← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 162

Sashe 106

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Jamal yayi yana kuma jin son mahaifiyarsa cikin zuciyarsa... Yasa hannu ya damk’e hannun mahaifiyar tasa cikin nashi, ya sumbaci hannun nata kad’an yace “I love you Maami nah.. Ina matuk’ar k’aunarki Rankidad’e..!”

Tai murmushi tace “Nima ina matuk’ar k’aunarka masoyinah Farin cikinka shine nawa... I can’t wait naga ‘yan jikokina ‘ya’yanka da Umaima suna guje guje cikin fad’in Masarautar nan...!”
Annashuwa da annuri ya kuma cika Jamal, wani irin sanyi yakeji can k’asar zuciyarsa... Bai kuma bin takan batun Zahra ba kaman yanda Giwa ta buk’ata hankalinsa yafi karkata kan cewa daren yau za’a shigo masa da Amaryarsa...!

Yana ficewa Giwa ta dubi Jakadiya ta nuna can gefe k’asan file tace ta zauna nan wajen... Babu musu Jakadiya tayi yanda Giwa tace

D’aya daga cikin Hadimanta Giwa tasa tai mata kiran Zahra...

Jim kad’an Hadimar suka shigo tareda Zahra, Zahran na mamakin dalilin kiranda Giwa tai mata da tsakar safiyan sanin cewa ba sonta Kakar nata take ba...

Zahra ta risina ta gaida Giwa... Gani tai Giwar ta amsa mata da sakin fuska, Ta nuna mata gefenta tace tazo ta zauna... Babu musu Zahra Ta isa ta zauna har lokacin da bata gama aminta da yanayin Kakar nata ba...

Giwa ta sakar mata murmushi tace “Zahra wata magana nake so muyi..!”

Zahra ta k’ak’aro murmushi tana mai jinjina kai ba tareda Ta amsawa Giwar ba...
Giwa taci gaba da fad’in “Zahra nace ba... Shin ina kika sami mayafin nan da kika baiwa Jakadiya..?”

Zahra ta d’anyi jim sai kuma tace “Mayafi kuma Maami..? Wanne mayafi kenan..?!”

Giwa ta murmusa tace “Karki damu Zahra mayafin ne bai cancanta Bayin cikin Masarautar nan su saka ba shiyasa na tambayeki... Kinsan akwai d’abi’u da al’adu na cikin Masarautar nan da har yanzu you’re not familiar with them... Sai a hankali zaki gama fahimtar komai... Zahra Maiyasa kika baiwa Jakadiya wannan mayafin..? Ko Kinsan cewa kin kusan saka Jakadiya cikin had’ari.. Ki dubi yanda ‘yan uwanta bayi sukai mata jina jina duk a dalilin sun ganta da babban mayafi irin wanda bata kamaceta ba... A nasu zaton sata tayiwa iyayen Gidanta..!” Giwa ta k’arashe cikeda kulawa

Cikeda tsoro Zahra Ke duban b’angaren da Jakadiya Ke risine, harga Allah sosai Jakadiya ta bata tausayi, bata so kowa ya cutu sabida ita koda kuwa bawa ne k’ask’antacce, ta maidoda dubantaga Giwa tace “But akan mayafi sai su mata irin wannan bugun Maami... Rhis isn’t good Maami, this has stop, bai kamata a barsu suna irin haka ba...Aunty Muhibbah ce ta bani wannan mayafin tace na baiwa Jakadiya kuma itama nasan batasan tsarin Masarautar nan bane da bata bata ba... Lo siento, esto es todo mi culpa..” ( I’m sorry this is all my fault..)

Ta fad’i cikin harshen Spanish tana duban Jakadiya da har lokacin kanta a k’asa yake tana haki da k’yar dan Giwa ce ta umarceta tayi hakan..

Giwa ta nanata “Muhibbah..?!” Ji tayi ma batasan waye mai irin sunan ba...

Zahra ta kuma Jinjina mata kai alamun tabbatarwa... Jakadiya ta d’ago a zabure jin an ambaci Muhibbah yarinyar da tun zuwanta Masarautar taceda Giwa ita sam bata aminta da ita ba...!
Duban Jakadiya Giwa tai Jakadiyar na isar mata da wani da idanu... Giwa ta maidoda dubanta ga Zahra ta murmusa tace “Kina iya tafiya abinki jikata...!”

