← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 162

Sashe 117

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Jikinmu ya d’auki rawa sabida tsananin firgici da tsoron yanayin da mukaga Izzatu ciki wacce bamusan da zuwanta ba sai bayyanarta....

Murmushi ta sakar min tace “Gimbiya Turai k’araso mana, ki k’araso ga Hadimarki Izzatu kuma Aminiya a gareki...!” Tana maganar tana duban bak’in tulun dake ajiye gabanta yana fidda bak’in hayak’i...

Fattu jiki na rawa yake furta “Rankidad’e kada ki k’arasa...!” Fattu batakai aya ba Ta had’iyi kalamanta sakamakon wani garin magani da Izzatu ta busa mata..

Jikina na rawa na isaga Izzatu dake tsaye gaban tulun...

Ta kuma murmusawa tace “Turai lek’a cikin tukunyar nan ki gani..!”

Jikina bai daina rawa ba sabida tsananin tsoro na lek’a tukunyar mai fitarda hayak’i.... Wani ikon Allah Magidancin mutumi na gani mai kamanni irinta mahaifinmu saidai baikai Mahaifina a shekare ba..!”

Na d’ago a tsorace ina dubanta, murmusawa ta kumayi tace “Wannan shine d’anuwanki Alfah da ya shiga duniya nemanki...! Lek’a ki gani ya girma... Yayi aure aure har yanada iyali wanda ya aura a yawonsa Ta duniya da sunan yana nemanki...! Kar ki damu basai kin sha wahala ba ni nasan yanda yake... Fitilar tsafi ya hasko min hakan... Ta kuma tura fitilar cikin Tulun tana dariya take furta “Kinga gashi har matar tasa ta haihu, matar da ya aura a yawon nemanki... Kin gani lek’o ki gani Turai..!” Ta k’arashe tana mai kuma tura kaina cikin tukunyar yanda naga mutumin rik’eda jaririya sabuwar haihuwa..!

Hawaye na zubo min nake k’ok’arin kai hannuna Ina furta “Alfah..! Alfah d’an uwana..!”

Maidodani baya Izzatu tayi tana mai ci gaba da sakin wane irin dariya lokaci guda take ci gaba da furta “Wannan basu kad’ai bane ahalinsa, wad’annan a yawon nemanki ya samesu, akwai ahalinsa da ya baro ya fito yawon nemanki wanda fitilar tsafi bai hasko mana duniyar da suke ba...! Amma zamu fara da wannan ahalin nasa kafin sauran su bayyana mana...!” Tana ida fad’in haka ta danna hannunta cikin tulun wanda tuni jan wuta ya soma fitowa daga ciki... K’ara ta saki wanda take mukaga gidan da muke ciki ya soma cida wuta... Tana kuma danna hannunta wutan na kuma kama ko wani kafa na cikin gidan... Dukda azaba da take sha hakan bai hanata tura hannunta cikin tukunyar ba... Muna a haka Giro ya shigo ya tadda wanann tashin hankalin... Take muka hango wannan matsafin ya bugawa Giro wata Sanda akansa... Tinda ya buga masa sandar bai kuma koda shurawa ba, Giro ya fad’I macecce a wajen... Fattu ta yunk’ura zatayo kan mijinta matsafin mutumin ya nunata da sandar hannunsa tuni Fattu ta komada baya jikinta na wane irin rawa...
Ni kuwa inaji Ina gani Izzatu ta janyoni waje ta turani cikin wani mota irin wanda ake zuba awakai, ta koma cikin gidan tana kallon yanda wutan Ke ci, Mutumi mai tuk’a motar ba kowa bane illa Wambai, Ina kuka Ina dubansa dan na ganesa shine Yayan AbdulJabbar da ya soma zuwa neman aurena a Masarautar mu kafin isowar AbdulJabbar... Ina hawaye na hango hawaye kwance shima cikin idanunsa,cikin rawar murya yake furta “Kiyi hak’uri babu yanda na iya ne, sun d’aureni ta ko ta ina... Amma ga wannan Taswiran zan baki ki adana duk daren dad’ewa shine zai toni asirin wad’annan azzalumai.... Ki b’oye wannan Taswiran cikin jikinki duk yanda za’ayi kada ki bari su gani...!”
Jikina na rawa na amsa Taswiran da Wambai ya bani na tura jikin k’ullin gashina... Daga nan isowar Izzatu naji yanda Ta busa min wani garin magani.....Tin daga haka farkawa nayi na ganni a wane irin sunkurumin d’aki, da ita da matsafin mutumin nan suna tsaye gabana... Izzatu tana kan wani jan Darduma mai d’aukeda tambarin masarauta... Nan ta soma sanar dani abubuwan da suka faru

