← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 162

Sashe 85

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Firgita ta farka daga baccin nata salati saman harshenta, Wai ashe daga kishingid’a har bacci b’arawo yayi gaba da ita... Baccin da zata iya cewa sam bataji dad’insa ba domin kuwa haka taita mafarkai sarara marassa dad’i ciki harda na auren Yarima Mahmood da Gimbiya Raheemah... Wai anyi aurensu sun taho masarauta tare... Gabanta ya kuma tsinkewa tana add’uan Allah ya hana wannan mafarki nata yuwa... Wayarta ta lalub’a taga time yaja sosai dan da alama magrib ma yana shirin karatowa... Sauri sauri ta mik’e ta kuma d’auro alwawa tazo ta tada Sallan la’asar wanda daga yin alwala tana jira a kira sallan baccin ya saceta...
Bayan ta gabatarda Sallan La’asar d’in ne ta koma gefe tai lamo tana tinanin mafarkin da tai... Abu biyu ne a mafarkin nata... Na farko bayan auren Raheema da Mahmood yayi Raheema ta dab’awa Zahra makami ta kasheta, sai kuma auren Jamal da Umaima wanda Jamal da Giwa suka taru suka jefa Umaimar cikin wata irin kasko mai girman gaske suka busneta ciki.... Duk iyaka k’ok’arinta ganin ta taimaki Zahra da Umaima bata iya taimakon su ba cikin baccin.... Ta lumshe idanunta a hankali tana karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Wad’annan aurattaya dake shirin wakana cikin Masarautar da alama sam babu alkhairi a tattaredasu... Shin ta yaya zata iya hana yuwar wad’annan auratayya...? Amasar data kasa samowa... Saida Ta jira akayi sallan Magrib kafin Ta mik’e ta nufi b’angaren Giwa ko Allah zaisa ta sami wani chance da zata iya karkato ra’ayin Umaima gameda Jamal....

A parlor ta tadda Umaimar harma da Jamal d’in alamun zance suke... Takaici ya turnuk’e mata mak’oshi, tai k’ok’arin sa kai da zummar juyawa dan ji tai bazata iya shigewa ba kuma... Saidai tuni Umaimar ta ganta, taceda ita ta shigo mana ai Zahra na ciki...
Badon taso ba Ta ida shigowa... Ta gaida Jamal babu yabo babu fallasa... Saidai ganin k’afarsa a guntule ba k’aramin mamaki ya bata ba... Ashe dai an guntule k’afar nasa..? Tai zancen cikin zuciyarta... Allah ya gani ko tausayi bai bata ba.. It is what he deserved after all..
Ta shige ta nufi wajen Zahra tana sinkayo muryarsa yana kuma kashe Umaima da salon k’aryarsa... A zuciyarta take Addu’an Allah ya fitar da Umaima daga sharrin wannan bawa nasa...

**

Giwa ta kuma karkatowa tana duban Jakadiya data kawo mata labari maras dad’i... Babu Ubandoma babu ahalinsa... Gasu Waziri har yanzu basu samu dawowa daga tambayo auren Yarima Mahmood ba...

Giwa ta tsare Jakadiya da idanu kana tace “Jakadiya dole a samo Ubandoma bazai yuwu Jafar ya kuma dawowa cikin Masarautar nan ba daga shi har Izzatu... A halin yanzu Bana buk’atar Izzatu koda kuwa itace zata sanar dani Duniyar da Saudatu take... Akan asirina ya tonu gwara na rasa Saudatu har abada... Zan iya sadaukar da komai akan na rasa mulki na...!”

Jakadiya Ta jinjina kai tace “Allah ya kareki ya kare Karagarki, a yanda nasan Ubandoma bazai tsaya nan kusa ba.. Zai wuya a samesa... Rankidad’e Anya kuwa abubuwan nan lafiya suke faruwa yanda suke faruwa a yanzu... Karfah ki mance ga auren Yarima Jamal da yarinyar nan Umaima da ya kafe akai babu jada baya..!”

Giwa ta murmusa cikeda izza da k’asaita tace “Har abada bazan tab’a barin hakan ya kasance ba... Sanin kanki ne mai auren Yarima Jamal yake nufi, inaji Ina gani bazan rasa d’ah na ba...!!”

