← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 161 OF 162

Sashe 161

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gimbiya Turai tai tsaye tana duban Giwa yayinda Giwar ma ta zuba masu idanu gaba d’ayansu yanda suka jeru gaba gareta cikin shiga irinta masu Mulki.. Ga Gimbiya Turai ga kuma ‘ya’yan Yarima Alfah Muhibbah, Umaima da kuma Zahra..! Mutanen dataso ganinsu a k’ask’ance a wulak’ance, mutanen dataso d’aid’aita rayuwarsu da k’arfin gaske.. Mutane data sace komai daga garesu ta azurta kanta dashi yau gasu nan sun tsaya gabanta bayan duk k’ok’arin da tayi Dan Ta kawar dasu a doron k’asa Ta kafa mulkinta da nata zuri’ar Allah bai nufa ba... Yau ga Turai itace Allah ya nufi nata zuri’ar da samun duka wad’annan abun... Sabuwar Jakadiya tai tsawa ma yaran ta hanasu abinda suke.. Aiko illahirin bayin suna ganin su Gimbiya Turai da kuma matar mai Martaba Gimbiya Muhibbah take suka risina waje yai tsit saima k’ok’arin kwasan gaisuwa da suke.. Gimbiya Turai ta soma takowa gaba ga Giwa tana kallon yanda Allah ya maida Giwa cikin lokaci k’ank’ani.. Izzatu ta zama k’ask’antacciya abun wulak’antawa abun gudu, abin tsoro... Giwa na hawaye take duban Gimbiya Turai.. Lokaci guda ta lumshe idanunta tana furta “Ya Shugabata..! Kimin aikin Gafara, nasan na zalunceki kuma ban cancanci neman afuwa daga gareki ba... Na zalunci kaina kin sakani a inuwa na fitar dake rana.. Kin cireni daga cikin k’angin Bauta kika bani ‘yanci amma na miki butulci.. Kin bani komai naki sarautar Ki harmada abinda yafi soyuwa a gareki Wato mijinki amma na zab’i naci amanarki na rufe idanu sabida son zuciya na miki butulci mafi muni...!” Cikin rawar murya Giwa taci gaba da fad’in “Nasan ban canci yafiyarki ba.. Amma Rankidad’e dukda haka zan nemi yafiyarki ya Shugabata..!”
Muryar Muhibbah ne ya katseta yanda take takowa gaba Gareta tana furta “Sabida kinsan tanada zuciya mai kyau zata yafe miki Ko ince ta riga ta yafeki tuntuni shiyasa kika sami k’warin gwiwar rok’onta gafara.. Shin idan ita ta yafeki ina Allahan mutanen da kika zalunta Giwa..? Shin mahaifinta Sarki Jamaluddeen da kika rabasa da raywuwarsa shi ya yafeki..? Kokuma ‘ya’yanta da kika rabasu da mahaifiyarsu sun yafeki..? Kika kashe matar Mahmood bayan kin datse mahaifarta Dan kar ya samu magaji sannan kika maida Ja’afar Bawa a gidan Mahaifinsa.... Kin mance da d’an uwanta Yarima Alfah wanda kika halak’asa kika kuma tarwatsa ahalinsa... Matar da kika maidata baiwa mahaukaciya a cikin gidan mijinta kika azurta kanki da Martabarta kika toshe duk wani hanya na kwanciyar hankali cikin rayuwarta, daga k’arshe kika kashe mijin nata kika hana ta masa takaba yanda ya kamata wannan matar kike neman yafiya da afuwa daga gareta..? Ki fad’a min Izzatu wannan matar ce kike rok’onta Ta tafe miki..!!” Muhibbah ta k’arashe cikin d’aga murya hawaye na gangaro mata, illahirin mutanen dake wajen hawaye na gangaro masu.. Lokaci guda Muhibbah taci gaba da girgiza kai tana furta “Saidai ita din tanada zuciya mai kyau na tabbata bazataso ganinki a yanayi Da kike ciki ba... Zataso Ki samu sassauci dukda tulin abubuwan nan da kika mata..!”

