← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 162

Sashe 30

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muhibbah tai mata K’uri ganin kaman tana son fad’in wani abu ne... Hannayen Zahra ta kamo kana tace “If you need someone to talk to... Don’t forget I’ll always be here kinji koh...!”

Jinjina mata kai Zahra tai murmushi saman fuskarta take furta “You’ve no idea how much your presence means to me... Thank you Tia for being here with me...!”

“Ki daina min godiya Zahra.. Haka nan Allah ya jefa k’aunarki cikin zuciyata....!”

Yarinyar ta kuma murmusawa kana tace “Nima Ina k’aunarki...!”

Suka kuma murmusawa a tare kana Muhibbah ta hangi textbook na mathematics a gefen Zahra da alama karatu zatai... Ta d’an gyara zamanta tana mai furta “Lissafi ne za’ai...” Tai maganan da sigan wasa to cheer her up..

Zahra takai dubantaga book d’in kana tace “Oh.. Exams zamu fara gashi I’m not good at mathematics shiyasa zan fara dashi... Ko zaki koya min ne.. Dama Paa ke koya min...”

Ta zaro ido kad’an “Ni da lissafi.. Lissafi ba layina bane inama kice biology ne ko chemistry maybe wannn na iya karambani...”

Zahra ta murmusa tace “Wannan ma zaki koya min... But I don’t believe baki iya lissafi ba....”

Muhibbah ta d’an dubeta kana tace “Maiyasa Paa d’inki bazai koya miki ba tinda dama shi yake koya miki...?”

Take mood d’in Zahra ya canza, Muhibbah kaw na hankalce da ita dan dama so take ta d’ago wani abu shisa ta ja zancen nasu yai tsawo...

Zahra Ta d’an girgiza kai tace “I don’t want him to be my tutor anymore..!”

Gyara zama Muhibbah Ta kumayi kana tace “But why...?”

Dubanta Zahra tai kana tace “Paa d’in dana sani a Spain yasha banban da Paa d’in da nake gani a Nigeria.....”

Sameena📚
[6/19, 9:22 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*021*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Gyara zama Muhibbah tai tana duban yarinyar sosai kana tace “I don’t get you Zahra... What exactly are you trying to say...?”

Without any hesitation Zahra ta d’ago tana dubanta had’ida furta “Paa ya canza, I’ve a feeling he’s hiding something from me... Something very serious..!” Ta k’arashe damuwa k’arara saman fuskarta...

Gyara zama Muhibbah Ta kumayi kana tace “Mai kike tinanin yana b’oye miki...?”

Zahra ta d’an dubeta kaman zatai magana sai kuma ta mik’e tsaye tana mai fuzar da huci a hankali, lokaci guda take furta “I don’t know, but jikina na bani its something that has to do with my Maama’s mysterious death... What if Paa yasan wani abu gameda mutuwar mahaifiyata... Mutuwan da gawanta kawai aka tsinta cikin d’aki..”

Mik’ewa tsaye Muhibbah ma tai had’ida dafa Zahra kad’an kana tace “But do you think your Paa can do something as evil as that...?”
Saurin d’agowa Zahra tai tana dubanta kana Ta shiga girgiza kai, lokaci guda take furta “No, no I don’t want to believe that... Paa bazai tab’a kashe mutum ba and much less my Maama, ya sota da dika zuciyarshi... But what I don’t understand here shine Maiyasa bazai sanar dani ba idan yasan wani abu ne gameda mutuwar nata, who is he protecting...?!” Ta k’arashe damuwa kwance saman fuskarta...

Muhibbah dake ci gaba da karantar yarinyar matsowa kusanta Ta kumayi kana tace “Then talk to your Father... Ask him... Ki tambayeshi meye yake b’oye miki...!”

Zahra ta d’an dubeta kana tace “But how... Paa kallon yarinya yake min har yanzu, I’m quite certain bazai Fad’a min komai ba...”

