← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 162

Sashe 41

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahmood ya d’anyi gyaran murya kad’an yana mai kuma gyara zamansa “Wato Baba abubuwa sun kuma rincab’ewa, dik yanda nake tinanin zasuzo da sauk’i amma abu yaci tura... Baba na rasa yardan mahaifiyata data ‘yanuwana, sun soma saka shakku da kokonto a gamedani...!”

Murmusawa irinta manya Baba Wambai yai kana ya soma fad’i cikin muryarsa da girma ya kama sosai “Sadauki.... Ni na sani za’azo wanann matakin.. Sai ankai yanda kowa zai juya maka baya a cikin Masarautar muddin zaka taho da batu na gaskiya...!”

Mahmood ya fuzar da fuci kad’an kana yace “Amma Baba banaso a sami wani conflict tsakanina da ahalina, banaso mu sami rashin jituwa... Baba ni ne Babba, yanzu da babu mahaifinmu kamata yai ace na had’a kan ahalin ba na wargazawa ba... Sannan mahaifiyarmu...”

Katsesa Baba Wambai yai da fad’in “Mahmood yak’i kake ciki tsundum, yak’i mafi had’ari... Yak’inda baka San yaya kamannin abokin gabanka yake ba balle kai yunk’urin kare kanka idan ya kawo maka sara....!”

Yarima Mahmood yai shiru yana sauraren Baba Wambai... Lokaci guda Baba Wambai ya mik’e yana mai furta “Ina zuwa....”
Jinjina kai kurum Mahmood yai ba tareda ya iya amsawa ba...
Baba Wambai ya shige wata ‘yar d’aki... Jim kad’an ya fito hannunsa rik’eda wata ‘yar k’aramar jaka ta fata mai kaman posa...

Zama yai yana mai mik’awa Mahmood ‘yar jakan “Ungo nan amshi wannan...!”

Mahmood yasa duka hannayensa guda biyu ya amsa a hankali yana mai juya ‘yar jakan....

Muryar Baba Wambai ya sinkayo yana mai furta “Mahmuda, inaji a jikina banida sauran lokaci mai tsawo a wannan rayuwar... Akwai abubuwa da dama da lokaci baida ikon ara mana kansa... Zanso ace ina numfashi a doron k’asa har zuwa wannan lokacin... Saidai bamukeda linzamin rayukanmu a hannayenmu ba...”

Cikin d’an sanyin jiki Mahmood ya katsesa da fad’in “Baba ka daina fad’in haka, tsufa bashine mutuwa ba... Zan iya zamtowa gawan fari na rigaka tafiyaga magaliccinmu wanann duka iko ne na Allah...!”

Baba Wambai yai murmushi irinta manya yana mai jinjina kai “K’warai kuwa Sadauki, maganarka gaskiya ne...Amma tsufa d’aya ne daga cikin alamominta kuma bazan maimaita yawan shekarunda nayi a baya ba sannan ni nasan abinda nake ji Mahmuda D’ah na... Wannan yak’i da keke tunk’ara ina mai rok’on Allah ya dafa maka cikinta... Sannan wannan k’undi dana baka akwai ranan da zaka buk’aci bud’esa... Inaso Kai masa ajiya mai kyau, irin yanda zaka ijiye abu mai matuk’ar mahimmanci a gareka....!”

Mahmood ya jinjina kai a hankali yana mai furta “In sha Allah zan ajiye wannan k’undi da kyau da aminci kaman yanda ka umarta Baba...!”

Baba Wambai ya jinjina kai yana mai sakin murmushi lokaci guda yake kuma sakawa Mahmood Albarka had’ida fatan samun nasara... Bayan sunyi sallama Mahmood ya tafi Baba Wambai ya isa ya d’aga k’asar katifarsa da k’yar ya ciro wani zanen ginin gidan sarauta mai yanayi da zanen dake lank’aye parlorn su Umaima...

K’uri yaima zanen hawaye na gangaro masa... Lokaci guda yake furta “Wannan shine iyaka abinda zan iya yiwa Mahmuda bayan amanan iyayensa dana ci akan dalilin son mulki da son zuciya irin tawa...!”Ya k’ara she yana mai shafa zanen da hannunsa Hawaye naci gaba da gangaro masa...

Yana nan tsaye ya sinkayo muryar Waziri daga waje.... Gabansa ya yanke ya fad’i......