Zahra ta jinjina kai had’ida risinawa kana Ta mik’e Ta fice...

Tana ficewa Giwa ta k’araso gaban Jakadiya tana sakin tsananin huci “Jakadiya wacece Muhibbah..?!”

Jakadiya ta risina tace “Allah shi taimakeki Muhibbah itace wannan yarinyar da nace miki inada shakku akanta tun farkon zuwanta Masarautar nan... Muhibbah itace bak’uwar Gimbiya Umaima data shigo da ita cikin Masarautar nan..!”

Giwa tai shiru tana nazari lokaci guda tana mai ci gaba da sakin huci... Sai yanzu hoton yarinyar ke kuma dawowa kwanyarta... Ta waigo tana duban Jakadiya bata daina sakin huci ba tace “Jakadiya ya zama dole duk yanda za’ayi musan wacece wannan yarinyar Muhibbah da dalilinta na shigowa Masarautar nan...!” Tana ida fad’in haka ta d’auki wayar salulanta ta shiga dialing layin Jamal...

**

A b’angaren Zahra kuwa tana ficewa b’angaren mahaifinta ta nufa tana tinanin Maiyasa a ‘yan kwanakin kowa ke son sanin abu gameda Aunty Muhibbah.. Itakam koda kowa zai tunanin Aunty Muhibbah ba mutumiyar kirki bace bazata tab’a yi mata wannan tunanin ba... Ta tabbata she’s a good person... Da wannan tunanin ta isa b’angaren mahaifinta...

Tinda ya tashi a bacci yake jiranta Ta Tashi, ko sauk’a k’asa yayi breakfast ya kasa, yafi so sai ya tabbata da Ta tashi taci abinci kafin shima ya sauk’a k’asa yaci abinci... Duk abubuwan da takeyi akan idanunsa, tin daga tashinta daga bacci har shigewarta bathroom dan yin wanka... Sanda Ta shiga wanka shima ya tashi ya fad’a bathroom d’insa dan yin wankan... A tare sukai wanka kowa a nasa band’akin lokaci guda... Koda Mahmood ya fito daga wanka idanunsa akan na’uran yana duban ko yarinyar nan ta fito daga bathroom... Bai mamakin ganin bata fito ba tinda yasan yanayin da take ciki na rashin tsarki....

Yana rik’e da k’aramar towel yana goge sumarsa kaman ance ya dubi na’uran ya hangota ya fito d’aure da towel daidai cinyarta, yau d’in batai amfani da bathrobe kaman yanda tayi jiya ba... Mutuwar tsaye yayi yana k’arewa santala santalan cinyoyinta kallo... Zuciyarsa taci gaba da bugawa... Ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta ya kuma kasa ci gaba da abinda yake...!

Zahra na nan zaune parlor tana kuma duba agogo tana mamakin rashin sauk’owan mahaifin nata yau har wannan lokacin... Kodai makara ne yayi... Tasan Paa d’inta baya shige irin wannan lokacin bai breakfast ba, Toh kodai hakan nada alak’a da abubuwan dake kan faruwa cikin Masarautar ne, k’ila fushi yake shiyasa har yanzu bai fito ba.. Itakam idan dai akan rashin auren Aunty Raheema ne da baiyi ba tafi kowa Farin ciki da faruwan hakan, koda mahaifinta baiso hakan ba...
Ta isa dining area tana duban breakfast d’in nasa shirye saman dining table ko tab’awa ba’ai ba... Ta d’an kuma komawa ta zauna tana mai ci gaba da duba time.. Gaba d’aya sai tana jin she’s responsible for everything that’s been happening..!

**
Yana gani ta nufi closet ta zab’o wasu kaya marassa nauyi Ta dawo cikin d’akin da zummar shiryawa, sosai bugun zuciyarsa ya k’aru ganin da gaske zame towel d’in takeda niyyan yi... Daidai nan yaji knocking daga k’ofarsa d’if ya kashe na’uran zuciyarsa bata daina bugawa ba.. Jallabiya kawai ya zira yana mai sinkayo muryar Zahra daga k’ofa tana fad’in “Paa are you there...? Paa..!” Tana maganan tana k’wank’wasawa a hankali kaman mai tsoron kada Ta d’agasa a bacci...

