Sashe 130
Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sharkaf Ta jik’e da gumi tana duban Giwa tana girgiza kai hawaye suna ci gaba da ambaliya a fuskarta sahu sahu, wani na bin wani... Ta kasa gasgata abubuwan da taji daga bakin wannan azzalumar mata wacce take tantama anya ‘yaradam ce..? Idan kuwa ‘yar adam ce Anya akwai zuciya cikin k’irjinta...? Hawaye had’eda zufan da ya wanke mata fuska take duban yanda Giwa Ke kuma sakin wane irin shewa akanta, ji tayi kaman maganan Ta ya d’auke cak sabida tsananin shiga tashin hankali da tayi domin kuwa ko kalma guda ta kasa furtawa, ga wani irin juyawa da kanta yake sai tanajin kaman a wani nisan duniya take sinkayo dariyar Giwa da shewarta... Bata kuma sanin meke wakana ba saidai kawai ganin Jamal tai tsaye kanta muguwar murmushinsa saman fuskarsa yake furta “Saudatu.!!! So you’re back..! Kin dawo dan Ki d’auki fansarki akanmu, kin dawo kin tarwatsa ahalinmu... Kin lalata komai, Na rasa k’afata guda d’aya, kin rabani da matata Umaimah..! Ban damu ba idan itad’in ‘yar uwarki ce, Umaima itace rayuwata, kuma har abada bazata tab’a sanin cewa ked’in ’yar uwarta bace, baza San cewa ga abinda na aikata ma ‘yar uwarta ba wanda suka had’a uba d’aya..! Ita d’in tawa ce bata da sauran ahali a halin yanzu da ya wuce ni Jamaluddeen..! Kece kika dad’a haukata Fu’ad sannan kika toni asirin Yazeed kika hana Mahmood Auren Raheemah..! Yazeed lost both his hands sabida Ke, he even lost his children duk a dalilin ki.. Ke harta aurensa ya rasa duk sabida Ke..! Ta yaya kike zaton zan goyi bayan a yafe miki..! Ai yanda Giwa ta fad’i Zata cika mana mulkin ahalinmu da gudan jininki babu ja babu komawa baya.. Sannan abu na k’arshe kafin Ki tafi daga wannan rayuwar zanso na sake d’and’ana zumarki dana d’and’ana a baya domin kuwa dukda shud’ewar shekarun nan, na lalata rayuwar ‘yan mata da dama banci karo da wacce naji dad’in kasancewa da ita sama dake ba..! Kafin na mik’a ki ma bokan Gimbiya ya gama abinda zai dake ya tura ma Sarauniya mai gadon Mulkin tsafi tarihin abinda muka aikata maki shekaru goma sha hud’u baya zai maimaita kansa...!” Ya kuma d’aga allurar dake hannunsa yace “Kinga wannan allurar ban mance da ita ba, musamman sabidake na zubata a syringe, sai na miki ita kafin na mik’aki ga bokan sarauniya, zan nuna miki k’arshen taurin kai yau, sai kinyi da kinsanin dawowa cikin wannan masarauta..! Zan miki wulak’ancin da ban miki irinsa a baya ba domin kuwa nid’in na k’ware wajen wulak’anta ‘ya’yan mutane ta hanyar lalata masu rayuwa wanda duk kece sila..! Duk yaran da na lalata ma rayuwa kece sanadi domin akanki na fara..! Da ace kin tsaya tun wancan lokacin an cika mulki da gudan jininki watak’ila da ban zamto abinda na zamto a halin yanzu ba... Dan ni da kike gani ban tab’a kusantar wata d’iya mace ba ba Ta hanyar fyad’e ba...!” Ya k’arashe yana mai k’ok’arin b’alle botiran rigarsa muguwar murmushin bata bar saman fuskarsa ba...
Allah ya gani babu abinda take fahimta saima idanunta da suka kakkafe suna kallon sama, haka nan Ta koma tamkar wacce bata numfashi... Ga tsananin nauyi da k’irjinta harma da harshenta suka mata, addu’an ma bata iya furtawa da baki... Iyakacin abinda Ta sani shine shine zuciyarta bata daina ambaton mahaliccinta ba, zuciyarta bata daina tsarkake mahaliccinta tana mai k’ak’antar dakai garesa had’ida neman taimakonsa da agajinsa daga hannun wad’annan mugayan mushirikan mutanen data fad’a hannunsu..! Tayi imani Ubangijinta maiji ne kuma mai gani wanda ganinsa da jinsa suka sha bambam dana ko wani makhaluk’i..!