Jakadiya ta d’an gyara zama tace “Allah shi taimakeki ga wani shawari... Tinda dai yarinyar nan da k’udurin sadaukarwa na k’arshe kike aje da ita... Mai zai hana Ki amince Yarima Jamal ya aureta, tinda a k’a’idan Sarauniya Tamuna sau d’aya zai tara da mace ta zama tata... Duk matayen Sarauniya sai yayi mu’amala dasu sau d’aya kafin su zama nata... Toh mai zai hana ki amince da auren... Daren da suka tare muka tabbatar mu’amala na auratayya ya shiga tsakaninsu sai mu d’auke ita Umaimar mu damk’ata ma Tal’udu kinga hakan ka iya sanyaya ran Tal’udu da fushin da yake dake... Anyowa Sarauniya sabuwar Amarya...! Rankidad’e inaga wannan shawari ce kawai ta kamata tinda mun sani Yarima na matuk’ar k’aunar yarinyar nan bazai tab’a janye k’udirinsa na aurenta ba..!!”

Giwa taiwa Jakadiya K’uri tana mai jin dad’in shawarin Jakadiya... Lokaci guda Ta saki murmushi tace “Madallah da wannan shawari naki Jakadiya... Dama Sadaukarwa ta Farko Jinin Sarki Jamaluddeen ne mahaifin Turai... Sannan na aje wannan yarinya Umaima ce jininta ya zamto Sadaukarwa na k’arshe.... Wannana shawari naki yayi Jakadiya, hakan za’ayi.... Zan amince ayi auren nan, sauran aiki naki ne Jakadiya... Dole kiyita zarya a sashen Yarima Jamal daren da aka kai masa Umaima... Idan har kika tabbata mu’amala ya shiga tsakaninsu mu kuma sai mu saceta akaitaga Tal’udu ya cika aiki ya baiwa Sarauniya Tamuna amaryarta Kinga jinin d’ah na ya kub’uta..!” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta...

Jakadiya ta jinjina kai tace “Wannan haka ne Ya Shugabata... Allah ya k’ara miki lafiya.. Jaaa zamaninki... Ki jima kiyi kargo zuri’arki suyi Kargo..!!” Ta k’arashe tana d’aga mata babban yatsa alamun jinjina....

Suna a haka sukaji k’aran shigowar motoci cikin Masarautar alamun su Yarima Mahmood Sun dawo....

Muhibbah da Zahra dake zaune d’akin Zahran a tare suka mik’e suka nufi jikin window... Zahra tai saurin yaye masu labulen suna hangen sararin waje ga wutace sun haske ko ina cikin Masarautar....
Zuciyarta ne yai wani irin bugawa sakamakon hangosa da tai yana fitowa daga cikin mota hasken wutan lantarki ya haske kyakkyawar fuskarsa mai cikeda k’warjini sai kirari ake masa
“Takwarka lafiya Hadari malfar duniya..! D’an na gada Kafi d’an na koya... Lafiya baya goya marayu..! Lafiya limamin sarakuna..! Lafiya Azurfa babu gauraye..! Lafiya linzamin sarakuna..!Laaafiya mai ado da tagulla..! Lafiya mai sulken yak’i.. Lafiya mai tambura goma sha biyu..! Lafiya Uban gabasawa..!! Lafiya zauna gari k’i tashi..! Lafiya Bango majinginan Al’umma..! Lafiya tada kufayi..! Lafiya cika sarari..!! Laaaafiya D’an mai kiran gabas Arewa ta amsa..!! Allah ya Jaaa zamaninka Uban Fadimatu Zahra’u...!!”

Muhibbah tai masa K’uri tana kallon yanda ake masa kirari yana takawa gwanin ban sha’awa... Sosai sarautar ta amshesa, batansan sanda take sakin murmushi zuciyarta na mata wane irin sanyi...

Yazeed dake hangowa daga can saman benensa anaima Mahmood d’in kirari yanaji kaman garwashin wuta ake watsa masa illahirin jikinsa...

Giwa da Jakadiya dake hangosa daga nasu b’angaren, yanda ake masa k’irarin yana takowa ba k’aramin tada masu hankali hakan yayi ba... Ga Waziri a gefensa yana rarraba idanu wanda shima ko ba’ace a firgice yake....Ko shakka babu sunga jinin mulki a tattareda Mahmood d’in wanda k’warjininsa yai bala’in firgita duk wani mai k’ullin a zuciyarsa....

