← Book details Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 162

Sashe 42

Muhibba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waziri ya jinjina kai yace “K’warai kinyi gaskiya amma bakida damuwa Ki barmin wannan zan kamo Bak’on Buzu yanda ya shiga ya fita.....!”

Ubandoma dake lab’e jikin k’ofa ya gama jin komai, a hankali yasa kai ya fice yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa ya zama dole ya samo wannan k’undin kafin ya isa hannun Waziri, Dan idan ya samo k’undin nan zai sami Abinda ya jima yana buri Wato ‘Yanci... Yana matuk’ar san ya tashi daga bauta ya koma ‘yantacce, wannan itace kad’ai Damarsa don ya tabbata idan ya samo wannan k’undin dik abinda yace Giwa tai masa in exchange zatai masa domin ta mallaki wannan k’undi koda kuwa menene...!Ya kuma sakin murmushi a hankali kana yasa kai ya fice cikin sauri.....

***

Koda labarin ciwon Wambai ya isa Fada sosai hankalin Yarima Mahmood ya tashi musamman da yaji irin abinda ya sami Wambai wanda idan ya had’uda tsufa da k’yar ake tashi saiko wani ikon Allah... Haka yaita tuna tattaunawarsu Ta k’arshe wanda tamkar bankwana Wambai d’in ke masa... Yana matuk’ar k’aunar Wambai baya k’aunar abinda zai cutarda Wambai... Tamkar mahaifi haka ya d’auki Baba Wambai dikda cewa shid’in d’anuwan mahaifinsa ne dama....

Shida Fu’ad suka garzayo zuwa asibitin babu b’ata lokaci Ubandoma na biye bayansu.... Suna doso kai d’akinda aka kwantar da Wambai Mahmood ya sinkayo muryar Majidad’i na fad’in ko Wanene bak’on Buzu sai ya zak’ulosa don shikeda alhakin ciwon mahaifinsa... Yasan shid’in ne shine bak’on Buzu amma baisan ya akai ciwon Wambai Keda alak’a da bak’on Buzu ba tinda yasan lafiya lou sukai sallama... Tabbas bazai bada wani clue ma Majidad’i da har zai fahamci cewa shine bak’on Buzu... On the other hand shima yanaso yasan komai in details, yanda akai bak’on Buzu Keda alhakin ciwon Wambai... Toh ko hakan nada alak’a da wannan k’undin da ya dank’a masa ne..?? Tabbas ya kamata Shima ya bincika don ko babu komai Baba Wambai ya masa abinda babu wanda ya masa shi tin dawowarsa cikin Masarautar...

Da sallama suka shigo cikin d’akin... Majidad’i da Innani suna ganinsu suka had’e FUSKA gaba d’aya tamkar sunga ajalinsu... Mahmood bai k’asa a gwiwa ba ya soma gaida Innani dake faman cika, Ta amsa da k’yar kana Fu’ad ma ya gaidata sukai mata yaya mai jiki... Nan ma da k’yar ta amsa...

K’warjinin Mahmood ya cika wajen gaba d’aya wanda hakan ya hana Majidad’i da mahaifiyarsa wulak’anta su Mahmood.... Amma kam tabbas Majidad’i ji yake tamkar ya fitarda Mahmood daga cikin d’akin, da ace yanada ikon yin hakan da yayi....

Bayan sun ida gaisawa ne Mahmood ke tambayarsu yanda al’amarin ya kasance....Innani ta karanto masa komai yayinda Majidad’i ya k’arada “Bak’on Buzu baici banza ba Innani wllhi sai na zak’ulosa na d’auki fansar mahaifina akansa...!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da sakin huci lokaci guda ya janye jiki ya fice daga d’akin gaba d’aya....

Mahmood yaima Wambai dake kwance saman gadon marassa lafiya K’uri tausayinsa na d’awainiya dashi.... A hankali ya isa jikin gadon ya dafa hannun Baba Wambai maras cannula... Lokaci guda yake karanto masa addu’o’in samun lafiya, cikin zuciyarsa na ayyanawa cewa in sha Allahu sai yanda k’arfinsa ya k’are wajen ganin Baba Wambai ya sami lafiya.. Akwai abubuwa da dama da yake neman amsoshinsu daga wajen Baba Wambai bayan dank’a masa wannan k’undi da yayi... A hankali ya furta “Allah ya baka lafiya Baba ya tashi kafad’unka....!”

