← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 162

Sashe 12

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

D’an dubansa tai da mamaki kana ta murmusa “C’mon Paa, kai da kanka kake ce min nan ba Spain bane, things are different here...Well, I’m starting to get used to it... Nasan bazamu tab’a komawa kaman yanda muke a baya ba... It hurts tho..!” Ta k’arashe tana mai zura safar k’afanta....
Dubanta yake da wasu irin idanu, shi kad’ai yasan mai yakeji cikin zuciyarsa, yanada good relationship da d’iyarsa, bazaiso wani ko wani abu ya b’ata wannan alak’a mai kyau da yakedashi shida d’iyarsa ba, Amsar socks d’in da take k’ok’arin sakawa yai lokaci guda ya sauk’o daga saman gado yana zira mata safar a k’afarta... Zahra tai masa K’uri tana dubansa had’ida tunanin anya ba wani abin Ke damun Paa d’inta ba... K’ok’arin amsar safan take tana furta “Paa you don’t need to do this... Zan iya sakawa da kaina, I’m not a little girl anymore Paa...” Tana maganan murmushi kwance saman fuskarta... Bai saurareta ba har saida ya ida saka mata, kana ya d’ago yana dubanta shima murmushin ne saman fuskarsa, lokaci guda yake furta “Well, to me you’d always be the same that little baby I used to carry on my arms... Bazaki tab’a girma a idanuna ba.. And you know why is that my Princess..?”
Ta girgiza kai tana mai dubansa itama murmushin ne saman fuskarta, lokaci guda yaci gaba da furta “It’s because you’re my daughter, my little baby...And I love you, so much..!” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa...
K’arasowa tai ta rungumesa tana k’ok’arin maida k’wallan da suka ciko idanunta.... Lokaci guda Yarima Mahmood yaci gaba da fad’in “Never doubt that my Princess...!”
A hankali itama take furta “I love you too Paa...So much...!”

Suka kuma duban juna su duka biyu kana Yarima Mahmood yace “Zahra, I want you to know that whatever happens, I mean ko menene always remember that your Paa loves you... Never doubt that kinji koh...!”

Ta jinjina masa kai a hankali tana duban yanayinsa, dikda da yarinta a tattareda ita zata iya karanto damuwa cikin idanunsa, koda shike tin bayan rasuwar mahaifiyarta haka nan yake wasu lokutan....
“Do you want us to have breakfast together by the pool side..?” Yai maganar yana rik’eda hannayenta..
Jinjina masa kai tai kana tace “Sure Paa..” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye had’ida zura k’aramar hijab d’inta na makaranta...
Hannunta ya kamo suka fito tare...
Kallo d’aya zakaiwa yarinyar ka fahimci tana cikin Farin ciki...
Take ya sanar da Ubandoma ya fad’awa Jakadiya a shirya masu karin kumallo a gefen swimming pool shida d’iyarsa a nan cikin b’angaren mahaifiyar tasa....

Fu’ad da fitowarsa kenan bayan ya gaida Giwa ya hangi Zahra da YarimaMahmood suna cin abinci cikeda Farin ciki, hasken ranan hantsi ya haske fuskokinsu... Murmushi ya saki a hankali kana ya nufo yanda suke....

Kuyangin dake tsartsaye gefe suka rusuna suna gaidashi... Fu’ad ya k’araso k’asaitaccen murmushi saman fuskarsa, Zahra ce ta soma hangosa ta fad’ad’a murmushinta tana fad’in “ Buenos dias Uncle Best, join us for breakfast...”

