Sashe 70
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babu musu Jakadiya Ta k’arasa wajen Uwargijiyar tata wacce ta koma tamkar wata abin misali cikin k’ank’anin lokaci... Tabbas Mulkin duniya ba komai bane, take Allah yake sauya al’amaransa ya maida bawa ba koman komai ba ya nuna masa kasawarsa da kasawar duk wani mulki da dukiya nasa... Bawa yabi Allah shine tsiransa, kada Allah ya jarabceka da d’an wani k’ank’ani mulki na duniya ko k’ank’anin arziki da zai gushe ka zata ka samu duk wani power da kake nema a duniya kuma zaka iya takawa kowa yanzu sai ya karb’e komai ya kuma maidaka ba kowa ba dan shid’in shi kad’aine mai dawammamen mulki da baida farko baida k’arshe... Ya Allah kada ka jarabcemu da bijire ma rahamarka garemu..Ameen!
A d’an tsakanin wannan lokaci idan Kaga Giwa dole ta baka tausayi, gaba d’aya Ta fice a hayyacinta Ta koma tamkar ba ita ba, yaranta har guda biyu kwance asibiti, duk San mulki irin na Giwa wanda k’asa ma da k’yar take takawa sabida Izza sai Gata nan tana taka k’asar asibiti cikin sanyin jiki da karb’an umarni daga wajen likitoci... Idan da ace Tanada sauran rabo tabbas zata fahimci darasi cikin abubuwan dake faruwa da ita...
Har kawo zuwa dare Fu’ad yana kwance unconscious bai farfad’o ba baisan yanda kansa yake ba, koda ace ya farfad’o su kansu likitocin basusan da mai zai farka ba, hauka ne kokuwa akasinta... Hakan yasa suka sanar da family d’in Fu’ad they should be ready for anything dan komai ka iya faruwa...
**
MASARAUTA
Sassafe ta ida shirinta tsaf da zummar barin gari, saidai ji tai bazata iya tafiya bata duba halinda Zahran Ke ciki ba, Ta mik’e ta nufi b’angaren Giwa yanda ta tadda Zahran da Umaima na shirin fita zuwa asibiti duba Jamal da kuma Fu’ad... A nan ne suke sanar da ita abinda ya sami yaran Sarkin... Harga Allah bayan abubuwan da sukai mata itada ahalinta zata iya cewa ko gizau bataji tausayinsu ba hasalima ma abinda ya cancancesu suka samu...
Umaima ta dafata kad’an tace “Ni kad’ai nasan labarin soyayyarku da Fu’ad, are you sure bazakije ki ganshi ba...?!”
Sauk’e ajiyan zuciya tai a hankali kana tace “Zanso hakan Umaima amma saidai nima kiran gaggawa na samu daga gida Mummy na asibiti ba lafiya tin daren jiya... Idan kinje ki gaisar min da Fu’ad... Harmada Jamal d’in...!”
Shiru Umaima ta d’anyi tana karantar yanayinta kana ta jinjina kai tace “Tace shikenan, zan fad’i sak’onki, kuma nima ki gaisar min da Mummy da kyau, kice ina mata fatan samun lafiya...!”
Ta jinjina kai a hankali tana murmusawa... Zahra ta k’araso sukai K’uri suna duban juna... Lokaci guda ta isa ta rungumeta tace “Tia ki gaishe da Mummynki, kuma idan kinje please ki had’amu a wayar na gaisheta...!”
Muhibbah ta jinjina mata kai a hankali kana ta Shafa kan yarinyar kad’an tace “Kiyi kaman yanda Nace miki jiya, apologize to your Paa kinji... Kinga dai abubuwan dake faruwa cikin Masarautar nan, your Paa is going through a lot Zahra... Please don’t add to his problems kinji... Try to be more understanding with him... Baya buk’atan tashin hankali daga gareki a halinda yake ciki yanzu...!”
K’uri Zahra tai mata sai kuma ta girgiza kai alamun k’in amincewa tace “That has nothing to do da amsoshin da nake nema daga wajen Paa.. I won’t stop har sai ya sanar dani...!”
Muhibbah ta lumshe idanunta a hankali zuciyarta naci gaba da tsinkewa, tabbas tasan tank’waro Zahra ba abu bane mai sauk’i... Murmuahin da yafi kama da yak’e ta sakar mata kana ta kuma masu sallama...