**
Jikin Mahmood na tsananin rawa yake warware k’undin...! Ga tsananin mamakinsu wannan alamun shatin kwabo da suka gani daga tsakiyar ginin coin mai irin alamun ne cikin k’undin wanda yakeda matuk’ar nauyi a hannu sai faman shek’i yake kaman an tsoma cikin ruwan silver..!
Baba Nomau dubi Mahmood da har lokacin jikinsa bata daina rawa ba bai kuma saki wannan shatin kwabon ba yace da Mahmood d’in “Ka natsu Mahmooda ka ambaci sunan Allah ka saka wanann shatin kwabo a jikin gini yanda yake d’aukeda alamun..!”
Jinjina masa kai Mahmood yai, yayi kaman yanda Baba Nomau yace, da sunan Allah saman harshensa ya manna wannan shatin kwabo jikin garun..!
Yana mannawa gaba d’aya Masarautar tayi wane irin girgiza wanda duk wani mahaluk’i da yake cikin Masarautar saida yaji wannan diri da d’aukacin Masarautar tayi.. Tsofaffin gini wasu saida suka b’anb’are wasu na zubewa k’asa..!
Baba Nomau yace dasu kowa ya nastu suci gaba da ambaton sunayen Allah suna tsarkakesa..!
Wannan dirin da d’aukacin Masarautar tayi sai gani sukayi wajen da Mahmood ya manna shatin kwabon gini yana bud’ewa kaman ana turasa...! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un zukata Ke ambato..!
Cikin iko na Ubangiji ginin nan yake bud’ewa suna hango wani alk’arya guda a bayan wannan ginin, domin kuwa cikin wannan gini wani masarauta ne mai zaman kansa..!
Mahmood ya yunk’ura zai danna kai ciki Baba Nomau yayi saurin rik’osa ya dawo dashi baya yace dashi, gini irin wannan da yayi shekaru da dama a rufe haka dole akwai wasu halittu dake rayuwa ciki wanda mu namu idanun bazasu iya gani ba..! Inaso cikinmu gaba d’aya wanda duk baiyi azkar na safiya na neman tsari ba Toh yayi yanzu..!” Sannan karanto masu addu’o’in neman tsari da zasu karanto kafin su shiga..! Ya kuma karanto matayassara daga littafin Allah mai tsarki..!
Su Duka suna masu yak’in da kariyar Ubangijinsu wanda babu abinda yafi k’arfin jkinsa..!
Kowa yayi kaman yana Baba Nomau yace, suka nufi cikin wannan gini da basa iya ganin komai sai jemagu da wasu irin k’wari marassa kyaun gani.. Ja’afar da Mahmood saiko Baba Nomau da Ubandoma sune suka shigo cikin wannnan kangon Masarauta mai tarin kayan al’ajabi .. Bakunansu basu daina ambaton Allah ba..!
**
Tun sanda ginin yayi wani irin diri fatar jikin Tal’udu ke fitar da wani irin bak’in hayak’i mai mummunan d’oyi, Kan Giwa da hannunta da ya tab’a cin wuta suna fitar da irin wannan hayak’in da kuma d’oyin... Jakadiya Ta razana matuk’a sai faman muzurai take tana tambayar Giwa mai ke faruwa...Giwa Ta rufa bak’ar Alkyabbarta hannunta rik’eda rik’eda fitilar tsafi.. Ta zauna saman Darduman tana fad’ida Jakadiya “Wannan shine cikan Mulkina Jakadiya..! Wannan alamu ce da take nuna Sarauniya zata cika mulki na a yau d’in..!!” Ta k’arashe tana mai kuma tura fitilar cikin Bak’in tukunyar Tana ganin yanda bak’in hayak’i ya rufe Tal’udu gaba d’aya...
Jakadiya tace “Amma Rankidad’e bamu ganin alamun Tal’udu bak’in hayak’i ya rufesa.!!”
Giwa taci gaba da fad’in “Sharad’in kenan ranan da Mulkina ya cika ranan Tal’udu zai bar cikin gidan nan tareda duk wani abu da yake daga tsatsonsa inada tabbacin wannan bak’in hayak’i alamu ce ta nasara..!!!”