Dafa kanta Fu’ad yai yana mai furta “Princesa de la mañana..” (Morning Princess) Yai maganan murmushi saman fuskarsa..
Daga ita har Mahmood murmushi sukai Mahmood na furta “Da alama k’aramin k’anina ya kusa komawa spain....”
Suka kuma murmusawa gaba d’ayansu kana Fu’ad ya zauna saman kujera guda yana mai gaida Yayansa Mahmood... Nan da nan d’aya daga cikin Kuyangin dake tsaye gefe guda ta k’araso tana serving Fu’ad....
***
Jerawa sukai itada Umaima suna tafe Umaima na bata gajerun tarihin cikin Masarautar, Muhibbah kaw sai kuma tambayarta take dik yanda suka shige, sosai ta ware idanu tana k’arewa Masarautar kallo tamkar bata tab’a kasancewa cikinta ba... Sashen Gimbiya Zeenat sukazo wucewa Umaima tace “Wannan shine sashen Gimbiya Zeenat amaryar Marigayi Maimartaba, bata jimada shigowa gidan nan ba Allah yaiwa Maimartaba rasuwa, da fari akasarin jama’an dake gidan sun zargeta da alhakin mutuwar Maimartaba tinda zuwanta bada jimawa ba ya rasu, toh amma dashike Giwa mutuniyar arziki ce itace tayi tsayin daka wajen ganin an daina jifan Gimbiya Zeenat da alhakin mutuwar Maimartaba, Giwa ita ta wanke Gimbiya Zeenat daga dik wani zargin da ake mata....Giwa wata irin mace ce mai son mulki lokaci guda kuma mai tsananin sauk’in kai ga Al’umman ta wannan yasa ta saye zukatan d’inbin jama’a dake Masarautar nan, ta d’auki Gimbiya Zeenat tamkar k’aramar k’anwa, bazaki tab’a cewa su d’in kishiyoyi bane, yanzu haka maganar da nake miki ana shirin had’a auren k’anwarta Rahima tareda Ya Mahmood, yanda zaki fahimci Giwa ‘yar uwa ta d’auki Gimbiya Zeenat..”

Tak’aitaccen murmushi saman fuskar Muhibbah tana mai kuma k’arewa sashen kallo idan bata mance ba wannan sashen ne jiya taga wata mace ta shige cikin dare, Ta d’an kaikaito tana duban Umaima kana tace “Ita matar da za’a aurawa Yarima Mahmood d’in a nan cikin Masarautar nan take...?”
Umaima ta jinjina kai fuska d’aukeda murmushi kana tace “Takan zo Masarautar nan wajen ‘yar uwarta ta jima sosai wasu lokutan, zan iya cewa akasarin rayuwarta ma ya dawo Masarautar nan ne...”
Jinjina kai Muhibbah tai a hankali tana mai linke bayanan cikin k’wak’walwanta....
Umaima tace “Muje mu fara zuwa mu gaisa da Giwa kafin na dawo dake sashen Aunty Zeenat...”

Jinjina mata kai tai a hankali kana suka nufi sashen Giwa....

Zahra Ta mik’e tana mai goge bakinta da tissue paper take fad’in “Paa, I’ll be going now nasan su Noor da Sultan na jirana... Uncle best idan na dawo zaka fitar dani kilisa as you promised...” Ta k’arashe tana duban Fu’ad baki a ture...

Abincinsa yake ci yana jinjina mata kai lokaci guda yake furta “But first we need to ask for your Paa’s permission... Idan ya amince sai mu fita amma saidai a d’auraki saman rak’umi...”
Gaba d’aya suka murmusa cikeda jin kana Zahra tai masu sallama ta wuce mahaifinta na saka mata albarka...

Gudu gudu Zahra ta fito dan tuni lokacin tafiya makarantar ta ya gauta... Saurin da take yazo da tsautsayi takalminta ya karkaci tai loosing balance tim kakeji ta fad’i k’asa cikin wasu duwatsu da aka k’awata wajen dasu... K’ara ta saki tana kame goshinta da k’afarta dake mata zafi.... Faruwan hakan yai daidai da shigowarsu Umaima da Muhibbah... A tare suka ambaci sunanta had’ida nufowa gareta... Yayinda kuyanga guda Ta nufi sanar dasu Yarima Mahmood cikin sauri...

Umaima na kiran sunanta tainai mata sannu saidai tuni Muhibbah ta d’agota ta azata saman cinyarta, tai saurin zame hijabin makarantar Zahra had’ida toshe goshinta yanda jini ke zuba ta umarci Umaima ta danne wajenda jinin ke zuba...Daidai kokacindasu Mahmood da Fu’ad suka k’araso cikin sassarfa Mahmood na ambato sunan Zahran....
Fad’i yake “Zahra, sweetheart..What happened to you Darling...!”

