Sashe 142
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jakadiya ta murmusa kad’an tace “Ki gafarceni Rankidad’e ai inaga ko ba al’adan gidan sarauta bane hakan ne ya kamata... Miji yaci abinci gaban matarsa domin ya samu daman yabonta... Hakan na k’ara dank’on k’auna tsakanin ma’aurata..” Ta k’arashe cikin hikima irinta wanda yakeda experience..
Ita dai Muhibbah tab’e baki kurum tayi kad’an dan dai Jakadiya bata San akan mai ake duka wad’annan abubuwan ba da bata tsaya b’ata bakinta tana wannan bayanin ba.. Auren da aka yosa babu soyayya wani dank’on k’auna za’a nema cikinsa.. Dan dai kai babu yanda ta iya ne tinda sharud’an da Rankaidad’e ya gindaya mata take bi.. K’in komawa sashen nasa ka iya janyowa yace ta fad’i jarawar... Ta dubi Jakadiya ta jinjina mata kai kad’an zatayi kaman yanda tace... Daga haka Jakadiya ce Tai mata Rakiya zuwa yanda suka baro Hadimarta na jiranta kana Muhibbah da hadimar suka nufi sashenta yayinda Jakadiya ta koma sashen madafi...
Da k’yar ta isa d’aki sai sauk’e fucin gajiya take, tana isa ta kwab’e kayanta ta fad’a bathroom ta gasa jikinta da ruwa mai d’umin gaske had’ida kayan k’amshi na wanka... Ta jima sosai cikin bathroom d’in kana ta fito d’aure da towel tana goge sumarta data wanke da wani towel d’in... Cikin zuciyarta take tinanin inama Ta sami dryer da ta busar da wannan gashin nata... Aiko tana tsaye tana ci gaba da tsane sumar nata taji knocking.. Ta janyo hijabi ta zira kana ta bada izinin shigowa.. Hadimarta ce ta shigo rik’eda ‘yar jaka ta risina ta ajiye mata tana mai furta “Aike ne aka bata ta shigo dashi..”
Muhibbah tasa hannu ta d’ago jakan tana juyawa, ga mamakinta k’aramar hand dryer ta gani mai kyau ciki..Toh waye yayo mata wannan aiken..? Ta dubi Kuyangar tace daga inane..?
Kuyangar tace “Allah shi baki yawan rai d’aya daga cikin Hadiman cikin gida ne ta shigo dashi tace Wai a baki..”
Jinjina kai tai tana kuma mamaki, watak’ila Umaima ne ko Zahra d’ayansu ta bata, toh amma ai basu san tana buk’ata ba..? Wata zuciya tace k’ila sunyi tunanin bakidashi kuma zaki iya buk’ata shisa suka baki.. Da wannan tunanin ta amsa kana ta sallami Hadimar.. Nan da nan ta jona ta shiga busar da sumarta...
Tsaf ta shirya cikin wani dubai material mai kyaun gaske wanda akai masa kwalliya da sequence mai ruwan zinari sai d’aukan idanu yake.. Batayi niyyan shafa komai a fuskarta ba amma sai tayi tinanin hakan ka iya janyowa ta fad’i jarabawrta, Sannan tafi so ta nunawa Rankaidad’e cewa ita d’in ba raguwa bace zata iya lashe jarabawarsa, ya kamata taje da k’arfin gwiwarta, sam bazata basa wani k’ofa da zaice ta fad’i jarabawarta ba... Ta zauna gaban dressing mirror ta shafa iyaka abinda idanunta ka iya gani wanda tasan baza’a kalleta ace fuskarta tayi fayau ba sannan baza’a kalleta ace tayi kwalliya mai yawa ba.. Abinka da wacce ta jima batayi ba dan zata iya cewa tin tana Collage of nursing rabonta da ta zauna tace zatayi kwalliya na musamman, Yo ita da burin fansarta ke kanta wani make-up ma zata zauna tanayi batada wannan lokacin... Kallo d’aya zakai mata Kaso sake kallonta, babu shakka tayi kyau.. Ta tupke sumarta a k’eyarta kana tayi d’auri wanda ake turosa gaban goshi... Ya salam ita da kanta tasan tayi kyau Masha Allah.. Alkyabba mai ruwan zinari ta rufa kan sequence material d’in wanda shi kad’ai ma d’aukan idanu yake ga kuma alk’yabbarta... Ta feshe jikinta da turaruka masu natsettsen k’amshi kana ta fito.. Daidai da hadimarta saida ta shaga da kallonta.. Ta risina tace “Ki gafarceni Rankidad’e.. Kin k’ara kyau fiyeda kullum...!”
Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Babu komai Hasiya, muje kimin rakiya zuwa k’ofa.”
Hadimar ta kuma risinawa cikeda girmamawa tace “Toh Rankidad’e..!” Muhibbah tai gaba Hadimar na biyeda ita.. Har k’ofan sashensa tai mata rakiya kana ya bata umarnin komawa...
Dikda zuciyarta dake tsananin bugawa hakan bai hanata daurewa ta nufo cikin parlorn kanta a k’asa sallama saman bakinta...
Daga nan yanda yake zaune ko k’yafta idanunsa bai iyayi, saima tsarkake mahaliccin wannan kyakkyawar halitta dake nufosa da yake... Tin daga yatsun k’afafunta yake duba har izuwa fuskarta.. Ita kaw da k’yar take takowa dan tasan babu shakka idanunsa akanta yake, sai had’e hanya take sabida yanda zuciyarta ke tsananta bugu, hakan sai ya zamto mata tamkar wani salo ne na tafiya... Da k’yar ta iya k’arasowa cikin parlorn ta risina gaba garesa had’ida baza alkyabbarta a k’asa irin yanda masu mulki keyi... Dak’ik’ai suka shura kaman bazaice komai ba sai gani tayi ya mik’e tsaye, zuciyarta taci gaba da bugawa tana tinanin Toh mai kuma ya mik’arsa tsaye...
Gabanta ya k’araso ya tsaya, zuciyarta naci gaba da tsinkewa, ga tsananin mamakinta hannayenta guda biyu taga ya mik’o mata... Ta d’ago idanunsa masu haske wanda kwalli ya k’ara masu haske tana dubansa dasu... Da gaske hannayensa yake mik’a mata... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa tana tinanin Ta mik’a masa nata hannayen ne kokuwa, k’in mik’awar ka iya janyowa ta fad’i jarabawarta tinda duk abubuwan nan da take cikin jarabawa ne.. Ta d’ago hannayenta a hankali ta mik’a saman nasa, ji tai ya rik’e hannayen nata cikin nasa, ya mik’ar da ita tsaye a hankali kana suka soma takowa a jere.. Zuciyarta bata daina tsinkewa ba har saida ya k’araso da ita gefen kujerar da yake zaune bisa ya zaunar da ita...
“Yanzu zan amsa gaisuwarki..” ya fad’i yana mai dubanta...
Ta murmusa kad’an tace “Na zaci ba’a gaisar da Sarki a saman kujera..!” Cikin sigan wasa tai maganan amma sam bata hango alamun raha saman fuskarsa ba.. Ta had’iyi sauran kalaman nata tana tinanin kardai tayi abinda zaisa ta fad’i jarabawarta.. Lokaci guda ta tsime ta sadda kanta k’asa tana gaishesa..
Ya amsa a tak’aice daidai sanda Jakadiya ta nemi izinin shigowa parlorn... Mahmood ya bata izini, ta shigo ta risina gaba garesu tace idan an bata izini zata gabatar da girkin Gimbiya...
Mahmood ya kuma jinjina mata kai yace anyi mata izini... Ta mik’e ta fice tana godiya... Jim kad’an Ta shigo tareda wata Hadima rik’eda parantin.. Jakadiya tai mata nuni da yanda zata ajiye.. Hadimar Ta isa ta ajiye tana mai kwasan gaisuwa daga garesu...
A tare Hadimar da Jakadiya suka nemi izinin fita...
Mahmood ya zauna saman darduma irin zaman da ake na cin abinci, Muhibbah ta k’araso cikin tsanaki tana serving d’insa, duk wani motsi da zatayi idanunsa na kanta... A haka ta ida jera masa komai Ta koma gefe saman Darduman ta zauna...
