← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 162

Sashe 77

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da tsananin mamaki take dubansa “Paa ka zaci bazan tab’a sani bane... Paa I’m not a kid anymore... For once in your life tell me the truth please..!!” Sauk’ar marin da taji a fuskrta ne ya sanyata had’iye sauran maganganun nata...
Dafe da k’uncinta take dubansa da jajayen idanunta masu cik’eda k’unci hawaye naci gaba da gangaro mata....
“I hate you... I hate you Paa..!!” Tana kaiwa nan ta fice a guje... Raheema na k’ok’arin tareta Ina ko tsayawa batai ba... Juyowa Raheema tai ta dubi Mahmood dake ci gaba da sakin huci, lokaci guda ta isa ta kawo masa ruwa tace dashi ya zauna yasha ruwa... Bai mata musu ba ya zauna ya amshi ruwan yana kwankwad’a zuciyarsa naci gaba da masa d’aci....
Bai tab’a zaton zaiga negative impact a irin tarbiyan tashin cikin turawa da d’iyarsa tai ba sai gashi yanzu yana gani...Muryar Raheema ya katse masa tinaninsa
“Your Highness, Kai hak’uri har yanzu ita d’in yarinya ce... But...!”
Shiru tai ta kasa ci gaba da magana sabida tsananin shakkunsa da take ji...

Wani duba Mahmood yai mata yace “Continue, ci gaba... Go ahead and ask me... Nasan kema shakku kike gamedani bayan abubuwan da kikaji Zahra ta fad’i mun... Right..!”

Saurin girgiza kai Raheema tai tace “Your Highness bazan tab’a saka kokonto ko shakku gameda kai ba, I know you’re a good person, kuma nasan ko meye kake b’oye mata is for her own good... Na sani bazaka tab’a yin abinda zai cuceta ba... Your Highness na yarda dakai d’ari bisa d’ari... Idan da zakabi shawarina, kai gaggawan d’auke d’iyarka daga Masarautar nan... Send her to boarding school, idan hakan bazai yuwu ba kafin ka rasa Martabarka da kimarka cikin Masarautar nan ka d’auke d’iyarka ku koma yanda kuka fito... Babu komai cikin Masarautar nan sai cin amana da tashin hankali, kai tunani Tunda ka dawo babu wani abu mai kyau da ya faru dakai sai akasin haka... Ka d’auki ku koma can Spain ki ci gaba da rayuwarku mai tsafta babu hayaniyar cikin Masarautar nan... But before then make sure ka sama wa d’iyarka uwa... Kar ka mance Zahra tana delicate stage ne yanzu... Gaba mai had’ari take, tanajin kanta itad’in yanzu young lady ce... A wannan shekaru na teenage da take ciki tana buk’atar uwa a tattareda ita your Highness... Ka sama mata uwa wacce zata kula da ita da shawarwari masu kyau ku tafi ku koma Spain... Shawarina kenan your Highness..!” Ta k’arashe cikeda kulawa...

Mahmood da yaima b’angare guda k’uri sai faman juya cup d’in dake hannunsa yake yana kuma jinjina maganan Raheema...
Raheema tai masa K’uri zuciyarta na mata dad’i, Tunda ta kula asirinsu ba kamasa zai ba gwara tai amfani da wannan damar ta saye zuciyarsa da kalaman kwantar da hankali, ta gwammaci suyi aurensu su tafi can Spain d’in dan dama ita wannan sarautar ba wai ya dameta bane muddin zata sami Mahmood ita shikenan koda sarauta ko babu sarauta ba damuwarta bane.... A hankali ta mik’e ta risina tace “Na Barka lafiya your Highness...!” Lokaci guda tasa kai zata shige sai sinkayo muryar Mahmood d’in tai ya ambato sunanta...

Taja ta tsaya kana ta juyo a hankali ta risina had’ida amsa masa...
A hankali ya furta “Thank you..!”

Raheema ta murmusa zuciyarta na mata wasai ta jinjina masa kai a hankali kana tasa kai Ta fice...
Tana ficewa ya d’auki wayarsa saman center table ya shiga dialing layin Turaki....

