← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 162

Sashe 111

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Drawer mai k’yallaye d’aukeda jini Muhibbah Ta soma janyowa idanun Umaima suka sauk’a kan fararen k’yallayen... Jikinta na matuk’ar rawa ta shiga warwaresu tana ganin jini had’ida sunayen mata rubuce jikin k’yallen... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa... Ita kaw Muhibbah data tabbata Umaima taga abinda zai sa ta aminta da duk abubuwan da take fad’I mata tuni ta soma neman muhimmin abinda ya shigo da ita... Aiko tana d’aga bakin katifa taci karo da Taswiran...! Ta saki murmushi a hankali tana mai furta “Alhamdulillah..!” Bayan duk tsawon lokacin nan Taswiran guda uku sun fad’a hannunta....

Ita kaw Umaima tsaye tayi da k’yallayen tana duban abin mamaki, jiri na neman kada ita... Daidai lokacin sukaji an banko k’ofa an shigo... Karaf suka d’ago idanunsu suna kallon wanda ya shigo.....

*MUHIBBAH*

*68*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Koda Babba cikin kuyangi masu kula da b’angaren Muhibbah ta shigo mamaki ne ya cikata ganin Hasiya sanye da Kayan Muhibbah... Ta k’araso cikin tsananin tashin hankali tana furta “Ke Hasiya lafiya na ganki da kayan Gimbiya...! Mai hakan yake nufi..? Ina ita Gimbiyar...?!”

Hasiya tai rau rau da idanu tace “Bata nan ta amshi tufafina ta saka kuma ta gudu...!”

Kuyangar ta dafe kanta tana furta “Shikenan Hasiya kin kashemu.! Ta yaya kika amince da hakan.. Hasiya kin kuwa San tashin hankalin da kika jefamu ciki.. Yanzu mai zamu sanar da Rankaidad’e..?! Wata k’arya kike so muyi dan kare kanmu...?!”

Hasiya tace “Ni taimakonta nayi dan tana buk’atar taimako amma ai ga tufafinta jikina ki barni na zauna nan cikin d’akin nata a matsayin ita Gimbiyar idan Rankaidad’e yazo sai na rufe fuskata... Amma idan ba haka ba bana tunanin munada wani mafita dan na tabbata Gimbiya tayi nisan da bazamu cimmata ba..!”

Sauk’e ajiyan zuciya Kuyangar tayi tace “Idan hakan baiyi aiki ba Hasiya kin sakamu a uku dan alhakin b’acewar Gimbiya zai rataya ne a wuyarmu..!” Ta k’arashe damuwa k’arara saman fuskarta...

**

Jikin Umaima ya d’auki rawa, yanda taga fuskar Jamal ba k’aramin firgitata yayi ba, gaba d’aya ta rasa gane wacce duniya take sai rawa da jikinta keyi... Ko motsa ‘yar yatsar k’afarta ta kasa sai tsananin tsoro da ya lullub’eta, ga wani irin b’ari da illahirin jikinta keyi...

Muhibbah kaw rabin idanunta naga kwalban turare dake bisa dressing mirror rabi na kan Jamal dan bataso tayi losing sight d’insa tasan yana iya masu komai yanda Ta hango fuskarsa a matuk’ar dame..!

Murmushi Jamal ya sakarwa Umaima yana k’ok’arin nufota yake furta “Baby don’t believe a single word da wannan mayaudariyar zata sanar dake... She’s a fraud Baby kin mance ne.. She tricked you..!”

Girgiza kai Umaima take tana kuma k’ok’arin jada baya cikin tsananin tsoro da firgici, muryarta na rawa yake furta “No... No don’t come near me..! No no please...!”

Jamal bai daina yunk’urin nufota yana furta “Baby ni ne fah... Ni ne Yarima Jamal d’inki, your husband...!”

Muhibbah dake hararan kwalban turaren tana takawa a hankali tana matsawa kusan dressing mirror d’in take fad’ida Umaima “Run Umaima, don’t listen to this criminal... Run, ask for help... Don’t just stand there..! Ki gudu Umaima karki sauraresa...!!”

Umaima kaw ta kasa katab’us shock d’in abunda tai discovering a yau d’in ya kasa sakinta... Ko motsi mai kyau ta kasa sai rawa da jikinta yake sabida tsananin tashin hankali....

