← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 162

Sashe 24

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai Muhibbah tai tana mai kuma duban hoton da yake k’unshe da wasu sirrika kana tace “Duk wanda ya zana tabbas ya iya zane...”
Umaima ta jinjina kai “Sosai kuwa, ai kyautace ta musamman akaiwa d’an Sarki...”
Muhibbah Ta kuma jinjina kai kana tace “Amma Maiyasa Yarima Jamal ya lank’aya hoton a nan dik irin mahimmancin da hoton kedashi a gareshi... Ya kamata hoton ya kasance yana kusa dashi ne...” Ta k’ara tana mai tsare Umaima da idanunta da suke farare k’al wanda suka dace da cute round face d’inta...

Umaima da tai shiru tamkar wacce tai nisa a wani duniyar na tunani a hankali ta soma takowa ta k’araso gaban hoton... Lokaci guda tasa hannu tana shafawa, hannunta nakan hoton take furta “Kasancewata masoyiyar zane ko wanne iri yasa ya aje hoton a nan, da fari naso ya bani kyauta amma ya sanar dani mahimmancin hoton a gareshi don haka ya aje a nan don na dinga gani....!”

Muhibbah ta jinjina kai a hankali tana mai kuma nazartan wannan zanen gida mai dadd’en tarihi da aka yishi da wane irin fasaha mai rud’ar dakai... Dan kashi dai zanen gidan sarauta ne mai kyaun gaske amma baka isa kace ga k’ofar shiga ba dukda cewa ta wata fuskar idan ka dubi zanen zakaga kaman ga k’ofofi rututu amma idan ka matso sosai k’ofofin zasu b’acewa ganinka sai Kaga Tamkar kwalliya ne ba k’ofofi ba.... Tana nan tsaye tana kuma nazarin hoton taji muryar Umaima na fad’iwa Zahra “Yauwa kin fito, dama fitowarki muke jira... Muje Hibbah...” Ta k’arashe tana mai janyo hannun Muhibbah da har lokacin bin wannan hoto takeda kallo...
Zarah kaw sai yaba kyaun da Muhibbah tai take Umaima na tayata, ita kaw Muhibbar bama tasan sunayi ba dan har wanna lokaci nazarin zanen nan take....

Suna tafe bisa matakala suna sauk’owa Zahra Ke fad’in “Nifah Aunty Umaima wllhi banson Kuyangar nan da Maami tace lallai lallai ita zatake kula da al’amra na, nifa ban saba haka a Spain ba, nafi ganewa nayi komai da kaina daga ni sai Paa d’ina....!” Ta k’arashe baki a ture daidai sanda suka ida sauk’owa Kuyangar kaw na biye dasu kai a k’asa...
A daidai sanda suka ida sauk’owa daga matakalan benen Umaima ta d’agawa Kuyangar hannu alamun ta daina binsu kana ta dubi Zahra tace “Aiko hak’uri zakiyi Gimbiya, dan nan da spain ba d’aya bane... Sannan a wannan stage d’in da kike dama dole a miki assigning Kuyangar da zatake kula dake da kuma al’amaranki musamman da shike babu mahaifiyarki a raye...!” Ta k’arashe cikeda tausayawa...
Kalaman Umaima na k’arshe ya sanya Muhibbah juyowa kad’an tana duban Zahra cikeda tausayawa musamman da taga yanayin da fuskar yarinyar ya shiga....
Hannun Zahra ta kamo kad’an kana tace “But you’ve your Grandma, and your Paa, ga kuma Uncles d’inki sanan ga Auntynki Umaima... Kuma duka suna sonki kinji koh...!” Ta k’arashe tana k’ok’arin cheering yarinyar...

Murmushi Zahra ta saki a hankali kana tace “Thanks Aunty Muhibbah... Amma saidai kin mance da mutum guda...!”

Muhibbah ta d’an zaro ido kad’an kana tace “Wa kenan...?”

Umaima tai karaf tace “Raheema matar Paa d’inta....”

Take annurin fuskar Zahra ya d’auke lokaci guda take furta “No, bana sonta, kuma bana so Paa ya aureta.... Ni ke nake nufi Aunty Muhibbah, kin manta baki lissafo kanki ba cikin wad’anda nake dasu a yanzu...”