Jakadiya tai K’uri tana kallon wannan tashin hankali tana mamakin ta ya za’a ce bak’in hayak’i had’ida mummunan d’oyi ya zamto nasara..!!
A daidai wannan lokaci su Mahmood suka iso...! Su Giwa suka soma hangowa tana zaune saman Jan Dardumanta na tsafi ga tukunyar tsafi gabanta gacan wani bak’in hayak’i turnuk’e gabanta wanda Tal’udu ne cikin hayak’in, bak’in hayak’in ya rufesa baka iya hango komai nasa..!
A take suka soma toshe hancinsu suna kuma k’arasowa wajen..!
Jakadiya ce ta soma hangosu, ta saki wani irin k’ara tana mai sililalewa k’asa Giwa kam hankalinta naga bak’in Tulu tana kuma tura fitalar tsafi ciki tana furta “Ya Ke Sarauniya uwar tsafi yau na cika miki k’udirinki na kawo miki Amaryarki da Ta gudu daga gareki shekara goma sha hud’u baya..! A yau na mallaka miki gudan jininta ki cika min Mulkina dashi..!!”
Mahmood dake tsnanin huci ne yai wani irin tsalle ya tokari bayan Giwa kwatsam fuskarta ya fad’a cikin bak’in tulu had’e da jan fitilar dake hannunta..!
Aiko fuskar Giwa na fad’awa cikin tulun nan wuta bal bal ya kama a cikin tukunyar ya shiga cin naman fuskarta..! Ta saki wani irin k’aran azaba mai muni gashi fuskarta ya rik’e cikin tulun mai ci da wuta..! Juyin duniya ta ciro fuskarta ta kasa cirewa sai ihu take zallan fuskarta na cikin Tulu yana cida wutan azaba..!
Jakadiya jiki na rawa tab’e furta “Kumin rai..! Kuji k’an baiwarku mai biyayya a gareku..!!”
Ubandoma yace “Allah yaji k’an masu jin k’an bayinsa na K’warai amma banda Ke Talle..!!!”
Batakai aya ba Mahmood dake ci gaba da sakin huci ya damk’o wuyarta da duka hannayensa biyu cikin wane irin yanayi da babu wanda ya tab’a ganinsa ciki yake furta “Ina Muhibbah..! Ina Muhibbah..! Ina matata nace..?!!”
Jakadiya da taji damk’a hannu na tsananin rawa take nuni da d’akin da Muhibbah da Jamal ke ciki wanda yake daga center k’ofar a bud’e..!
Jifa yayi da Jakadiya tana ida nuna masa ya nufi d’akin a guje..! Jakadiya bata fad’a ko ina ba sai hannun Giwa dake ci gaba da kururwa tana kalaumen iska tana neman agaji take fad’in a cire mata tulun azaban da ya kame fuskarta..!! Aiko Giwa tanajin ta capko mutum ta damk’e Jakadiya gam tana fad’in sai ta cire mata tulun azaban dake mak’ale a fuskarta..! Jakadiya na kokawar k’wace kanta daga hannun Giwa, inaa Giwa bata daina janta ba tana fad’in ta cire mata tulun har saida suka dangana da hayak’in Tal’udu..! Jakadiya na kururuwa tana fad’in su ceceta zata mutu, inaa tuni Giwa ta jefata cikin hayak’in Tal’udu..!
Babu wanda ya iya kusantar wutan tsafin da yake tasowa daga jikin Tal’udu yana haurawa jikin Jakadiya ...Tun ana hango hannun Jakadiya da take d’agowa sama har dai aka daina hangowa..!
Baba Nomau da Ja’afar da Ubandoma suka fantsama sauran d’akunan dake jere wajen Ja’afar yana tokarin ko wace k’ofa tana bud’ewa..! Wani kayan tashin hankali da al’ajabi shine ko wane d’aki sai Sun tsinci gawan mace budurwa..! (Idan baku mance ba wad’annan ‘yanmata sune wad’anda Jamal ya lalata masu rayuwa Tal’udu da Giwa suka ajesu a wad’annan d’akuna da sunan sud’in matayen Sarauniya ce wanda d’aya d’akin da a kullum yake bud’e shine Saudatu... Sun rigada sunyi tsafi da wad’annan ‘yan mata sun halak’asu...)