← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 162

Sashe 96

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ansar na ficewa Baffah Yawale ya taro ruwa a dispense ya kawowa Mommy... Babu musu Ta amsa ta kurb’a...
Bafah Yawale ya koma mazauninsa ya zauna, saida dak’ik’ai suka d’an shura kana yai gyaran murya yace “Murja ni inaga bata nan zamu b’ullowa yaron nan ba, idan har yana ganin yarinyar bazai tab’a cireta a zuciyarsa ya mance da ita ba... Idan bata gidan nan shine zai manceta gaba d’aya... Amma muddin yana ganinta Toh fah bazai mance ba....!”

Mommy ta dubesa jiki a sanyaye tace “Yawale mai kake nufi...? Kasan dai bazan iya koran Muhibbah ba, dikda abinda taimin I still love her like my own daughter... Bazan iya korinta ba..!”

Baffah Yawale ya murmusa yace “Murja kenan.. Ai nima ba abinda nake nufi ba kenan, ba korinta zakiyi ba... Aurarta zakiyi ga wani daban, kinga idan kika aurarta Ansar yasan ta haramta garesa shikenan dole ya cireta daga zuciyarsa gaba d’aya ya rungumi k’addara ya zauna da matarda Allah ya had’asa zaman aure da ita Wato ‘yar uwarsa k’anwarsa Hameeda... Kinga shikenan hankalinki kema ya kwanta..!”

Mommy tai shiru kaman mai nazari sai kuma tace “Toh amma waye mijin da za’a aura mata..? Ina zan samo mata miji da zai dace da ita wanda bazai mata gori daga baya ba..?!”

Baffah Yawale ya murmusa yace “Murja kenan... Ai samun miji ga kyakkyawar yarinya kaman Muhibbah bazai wahala ba... Ni zan tafi da hotonta wajen manyan mutane masu mutunci a haka zamu sama mata miji... Amma ita yarinyar karki sanar da ita an fasa aurenta da Yakubu shima Yakubun ki barsa akan za’a aura masa Muhibbah saidai yaji daga baya ba shi aka aura mata ba... Ina mai tabbatar miki rana guda za’a d’aura aurenta da Yakubu amma ba dashi ba da waninsa...Kinga dole yayi hak’uri ya rungumi k’addara... Ki share zancen Yakubu ki daina damun kanki ki bar min wuk’a da nama... Ni nasan duk yanda zanyi...!”

Mommy ta jinjina kai tace “Nidai idan har bazata auri Ansar ba toh shikenan, amma Yawale ka tabbata gidan mutunci ka kai Muhibbah..!”

Baffah Yawale ya Washe baki cikeda jin dad’i yace “An gama Hajjaju... Wannan ai mai sauk’i ne... Ina mai tabbatar miki yanda Yakubu ya makance da soyayyar yarinyar nan har yana sa’insa dake kika sake kika amince ya aureta Toh fah saidai Ki zuba mishi idanu Don kin haifo mata shine...!” Ya k’arashe yana mai kuma tunzura Mommy....

Mommy tace yaje yayi duk abinda ya dace... Baffah Yawale ya fice yana Washe baki...

Daga nan yanda suke tsaye suka hango ficewar mutumin daga gidan...

Turaki ya k’arasa ya tadda mutumi mai teburin kayan miya, yai masa sallama da musabaha suka gaisa... Idanunsa naga k’ofar gidan su Muhibbah da Baffah Yawale Ke k’ok’arin burka babur d’insa....

Mai Teburin kayan miya ya dubi Turaki yace “Bawan Allah na nawa za’a baka...?”

Turaki ya d’anyi gyaran murya yace “Tambaya nake dama...!”

Mai kayan lambu yace “Allah yasa na sani...!”

Turaki yai nunida gidansu Muhibbah yace “Da Allah wata yarinya nake nema a can gidan sunanta Muhibbah.. Ko ka santa...?”

Mai kayan lambu ya Washe baki yace “Aw Muhibbah... K’warai na santa... Ai d’iyar rik’o ce a gidan... Yaron gidan likita shine zai aureta...Idan ban b’ataji ba ma sati mai zagayowa za’ai bikinsu... Kaga wancan wanda yake k’ok’arin burka babur shine K’anin mai gidan, kuma a yanda naji basa so yaron gidan aure ita yarinyar... D’iyar wancan k’anin Baban nasa sukeso ya aura...!” Mai kayan lambu yaci gaba da zuba bayani kai kace tanbayrsa akai...