Muhibbah ta murmusa kad’an kana tace “Aw ai gani nayi ni ba jimawa zanyi a Masarautar ba shiyasa... But Kiyi hak’uri kar Ki d’auka da wani nufi kinji.... You’ve me as well..!” Ta k’arash murmushi fal fuskanta....

Cikeda jin dad’i Zahra ta rungume Muhibba tana fad’in “Gracias Tìa Hibbah....!”
Ta murmusa itama kana tace “Wait mai kikace kinsan bana jin Spanish...”

Zahra ta rausayar da idanu kana tace “Well, Assignment...!”
Muhibba ta girgiza kai kana tace “No way... I hate assignments... Nadai San Gracias godiya ne but Tia... Ban sani ba....”

Zahra ta d’an kuma darawa kad’an had’ida yin fari da idanu kana tace “Tia Sabon sunan da zanke kiranki dashi kenan.... Tia means Aunt in Spanish...”
Suka d’an dara gaba d’aya a tak’aice harda Umaima daidai lokacinda Raheema ta shigo parlorn Kuyangarta na biyeda ita a baya....
Cak Ta tsaya tana dubansu yanda suka cika da Farin ciki gwanin ban sha’awa...
Zuciyarta ta soma mata zogi, hannu ta d’agawa Kuyangar nata alamun dakatarwa kana ta soma takowa garesu cikeda k’asaita.....

SameenaAleeyou 📚[6/14, 6:09 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*

*018*

*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*

Raheema na K’arasowa tai k’ok’arin d’aura fake smile saman fuskarta mai cikeda k’asaita, a daidai lokacinda Umaima tai noticing d’inta.... Umaima ta tareta da fad’in “Barkada isowa Gimbiya Raheema kuma matar Yayanmu....!” Tai maganar murmushi fal fuskarta...
Dik sanda aka ambaceta da matar Mahmood ji take kanta na kuma fashewa, tana jin wani irin dad’i can k’asar zuciyarta... Ta d’an fad’ad’a murmushinta had’ida furta “Barkanki Gimbiya Umaima kuma k’anwar mijina....!” Suka kuma murmusawa a tare kana Raheema ta kaikaito tana duban Zahra da tai kaman bataji isowar mutum wajen ba... Ta d’an tako zuwa gaban Zahra kad’an kana tace “Daughter ya jikin naki.... I’m glad you’ve recovered....!” Ta k’arashe cikeda kulawa

Rausayar da idanu Zahra tai kana tai wasu ‘yan maganganunta cikin harshen spanish sannan ta sakarwa Raheema murmushin yak’e tace “Oh really... Well thanks then.. If you’re really sincere...!”Ta k’arashe tana mai janyo hannun Muhibbah had’ida furta “Tia Hibbah muje, let’s sit together... There’s a lot more I need to know about you....” Ta k’arashe murmushi fal fuskanta yayinda Muhibbah ta saci kallon Raheema dake binsu da wane irin kallo kana Ta maidoda dubantaga Zahra tana mai ci gaba da amsata cikeda Farin ciki...

Fuzar da huci kad’an Raheema tai daidai sanda wayar salularta ya soma ringing... Gimbiya Zeenat ce mai kiran nata....
Rai b’ace ta d’aga wayar...
Daga d’aya b’angaren Gimbiya Zeenatu tace “Kina ina...? Maza kizo ina nemanki...!” Bata jira amsar Raheemar ba Ta katse kiran.....

Rausayar da idanu Raheema ta kumayi tana hangen su Zahra da Muhibbah daga nan yanda take tsaye ta cikin k’ofar glass sai raha suke daga cen yanda suke zaune a farfajiyan haraban.... Ta kafe Muhubbah da wani irin duba na tsana kana Ta juya ta fice Kuyangarta na take mata baya...

Tana isa ta tadda Gimbiya Zeenat a d’aki sai faman safa da Marwa take...
“Aunty lafiya irin wannan kira haka....!”