Daidai nan Muhibbah tayi nasan rabza masa kwalban turaren akai... Ya fad’i k’asa had’ida rik’e kansa yana mai sak’in k’ara... Umaima ma k’aran ta saki Ta mak’ale b’angare guda had’ida kame kanta da duka hannayenta biyu, jikinta bai daina rawa ba.. Kana gani kasan ba’a hayyacinta take ba... Muhibbah tai saurin tura Taswiran cikin rigarta, ta shiga janyo hannun Umaima tana fad’in “We need to get out of here Umaima.. Bamuda lokaci, bani hannunki..!!” Bata kai aya ba taji sauk’an wani irin abu a goshinta wanda ya sanyata zubewa a wajen duniyar na juya mata bata iya fahimtar komai ba saima lumshewa da idanunta sukai jini na kwarara daga goshinta...

Sandar crutches d’insa ya rabza mata akai da iyaka k’arfin da Allah ya hore masa... Cikin rawar jiki Umaima ta mik’e tana ambato sunan Muhibbah inaaa bata iya komai sai k’ok’arin bud’e lumsassun idanunta take cikin tsananin azaba...! Da k’yar tana ganinsu nesa nesa take iya furta “Run Umaima..! Run.! Ask for help..! Ki gudu, ki tsira da rayuwarki...!!”

Cikin kuka Umaima ke fad’in “Bazan iya barinki a haka ba...! Ki tashi mu gudu dan Allah..!!”

Inaa tana maganan ma cak ji tayi kaman numfashin Muhibban ya d’auke.... Umaima ta juyo ta hangi Jamal dake k’ok’arin zuba wani ruwan magani cikin handkerchief, a daburce Ta mik’e tana furta “Help..! Someone help us..!!” Ta nufi k’ofa a guje... Saidai tuni Jamal ya cimmata, Ta shiga bige buge tana k’ok’arin k’wace kanta saidai k’arfin namiji da mace ba d’aya ba balle ma ita da take cikin yanayi na matuk’ar tsoro...Tuni ya matseta sosai cikin hannunsa sai hura hanci yake yana haki, lokaci guda ya danna mata handkerchief d’in a hancinta... Aiko tana Shak’an ruwan maganin idanunta suka lumshe jikinta ya sake gaba d’aya, cak Ta daina duk buge bugen da take...
Jamal na murmushi yake furta “Where do you think you’re going Sweetheart..? You’re mine, Ke tawa ce Umaima... Idan kinga kin fice daga gidan nan ni ne kawai zan fitar dake...!” Ya k’arashe zancen nasa yana mai d’aurata saman gado... Haka yana cangwala sandarsa ya isa jikin wani drawer ya zaro igiya doguwa ya shiga d’aure Umaima jikin gado, tsaf ya gama d’aureta yana mai sakin murmushi... Maidoda dubansaga Muhibbah tai wacce take yashe a wajen lifeless kana ya furta “You’re now under my custody Muhibbah..! Zaki d’and’ani azaba zakiyi danasanin shigowa cikin Masarautar nan balle har kiyi gangancin zab’oni a matsayin abokin gaba...!!”

Take ya isa gareta da igiyoyin nasa ya shiga d’aureta tin daga hannayenta har zuwa k’afafunta, wane irin d’auri yayi mata ya had’e hannayen da k’afafun ya d’aure waje guda... Sai gumi yake yana haki yana ciza labb’ansa sabida tsananin bak’in zuciya...