SameenaAleeyou📚*MUHIBBAH*

*54*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Kaman ance ya d’aga kansa sama b’angaren d’akin Zahra, nan ya hangosu su duka biyun suna dubansa, idanunsa ya sauk’a kan Muhibbah wacce baisan ta dawo Masarautar ba...Cak ya tsaya ba tareda ya ci gaba da tafiya ba... Harga Allah ganinta tareda Zahra ba k’aramin sanyaya zuciyarsa yayi ba dukda cewa yau d’in gaba d’aya zuciyarsa a cubkunshe take bayan decision da ya yanke na auren Raheemah... Turaki dake gefensa ya d’aga Kai yana duban abinda yake kallo... Take Turaki ya saki wata irin sassanyar murmushi dan yaga abinda Mahmood ya gani... D’an matso da bakinsa kusan Mahmood d’in yai yace “Rankaidad’e jama’an Fada na kallonka, ya kamata ka sauk’e idanunka bamu fatan Mai Martaba Amale yai tuntub’e gaban Talakawansa..!!”

Sai sannan ya janye idanunsa ya aikawa Turaki wata irin duba cikeda k’asaita ba tareda yace komai ba.. Shi kaw Turaki sai k’ok’arin tsime dariyarsa yake a matsayinsa na hannun daman Mai Martaba... A haka akaiwa Yarima Mahmood rakiya zuwa b’angaren mahaifiyarsa Giwa...

Kafin su shigo Giwa da Jakadiya sunyi k’ok’arin kintsawa... Yarima Mahmood na shigowa Giwa ta isa garesa da fari’arta wanda da gani kasan da k’yar take nuna hakan... Waziri na bayansa kai a k’asa sai faman muzurai yake yana kuma kod’a Sarki Mahmooda...!

Giwa kanta yau d’in kirari tai masa irinta Saraki...Ta rik’o hannayensa bayan tawagarsa sun fice, sannan Ta sallami duk Hadiman dake cikin parlorn ya rage saura su kad’ai...Fuska a marairaice Giwa Ke fad’in “Alhamdulillah..! Allah zai cika min burina na ganinka saman Karaga Sadauki...! Yau ina ma mahaifinka nada rai ya ganka saman Karagar nan.. Babban burinsa kenan ka gajesa ka gaji gidanku...! Nafi kowa Farin ciki da wannan Al’amari... Na godewa Allah da ya karkato da hankalinka daga can k’asashen Yamma ya dawo dakai gida, mahaifarka ka kuma amince zaka gaji Gidanku... Sadauki ka gama min komai...!!” Ta k’arashe tana matsan k’walla...
Harga Allah yaji babu dad’i ganin yanda Giwa Ke farin ciki zai zamto Sarki... Anya hukuncin da ya yanke bai tsauri ba... Maiyasa zai zab’i ya watsawa mahaifiyarsa k’asa a idanu... Amma idan hakan shine zaman lafiyar d’iyarsa fah..! Mahaifiyarsa tanada sauran yara a nan, idan ta rasashi akwai sauran ‘yanuwansa, hasalima this is not the first time da ya tafi Turai ya zauna da family d’insa, dan ya kuma yi bazai zama bak’on Al’amari ba.. Sannan Zhara ita kad’ai yakeda... Bazaiso ya rasata ba, he’s doing all this for her.... But still mahaifiya mahaifiya ce ko yayane... Kuma ko ‘ya’ya nawa takeda tana son ‘ya’yanta equally, bazataso taga babu guda d’aya ba...Take yaji duk babu dad’i, ya d’ago hannu ya shafi fuskar Giwa yace “Maami Ki daina yawan shiga damuwa, everything will be alright in sha Allah...!”

Jamal dake tsaye daga bayan Giwa ya k’araso cikin dogarawa da sandar crutches d’insa yana sakarwa Mahmood d’in Murmushi yake furta “Congrats Yaya..! I’m so happy for you, zaka angwance kuma za’a nad’aka matsayin Sarki...!”

Mahmood ya sakar masa murmushi kana ya bud’e masa hannayensa yace “Come here, give your big brother a hug..!”

Jamal na murmushi had’ida sinne kai yake furta “Yaya kaifa yanzu Sarki ne..!” Ya k’arashe yana shafa kai alamun jin nauyi...

Murmushi mai kyau Mahmood yai yace “Koda ace ni sarki I’ll always be your big brother kaji koh..!” Ya k’arashe yana d’an buga kafad’an Jamal d’in kana ya k’arada “Ya jikin naka..?”

“Da sauk’i Yaya Alhamdulillah..!”

Mahmood yace “Masha Allah.. Allah ya k’ara maka lafiya...! Ka shirya gobe da safe in sha Allah zamuje asibiti mu duba Fu’ad...!”
Chapter 85 · 0% Book details