Umaima tace ta bari su fita tare ko ma a kaita gida a motar masarauta.. Fir Muhibbah tak’i hakan hasalima sauri sauri ta fice daga Masarautar...
Tana tafe tana neman abin hawa ya hangeta, tinda ya fice daga Masarautar jiya bai dawo ba, hasalima watsewarsa ya gama a club sai yanzu ya nufo gida dan jin yanda al’amra suka kwana...
Yana hangota ya saki murmushin nasa yana mai shafa hab’a... Lokacin da yake jira, dama itama shak’e yake da ita... Kaf takaicinsa zai sauk’esu ne akanta Ta yanda gobe ko mai irin sunansa taji zata basa Girma...! Ya k’arashe tinanin nasa yana karya kan Mota...
Tana tsaye bakin kwaltar da babu mutane sosai babu ababen hawa saman kwalta saiko jifa jifa abinka da hanyar da ba’a faye bi ba.... Kaman daga sama taga bak’ar G-wagon taja ta tsaya gabanta, haka kurum taji bata aminta da motar ba dan tasan ba motar k’anan mutane bane, idanunta suka sauk’a kan plate number na motar aiko nan Ta hango Prince Zeed rubuce jiki... Innalillahi kawai take karantowa Ta soma janye luggage d’inta cikin sauri tana San barin wajen... Saidai tuni motar taci gaba da nufota, daidai gabanta ya kuma jan birki ya zube glass yana k’arema Fuskarta dake cikeda tsoro wane irin duba... Ya sakar mata murmushin nan nasa kana yai gyaran murya kad’an “Look who’s here...! Tafiya cikin rana bai kamace Tough girl irinki ba Rankidad’e... Shigo mana let me give you a ride..!”
Take taji k’arfin hali na zuwa mata, Ta murmusa kad’an dukda tsananin tsanar wannan fuska tasa da takeji... “Karka damu Your Highness.. Ai mu talakawa mun saba da wahala... Yanzu ba da jimawa ba zan sami abin hawa irin namu na talakawa...!”
Yazeed ya kuma murmusawa yace “Ba’a rejecting offer d’ina... So dole ki shigo...!”
Jada baya ta soma tana fad’in “Ni kuma nace bazan shiga ba Rankaidad’e.... Why can’t you just go ahead....!”
Fitowa yai daga cikin motar zuciyarta naci gaba da tsinkewa, taci gaba da janye jakarta cikin sauri saidai tuni ya cimmata....
Dosowarsu hanyar kenan zasu nufi masarauta ya hangi Yazeed na kokawan tura mace cikin mota... Yai saurin duban Turaki dake driving yace “Wait... Mai nake gani haka...!?”
Sai sannan Turaki ya kula da abinda ya gani....
Mahmood ya furta “Wacece yarinyar can da Yazeed yai forcing d’inta cikin motarsa... Lets follow them Turaki... Muyi saurin bin bayansu, jikina na bani wani abu maras kyau Yazeed zai....!”
Turaki ya karya kan Mota yana fad’in “Got it your Highness...!” Take motarsu tabi bayan motar Yazeed...
Suna ganin yanda motar Yazeed ke sharara gudu saman kwalta tamkar mai shirin barin gari... Mahmood K’uri kawai yai wa motar yana ganin yanda Yazeed Ke wasa da k’arfen nasara saman kwalta... Shikadai sai murza ‘yan yatsunsa yake yana ganin tamkar Turaki ba gudu yake ba, traffic light ya raba tsakaninsu... Cikin tsananin huci yake fad’iwa Turaki “Speed it up Turaki we can’t lose them.!!”
Turaki jinjina kai kurum yake yana mai ci gaba da falfala gudu had’ida k’ok’arin ganin Yazeed bai kufce masa ba saidai duk iyaka k’ok’arinsa suna karyo kwana suka nemi motar Yazeed suka rasa, mashigar hanyoyi ne har guda hud’u suka rasa wannene d’aya Yazeed yabi....