Gaba d’aya mutanen dake cikin d’akin suka amsada Ameen...
***

Fitowarsu daga cikin asibitin Mahmood yaga kiran Turaki na shigo masa, excusing kansa yai ya nufi ‘yar wata hanya nan cikin asibitin domin amsa kiran Turaki yayinda Fu’ad da Ubandoma suka nufi mota....

Yana tafe yana k’ok’arin amsa kiran ya hango Juwariyya d’iyar Baba Wambai... Tabbas tsaf ya ganeta don ga kamanninsu nan tanadashi dikda cewa rabon da yaga yarinyar zai iya cewa tun wani zuwansa Nigeria lokacin yana Spain... Abinda ya tafida hankalinsa ya mantar dashi wayar da zai amsa shine sinkayo muryar Juwariyya da yai cikin waya tana fad’in “Ni fah Raheema babu wani binciken k’wak’waf da zan maki gameda Muhibbah sabida ni yanzu abindake gabana yafi k’arfina... Ni dama ba ‘yar bincike bace kawai dai Ina baku information ne gameda Yaya na Dan nima banaso yai sarauta sabida na tsani matarsa nafi so Ya Mahmood yai shisa nake baku duk wani information akan abindake faruwa cikin gidanmu... Amma ni harga Allah ba ‘yar bincike bace bazan iya wani bincike kan wata Muhibbah ba... Naji da jinyar mahaifina ne ko naji da wani bincike...Mtsww..!” Taja dogon tsaki tana mai katse kiran take ci gaba da fad’in “Ko sun zata sabida abin duniya nake masu aiki oho... Allah ya sawak’e su sakani wani aikin da banyi niyya ba ina a matsayin jinjin sarauta... Yanda suke jin kansu d’oyiyin Sarki nima jikar Sarki ce nafi k’arfin......!” Burki taiwa kalamanta sakamakon hango Yarima Mahmood da tai fuskar nan nasa tamau ya tsareta da idanunsa masu firgita dik wani mai laifi....

Jikin Juwariyya ya d’auki rawa, tasan Yarima Mahmood ya gama sauraren wayarta yaji komai, ai ko irin duban da yake mata tasan ya riga da yaji wayar da take da Raheema... Juwariyya ta had’iyi miyau da k’yar tana murza wayar salulanta da duka hannayenta biyu... Lokaci guda kuka Ke k’ok’arin zuwa mata, tuni ta soma kuka tana k’ok’arin duk’awa gaban Mahmood dake tsaye hannayensa hard’e Ta baya tana fad’in “Yaya Dan Allah kayi hak’uri... Wllhi Anty Raheema so take kawai Kai sarauta shisa Ta sakani nake kawo mata rahoton dik abinda ke faruwa cikin gidanmu gameda neman mulkin da Ya Majidad’i yake... Yaya wllhi mu kai muke so kai sarauta shisa.. Amma babu wani abu mai muni da mukai sai yanzu da Anty Raheema Ke cewa nai mata bincike kan Muhibbah Wai Dan kar ta sace mata kai... Yaya Dan Allah....!” Kanta a k’asa tana duk’e take maganaganun saidai d’agowar da zatai ta hangi wajen wayam babu Mahmood babu dalilinsa, b’at ya b’ace a wajen ba tareda yace da ita k’ala ba....
Juwariyya ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali had’ida dafe k’irjinta... Idan bata mance Innani na basu labari a lokutan baya idan aka sameka da laifin cin amana a Masarautar hukuncin kisa ake yankewa mutum idan bawa ne, idan kuma d’ah ne hukuncin shekaru masu yawa ake yanke masa a kurkukun masarauta... Ta kuma Sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana mai ayyanawa har abada Ta dena aikiwa Raheema da Gimbiya Zeenat.. Yo ita koma sanin wanann Muhibbar da suke cewa tai masu bincike kanta batai ba....Toh wacece Muhibbah...? Sannan mai ya kawota Masarautar..?”Take taji tana son sanin ko wacece Muhibbah... Lokaci guda kuma ta shiga neman layin Raheema Dan sanar da ita abinda ke wakana....