Giwa na hawaye take furta Saudatu..!!”
Muhibbah Ta jinjina kai tace “K’warai ni ce nan SAUDATU wacce kika k’udiri niyyan cika Mulkinki da ita kuma nice nan MUHIBBAH wacce Ta miki alk’awari zata kawo k’arshen Mulkin ki da zaluncinki da taimakon Allah.. Yau gashi na cika miki alk’awarinki GIWA...Na fad’a miki dama zaki koma sharan cikin Masarautar nan Sai ya fiki daraja, zaki kasance cikin k’ask’anci da tozarci yau gashi nan duk sun tabbata akanki... Ki sani Allah baya barin zalunci ya tabbata...!!!” Ta k’arashe hawaye na gangarowa daga idanunta... Daidai nan Gimbiya Turai Ta k’araso ta rungumeta su duka biyun suna hawaye kana Gimbiya ta bud’e murya tace “Duk abinda zan fad’i d’iyata ta riga ta fad’i maki Izzatu.. Bayan tulin abubuwan da kika mana zan barki ki k’arasa jinyarki cikin Masarautar nan dan iyakacin abinda zan iya miki kenan dan nasan bakida wani wajen zuwan da yafi nan..!” Ta kuma duban tsohuwar Jakadiya da kanta Ke kife k’asa tana matsan hawaye itama kana tace “Ke kuma Jakadiya bayan cin amanan Masarauta da kikayi hukuncin ki daga Masarauta shine kiyita kula da ita har k’arshen rayuwarta tinda tare kuka jima kuma sak’awa kuna k’ullawa... Ubangiji ya sassauta miki Izzatu...!!”
Giwa ta shiga godiya tana hawaye Jakadiya ma na hawaye tana godiyan dole dan Allah ya gani kukan hukuncin kulada Giwa da aka yanke mata kawai take, kashi futsari cin abincin Giwa da komai ya dawo hannunta...
Kafin su baro wajen Gimbiya Turai ta tsawatar ma Bayin da yaransu akan wulak’anta mutum, a cewarta duk cikin masarauatr babu wanda yake abun wulak’antawa daga masu Mulki har b’angaren Bayi.. Masarauta bazata lamunci mummunan d’abi’a ba.. Kowa yanada ‘yancin rayuwa mai kyau a matsayinsa na d’an adam cikin Masarautar... Wannan jawabi nata sosai ya kuma yin dad’i ma ahalin Masarautar gaba d’aya... Rayuwar masarautar ta kuma sauyawa kowa daraja kowa yake da mutuntawa babu wulak’anci babu tozarta kowa... Giwa da Jakadiya suna can b’angaren su suna jinya dukda cewa wasu lokutan Jakadiya bata iya jurewa.. Sosai Jakadiya tayi nadaman rayuwar data tsinci kanta ciki, da ace batabi son zuciya ba da yanzu tana nan cikin Masarauta a matsayinta na Jakadiya gashi yanzu ta dawo b’angaren k’anan bayi wanda ko matsayin shiga sashen masu mulki basu dashi... Bayan faruwan haka da kaman sati biyu Jakadiya ta farka daga bacci cikin dare taga wani irin k’atoton bak’in kumurcin maciji ya kanannad’e Giwa ga wasu irin kukiyoyi munanan sai yagan naman jikinta suke... Giwan tana sakin wane irin k’ara na azaba... Ai da rarrafe Giwa ta fice daga d’akin tana neman d’auki.. Saidai tana ficewa k’ofar ya rufe da Giwa... Akayi akayi a bud’e tun cikin daren k’ofa Ta kasa bud’uwa.. Tun ana sauraro gurnananin ihun Giwa har dai aka daina saurarowa, wajen yai tsit alamun ran Giwa yayi halinsa...! Allahu Akbar kabiran... Yau babu Giwa, Duk Mulkin data baza a doron k’asa yau Ta tafi a wulak’ance..... Rayuwa kenan, yau kaine gobe ba kai ba... Haka da k’yar aka b’alla k’ofar aka fitar gawan Giwa wanda banda d’oyi baya komai... Da k’yar daga cikin tsirarru suka fitar da ita daga cikin Masarautar ko ina suka nufa da ita sai Allah ko Sun mata sallah ko basu mata ba Allah kad’ai ya Sani dan labarin mutuwar Giwa bai isa cikin Fadah ba saida gari ya waye sosai... Dukda abubuwan da Giwa tayi wanda hankula suka gaza d’auka hakan bai hana ahalin Masarautar tausaya ma irin mutuwar da tayi ba.. Da k’yar aka sanar da Fu’ad dake can k’asar Spain.. Ya nuna damuwarsa da tausayin yanda mahaifiyarsa ta k’are dama yasan akwai rana irin wannan da zaizo tunda Giwa dai babu wani abu na alkhairi data shuka a rayuwarta sai akasin alkhairi.. Ta kashe rayuka da dama ta cutar da dama sannan uwa uba laifin Shirka da take wanda Allah na yafe ko wani irin laifi da rahamar sa idan yaso matuk’a baka mutu kana shirka ba... Mutuwar Giwa ya zamto wa’azi Babba ga d’aukacin Al’umman cikin wannan Masarauta harmada wad’anda labarinta ya cimmasu... Kaman anyi ruwa an d’auke yau babu Giwa da ahalinta da duk wani Mulkin zalunci datayi a Masarautar...

