a guje tana ambatonsa.. Ya waigo yana dubanta, bata daina haki ba take mik’a masa Takardun dake hannunta, lokaci guda take furta “Paa Aunty Muhibbah tace na baka wannan..!!”

Cikin sauri Mahmood ya amshi takardun, jikinsa har na rawa yake warwaresu..! Ga tsananin mamakinsa Map d’in nan ne mai d’aukeda wani irin rikitaccen zane..! Ya d’ago yana dubansu kana yace “Gashi nan..! Alhamdulillah ya zanen nan..!!” Gaba d’aya suka mik’e sanda Mahmood ya k’urawa zanen idanu yana karantarta..! Babu shiri ya nufi saman benensa a guje su Ubandoma dasu Jafar na biye dashi..! Can saman tsauni ya hau ya tsaya yana karantar fad’in Masarautar da kuma zanen..!

Daga can b’angaren hagu daga Masarautar ya hango hanyar da yayi linking wannan Taswira..! Tabbas wani gini ne cikin Masarautar wanda hankalinka da tunaninka bazai baka akwai wani mihimmin abu wajen ba, anyi amfani da wad’anda sukeda ilimin sanin gini na zamanin da sai aka b’atar da ginin cikin ado da kwalliya wanda zakayi zaton ginin kwalliya ce kawai ga Masarautar..! Babu shiri ya nufo k’asa suka kuma biyo bayansa har saida ya tsaya gaban wannan ginin... Ya isa yana shafawa a hankali yana mai kuma bin diddigin zanen..! A daidai center ya hangi wani alamu kaman shatin kwbo wanda akai masa ado a tsakiyarsa da alamun tambarin masarauatr su..!

Ya saka hannunsa yana shafe shatin kwabon..! Baba Nomau da yayi masa k’uri tamkar mai nazari ya bud’e muryarsa da girma ya kama yace “Akwai wani sirrin k’unshe da wannan alama..! Mutanen zamanin da sun yarda da alama musamman mai d’aukeda tambari irin wannan na sarauta..!

Muryar Ubandoma da shima yayi nisa cikin zurfin tunani suka sinkaya yana fad’in “Mahaifina ya bani wani labari cewa akwai wani fursuna da aka ginata shekaru d’aruruka, tin zamanin wani Sarki can da jimawa..! Wannan fursunan ba’a tab’a rufe kowa cikinta ba ko shi Sarkin da ya ginata, ko wani sarki yakanyi zamaninsa ya shud’e ba tare da ya bud’e wannna fursunan ba, kuma ko wani Sarki kafin ya bar duniya yakan barwa Babban d’ansa mabud’in wannan bak’in fursunan... Kenan mahaifin Sarki AbdulJabbar bai barwa Sarki AbdulJabbar mabud’in wannan fursunan ba ya bar mabud’in hannun babban D’ansa Wambai tinda dama ko wani Sarki ma babban d’ansa yake barin mabud’in..! Kuma wannan fursunan Tanada mabud’i ne guda d’aya tak a duniya..!!”

Ya d’anyi fasali kaman mai tunani sai kuma yaci gaba da fad’in “Lokacin da hankalin Giwa ya tashi na neman wanene Bak’on Buzu da yake ziyartan gidan Wambai Tabbas naji tana maganan neman wani k’undi daga hannun Wambai wanda shine dalilin da yasa na zaga na shiga gidan Wambai Dan na samo wannan k’undi ganin irin mahimmancin da yake dashi a wajen Giwa..! Na tabbata wannan k’undin yanada alak’a da wannan zanen..!!”

Ai Ubandoma bai gama rufe baki ba Mahmood ya soma jada baya yana furta “Tabbas ni ne Bak’on Buzu, na b’atar da kama ne domin na samo amsoshin da na dawo k’Asar nan ina nemansu kuma Tabbas Wambai ya bada Bak’on Buzu wani k’undi wanda yace akwai lokacin da zan buk’aci bud’e wannan k’undin..! Tabbas mabud’in wannan Taswira yana cikin k’undin da Wambai ya bani..!!”

Daga haka ya nufi d’ajinsu a guje Dan d’auko k’undin da Wambai ya damk’a masa...

*MUHIBBAH*

*76*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Chapter 129 · 0% Book details