“Turai ko Ince Baiwa Izzatu mai k’wacen miji daga rana mai kaman ta yau kin fita daga rayuwar AbdulJabbar, kin fita daga rayuwar mijina kuma uban ‘ya’ya na, wannan waje da kike gani shine zai zamto ma’ajiyanki, Sarki AbdulJabbar ya zaci kin mutu a cikin gobaran da ya tashi a gidanki, Wuta ya cinyeku keda Mijin Hadimarki...! Amma kar Ki damu nayi mutunci tunda Hadimarki da d’iyarta sun rayu, suna cikin Masarautar nan a nan b’angaren bayi, tinanin Hadimarki ya shafe bazata iya tuna komai ba balle ta sanar da AbdulJabbar... Sannan d’an uwanki Alfah a lokacin da na isa gareshi ya tafi ya koma ga asalin iyalansa na farko, matarsa da babbar d’iyarsa mai shekaru biyu a duniya hakan yasa ban cimmasa a wannan gidan ba, zai koma ya samu wuta ya cinye iyalansa, koda shike nayi mutunci shima, na taho da gudan jininsa ciki Masarautar nan, jaririyar da amaryarsa Ta haifa wacce ya aurota a yawon nemanki na taho da ita cikin Masarautar nan, zan goyata a matsayin d’iyar d’an uwana daga k’arshe itama zanyi sadaukarwa na k’arahe da ita daga tsatson mahaifinki Sarki Jamaluddeen wanda ni ce nan nayi sanadiyar mutuwarsa...! Ko ba dad’e ko ba jima sauran ahalin Alfah zasu bayyana mun kuma sai nayi ajalinsu suma dan babu wani dangin Jamaludden da zasu rage a doron k’asa balle wataran suyi sanadin Mulkina..!!”

Ta kuma kecewa da dariya kana ta d’auko wata doguwar wuk’a tana fad’in zata cire harshena yanda bazan kuma yin magana ba... Wani ikon Allah wuk’an bai yanka harshena ba, gani nayi Ta ambato Jakadiya dake tsaye daga waje, Jakadiya ta shigo ta baiwa Jakadiya umarnin ta bud’e bakina da k’arfin gaske...! Haka sukayi tarayya itada Jakadiya suka bud’e bakina matsafin mutumin nan ya zuma min wani abinda bazan iya cewa gashi nan ba... Tin daga wannan lokacin naji harshena ya d’aure ban iya cewa komai, sannan ina fama da gushewan hankali na wasu lokuta wasu lokutan kuma nakan jini cikin hankalina, da alama asirin gushewan hankali da sukai min baiyi wani tasiri akaina ba... Na zauna cikin ukuba hannun wad’annan matsafa na tsawon shekaru dan har girma ya soma sauk’a min... Wata rana Izzatu ta shigo...!” Taja Burki ta d’aga kai tana duban Ubandoma wanda Ke duk’e gabanta yana hawaye...

Hannu tasa ta share hawayen da suka zubo mata, lokaci guda taci gaba da fad’in “Izzatu ta shigo tana fad’in d’an uwana Alfah yana wanann gari kuma kusada Masarautar nan, da alama bai jadadda da batun nemana ba... A lokacin ina cikin yanayi na hankali amma sanin halin wannan muguwar mata zata iya yin komai idan Ta fahimci a hayyacina nake hakan yasa na nuna mata a lokacin ma cikin hauka nake tuburan... Tinda naji tace Alfah na garin nake neman hanyar guduwa na sami yanda zan gana da d’an uwana domin na kub’utar dashi daga sharrin wanann azzalumar mata... Wata rana na samu na gudu, wannan mutumin ya mance bai d’aureni ba dan dama shine da Jakadiya masu lura da yanda nake... Shi yake d’aureni da sark’ok’i Jakadiya tana bani abinci, sun cutar dani sun d’aureni tsawon shekaru babu ibada ga mahiccina yanda ya kamata, saidai idan Ina cikin hankali nayi ishara a zuciyara tinda haukan nawa zuwa zuwa ne...Rayuwata haka taci gaba da tafiya cikin halin ha’ula’i a wannan kurkuku... Ranan dana samu na gudu domin na nemi d’an uwana Alfah a ranan bukin wata k’aramar sallah ne...!”

*MUHIBBAH*

*71*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Gimbiya Turai taci gaba da fad’in “Ranan bukin hawan doki na, Washe garin sallah kenan... kasancewar hankula sun karkata zuwaga shagulgulan bukin sallah ni kuma nayi amfani da wannan damar na gudu na fice cikin Masarauta da zummar neman d’an uwana Alfah dukda sanin cewa bansan ta yanda zan soma nemansa ba balle nayi tunanin samunsa, wani ikon Allah sai na hangi Jakadiya rungume da mutum saman kafad’arta sai faman waige waige take da alama wani hidiman yasha gabanta sunma mance Sun barni a kwance kuma a bud’e... Sannan akwai duhun dare a lokacin zai wahala a ganeni...Na dinga lallab’awa ina bin bayan Jakadiya a nawa tunanin itace zata kainiga d’anuwana Alfah... Aiko cikin wane ikon Allah sai na hangeta ta isaga Izzatu ta duk’a gabanta kana ta’aje wata ‘yar matashiyar yarinyar data aza a kafad’arta, cikin yanayi na firgici take furta “Rankidad’e munje har yanda Yarinyar take rayuwa da iyayenta saidai naga abin al’ajabi...!”

Cikin huci Izzatu taceda Jakadiya “Mai kika gani Jakadiya..?!”

Jiki na rawa Jakadiya take nuna yarinyar dake kwance tamkar gawa kana tace “Wannan yarinyar da za’ayi asirin gadon Mulkin su Yarima da ita d’iya ce ga wannan mutumi da kika nuna mana hotonsa a tukunyar tsafi kikace duk wanda ya gansa cikin garin nan ya sanar dake..!”

Izzatu ta zaro idanu waje tace “Kina nufin d’iyar Alfah ce..?!”

Jakadiya ta jinjina kai tace “K’warai Rankidad’e da idanuna naga mutumin...!!”
Chapter 117 · 0% Book details