Muguwar kallo Gimbiya Zeenat ta watsa mata kana tace “Raheema Wai lafiyarki kuwa.... Kan wane dalili zaki k’i d’aga wayar Juwariyya bayan kinsan kalan information d’in da muke samu daga wajenta.... Sanin kanki ne wannan Majidad’in ba yarda da uwarsa mukai ba, na tabbata ko asiri sai tayi dan d’anta ya d’ale Karagar mulkin nan... Mu kuma babban burinmu shine Mahmood ya sami mulkin domin mu sami yanda muke so... Amma kan mai Juwariyya data juyawa ‘yanuwanta baya zakiyi banza da kiranta harda baiwa Kuyangarki wayar kice bakida lokacin d’agawa... K’ilan baki son mijin naki ya sami sarautar ne koh...?” Ta k’arashe tana kuma aika mata wani duban...

Fuzar da fuci kad’an Raheema tai kana tace “Allah Aunty na zaci wani abinne... Yo kan wannan ne dama...?”

Gimbiya Zeenat ta kuma watsa mata harara kana tace “Ban fahimceki ba, wannan d’in k’aramin abu ne... Muna magana ne kan sarautar mijinki Raheema...!”

“Aunty nifa yanzu ba sarautar Mahmood bane gaba na... Wllhi ni yanzu na mallakesa gaba d’aya shine damuwata da sarauta ko babu sarauta... Ni shi d’in kawai nake so na mallaka, babu ruwana da wani sarauta ko rashinta as long as he’d remain mine, ni kad’aina and no body else’s...!” Ta k’arashe tana sakin huci...

Shaye da tsananin mamaki Gimbiya Zeenat Ke dubanta kana tace “Eh lallai na yarda...! Toh barikiji na fad’a miki, wllhi wllhi bazan zauna na zuba miki idanu Ki rusa min plans d’ina ba... Dole Mahmood yai sarauta dan idan ya aureki bai a matsayin Sarki banga amfanin auren ba.... Dan haka dole kici gaba da baiwa Juwariyya had’in kai tana kawo mana rahoton dik abinda Ke wakana cikin gidansu...!” Daga haka Gimbiya Zeenat tasa kai zata shige...

Raheema ta katseta da fad’in “Aunty duk bazaki fahimci Abinda nike nufi ba, amma idan kika fita kikai tozali da shegiyar yarinyar nan mai bak’in shishigin masifa da nake baki labari zaki yarda ba yak’in neman mulkin Mahmood bane gabanmu yak’in raba wannan tsinanniyar da Masarautar nan ne babba gabanmu....!” Ta k’arashe tana mai k’arasowa gaban ‘yar uwar tata....
Dubanta kurum Gimbiya Zeenat tai kana ta saka Kai Ta shige dan ita bama ta d’auki maganan Raheema da mahimmanci ba, yo har wata tsiyace zatazo ta tsone masu idanu bayan suna d’iyoyin sarki jinin sarauta gaba da baya... Ta tabbata shashanshanci ne kurum irin na Raheema ba wani abu ba....

**

Daga yanda suke zaune su Duka ukun Sun kafeta da idanu Fu’ad yai gyaran murya kad’an kana ya furta “She’s different...! Way too different, bansan a wani sahu zan ajeta ba... But her beautiful eyes sunada matuk’ar gizo ka dubi cikinsu and tell her how exactly you feel about her....!”

K’asaitaccen murmushi Yazeed yai yana mai jefa grapes cikin bakinsa kana yace “While you’re here thinking of how to approach her... prince Yazeed already had body contact with her..!” Ya k’arashe yana mai kuma daidaita kishingid’arsa shu’umin murmushin saman fuskarsa, yanayi yana shafar hab’arsa

Daga Fu’ad har Jamal dubansa sukai da tsananin mamaki... Jamal yace “Yazeed mai kake nufi... Wai kana nufi har ka mata magana...?”

Murmushin bata bar saman fuskarsa ba, idanunsa kan Muhibbah da ko shakka babu a tsarge take a wajen dan tasan ‘ya’yan Sarkin ita suke duba probably ma magananta suke...

Yazeed yaci gaba da fad’in “Prince Yazeed never fails...! Kuma babu macen da Ta tab’a rejecting d’insa duk fad’in duniyar nan.... And believe me, she and I have an unfinished business...!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin murmushin nasa....

Girgiza kai Jamal yai kana yace “But you’ve your own wife Yazeed... Kar ka b’ata mata lokaci...”
Chapter 24 · 0% Book details