**

Raheema na fitowa ta hangi Yazeed tsaye hannayensa hard’e yana dubanta muguwar murmushin nan saman fuskarsa, murmushin itama ta sakar masa kana tabi wani hanya, saida ya waiga gefe da gefe kana yasa kai shima yabi bayanta....

Yazeed ya dubeta yace “So tell me plan d’in yayi working...?!”

Murmusawa tai tace “Kaid’in na daban ne... Na tabbata bayan abinda ya faru Mahmood zai aureni ya d’auke d’iyarsa mu bar k’asar nan...!”
Ta kuma takowa zuwa gaban Yazeed lokaci guda tasa hannu ta dafe fuskrsa, cikin kissa take furta “Yanzu ka hak’ura kenan ka bar wa Yayanka ni..?!”

Murmushin nan nasa saman fuskarsa yake furta “Akan SARAUTAR nan babu abinda bazanyi ba, babu abinda bazan sadaukar ba... That throne is mine.... So na zab’i na rabu dake muddin zan gaji sarautar mahaifina...!!”
Ya k’arashe yana mai d’an bubbuga fuskarta yanda akewa yara...
Yazeed yaci gaba da fad’in “Mahmood is all yours ke kad’anki sai yanda kikaso kiyi dashi...!”

Suka murmusa a tare kana Yazeed yace “Yaushe zaa bani na k’ashe tinda na sallamawa Mahmood..?”

Ta murmusa tace “Karka damu Prince akwai farewell da zamuyi... Just make sure you didn’t ruin our plans...!”

Yazeed ya murmusa yace “An wuce wannan ai tinda har aka sako Zahra ciki... She’s his greatest weakness... Ina mai tabbatar miki nan bada jimawa ba zakiji ya tafi masarautar ku neman aurenki..!”

Raheema ta kuma murmusawa cikeda jin dad’i tace “At last burina zai cika... Na Barka lafiya Your royal Highness...!”

Yazeed ya jinjina mata kai alamun amsawa murmushin nan nasa saman fuskarsa...

**

Cikin rashin fahimta Turaki ya mik’e tsaye yana furta “You can’t be serious your Highness... Please think your decision through, Your Highness you can’t leave... Musamman yanzu da family d’inka suka fi buk’atarka... Ka duba kaga halinda Jamal da Fu’ad ke ciki, haka zaka tafi ka barsu... And and ina labarin neman justice da kakewa mahaifinka da matarka... Ina maganan search for Ja’afar da kake...? Shin duk ka mance wanann zaka aje komai ka tafi.... Your Highness ina alk’awarin da kayiwa Wambai... Are you going to leave all this behind.... Sannan bayan duka wannan ka zab’i ka auri macen da baka so ka tafi kai rayuwa cikin k’unci... C’mon your Highness, think about all this... This is not the right time for you to leave...!”

Katsesa Mahmood yai da fad’in “Yes Turaki na zab’i na bar komai behind for my daughter.. Can’t you see I’m loosing my daughter here... It’s over I’ve made up my mind zan auri Raheema na d’auki d’iyata mu koma Spain... She’s better off this way Turaki banso mukai peak d’in da zan rasata gaba d’aya... Zahra ita kad’ai nake gani na tuna Aliya.... Nothing can stop me now Turaki... Ka shirya within the week zamu tafi Masarautar su Raheema neman aurenta..!”

Turaki dake dubansa cikeda mamaki girgiza kai kurum yake hannayensa dafe da kunkumi, ya kasa yarda da abinda yakeji daga abokin nasa....

**

D’aki ne mai tsananin duhuwa wanda baka iya ganin komai koda kuwa tafin hannunka ne sabida tsananin duhuwansa, Ubandoma ya sa hannu ya daki k’ofar take haske ya bayyana...

Cikin sauri tasa tafukan hannayenta biyu tana kare fuskarta.... Ubandoma ya isa ya aje mata kwanon abincin dake hannunsa...