Bayan wasu kwanaki da faruwan wannan al’amari Ja’afar da Ubandoma suka fito da Waziri, ya koma kaman bashi ba duk ya jeme ya zama abin tausayi, suka gurfanar dashi gaban Mai Martaba.. Mahmood yace yaci Albarkacin Yazeed, Masarauta tai masa rangwame yajesa an tub’esa daga sarautar Waziri sannan bazai sake tako k’afarsa cikin Masarauta ba har abada..Waziri yana kuka yana godiya haka ya fice daga Fadah babu rawani...

**
Kwanaki sun tafi, satuttuka sun shud’e har an soma k’irga watanni...
Tsaye take gaban k’atoton madubin d’akin nata tana d’aura d’ankwali.. Kallo guda zakai mata ka fahimci hutu da kwanciyan hankali sun Zauna a wajen.. Ta k’ara cika da kyau ga wani annuri na musamman daya cika fuskarta... Zahra ce ta shigo da sallama tana fad’in “Your Highness Mommy unborn Ke kad’ai ake jira a rufawa Amarya Alkyabbarta.. Ummi tace babbar Ya Uwa baza’a rufawa Aunty Umaima Alkyabba ba sai kina nan...!”

Muhibbah Ta murmusa a hankali tace “Aiko Ummi tayi gaskiya dan ko an rufa alkybbbar nan sai an yaye na sake rufa ma ‘yaruwata...!”

A tare suka murmusa kana Muhibbah takai dubanta ga cikinta mai kimanin watanni biyar wanda har ya fito waje kaman wani cikin wata bakwai... Zahra Ta d’anyi gyaran murya tace “You know I can’t wait Baby na ya fito duniya zanfi sonsa fiye da kowa.. Coz I’d be his or her Godmother..!
Muhibbah ta d’an ja hancinta kad’an tace “Toh Sarkin ‘yan surutu zaki shige muje ne ko kuwa..!”
Zahra na murmushi tace “Tia..!”
Muhibbah Ta dubeta tace “Yes princess..”
D’an kwantowa jikinta tai kad’an tace “I love you..”
Murmushi saman fuskarsa Muhibbah ta rungume ‘yar uwar tata had’ida furta “I love you too Baby..!” Suka kuma sakar ma juna murmushi kafin suka nufo downstairs yanda Hadimansu Ke jiransu...

Ansha Bikin Yarima Ja’afar da Gimbiya Umaima lafiya.. Amarya da ango sun tare a b’angaren su wanda Sarki ya k’awata masu shi da kayan alatu.. Saidai Fu’ad bai samu yazo ba dan jarabawa suke.. Zahra ce taita nuna masa Bikin Ta hanyar tura masa pictures wasu lokutan kuma Sai ya kirata suyi video call tana had’asa da mutane ‘yan biki su gaisa...

A haka akaci biki lafia aka tashi.. Rayuwa tayi dad’i Ta ko wanne b’angare sai son Barka...
Amarya Umaima da angonta Ja’afar sun bud’e Sabon shafin soyayya na rayuwarsu... Zahra ma ta maida hankalinta sosai ga karatunta...

A haka Muhibbah Ta isa watan haihuwarta yanda Ta haifo d’anta namiji kyakkyawa mai kama sak da mahaifinsa.. Kaman Kakin Mahmood.. Allahu Akbar Zo kaga murna wajen Mahmood Dama d’aukacin mutanen cikin wannan masarauta.. Babu ya Gimbiya Turai wacce bayan tsawon shekarun nan yau Allah ya nuna mata gudan jinin Mahmood d’inta.. Allahu Akbar lallai mai rai kar ya zamto mai cire tsammani ga Rahamar Ubangijinsa...Bayan Giwa tayi duk yanda zatai ganin cewa Mahmood bai samu Magaji ba yau Sai gashi Allah ya azurtasa da Magaji..
Chapter 161 · 0% Book details