K’arasowa yayi ya bud’e had’ida sakar mata murmushi mai kyau...

“Buenos dias paa..!” (Barkada safiya Paa)

“Buenos días princesa..” (Barkada safiya Princess) Ya fad’i kyakkyawan murmushin bai bar saman fuskarsa ba...

“Paa yau ka makara.. Lafiya kuwa.. Espero que todo esté bien con usted..!” (Ina fatan lafiya kake)

Fitowa yayi ya nufi downstairs yana fad’in “Todo esta bien cariño..!” (Komai lafiya sweetheart)
“Vamos a desayunar ... Sé que aún no has comido” (Muje Mu Karya kumallo dan nasan bakiyi ba tukuna)

Tana murmushi biye dashi take fad’in “Por supuesto que todavía no he desayunado..( K’warai banci karin kumallo ba)..” Ta d’an murmusa a hankali sai kuma tace “Ta ya zanci abinci bayan ban tabbatar da cewa Paa d’ina ya tashi cikin k’oshin lafiya yaci abinci ba after all that has happened..!” Ta k’arashe tana mai zama a kujeran dake daga gefe lokaci guda tana mai ci gaba a karantar yanayinsa, batayi zaton zata gansa cikin annashuwa ba bayan duk abinda ya faru na aurensa da Aunty Raheema da bai yuwu ba...

Ta d’an muskuta tace “Paa you seems to be in a good mood... I thought zakayi fushi dani na b’ata tsakaninku da Aunty Raheema da nayi...? Paa I’m sorry.. I truly am...!”

Katseta yayi da fad’in “Is okay Zahra... Everything is fine.. I promise..!”

Zahra Ta d’an d’ago ta dubesa tace cikin sanyin murya “You’re not mad at me..?!”

Murmushi ya sakar mata yace “Of course I’m not...! Oya eat your food before it gets cold..!”

Ta jinjina kai a hankali tace “Alright Your Highness..!” Suka sakar ma juna murmushi a tare tana mai cakalan abincin kaman tana tsoro...

Mahmood na hankalce da ita... Ya zari tissue paper ya goge bakinsa kad’an, har lokacin bai daina karantar Zahra ba.. Saida yai gyaran murya kad’an yace “Princess, is something bordering you... You look a little bit disturbed.. Tell me akwai abinda Ke damunki ne..?!”

Sauk’e ajiyan zuciya tai a hankali tace “Paa it’s about Aunty Muhibbah.. Do you remember her..?!”

Gyara zamansa sosai yai jin ta ambaci Muhibbah yace “What about her.?!”

Zahra ta d’an kuma muskutawa tace “Paa why’s everyone so curious about her this days.. First it was you, and now...Grandma ta kirani asking questions about her.. Paa I believe she’s a good person... But Maiyasa zata bani mayafi tace na bawa Jakadiya ta yafa..!”

Zuciyarsa Ta kuma tsinkewa, ya aje spoon d’in da yake juyawa cikin mug yana mai kuma tsareta da idanu... Sosai ya gyara zamansa yace “Tell me everything Zahra... Ta bawa Jakadiya mayafi, kuma ma Ke ta bayar tace ki baiwa Jakadiya..?!”

Zahra Ta jinjina kai tace “You remember that day..? Ranan da nace maka ita ta had’a gaba d’aya plans d’inta tace min I should trust her..!”

Mahmood ya jinjina kai yace “I remember..!”

Zahra taci gaba da fad’in “Paa the truth is that ta bani wannan mayafin tace na baiwa Jakadiya ta saka, idan har Jakadiya ta yafa toh Babu halin ta bini Mu fita tare kaman yanda ka umarta kace Jakadiya tamin rakiya...! Toh na bata wanann mayafin Ta yafa muka had’uda Uncle Jamal yace zai assigning wata Hadima Ta min rakiya sabida Jakadiya zatai masa wani aikin...! Toh sai nace masa he shouldn’t bordered zan sami wata cikin Hadimaina tamin rakiya... Paa believe me I didn’t know an hana Hadiman cikin Masarautar nan yafa mayafi mai kyau... It was never my intention na cutar da Jakadiya... A dalilin wannan mayafin nayiwa Jakadiya Duka an ji mata ciwo Paa... All because of me..!” Ta k’arashe cikin rawar murya....
Chapter 106 · 0% Book details