**
Suna isowa gidan Yazeed ya zakayo Ta yanda take zaune ya bud’e motar ya shiga fincikota da iyaka k’arfinda Allah ya hore masa, sosai jikinta ke rawa tana tarjewa tana fad’in kada yazo kusanta... Take abubuwan da suka faru da ita shekarun baya suka shiga dawo mata... Sosai ta shiga matsanancin tashin hankali tana mai furta “Please don’t... Don’t please..!!”
Tarjewa yakushi cizo da dik wani abinda take tunanin zai ceceta hannun wannan azzalumin bawa tayi amma a banza...
Haka Yazeed ya dinga janyota har suka shige cikin gidan...
**
Suna nan suna tunanin hanyar da zasu bi Mahmood yai shiru tamkar mai nazari sai kuma ya d’ago ya dubi Turaki yace “Ina tinanin nasan yanda Yazeed ya tafi... Around this place idan ban mance ba akwai guest house d’in mahaifinmu... Inada tabbacin can Yazeed yakai yarinyar nan... Lets go before he does something to her...!”
Cikin sauri sukabi hanyar da Mahmood yakeda tabbacin nan ne gidan yake...
Aiko suna zuwa suka hango motar Yazeed.. Suka dubi juna a tare... Babu shiri suka nufi cikin gidan....
A daidai sanda suka shigo parlorn daidai lokacinda Allah ya baiwa Muhibbah daman roza ma Yazeed flower verse a kansa... Ta taso a guje tana kuka sosai... Da tsananin mamaki Mahmood ke dubanta “Muhibbah..!!” Ya fad’i zuciyarsa na bugawa...
Bata iya cewa komai ba sai kuka... Tsananin tsoro bayyane saman fuskarta... Zuciyar Mahmood taci gaba da bugawa da sauri da sauri, shi kad’ai sai sakin huci yake suna sauraro muryar Yazeed alamun yana neman Muhibbah..
Cikin zafin nama Mahmood ya nufi yanda yake sinkayo muryar Yazeed d’in... Turaki na kiransa inaa ko waigawa baiba... Yana hango Yazeed ya tafi ya dunk’ule hannu yakai masa naushi a hanci, take Yazeed ya zube bakinsa da hancinsa na fidda jini... Cikin wane irin karaji Mahmood yasa hannayensa biyu ya kuma d’ago Yazeed sama ya k’ara masa wata naushin, dukan sa’a yakewa Yazeed wanda Ke kwance waje yana haki da k’yar...
Mahmood na nunasa da yatsa yake fad’in “Kaci amanan iyalanka, ka wulak’anta Martaban gidanmu... Ka zakunci ‘ya’yanka... You should be ashamed of yourself Yazeed...!!” Ya k’arashe yana kuma kai masa tokari da k’afa... Yazeed bai iya komai sai haki da k’yar jini da yai masa faca faca a fuska ga yanda Muhibbah ta fasa masa da verse ga kuma uban bugun da yaci hannun Mahmood...
Fitowa yai yana huci, Turaki ya taresa yace “Ina Yazeed..?!”
Wane irin duba yaiwa Turaki ba tareda ya amsasa ba saima tambayarsa yarinyar da yayi...
Turaki yai masa nuni da yanda Muhibbah ta tak’ure ta kifa kanta tana cazgan kuka...
A hankali ya isa gabanta ya durk’usa, yana mai k’ura mata idanu cikeda tausayawa...
Tai saurin d’agowa da zummar jada baya.. Mahmood ya d’an bud’e murya kad’an yace “Karki damu we won’t hurt you, you’re safe now... Did he do something to you..?!”
Tai saurin girgiza masa kai alamun a’a hawaye naci gaba da ziraro mata...
Mahmood ya jinjina kai had’ida kauda kai gefe yana mai fuzar da huci a hankali....
Gyaran murya ya kumayi yace “Mai ya fito dake daga masarauta kuma Ina zakije da kaya...?!”
Tasa hannunta share hawayen fuskarta, cikin rawar murya tace “Gida Zanje...!”
Mahmood yace “Kina nufin garinku..?!”
Tai saurin jinjina masa kai alamun eh...
“Ina ne garin naku..?!”
“Bauchi..!” Ta basa amsa a tak’aice...
Juyawa yai ya dubi Turaki dake binsu da kallon mamaki, lokaci guda ya mik’e had’ida furta “Saka luggage d’inta a mota, zamu tafi Bauchi yanzu..!”