Matsawa da baya take tsoro bayyane saman fuskarta
Lokaci guda Ubandoma yace “Ki kwantar da hankalinki Kin kub’uta daga hannun azzalumai bazan miki komai ba....!”
*MUHIBBAH*

*50*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Ubandoma ya koma gefe ya zauna yai mata k’uri yana duban yanda take jefa abincin cikin bakinta hannu baka hannu k’warya alamun ta galabaita da yunwa.. Shikadai saiko mahaliccinsa yasan abinda yake k’ullawa cikin zuciyarsa.... Ya sani duk duniyar nan yanzu Giwa batada burin da ya wuce ta sami Izzatu... Bazai bari hakan ya kasance ba dan shima nada nasa shirin akanta... Watak’ila Izzatu ta zamto mabud’in samun ‘yancinsa.... Ya saki murmushi a hankali kana ya matso kusanta yace “Ki kwantar da hankalinki bazan sake d’aureki da sark’ok’i kaman yanda nakeyi a baya ba... Kin fahimceni...?!”

Bata amsasa ba saima ci gaba da tura abincin da take cikin bakinta... Mik’ewa Ubandoma yai ya fice daga cikin d’akin ya kuma kulleta nan cikin d’akin kana yai tafiyarsa....

Ubandoma na ficewa mahaukaciya Izzatu ta mik’e tana shafa ginin da Ubandoma ya ijeta ciki a hankali hawaye na gangaro mata... Cokalin da Ubandoma ya kawo mata abinci dashi ta soma karjan ginin tana saka hannunta tana gogewa... Cikin ikon Allah ginin sai ya soma b’anb’arewa yana zubewa duk yanda ta karje da cokalin... Ta zauna sosai tana ci gaba da karje ginin da iyaka k’arfinta bataji bata gani sai aikin abu guda take karje garu.. Ginin sai zuba yake a hankali tana kuma samun hanya...

**

A can asibiti kuwa yau ake saka rana sallaman Jamal shi kuwa Fu’ad har yanzu babu yanda yake, ya farfad’o amma da alama muggan k’wayoyi sun kuma juya masa kwanyarsa dole akai transferring nasa to psychiatric ward... Shi kad’ai yake buga kansa jikin garu yana jin ciwo ma kansa tinda ya farka, aikin abu guda yake babu magana babu komai sai dukan kansa jikin garu ala dole aka dadd’aure Fu’ad da manyan sark’ok’i a fannin mahaukata dake nan cikin teaching hospital d’in, Giwa bata iya komawa ta gansa ba dan bazata juri ganin d’anta a d’aure da sark’ok’i ba cikin hauka tuburan...

Shi kuwa Jamal alla alla yake ya dawo gida sabida duk dare akwai yanda yake zuwa cikin Masarautar, idan baije ba komai ka iya faruwa... Saidai yana tinanin ta yanda zai soma shiga Masarautar a matsayin gurgu makasashe saman wheelchair... Hawaye masu tsananin d’umi suka ciko idanunsa, Umaima dake gefe murmushi Ta sakar masa tace “Yaya Dr yace yanzu zai sallameka mu koma gida... I’ll park your belongings..!” Ta k’arashe tana mai isa yanda kayayyakin nasa suke...

Cikin rawar murya yake furta “I can’t Umaima, bazan iya komawa Masarauta a haka ba... Dan Allah ki ce masu su dawo min da k’afata....!” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa...

Gaban wheelchair d’in nasa ta k’araso ta d’an duk’a kad’an tace “Ya Jamal I thought we’ve already talked about that.... Yaya please ka karb’i k’addararka babu wanda Yafi k’arfin hakan... Tsautsayi tana kan kowa... Shin kanaso ka zamto cikin mutane wanda basa yarda da k’addara ne...? Yaya kada ka zamto mai butulci wa mahalaccinka... Kaji please..!” Ta k’arashe kaman zatai kuka...

Dubanta yake da idanunsa masu rauni kana yace “Nasan kina fad’a min haka ne kawai dan naji dad’i amma babu wanda zai kuma accepting d’ina the way I’m, even you Umaima bazakiso ki auri nakasashe irina ba...!”
Chapter 77 · 0% Book details