SameenaAleeyou📚
[7/6, 1:10 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*028*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Daga yanda Wambai ke tsaye yana iya sinkayo muryar maid’akinsa da Waziri suna gaisawa cikeda girmamawa, ya kuma sinkayo muryar Waziri yana tambayarta ko Wambai na Gida dikda cewa safiya ne sosai...

Innani Ta jinjina kai tace “Aikuwa Yana nan yana tareda bak’o....!”

Gaban Waziri ya yanke ya fad’i, lokaci guda yake furta “Bak’o kuma da safen nan...?!”

Innani tace “Eh bak’on Buzu bai jima da shigowa ba, bara na lek’a sai na maka iso...” Ta k’arashe tana nufan sashen parlorn Wambai...

Shidai Waziri sai faman safa da marwa yake a wajen yana sab’a babban riga yana murza hannayensa waje guda.. Waye kuma bak’on Buzu...? Bai ida tinanin ba ya sinkayo muryar Innani cikin wane irin k’aran gaske tana furta ta shiga uku ta lalace, tana kururuwa tana salati tana kiran sunan mijinta....
Babu shiri Waziri ya nufi parlorn da saurin gaske kaman zai kifa da k’asa, hakan ya kuma janyo hankulan sauran mutanen dake gidan ciki harda Juwariyya autar Baba Wambai...

Waziri yai tsaye yana duban ikon Allah, Wambai kwance k’asa tamkar baya numfashi.... Innani sai kuka take tana kuma jijjiga mijinta Juwariyya ma na tayata... Cikin k’ok’arin kwantar da hankali Waziri ke basu baki yana k’ok’arin duba Wambai... Hindu mai aikace aikace na cikin gidan ita ta janye Innani da k’yar tana mai kuma tausanta had’ida bata baki, Waziri ya d’an tattab’a wasu jijiyoyin jikin Wambai lokaci guda ya fuzar da fuci a hankali yana mai sanar dasu su kwantar da hankulansu Wambai na numfashi... Lokaci guda ya umarci Hindu ta kawo masa ruwa ya zubawa Wambai... Innani kaw har lokacin bata daina kururuwa tana salati ba, Juwariyya kuma jin mahaifin nasu bai mutu ba ya sanyata neman layin Yayanta Majidad’i ta sanar dashi halinda ake ciki, ba zallan Majidad’i ba ma harta sauran yayyenta mata dake gidajen aurensu saida ta kirawosu ta sanar dasu, yayyenta maza dake karatu Jami’a saida ta kirawosu suma...

Majidad’i na K’arasowa ya kirawo likita a fujajan, mintoci kad’an likitan ya iso.. Nan ya buk’aci dik su fice a parlorn su barsa ya duba jikin Wambai...

Waziri yai amfani da wannan da wannan daman ya keb’e ya kirawo Giwa ya sanar da ita halinda ake ciki... Yana tsaka da wayar ne ya sinkayo muryar Innani tana tambayar likita maike damun mijinta... Cikin sauri Waziri ya katse kiran yana mai sanar da ita dik halinda ake ciki zai sanar da ita...

Gaba d’aya suka nufo likitan suna sauraren abinda yake fad’i....

“Wato a gaskiya Majidad’i bazan b’oye maku ba, Wambai ya sami bugawan zuciya had’ida shanyewar b’arin jiki lokaci guda, wanda hakan yasa zaiyi matuk’ar wahala ya sake yin magana saiko wani ikon Allah duba da yanayi na tsufa da yake ciki..Paralyze d’in ya shafi idanunsa guda da kuma kunnensa guda had’ida b’angaren harshensa wanda hakan yasa a halin yanzu baiji da kunne d’aya sannan bazai iya magana ba sabida b’angaren harshensa da ya shanye sannan idanunsa guda bazai sake gani dashi ba....!”

Ai likitan bai ida rufe baki ba Innani ta dafe k’irji tana kuka take fad’in “Lafiya lou fah na barsa da bak’onsa... Toh mai bak’on Buzu ya sanar dashi ni...?!”

Gaba d’aya suka dubi juna “Bak’on Buzu...?!” Majidad’i ya nanata...
Innani ta jinjina kai “K’warai kuwa bak’on Buzu, ai ya kwana biyu yana ziyartan mahaifinku...”

Waziri ya cab’i zancen da fad’in “Shin waye bak’on Buzun kuma a ina yake kuma daga ina yake...?!”

