← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 162

Sashe 68

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muhibbah ta kuma lumshe idanunta wasu hawayen suka zubo mata... Tabbas bata kula da tafiyar Mahmood ba sabida duhun dare kuma muryar yaran Sarkin kusan duka iri guda ne ashe Mahmood ya tafi bata sani ba... Ashe amanarta ya damk’a hannun ‘yanuwansa da ya aminta dasu.... Wasu hawayen masu d’umi suka kuma gangaro mata sanda Fu’ad Ke ci gaba da fad’in
“Ga mamakinmu Yazeed ya amsa masa bai masa gardama ba, yace ya jeshi babu matsala shi zai kula damu gaba d’aya... Bayan tafiyan Yaya Jakadiya Ta cimma Yazeed da sak’on Giwa kan cewa a daren ranan zamu yarinya muyi mata fyad’e mu dukanmu uku idan har munaso mu tsira da mutuncin gidanmu... Yazeed ya sanar da ita cewa anyi an gama... Dan koda Jakadiya Ta tambayesa ina za’a sami yarinya cikin daren nan sai ce mata yai akwai yarinyar da suke tafe da ita.... Jakadiya tace hakan yayi su tabbata sunyi yanda aka umarcesu... Ta bada garin magani ma Yazeed kan cewa duk wanda yazo amfani da ita cikinmu sai ya Shafa a al’aurarsa kaman yanda malamin Giwa yace... Muna jin sautin murya ana k’walla kiran suna SAUDATU alamun ahalinta na nemanta, kafin tayi yunk’urin amsawa Yazeed yai saurin rufa mata alkyabbansa akanta ya toshe bakinta ya janyota muka shige wani lungu nan bayan masarauta.... Jamal wanda shima da alama yasan abinda Ke wakana shi ya d’aure idanun yarinyar da k’yalle duk ihu da birgima da take.... Abinda ban tab’a gani ba shi ya faru gaban idanuna... A gabana Yazeed ya lalata rayuwar yarinyar cikin wulak’anci da cin zarafi.... Bayan ya gama Jamal ma yayi... Ina kuka ina sanar dasu ni k’aramin yaro ne haka suka tirsasa min shafa wanann garin maganin a al’aura na abin mamaki kuwa sai ji nayi ina matuk’ar son kasancewa da mace... Nima nabi sahunsu... Muka wulak’anta k’aramar yarinyar da Yaya ya bamu amanan cewa mu kaita ga iyayenta.... Koda muka gama sai k’arasowa Jakadiya Tai ta d’auki yarinyar wacce ko numfashi batayi tace kar mu damu bata mutu ba ita zata kula da ita, a cewarta ita zata Kai yarinyar ga iyayenta Ta sanar dasu an tsinceta an mata fyad’e.... Nidai tindaga wanann lokacin kuka kawai nake bansan meke faruwa ba, umarni kawai suke bani sai ganin dogari guda biyu nayi Yazeed da Jamal suka janyoni muka bi bayan dogaran... Ina tambayarsu Ina Yarinyar... Jakadiya ta Kaita gida..? Sai ce min sukai eh Jakadiya takaita ga iyayenta... Kuma yanzu zamuje ne mu tabbatar da hakan... Hakan yasa nabi bayansu muka k’arasa wani gidan wanda gidansu Yarinyar ne.... Dogaran su suka sanar da mutumin cewa anyiwa d’iyarsa fyad’e tana can asibitin bayan Fada yazo ai masa rakiya yaje ya ganta... Mutumin ya kame k’irjinsa yana salati... Ashe Jakadiya na biye damu amma babu yarinyar a tattareda ita... Tanayi tozali da mutumin mukaji Ta ambato sunansa... Tace Saudatu d’iyarka ce....??! Mutumin ya zaro idanu waje bai iya bata amsa ba... sai gani nayi ta juya cikin sauri ta janyo Dogari guda sunyi magana...