Gefe ya koma yana sauk’e haki yake dubansu su duka biyu, itadai Umaima a nan zai barta yayita kula da ita har ya samu ya shawo kanta su gudu tunda babu mai tuhuma Ina take, matarsa ce babu wanda zai zargesa akanta...ita kuwa Muhibbah tunanin abinyi yakeyi da ita... Take tunanin tattaunawar Giwa da Jakadiya da ya sinkaya ya fad’o masa cewa zasu baiwa Aljanah Sarauniya Tamuna matarsa Umaima matsayin sadaukarwa, Toh mai zai hana ya canzawa Giwa Umaima da wannan ‘yar lek’en asirin, sai Giwa ta bada ita ga Bokanta a matsayin fansar matarsa Umaima, idan yaso shi sai ya d’auki matarsa su gudu daga Masarautar, bayada buk’atan komai cikin Masarautar, ya zab’i ya tsira da rayuwar matarsa...! Take ya saki wata irin muguwar murmushi yana duban Muhibbah da har lokacin idanunta a lumshe suke saiko Jinin dake kwance goshinta, d’aure da manyan igiyoyi... Yasa hannu ya d’an shafi k’eyarsa yanda Ta kwad’a masa kwalban turare yaga d’an jini kad’an... Murmusawa ya kumayi yana mai furtawa a fili... “Ba’a zubar da jinin ahali Sarki AbdulJabbar a banza yarinya..! Kinyi babban ganganci.. Wannan Jinin da kikayi sanadiyar d’igansa zaki biyasa da rayuwarki..!!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin wata murmushi lokaci guda ya kullo k’ofa ya fito ya nufi b’angaren Giwa...

**

Cikin rashin gane inda kalaman nasa suka dosa Mahmood d’in ya kamo hannunsa suka zauna saman doguwar kujera dake cikin d’akin ganawa da marassa lafiyan.... “Fu’ad ka natsu ka sanar dani... Mai kake son cewa..?!”

Fu’ad na hawaye ya d’ago yana dubansa sai kuma ya sadda kansa k’asa yace “It was that night... Daren Washe garin sallah k’arama..! Yaya ka tuna, shekaru goma sha hud’u da suka shud’e...!”

Mahmood ya kuma gyara zamansa yace “Fu’ad ban fahimci mai kake nufi ba, anyi bikukunan sallah da yawa wanne kake nufi..? Kuma mai ya faru lokacin..?!”

Fu’ad yasa tafukan hannayensa duka biyu ya shafi fuskarsa sai kuma yaci gaba da fad’in “Bikin k’aramar sallah wanda bayanshi da kad’an akayi bikin aurenka...!”

Yai shiru yana duban Fu’ad sai kuma ya soma tuno abinda ya faru “We were all together, ni da kai da kuma Yazeed da Jamal, it was such a nice evening..! Tun bayan wannan shekaran bamu sake wata fita saman Dawakai tare ba the four of us, koda kuwa kilisa ne.. How can I forget that Eid.. Yana d’aya daga cikin best Eid na rayuwana gaba d’aya sabida kiran da Mai Martaba ya min a lokacin ya sanar dani an saka aurena da Aliya bayan duk gwagwarmayar da muka sha da Maami na k’in amincewa da auren da tayi... But at the end wannan daren Mai Martaba ya kirani ya sanar dani ya saka mana ranan aure, Kaga kuwa bazan tab’a mance wannan daren ba..!”Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa sai kuma yaci gaba da fad’in “It was such a memorable Evening..! Munyi wasan Dawakai sosai Ni da kai da Yazeed da kuma Jamal harmada Ja’afar... Mukayi dare a hanyarmu Ta dawowa, bamu dawo Fada da wuri ba..!”

Fu’ad ya jinjina kai yace “That same night... Komai ya fara ne daga wannan daren, halinda na tsinci kaina ciki ya soma ne daga wannan daren Yaya...!”

Mahmood ya tsaida murmushin da yake lokaci guda yana mai duban Fu’ad d’in, sai kuma yaci gaba da fad’in “Something happened that night, kaman mun tsinci mutum a hanyar mu ta komawa gida.... I think it was... A girl... Yeah a girl, we even helped her...! But wait, na tafi na barku tareda Yarinyar..! Mai Martaba ya aiko sak’on yana nemana...! What happened that night Fu’ad..! Mai ya faru sanda na barku da yarinyar..? Tell me Fu’ad..! Tell me everything..!!” Ya k’arashe tashin hankali k’arara kwance saman fuskarsa...

Fu’ad yaja wane irin dogon numfashi yana mai lumshe idanunsa, lokaci guda yaci gaba da fad’in “After you left, Jafar left as well...! Ya rage saura mu uku da yarinyar.. Ni Yazeed da kuma Jamal...! Yaya we did something terrible to the girl...!!” Kuka ya hana Fu’ad ci gaba da magana...
Chapter 111 · 0% Book details