Janyo hannunta Muhibbah tai suka zauna saman kujera kana tace “In that case, maybe baiso Ki damu ne... Tinda kince har yanzu kallon yarinya yake miki wacce bakisan komai ba... But if I were you, zan bud’e idon mahaifina ya gane cewa ni fa yanzu ba yarinya bace... I can differentiate what’s right from wrong... You’re already a young lady now... So bai kamata Ki bari yaita treating d’inki kaman wata k’aramar yarinya ba musamman in some cases like this... We’re talking about your Mother here Zahra... Idan har da gaske kasheta akai cikin Masarautar nan and your Paa knows something about it, but baidata cewa coz he’s protecting someone kaman yanda kika ce... Ni a ganina Ke bai kamata kiyi shiru ba.... Mahaifiyarki Ta cancanci adalci koda kuwa nan d’in gidan sarauta ne da basu d’auki doka kan masu mulki a bakin komai ba..!” Yanda take maganan zaka fahimci tamkar tana fitar da wani abu ne da ya jima yana cin zuciyarta...

Zahra tai shiru tamkar mai tinani yayinda Muhibbah taci gaba da karantarta.... Lokaci guda Zahra ta shiga jinjina kai tana mai furta “You’re right... I need to find out about everything..!”

Jinjina kai Muhibbah tai cikeda jin dad’in yanda cikin sauk’i tai convincing yarinyar... Lokaci guda take ayyana yanda zata tarwatsa rayuwar Mahmood Ta hanyar amfani da gudan jinin da yafiso a rayuwarsa... Tabbas D’iyarsa itace weakness d’insa....
A haka Umaima ta shigo ta taddasu...

**
A b’angaren Mahmood yana ficewa ya tadda Ubandoma yanda yake samar dashi zuwan Waziri... Jinjina kai Mahmood yai cikeda sarauta kana yaceda Ubandoma a shigar da Waziri d’akin ganawa na bak’i....
Ubandoma ya kuma aza babban riga yana d’agowa Yarima Mahmood hannu alamun jinjina, lokaci guda yake furta “An gama Rankashi dad’e... Allah shi baka gidanku... Waziri godiya yake...!” Lokaci guda Ubandoma ya kuma aza babban riga kana ya shige cikin sauri...

Daidai nan Yazeed ya k’araso wajen shu’umin murmushin nan saman fuskarsa, hannunsa na dama rik’eda hannun d’ansa Sultan...”Taking a break your Highness...?” Ya fad’i murmushin bai bar saman fuskarsa ba...

Murmusawa kad’an Mahmood yai kana ya shafi kan Sultan yace “Hello your Royal Highness..!”

Yaron ya d’ago fuskarsa yana murmushi yake duban iyayen nasa kana ya dubi Mahmood yace “Do you also think one day I’ll become a King Uncle...?”

Duban Yazeed dake ci gaba da sakin shu’umin murmushinsa Mahmood yai kana ya maido da dubansaga Sultan ya shafa gashinsa kad’an kana yace “Of course Champ, one day zaka zama Sarki mai mulkin Masarautar nan... But when that time comes inaso kasa a ranka cewa shi shugaba Bawan Al’ummansa ne mai masu hidima da tausayinsu kaji koh...!”

Saurin katse tattaunawar Yazeed yai da fad’in “Sultan jeka Hauni ya d’auraka saman doki, I’ll catch up with you in a bit....!”

Yaron ya jinjina kai cikeda jin dad’i kana ya wuce...

Duban Mahmood Yazeed yai kana yace “Yaya I’m sorry, but you’ve no right to discipline my son... Idan akwai wanda yafi dacewa ya baiwa d’ah na horo that person should be me,just me and no one else...! Sabida Kai bakada Magaji shine bari ka cire masa son mulki da izza... Sultan jinin sarauta ne dan haka dole ya zamto namijin gaske maiji da mulki da izza...!”

Jinjina kai Mahmood yai kana yace “You’re right... He’s your Son, after all...”

Yazeed ya kuma jinjina kai cikeda jin dad’i kana yace “K’warai kuwa d’ah na ne kuma Magajin Masarautar nan..!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya shige shu’umin murmushinsa saman fuskarsa...

Yarima Mahmood ya bisa da kallo har ya b’acewa ganinsa kana yasa kai yai shigewarsa...