Dogarin yana dawowa baiyi wata wata ba ya zaro Takobi da niyyan cire kan mutumin ni kuma nai k’ok’arin kare mutumin Jamal da Yazeed suna k’ok’arin janye ni... Ina fad’i masu bazai yuwu munaji muna gani mu bari a kashe bawan Allahn nan ba bayan cin zarafin da akayiwa d’iyarsa wacce bamusan yanayin da muka barta ciki ba... Yazeed yana janye ni yana yunk’urin hanani saiga wani mutumi ya fito daga cikin gidan Dogari guda ya cakka masa Takobi a ciki... Nayi k’ara na finciko Takobin dake d’amaran d’aya Dogarin nayi k’ok’arin kare Mahaifin yarinyar saidai tuni k’addara ta riga fata ainka da k’aramin yaro Takobin yamin nauyi sosai ban ankare ba sai ji nayi na sare k’irjin mahaifin yarinyar da takobi b’angaren da yake rik’eda tin sanda Labarin fyad’en ya isa masa.... Na saki wane irin k’ara a wajen na kama kaina dake tsananin bugawa, take na zube wajen ban farka ba saida naji d’umin zafin wuta da sautin k’onewar abubuwa, turirin hayak’i shi ya tadani... Naga gidan su yarinyar nata faman ci da wuta... Na yunk’ura zan fad’a cikin gidan Ina mai sanar dasu Yarinyar da mahaifiyar na cikin gidan mu taimaka masu... Yazeed ya janyoni baya ya kikkifa min mari masu zafin gaske yace yarinyar da mahaifiyarta sun mace cikin gidan wuta ya cinyesu, nima idan na shiga saidai nabi sawunsu.... Haka Ina kuka suka janyeni muka nufo Fada Giwa da Jamal suka kafa min warning kan cewa babu abinda ya faru idan kuma nayi gigin sanar da wani fa abinda ya faru zan mance cewa ni ahalin gidan ne musamman Yaya Mahmood wanda ake shirye shiryen bikinsa a lokacin....!! Shin Ta yaya zan iya yafe wa kaina wannan babban laifi wanda muka aikata... Ki fad’a min Muhibbah..!!” Ya k’arashe cikin tsananin kuka...

Itama d’in kuka take sosai... Tabbas farkawa kawai tai ta ganta a wani d’aki a kulle ga wani tsohon mutumi kaman maye yanata zagaye kanta da jan k’yalle yana maganganu marassa dad’in sauraro... Ganin haka yasa tai likimau dukda azaban da takeji wanda bata tab’a jin irinsa ba... Hankalinta bai gama tashi ba saida taga wannan tsinannen halittan ya duk’a ya bud’e k’afafunta yana katsan wani abu a al’auarta ga tsananin zafi da zogi mai d’imautarwa da takeji har k’wak’walwan kanta.... Ta kuma rintse idanunta dan hawayen ma sun daina fitowa... Tana jin sanda tsohon mai k’irar abin tsoro ya mik’e ya fice rik’eda k’ok’on da ya gama katse jinin dake fita daga al’aurantar a hannunsa... Ta hango sararin waje daga yanda take kwance cikin d’akin mai tsananin duhuwa... Dukda azaban da takeji hakan bai hanata furta Basmala ba ta karanto ayatul kursiy ta karanto falak’i da nasi... Cikin wane ikon Allah yunk’urin da zatai sai ji tai Ta mik’e zunbur... _Laa ilaha illa Anta subhanaka inni kuntu minazzalumin_ Shine addua’an da harshenta keta nanatawa... Tafiya kawai take ba tareda tana ganin hanya ba take kuma nanata addu’an... Tabbas taji ana kirawo sunan ya da wani irin sauti amma wannan addu’a bai bar saman harshenta ba, duk razanata da ake da abubuwa na ban tsoro bakinta bai daina karanto wannan addu’a ba har saida Ta bud’e idanu Ta ganta a wajen Masarautar... Sai lokacin zafin ciwowwukan dake jikinta suka kuma dawowa ga busasshen jini dake bin k’afarta... Wato ashe Jakadiya ita ce ta kaita ga wannan matsafin mutumin data farka ta ganta gabanshi.... Ashe Mahmood baida laifi hasalima baisan komai ba... Ta zalunci bawan Allah ta had’asa fad’a da d’iyarsa... She needs to stop Zahra tun kafin lokaci ya k’ure...