Turaki ya jinjina kai yace “Na gode...!” Sukai sallama mai kayan lambu yaci gaba da ‘yar wak’e wak’ensa abinka da mutane wanda bakinsu bai iya yin shiru...

Turaki na k’arasowaga Mahmood ya sanar dashi yanda duk sukaida mai kayan lambu....

Mahmood yace “What..! No Turaki dole musan abinyi... She can’t get married... Idan tayi aure komai ya lalace Turaki... Wannan yarinyar must answer to me first...Idan ta kama na janyota da kaina Ta koma cikin Masarautar nan zanyi Turaki...!!” Ya k’arashe cikeda tsanar hallaya irin nata....

Turaki yace “Alright your Highness... Bamuda time muyi sauri mubi bayan mutumin kafin ya b’ace mana...!”

Cikin sauri suka nufi mota Turaki ya tada sukabi bayan Babur d’in Baffah Yawale....

SameenaAleeyou *MUHIBBAH*

*60*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Daga cen nesa da k’ofar gidan da Yawale ya shige sukai parking, suka k’araso k’ofar gidan Turaki ya bud’e murya yai sallama, saidai basuji an amsa masu daga ciki ba... Sun kusan minti biyu tsaye wajen babu wanda ya lek’o daga cikin gidan har kaman zasu juya saiga wani yaro ya fito rik’eda allon karantu Ta ‘yan makarantar zaure... Turaki yai saurin taresa da fad’in “Kai Yaro gidan nan kake...?!”

Yaron ya jinjina kai yace Eh... Turaki yace “Shiga ciki kace ana sallama da mai gidan...”

Yaron ya dubesu da mamaki sai kuma yace “Ai masu gidan sunada yawa, k’ofofi kashi kashi ne cikin gidan... Wanne zan kirawo maku...?!”

Turaki ya d’an shafi kansa yace “Toh..! Bakaga wani mutumi da ya shige yanzu ba da Babur..?”

Yaron yai shiru kaman mai nazari sai kuma yace “Kodai Baffah Yawale kuke nufi shine naji k’aran babur d’insa yanzu...”

Turaki yaji sunan kaman wanda mai kayan lambun can na k’ofar gidansu Muhibbah ya fad’a masa, saurin jinjina kai yai yace “Yauwa shi dai... Shiga kace ana sallama dashi..!”

Yaron ya jinjina ya koma cikin gidan... Jim kad’an ya fito yace dasu Wai yana zuwa....

Bayan shigewar yaron da wasu mintoci Yawale ya fito yana mamakin Ina ya samu bakin buzaye shida babu kowa nasa k’asashen hamada..

Iso yai masu cikin Zauren yanda tabarma ke shimfid’e, yai masu sannu da zuwa suka gaisa gaba d’aya, Yawale ya bud’e murya yace “Saidai kuma ban gane daga ina bane..?”

Turaki ya d’an murmusa yace “Eh Toh daga k’asashen can arewacin hamada muke, dama tambaya mukazo gameda d’iyarku mai suna Muhibbah...!”

Ai Tun kafin Turaki ya rufe baki Yawale ya soma fad’in “Fad’uwa tazo daidai da zama, dama mun rasa mijin da zamu aura mata, Allah yasa idan kun aureta kuyi nesa da ita da garin nan... Ku tafi can k’asarku da ita yanda bazata kuma dawo mana ba, bazamu kuma cin karo da mai irin fuskarta ba..!”

Turaki da Mahmood suka dubi juna da mamaki, Baffah Yawale yaci gaba da fad’in “Kar Kuji komai ba’a mata miji ba, dama uwar goyon nata tace duk wanda ma samu na aura mata, ko kuturu ko makaho kai ko wane irin mutum ne... Toh Alhamdulillah tinda ta samu mutumin da zai ketara da ita wata Nahiyar ai abin ai godiya ne... Dama mu kasancewarta kusa damu ne bamu fata... Wata sati ake bukin d’aura mata aure... Bayin Allah sadaki kawai zaku kawo ni ko yanzu zan kirawo shaidu a d’aura auren...!”

Turaki yai murmushi wanda yafi kamada yak’e yace “Oh haka ne Baba..! Toh ai inaga zamu koma dai muyi shawari da magabata...”