Yana shigowa parlorn ganawa da bak’in Waziri da Ubandoma suka risina suna kwasan gaisuwa... Mahmood ya k’arasa ya zauna a mazauninsa kana Ubandoma yai ficewarsa ya basu waje...

Mahmood ya dubi Waziri kana yace “Naji dad’i daka amsa kirata ta gaggawa Waziri...”

Waziri ya kuma risinawa kana yace “Allah shi baka yawan rai Farin cikin nawa ne, da sarki mai jiran gado zai nemeni... Ka fad’i dik abinda kake so Waziri yai maka shi a Masarautar nan Rankashi dad’e..!”

Shiru ne ya d’an ratsa tsakani kana Mahmood ya d’anyi gyaran murya yace “Waziri..!”

“Allah shi baka yawan rai...!” Waziri ya amsada haka...

Mahmood yaci gaba da fad’in “Mai zakace gameda b’acewan Ja’afar a Masarautar nan...?!”

Tambayar da ya sanya Waziri saurin d’agowa yana duban Mahmood saidai gizo da k’warjini had’ida cika idanun da Yarima Mahmood kedashi ya sanyashi saurin sadda kansa... Lokaci guda yake furta “Allah shi taimakeka Jafaru dai rana d’aya aka nemeshi aka rasa cikin Masarautar nan...!”

Shiru ya kuma ratsa tsakani kana Mahmood yace “Yaushe ne aka fahimci cewa Jafar baya Masarautar nan...?”

Waziri da gaba d’aya tamkar a birkice yake ‘yan kame kame ya soma da fad’in “Eh toh... Allah shi taimakeka Yau kusan shekara guda kenan idan ban b’ata lissafi ba...!”

Jinjina kai Mahmood yai kana yace “Kenan hakan yana nufin, da mutuwar mahaifina, da mutuwar matata da b’acewan Jafar sun faru ne a jere, d’aya na bin d’aya right Waziri...?!”

Shiru Waziri yai kaman mai tunani kana yace “Eh Toh hakan ne yake a bayyana Allah shi jada ranka...!”

Shiru ya biyo baya kana Mahmood yace “Yanzu kai a naka shawarin Waziri ta ina za’a fara nemo Jafar sabida ina buk’atarsa a Masarautar nan...!”

Waziri ya d’an d’ago yana duban Mahmood kana yace “Eh Toh Allah shi taimakeka ban isa ince ga nan ta yanda za’a soma neman yaron nan ba don kar a sami mishkila ko akasi....”

Jinjina kai Mahmood yai kana yace “Haka ne Waziri... Toh amma ni inada aiki da zan baka....!”

Waziri ya kuma gyara zamansa kana yace “Mecece wannan aiki Rankashi dad’e....?”

Mik’ewa tsaye wannan karon Mahmood yai hanayensa hard’e ta baya, yana d’an takawa kad’an irin yanda masu mulki keyi kana yace “Inaso ka wakilta masu bincike... A bincika duk k’asashen da muke gab’a dasu dan na tabbata bawa kaman Jafar bazai nisan da zai tsallake wad’annan k’asashenba...”

Sauk’e ajiyan zuciya a hankali Waziri yai kana yace “An gama Allah shi baka yawan rai... Za’a baza dakaru domin a zak’ulo Jafar yanda ya shiga ya fita...!”

Yarima Mahmood ya jinjina kai kana yace “Da kyau Waziri... Kana iya tafiya...!”

Waziri ya kuma mik’a godiyarsa kana ya kwashi babban rigarsa a hannu ya fice....
Yana ficewa sukaima juna wane irin duba shida Ubandoma tamkar wasu mak’iya... Waziri yaci gaba da sab’a babban rigarsa takalma a hannu ya fito daga b’angaren Maimartaba yanda nan cikin b’angaren sashen Mahmood yake....

Waziri yana fitowa wata Kuyanga dake daga b’angaren Gimbiya Zeenat Ta k’araso tai masa gaisuwa kana ta mik’a masa takardan dake hannunta...
Yasa hannu ya amsa yana karantawa.... Babu b’ata lokaci yaceda Kuyangar Ki sanar da ahugabanki Waziri Yana nan tafe....
Kuyangar ta jinjina kai kana tai shigewarta...
Chapter 30 · 0% Book details