Muryar Fu’ad ne ya dawo da ita daga duniyar tunaninda ta tafi yanda yake fad’in “Baya duk abubuwan da kikaji gamedani nasan bazaki tab’a sona ba Muhibbah... Will you still accept me...?!”

Wani irin duba take masa da idanunta masu zuban hawaye, tsanarsa na kuma ratsa zuciyarta lokaci guda take furta “Ka cuceni Fu’ad... Kasa na fara soyayya dakai... You’re a Criminal, I’d never love someone like you... Never, ka mance ka tab’a soyayya da wata mai suna Muhibbah... I hate you.. Na tsaneka Fu’ad, bazan tab’a soyayya da criminal irinka ba... Kuma kasan meye.. Hauka shi ya cancanceka bayan abinda kukayiwa yarinyar can da ahalinta... Ina fata ka tabbata cikin hauka Fu’ad, kada Allah ya kawo rananda zaka warke..!!!” Tana kaiwa nan ta mike ta fice a guje tana kuka sosai, kukanda batasan na tausayin kanta bane ko na tausayin Mahmood ne wanda baida laifi ko k’ank’ani cikin duk abinda ya faru da ita...

Cikin wane irin k’ara Fu’ad ya k’walla mata kira yana mai kuma tamke kansa dake ci gaba da sara masa... Lokaci guda ya shiga tattaran pills d’in da baisan adadinsu ba yana turawa cikin bakinsa.....Take ya zube a wajen rik’eda kansa tamkar maras numfashi...

Gudu kawai take cikin Masarautar tana addu’an cimma Zahra Ta tareta kafin Ta isa babban Zauren Taro Ta tozarta Mahmood... Saidai tana isowa ta hango Zahra ta fito daga Zauren a guje tana kuka sosai... Tana hango Muhibbah ta fad’a jikinta tana mai kuma fashewa da kuka... Take Muhibbah ta rungumeta hawaye masu tsananin zafi na gangaro mata... Tabbas d alama ta makara Zahra ta riga ta yarfa Mahaifinta cikin d’imbin jama’an Masarauta...

D’ago idanun da Muhibbah zatai suka had’a ido da Mahmood wanda fitowarsa kenan daga parlorn ya biyo bayan Zahra...
wasu irin kwantattun hawaye Muhibbah ta hango cikin idanunsa wanda ko ba’ace ba jarumta ne da tsananin k’arfin hali suka hanasu zubowa.....

SameenaAleeyou 📚
[8/14, 10:58 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*45*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Hawaye ne suka ci gaba da gangaro mata su biyun suna duban cikin idanun juna, Ta kasa janye idanunta daga barin dubansa ta kuma kasa sakin Zahra dake shesshek’ar kuka saima dad’a matse Zahra da tai cikin jikinta hawaye masu tsananin d’umi suna kuma gangaro mata.... Tana ganin sanda Mahmood yasa kai ya fice daga wajen baki d’aya Turaki na biyedashi... A hankali ta lumshe idanunta wasu hawayen na kuma gangaro mata tsananin tausayin Yarima Mahmood da d’iyarsa cikin zuciyarta...

Zahra ta d’ago tana dubanta, cikin kuka take fad’in “Dan Allah ki fitar dani daga Masarautar nan wllhi banson zama a nan... Na gaji na gaji da rayuwa cikin gidan nan... Dan Allah ki fitar dani daga gidan nan..!” Kuka yaci k’arfinta..

Muhibbah tai saurin rungumo kanta cikin k’irjinta cikeda tausayawa, cikin tsananin rawar murya take furta “Everything will be ok Zahra.. Ki kwantar da hankalinki kinji komai zai shige ya zama tarihi... Zo muje you need to rest..!!” Bata jira amsar Zahra ba ta janyeta suka nufi Fadar Giwa...
Har lokacin jikin Muhibbah a matuk’ar sanyaye yake...
Chapter 68 · 0% Book details