Saida wasu dak’ik’ai suka shura kafin ya d’auki spoon ya d’ebo abincin da Bismillah yakai bakinsa still idanunsa akanta, itama wannan karon idanu ta d’an d’ago tana dubansa dan taga kalan expression d’in da fuskarsa zai bada... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa ganin ya bar abincin cikin bakinsa shi bai tauna ba shi bai had’iye ba... Idanunta suka firfito tana fad’i cikin zuciyarta.. Shikenan k’ila abincin ya bada taste maras dad’i ne dan idan bata mance ba ko tasting abincin batai ba... Taga ya had’iyi first spoon da k’yar, jikinta a mugun sanyaye take ayyanawa cikin zuciyarta shikenan na fad’i.... Jakadiya ce ta nemi izinin shigowa..
Tana shigowa ta risina ta gaidasu... Lokaci guda taci gaba da fad’in “Allah shi taimakeka abincin Gimbiya ya zaga cikin Fadah kaman yanda yake a al’ada... Kuma..!” Ta d’anyi shiru kaman bazatace komai ba, Muhibbah na kuma zaro idanu tana dubanta...
“Ina sauraronki Jakadiya.. Kuma mai..?”
Jakadiya ta murmusa tace “Mafi rinjaye Sun yana hasalima ba’a sami wad’anda suka kushe wannan girki ba... Masarauta tayi dace Rankaidad’e hannun Gimbiya mai Albarka ne...”
Muhibbah bata San sanda Murmushi mai kyau ya kufce mata ba, harda ‘yar sauk’e ajiyan zuciyarta... Shikaw yai mata K’uri yana kallon yanda farin ciki ya mamayeta...
Duban Jakadiya ya jinjina kai a hankali kana ya Bawa Jakadiya izinin tafiya...
Har lokacin Muhibbah bata daina sakin murmushi ba, Ta d’an tsuke fuska kad’an ta waigo tana dubansa had’ida d’aga masa gira guda alamun an wuce wannan...
Spoon d’aya zuwa biyu yai ta nemi izinin tafiya... Ya jinjina mata kai alamun yayi mata izini, saidai tana isa k’ofa ta sinkayo muryarsa yana furta “And where do you think you’re going Your highness..?!”
Ta tsaya cak had’ida lumshe idanunta zuciyarta naci gaba da tsinkewa... Izuwa lokacin ya mik’e ya nufo yanda take tsaye hannayensa hard’e Ta baya ya d’an kwanto da hab’arsa saitin kafad’arta, cikin sigan rad’a yake furta “Find some clues that will lead you to the next part of the exam..!” Yana ida fad’in haka ya juya ya nufi upstairs cikin takun k’asaita...
Muhibbah ta bi bayansa da kallo har ya shige had’ida fuzar da huci kad’an....clues dazasu leading d’inta... Tai tsaye tana k’arema parlorn kallo tana tianin wasu clues kenan... A hankali Ta shiga zagaye parlorn tana neman clues d’in... Harta pillows saida ta d’add’aga... Can idanunta suka sauk’a gefen yanda ya zauna, akwai remote control a wajen... Tai saurin k’arasawa ta d’aga remote d’in dan taga kaman akwai takarda k’asan remote d’in
Aiko takarda ce a ninke, ta warware tana karantawa an rubuta, _Escalera.._ (Staircase)
Ta rik’e takardan tana juyawa tana nanata kalman ya mata kama da yaren Spanish.. Toh mai Escalera yake nufi.. Ta d’an dafe kanta tana tunanin words d’in data sani a yaren bata fahimci menene ba... Amma kuma ya mata yanayi da escalator... Ta juya hagun da dama bataga alamun escalator ba amma akwai matakalan bene... Cikin sauri ta nufi matakalan benen tana dubawa... Nan jikin staicase taga anyi drawing arrow ya kalli sama an rubata a k’asan arrow d’in _Sigue moviéndose recta_ (Ci gaba da tafiya a mik’e)
Taita nanata kalaman dan akwai words d’in data fahimta hakan yasa ya mik’e taci gaba da hawa benen...
Tana cikin cikin tafiya taji kaman Ta taka wani paper, tai saurin duk’awa ta d’auki paper d’in ta warware an rubuta _Sigue tu izquierda_ (Ki bi b’angaren hagunki)
Nan ma Kalmar izquierda ta fahimta yana nufin hagu, take ta soma bin wannan b’angaren tana k’arema ko ina kallo ga d’akuna a jere... Nan ta kuma cin tuntub’e da wani takardan.. Ta duk’a ta warware tana karantawa an rubata _Segunda a la última habitación_ (D’aki na kusa da k’arshe)