Muryarsa data sinkayo daf da ita ya haifar mata da fad’uwan gaba mai tsanani, abubuwan da suka faru suka shiga dawo mata.... Take taji zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, kasa d’agowa tai ta dubesa sabida tsananin zogi da zuciyarta Ke mata saima k’ok’arin d’aure k’afar Zahra take da d’ankwalinta da tuni ta zamesa tana baiwa yarinyar agaji na gaggawa...
Jin muryar mahaifinta ya sanyata saurin d’agowa tana ambato sunansa cikin kuka “Paa..It hurts... My leg hurts Paa..!”

Tuni Muhibbah ta janye jikinta daga wajen yayinda Umaima ke sanar dashi fad’uwa tai, tuni ya d’auketa cak ya nufi ciki da ita yana sanar da Fu’ad ya kirawo family Dr d’insu yanzun nan...

Jikinta sai rawa yake zuciyarta naci gaba da bugawa ta koma sashen da akai mata masauk’i, ganin Mahmood da Fu’ad da tai kusa da ita ya jefata cikin tsananin tashin hankali, anya zata iya k’arasa abinda ta fara...? Tai saurin rintse idanunta had’ida zama bisa sofa, shigowarta da kad’an kuwa ta sinkayo ringing d’in wayarta cikin sauri ta isa domin d’aga kiran dan tasan mai kiran nata bazai wuce Ansar ba....
***

Prescribing magani likitan yai bayan ya gama dubata, Yarima Mahmood yace “Dr kana ganin basai anyi hoton k’afarba...?”

Likitan ya d’an girgiza kai kad’an kana yace “Babu abinda ya sameta, da zaran tayi amfani da wannan magungunan dana rubuta shikenan, babu wani fracture, and it’s a good thing ta samu taimako na gaggawa... Wanda dik ya d’aure mata k’afar yayi k’ok’ari wajen bata agaji irin wanda ake so...”
Sai yanzu abin ke zuwa kansa, ya d’an dubi Umaima dake zaune gefen Zahra tanai mata sannu kana ya maidoda dubansa ga likitan yana mai furta “I’ll walk you out Doc..”
Dr ya jinjina kai yana mai furta “Godiya nake your highness..” Ya k’arashe yana mai sallamawa Zahra had’ida fatan samun sauk’i...

A iyaka tinanin Mahmood Umaima batada wani ilimin abinda ya shafi asibiti, toh ya akai har ta baiwa Zahra irin taimakon da ake so cikin gaggawa.... Da wannan tunanin ya shigo d’akin bayan yayi rakiyawa Dr... A daidai bakin k’ofa ya tsaya yana jin tattaunawar Zahra da Umaima...

Zahra taci gaba da fad’in “I feel bad Aunty Umaima, I treated her badly... Gashi ita ta taimaka min... Kinada gaskiya she’s a nice person... Please tell me Aunty Umaima, am I really a bad person...?” Ta k’arashe kaman zatai kuka...

Hannunta guda Umaima ta kamo murmushi saman fuskarta kana tace “You’re not a bad person Zahra, and I’m sure Muhibbah ma bata d’aukeki haka ba... Ita da kanta ta fad’a watarana zakuyi shiri, and naji dad’i da tun ba’aje ko ina ba kin fahimci hakan... D’an Adam ko wane iri ne babu kyau wulak’antasa kinji sweetheart...”

Jinjina mata kai tai kana tace “Yeah I know Aunty Umaima, my Paa taught me to always be nice toward others... Please kice wa Muhibbah na gode...!”

“Muhibbah...!” Suka sinkayo muryar Mahaifin Zahra...
A tare suka juyo suna duban k’ofa kana Umaima ta d’an risina, murmushi saman fuskarta take fad’in “Eh Yaya, Muhibbah itace wacce Ta baiwa Zahra agaji na gaggawa, ita d’in karatun zama malamar jinya take....”

Shiru yai tamkar mai nazari yana sauraren Umaima kana yace “Wacece MUHIBBAH...?”

***
Chapter 12 · 0% Book details