Turaki bai rufe baki ba suka sinkayo muryar Mahmood daga cikin nad’insa ta buzaye yana fad’in “Babu shawari Baba... Mune nan magabatan wanda mukazo nemawa auren... D’an uwana k’anina zan nemawa aurenta... Yanzu basai anjima ba zan damk’a maka sadaki...!”
Ya k’arashe yana mai zira hannu cikin aljihun babban rigarsa Ta buzaye, ya ciro wata ‘yar jaka ta fata ya mik’awa Baffah Yawale...

Yawale hannu na rawa ya amshi ‘yar jakar Ta fata, ya shiga warwareta yana ganin abin mamaki.. Silallala ne zallan zinari wanda darajarsu zai iya kaiwa dubu d’arurruka....

Yawale ya kuma murtsuka idanu yana ganin wannan ikon Allah, a ina mutane irin wad’annan suka sami wannan dukiya shidai bai gansu da wata babbar Mota ba hasalima bai gansu da abin hawa ba, daga su sai suturan jikinsu ya gansu...

Kaman Mahmood yasan tunanin da yake ya soma fad’in “Kar kaji mamaki Baba sabida mu haka al’adarmu take, mace Tanada matuk’ar daraja, duk mutum yakaiga talauci sai ya nemo silalla na zinari kafin a basa mata, iyayenmu sukan bar mana gadon Rak’uman da muke kiwo Dan muyi kud’in aure dasu....”

Yawale ya jinjina kai har lokacin jikinsa rawa yake yana juya coins na zallan gold a hannunsa... Lokaci guda yace “Ai..Toh... Toh ai shikenan, kasan kowa da al’adarsu... Babu komai sati mai zuwa kuzo ku amshi auren d’an uwanku...!”

Mahmood ya jinjina masa kai ba tareda yace komai ba saima k’ok’arin mik’ewa da yake da zimmar tafiya... Yawale ya tsare fararen k’afafunsa da kallo wanda da gani kasan hutu da jin dad’i ya zauna a wajen babu wani alamun tafiya cikin hamada a k’afafun balle har ace makiyayi ne mai kiwon Rak’uma cikin Hamada...Anya wannan ba manyan mutane bane suke son b’adda kama... Wad’annan basuyi kamanceceniya da gajiyayyu ba... Shifa baya fata yarinyar nan ta samu wajen maik’o yafi so ta tagayyara, kardai ya kaita yanda zata huta... Toh amma ai shi dama so yake ta fice daga rayuwarsu dan idan har tana tareda Murja da kuma Ansar sam bazata tab’a bari ya cimma burinsa akan dukiyar D’an uwansa da ya mutu ya barwa Ansar da Murja gado, kuma dukiyar Murja ma harinta yake tinda batada magaji bayan Ansar d’in... Idan kuma Ansar ya mutu baida Magajiya face d’iyarsa Hameedah wacce zata zamto matarsa , komai ya dawo hannunsa a sauk’ak’e....

Sallaman Matarsace rik’eda ruwa a faranti ya dawo da Yawale daga duniyar tunanin da ya tafi, da alama baima San bak’in nasa sun fice ba har sun tafi....

Matarsa ta tambayesa Ina bak’in...? Yace Ai har sun tafi Ta koma da ruwan... Ya k’arashe yana mai b’oye silallan zinarin cikin aljihunsa.... Bai isa kowa yaga wannan dukiya ba, ko Murjah bazata gani ba... Kasuwa zai tafi ya saida guda d’aya tak ya kaiwa Murja a matsayin kud’in auren Muhibbah... Sauran kuma ya dafe Allah ya kashe ya basa, shikenan ya samu kud’ad’en da zai kayan d’aki wa Hameedah a sauk’ak’e...

**
Har suka shige Mota Turaki bai daina mamakin abinda Mahmood yai ba, shi tsananin mamaki ma ya hanasa furta koda kalma.... Da alama shi kuwa Mahmood d’in ko a jikinsa...

Turaki ya nusa kad’an yace “Your Highness, ka tabbata da abinda kayi..? Shin waima cikin k’annenka waye ka nema masa auren Muhibbah, Yazeed ne ko Jamal ne kokuwa Fu’ad ne..?!”

Ba tareda ya dubesa ba yace “Maiyasa ka faye gaggawa Turaki..?!”
Chapter 96 · 0% Book details