Innani tai jigum tamkar mai tinani kana tace “Wambai ne kawai zai iya baku wannan amsa don ni kaina ban tab’a ganin Fuskar bak’on Buzu ba kuma ban san daga wace duniya yake zuwa ba...!?”

Gaban Waziri ya kuma yankewa ya fad’i sanda Majidad’i Ke fad’in “Ta yaya Baba zai iya amsa mana bayan ya zamto bebe kuma makaho... Innani ina san sanin wanene bak’on Buzu don jikina na bani yanada nasaba da ciwon mahaifina....!”

Waziri yai saurin jinjina kai yana mai furta “K’warai kuwa Majidad’i kayi gaskiya, dik yanda bak’on Buzu ya shiga ya fita ya zama dole ka zak’ulosa ya amsa hukuncinsa...Bazanso ganin Yayan aminina Sarki mai rasuwa kwance haka ba..!”

Majidad’i na sakin huci yake fad’in “I’ll make it my mission to catch whoever is responsible for my father’s illness and make him pay...! Bak’on Buzu...!! Ka shirya domin sai na zak’uloka ko a ina kake..!!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da sakin fuci...
Ya dubi Likita yace “Yaushe za’a tafi dashi asibiti....?!”

Likita yace “Ko yanzu ma dan zamansa a gida komai ka iya faruwa...!” Babu b’ata lokaci suka d’unguma suka tafi asibiti...

Tareda Waziri akai komai domin ko giftawa baiba... Babban tashin hankalinsa shine da akace Wambai bazai sake magana ba, shin ya za’ai yasan cewa ya bud’e sirrinsuwa Mahmood ko bai bud’e ba... Shin ya basa k’undi ko bai basa ba.... Ya zama dole ya bincika gidan Wambai ya samo wannan k’undin tin abubuwa basu ida rincab’e masu ba....

**

Giwa ta kuma fuzar da fuci tana duban Waziri lokaci guda ta marairaice fuska tana fad’in “Waziri dole kayi ko menene ganin cewa k’undin nan ya dawo hannunmu... Bazamu bari Wambai ya dank’awa Mahmood ba...!!”

Matsowa Waziri yai cikeda tausayinta, ji yake tamkar ya rungumeta ya lallasheta Ta daina kukan nan... Lokaci guda yake furta “Karki damu Gimbiya, alk’awari nai miki muddin Waziri na numfashi bazakiyi kuka ba, sai yanda k’arfina ya k’are wajen ganin Duka burikanki sun cika... Wannan k’undi nayi maki alk’awari har abada bazai isaga Mahmood ba....!!”

Ta saki murmushi a hankali tana mai kuma duban Waziri wanda shid’in ma ita yake duba yana sakin murmushi...
Giwa ta nusa tace “Toh shi wannan bak’on Buzun fah, mai kake tinani gamedashi... Anya babu wani rufeffen al’amari gameda Shi,... Kasan fah gidan nan kowa ba abin yarda bane... Anya wani bai rigamu isaga Wambai ba koda ba Mahmood bane...?!”

Murmusawa Waziri ya kumayi kana yace “Bakida damuwa da wannan, na riga na ziga Majidad’i cewa dik yanda Bak’on Buzun nan yake ya zak’ulosa domin kuwa shikeda alhakin ciwon mahaifinsa... Kinsan halin yaron da kafiyan bala’i na tabbata sai ya nemo koma wanene wannan bak’on Buzun... Muna nan dake zakiga yanda za’a zak’ulo Bak’on Buzu a yanke masa hukunci mafi tsauri... Yanzu abinda Ke gabanmu shine binciko wannan k’undi dake cikin gidan Wambai, zan tura yarana cikin dare suje su bincika gidan tinda yanzu hankulan mutanen gidan gaba d’aya ya karkarta zuwa asibiti... Zasu bincika gidan sannan su kawo min wannan k’undi... Babu wanda zai fahimci cewa mai akai saidai suyi tinanin cewa b’arayi ne suka shiga gidan cikin dare...!”

Giwa ta girgiza kai kad’an kana tace “Waziri zama bai ganmu ba, ai bazamu bari Majidad’i ya rigamu capko Bak’on Buzu ba, ya kamata kafin Majidad’i ya gane ko wanene bak’on Buzu mu ya kamata mu soma cimmasa koma shid’in wanene Dan idan ya rigamu ko shakka babu bana haufin hakan ka iya tona asirinmu...!”
Chapter 41 · 0% Book details