Raheema dake kwance saman gado tana jiran Yazeed ya fito daga bathroom sai ganin kiran Juwariyya tai na kuma shigo mata... Tsuka tai had’ida tura wayar gefe tana furta “Banza kanki akeji har ni zaki nunawa Mulki da sarauta... Dama ki dawo kan hanya ne yarinya...!” Tana nan a haka Yazeed ya fito d’aure da towel yana goge sumarsa da k’arama guda d’aya... Cikeda salo Raheema ta mik’e ta isa gareshi had’ida shigewa cikin jikinsa tana fad’in “You look handsome my Prince..!”
Yazeed ya tallafota suka nufo gadon a haka bakunansu cikin na juna.... Har wannan lokacin wayar Raheema bai daina ruri ba, k’arshe Yazeed ne ya danna wayar a silent saidai tuni Raheema ta hango shigowar sak’o tai k’ok’arin ture Yazeed kad’an Ta janyo wayar... Dik yanda Yazeed Ke k’ok’arin k’wace wayar Raheema tak’i saki har saida ta ida karance sak’on... Jikinta ya d’auki rawa... Innalillahi kawai take ambata, shikenan Mahmood yasan komai... Lallai wannan Juwariyyar anyi babban jaka gidahuma...

K’ara Ta saki had’ida tura Yazeed daga kanta ta mik’e babu shiri tana k’ok’arin zira tufafinta.. Yazeed na tambayarta meke faruwa inaa ko amsasa batai ba ta suri handbag d’inta saida ta kusan k’ofa ta juyo tana fad’in “Zeed I can’t lose Mahmood... I just can’t, I need to go right now....!!” Bata ko jira cewar Yazeed ba Ta fice cikin sauri tamkar zata kifa k’Asa......

Yazeed ya fuzar da huci cikeda b’acin rai yana mai jifa da pillow guda, ya kuma dunk’ule hannunsa ya daki cikin katifa lokaci guda yake furta “Mahmood..! Komai Mahmood.. Kowa Mahmood...!! Mahmood Mahmood Mahmood..!! Zancen kenan, na gaji da jin wannan sunan... I hate you Mahmood... I hate you more than anything in this world...!!” Ya k’arashe yana mai kuma dukan garu da hannunsa kana ya mik’e ya soma shiryawa Shima... Ransa gaba d’aya a jagule...!!
***

Har suka iso gida bai daina juya kalaman Juwariyya cikin kwanyarsa ba, if there’s one thing he hates shine ai abu akansa bayan idanunsa koda abin amfanin kansa ne.... For what Raheema zatai masa haka...! Ita wacece da zatai katsalandan haka cikin rayuwarsa... Waya bata wannan damar...?!! Yana tinanin yana mai ci gaba da murza zoben azirfa dake yatsarsa guda... Idanunsa kaw tinda ya shige motar na kallon window... Fu’ad dake gefensa ya kula da yanda yanayin Yayan nasa ya canza tin bayan shigowarsa motar... Yaso tambayarsa ko akwai abindake damunsa ne amma sai yai shiru zuciyarsa na mai raya masa cewa k’ila sabida ganin jikin Baba Wambai ne ya sanyasa cikin yanayin... A haka suka iso Fada...
Suna isowa Ubandoma dake zaune gaban Jeep d’in ya fito ya bud’ewa Mahmood yanai masa Fadanci... Dogarai ma sai zuba masu fadanci suke daga Mahmood d’in har Fu’ad... Fu’ad yaso bin bayan d’anuwansa ganin yanda ya shige sashensa cikin sauri yana fad’iwa Ubandoma yai masa kiran Jakadiya....

K’arar da wayar Fu’ad d’in yai ya sanyasa baibi bayan Mahmood ba... Sahibarsa Muhibbah ce mai kira, Dan tinda ta hangi shigowar mota Fada jikinta ya bata su Fu’ad da Mahmood ne suka dawo...

Fu’ad ya d’aga wayar cikeda jin dad’i yana mai zolayarta da fad’in har tayi kewarsa kenan tinda basu jima da yin waya ba....

Daga d’aya b’angaren Muhibbah ta murmusa kad’an kana tace “Karka laifina Prince... Soyayya Ke d’awainiya dani...!”

Fu’ad ya kuma murmusawa kana yace “Toh ai ked’in ce kin hanani ganin kyakkyawar fuskarki cikin Fada da yanzu na k’araso har yanda kike....!”
Chapter 42 · 0% Book details